← Book details Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 49

Sashe 28

Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau ma kamar kullum tafe take tana waƙar ta sai ga wasu yara sun zo wucewa kowannen su da kaji biyu a hannu. Ƴar wuƙar ta da banyi tunanin daga ina ta same ta ba ta zaro tare da nufar yaran.

Dariyar mugunta tayi haɗi da kallon su sannan tayi shiru, jikin yaran in banda karkarwa babu abinda yake yi kowa sai addu'a yake cikin ransa.

Kamar ba ita ta gama murmushi da dariyar nan ba ta haɗe rai. Kallon ɗaya su tayi tace
“A! Ɗan Manunu ina zaku je haka da kaji”
Cikin rawar murya yaron da ta ƙira sa Ɗan Manunu yace:
“Ƴar Iya aikan mu aka yi mu siyar, don Allah kar ki mana komai”
Hararar Ɗan Manunu Ƴar Iya tayi tace
“Don ubanka nace zan ma wani abu ne?”
Jin ta ɗau zafi yasa Ɗan Manunu sunkuyar da kai ƙasa tare da faɗin
“Kiyi haƙuri don Allah”.

Dariya take abunta kamar ba wacce ta tsare gida yanzu ba, can kuma tayi shiru tana bin yaran da harara, Allah sarki su kuwa kawunan su ƙasa kamar bayi a gaban sarki.
“Kuzo nan ɗaya bayan ɗaya,saura ku gudu Aradu duk na san gidan iyayen ku, kuma Aradu wanda ya gudu har uwar sa sai na yanka”
Ƴar Iya ta faɗa tana fitar da ƴar wuƙar ta waje.

Ɗaya bayan ɗaya kowa yake zuwa, haka zata karɓi kazar a gaban idon su ta yanka , in ta yanka sai ta bayar sannan tace
“Wuce gida don ubanka, ai ana buƙatar naman a gida maza a je a ci”

Haka Ƴar Iya ta kammala yanka kajin nan tas sannan ta wanke jinin da ruwan rijiyar dake gefen su sannan ta wuce gaba hankali kwance.

Ba Ƴar Iya ce ta koma gida ba sai wajajen Ishã don kuwa sai da ta biya gidan A'i taci abinci duk da cewa bata ƙoshi ba tukun ta dawo. Dawowarta kuwa yayi dai-dai da dawowar Baffi daga masallaci. Jijjiga kansa yayi cikin ransa yana roƙawar Jikar tasa shiriya a wurin Ubangiji. A zahiri kuma murmushi yayi tare da faɗin
“Shalelen Iya an dawo kenan?”
Murmushin ta maida masa, ko ba komai in taga Baffi tana jin wata irin nutsuwa
“Eh wallahi Baffi, sannu halan daga. Masallaci kake”
“Eh daga can nake” Baffi ya amsa mata.
“Sannu to, mu shiga mana”
Bin bayan ta Baffi yayi suka shiga tare.

Bayan sun shiga Iya ta kawowa Baffi langar tuwon sa da ta miya sannan ta ɗebo masa ruwa a kofin silver. Bayan ta gama da Baffi ta haɗawa shalelen ta ma nata abincin. A nan suka ci abinci dare can suka baje hira a wajen.

Ana cikin hirar Baffi ya ɗan yi shiru can kuma ya maida kallon sa ga Ƴar Iya. Baffi yace
“Shalelen Iya Ni kuwa kina zuwa gidan ƙawar ki A'i?”
Cike da basarwa ta ce
“Eh Baffi ɗazu ma naje, wani abun ne halan?”
Girgiza kai Baffi yayi yace
“Aah babu komai”.
Daga haka yayi shiru yanayin fuskar shi na sauyawa.
Jin shirun da Baffi yayi yasa Ƴar Iya ɗagowa ta kalle shi dai-dai lokacin da ta tura langar tuwon ta da ƙafa. Ƙwalalo ido waje tayi saboda yanayin hasken farin wata yayi dau, kana iya ganin komai ba tare da ka haska ba.

