Sashe 46
Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_Tabbas addinin musulunci haske ne kuma ni'ima ne, wane addini ne cikin addinai ke da irin wannan ni'ima?, Babu. Alqur'ani da kuke gani ƴan uwa abincin ruhinmu ne, wallahil adhim duk wanda ya riƙe Alqur'ani babu wata musiba da zata same shi sai dai abunda Allah ya riga ya rubuta zai same shi._
_Azkar, wato ambaton Ubangiji shima makami ne na mumini, Allah maɗaukakin sarki ya nuna mana muhimmanci ambatonsa a cikin Alqur'ani a wurare daban daban, haka hadisai ingantattu sun zo akan muhimmancin ambaton Allah_
_Akwai zikirorin safiya da maraice waɗanda suke da matuƙar muhimmanci. Imam Annawawi Allah yayi masa rahama yace “Madallah da masu ambaton Allah musamman zikirorin safiya da maraice, ida mutum bai yi su duka ba to ya daure da safe ya karanta ɗaya haka da yamma”. Saboda haka ƴan uwana, mu riƙe azkar ɗin nan da kyau wallahi zamu ga faidar hakan, babu wani da ya isa ya cutar da mu sai dai abunda Ubangiji ya riga ya rubuta zai same mu_
_Ƴan uwana mata ina ƙira gare mu da muji tsoron Allah kuma mu sani shirka itace mafi muni daga cikin kaba'ir. Idan muka dubi ayoyin da suka zo cikin Alqur'ani zamu tabbatar da hakan, mu tuna lokacin da Luƙmanul Hakeem yake yiwa dansa wasiyya, shirka itace abinda ya fara tsawar masa akai, ayar tana suratul luƙman. Akwai makamantan ayoyi da suka zo, saboda haka mu kiyaye, kada mu bari shaidan yayi galaba akanmu har ya kaimu ga halaka._
_Wasu matan suna cewa shirka sai ka je wajen boka, sai su fake da ai wane malami ne, duk wani malami da zai yi duba, bugun ƙasa shima boka ne, saboda haramun ne hakan, akwai hadisin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama, inda yake cewa “Duk wanda yaje wurin boka ko ɗan duba, to haƙiƙa ya kafurcewa abinda muka sauƙarwa Manzon Allah”. Mata muji tsoron Allah, duk wata buƙata ko buri da kike son cimmawa to ki roƙi Ubangiji, babu abinda yafi ƙarfinsa in kika ga ya Hana ki ko bai biya miki ba to ki saka a ranki ba alkhairi bane abun kamar yadda yazo cikin suratul baƙara, Allah maɗaukakin sarki yace “Zaka ga kana ƙin abu yayinda abun ya kasance alkhairi a gare ka, zaka ga kana ƙaunar abu yayinda abun ya kasance sharri gareka, Allah shine mafi sanin abinda ku baku sani ba”. Don Allah ƴan uwa na mu guji zuwa wurin irin malaman nan ko ince yan duba, in Zaki yi addu'a kiyi da kanki ba sai wani yayi miki ba, babu wani hijabi ko shamaki tsakanin ki da mahaliccinki, so ki roƙe shi duk abinda kike so kina mai ƙaskantar da kai, sai kiga addu'ar ki ta karɓu wurinsa, idan shawara ne ma kiyi istikhara zaki ga kin dace_
_Mu haɗu gobe don jin yadda zata kaya_
_Taku Diamond Bhatool ta gargajiya, ina ƙaunarku fans ɗina_
[8/26, 8:15 PM] 𝙳𝚒𝚊𝚖𝚘𝚗𝚍_𝙱𝚑𝚊𝚝𝚘𝚘𝚕💎: Follow the DIAMOND BHATOOL'S LIBRARY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VamEf2Y4dTnFmjl4Dv1Z
https://chat.whatsapp.com/IWQW3ytbVc611XLon2sn66
🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
SHAFI NA “““77&78 ”””
Idanuwa ta ƙwalalo kamar zata yi kuka yayinda su Fauzah ke kwasar dariyarsu.
“Haba ƙawa ta duk kin sauya kamar ɗiyar Indiyawa taya zan gane ki?, Matso kusa da ni don Allah, yaushe gamo?”
Kusa da juna suka zauna nan Khairy tace “Fauzah, Ayrah, Yesmeen, ku haɗu da ƙawata ta yarinta abokiyar ƙiriniyata kuma mai suna na A'i” ta faɗa tana nuna A'i da yatsa fuskarta ɗauke da murmushi. Ta juya kuma ta kama kafaɗar A'i “Ƙawata A'i ki haɗu da ƴan uwana kuma ƙawayena wannan Fauzah,wannan Ayrah wannan kuma Yesmeen”.
Nan kowa yaji daɗin haɗuwa da ƴan uwansa don Ai ma ba baya ba wurin sabo, tsiyarsu ta da dai ta bari amma akwai barkwanci ta shega. Nan suka fara hirar yaushe gamo.
Ƙiran sallar Ishã yasa Ai faɗin “Gashi ban girka komai ba saboda nauyin jiki, bari ya shigo sai ya nemo muku shayi da bredi don ba iya cin girkinmu zaku yi ba”
Harararta Khairy tayi tace “Ba sai kin faɗa mana kina da ciki ba ai mun gani, kin faɗa kin maimaita”
“To ke ina ruwanki don ke baki da shi kuwa baki isa hana Ni faɗa ba" nan dai suka yi ta jan magana Khairy team ɗin ta ita kaɗai su suma duk suna bayan A'i.
Shigowar Iliya mijin A'i ta sanar da shi game da baƙinta, ai bai manta lokacin bikinsu ba tuni ya fita ya nemo musu bread bisa umarnin uwar gida. Tare da ita suka tasa tsire da bread ɗin a gaba suna ci suna hira har suka kammala.
Bayan sun kammala ne Fauzah tace “Ƙawarmu ki taya ƴar uwarmu murna, ta samu lafiya” nan suka kwashe komai suka faɗa mata dom a cewarsu ciwon su ne duka, A'i tayi kuka kam sai tsinewa Inna Zaliha take, daga baya kuma ta dawo lafta mata godiya da albarka tunda yanzu tayi sanadin wayewar ƙawar mu ga kuma wani mahaukacin kyau da kika yi”.
Sai da suka yi sallah tukun suka miƙe suka ce sai watarana zasu kara zuwa, nan suka rabu suna sharar ƙwalla. Har sun kama hanyar gida Khairy tace “Zamuje dandali? Don nasan gobe za'a wuce”
“Eh muje mu gani”
Ba su suka koma gida ba sai wajajen goma na dare. Suna komawa kuwa suka yashe sai bacci.
Bayan tafiyarsu granny ta so abar Khairy tayi ko sati ɗaya ne sai dai saboda makaranta yasa tace in anyi hutu zata zo ko sati ne tayi. Suma su Baffi da iya tare da Baba duk basu ji haushi ba, sunji daɗi da zancen ma saboda Khairy ce mutum ta farko da ta fara yin karatun boko.
Washegari bayan sun karya dukkansu harda iya suka ɗunguma sai gidan Arɗo, nan suka yi masa sallama ya haɗa su da tsaraba irinta ƙauye. Sunyi matuƙar farin ciki tare da yaba halacci da karamci irin na ƴan ƙauyen. Iya da Baba harda kukan su kafin su rabu, daga nan motar su ta tashi sai Adamawa.
Wuraren la'asar suka isa kowa jikinsa yayi tsami, sai da Daddy ya ajiye Sheikh Imam kafin su zarce gida baki ɗayansu. Babu wanda yasan da dawowarsu sai dai horn ɗin motar da suka ji ya tabbatar musu da cewa sune.
Tuni kowa ya fito ana musu sannu da hanya. Kafin maghrib an cika dining ɗin granny da abinciccika. A nan aka yi dinner gabaɗaya ranar. Bayan an kammala Daddy yayi addu'a tare da fara musu bayanin abinda ya faru a can, bai ɓoye musu ba don yanzu an riga an zama ɗaya. Bayan ya kammala wasu harda kukansu, kowa yaji kabarin ajikinshi. Kamar wancan lokacin Daddy ya ƙara jan hankalinsu akan rayuwa daga nan kowa ya koma bangarensa.
_______________________________________________
Hamma Zaki ya shigo gaida granny Amma bai sameta ba, da ya tambayi mom.ta faɗa masa ai sun tafi garinsu Khairy don kammala aikin da Sheikh Imam ya fara. Haka kawai ya tsinci kansa a damuwa yana ta fatan Allah yasa a dace. Zuwansa uku bai semeta ba, gashi numbers ɗin su duka basa tafiya.
Bayan sunyi waya da Mom me ya tambaye ta ko granny ta dawo? Tace masa eh, bai san MEH yasa duk ya damu da yarinyar ba, “Ko dan ta cancanci a tausaya mata ne” ya bawa kashi amsa. Wanka yayi ya shirya cikin Farar jallabiya tas tare da feshe jikinsa da turarensa da har yau bai daina amfani da irinsa ba wato _Imperior majéste._
Ganin irin wankan da yasha yasa Pretty tsayawa tana binsa da kallon mamaki.
“Sweetheaft ina zuwa haka?”
Ko kallonta bai yi ba ya ɗauko key ɗin motarsa ya fito, bayansa ta biyo tana faɗin “In dai hira kaje da kai da ita duk Allah yana ganin ku ” ta faɗa tana komawa.
Shi fa har yau mamakin irin ɗabi'unta yake, ace mijinka zai fita ba zaka yi masa addu'a ba sai ma mita da rashin ɗa'a.
Jan motar yayi zuwa gidansu. Bayan sun gaisa da mom ya bi ko ina suka gaisa kamar yadda ya saba. Party ɗin granny shine ƙarshen zuwa. Yana shiga ya tarar da granny zaune bisa lallausan carpet ɗin dake parlourn sai Khairy da kanta ke cinyar grannyn. Sallamar da yayi dama ba ji suka yi ba sai da ya doso cikin ɗakin ƙamshinsa ya karaɗe ƙofofin hancinsu.
Zama yayi kan kujera yana faɗin “Granny sallamar ma ba zaki amsa bane?”
“I haƙuri maza, wallahi duk na gaji ne, jiki na ma ciwo yake, ina irin maganin zafin nan da ka taɓa bani, da zan samu ma shi nake so”.
Haka kawai ta kasa ɗaga ido taga fuskar da ta saba gani jikin photo a zahiri. Kanta ƙasa tace “Ina yini” kamar bazai amsa ba yace “Lafiya, ya jikin ki?”
Tayi mamaki sosai jin ya tambaya ta, don a yadda su Fauzah ke bata labarinsa ba ya son wargi ko kaɗan”
Murya a sanyaye ta amsa da “Alhamdulillahi, naji sauƙi”
Daga haka ta fara ƙoƙarin miƙewa don tafiya ɗakinta, har ga Allah ba zata iya zama wuri ɗaya da shi ba.
Zata fara tafiya taji yace “Ina zakije, ni tafiya ma zanyi, Allah ya sauuwaƙe”
Kunya ce ta lulluɓeta tace “Ameen na gode” ba tare da ta kalleshi ba yayin da shima hankalinsa yake kan wayarsa. Daga haka ta koma ta kwanta akan cinyar grannyn.
Miƙewa yayi yana faɗin “To granny mu tashi lafiya, man zafin zan bayar a shigo miki da shi”
Amsa masa tayi da faɗin “To maza, mu tashi lafiya, ka gaishe da ifritiyar matarka”
Murmushi yayi yace “Granny dai”. Daga haka ya wuce ba tare da ya amsa mata ba.
Sun sha hirar su sosai duk da sun gaji kafin su kwanta, ɓangaren sauran ma daren ranar kowa sun sha hirar da mahaifiyarta, wanda duk a
_________________________________________________
*A GURGUJE*