Tafi minti biyar tana kallon Baffi, iya kam dama bacci ya ɗauke ta bata ma san me ake yi ba. Hawayen dake zirarowa daga idon Baffi babu ƙaƙautawa shine yaja hankalin Ƴar Iya ya kuma sanya ta faɗawa duniyar tunani a karo na farko cikin rayuwar ta.

Ko me ya samu Baffin ta yake kuka? Nan da nan ita ma yanayin fuskar ta ya sauya izuwa mai nuna tsantar damuwa.

Wannan shine karo na farko da ta taɓa shiga irin wannan yanayin! Karo na farko da taji kukan wani mahaluki ya taɓa zuciyar ta har take jin rauni cikin ta! Karo na farko da taji zuciyar ta na bugawa ko me yasa?

Ba komai ne ya sanya Ƴar Iya shiga wannan yanayi ba sai jin ana mata magana cikin kunnuwan ta. Ba zata iya tantance Muryar waye ba ammah tanajin koma waye mai irin Muryar nan yana kashe mata jiki. Wannan ba shine karo na farko da taga damuwa a fuskar Baffi ba amma wannan ya tsaya mata.

Cikin kunnen ta na dama taji ana faɗin
“Ke Ƴar Iya baki ganin yadda Baffin ki yake hawaye ne?”
Cikin kunnen ta hagu kuma taji ance
“Yo ke Menene naki a ciki? Kin taɓa shi ne?”
Caraf a kunnen ta na dama aka ce mata “Ƙwarai kina da haɗi da shi, kin manta matsayin uba yake gare ki?”
“Amma ai ba uban bane” Muryar ta doke ta cikin kunnen ta na hagu.
“In kin faɗi haka baki kyauta ba, shi uban naki ya damu da ke ne?”

Toshe kunnuwan ta tayi tare da sakin wata irin ƙara sannan ta miƙe. Dai-dai wurin da Baffi yake
“Baffi na me yake damun ka”
Goge hawayen fuskar shi Baffi yayi yace
“Babu komai shalelen Iya, yau ba zaki fita dandali bane?” ya ƙarasa tare da sakin murmushi.
“A'ah Baffi, sai ka faɗa min me yake damun ka”
Murmushi yayi tare da faɗin
“Babu komai shalelen Iya”
Haɗe fuska tayi tana faɗin
“Allah Baffi duk cikin ƙauyen nan kowaye ya taɓa ka bana ƙyakewa Aradu rama maka zanyi”
Baffi yaji daɗin maganar hakan yasa ya ƙara yin murmushi.
“Ina roƙon Allah ya nuna min auren shalelen Iya ko ba komai akwai shagali”
“Hhhhh kaji Baffi”
Ta faɗa tana sakin wata mahaukaciyar dariya
“Baffi ai Ni ba zan yi aure ba”
Fuskar Baffi ta sauya ganin hakan yasa ta ce
“Kai ɗin so kake nayi aure?”
“Ehmana shalelen Iya kinga na kusa mutuwa”
“Aah Baffi na, to ai zanyi kafin ka mutu ɗin”

Murmushi Baffi yayi yace
“To Allah yasa!”
Ba tare da ta amsa ba ta cika bujen ta da iska daga bakin zauren tace
“Na fita zaga gari”

Washegari da safe bayan ta farka kamar kullum, ko fuska bata wanke ba ta jawo ɗumamen ta da Iya ta gama rabawa. Tana gama cinyewa ta cika bujen ta da iska.

Tayi yawo sosai sai da Azahar ta wuce gidan A'i, guntun abinci taci bata wani daɗe ba tace zata tafi.

Da yammaci Ƴar Iya ta nufi fada, a can ta zauna gaban Arɗo. Cike da tsoro Arɗo ya gaida ta.
“Ƴar Iya ina wunin mu”
Babu kunya ta amsa da “Lafiya ƙalau”
Nazartar ta yayi na wani lokaci kafin yace
“Lafiya dai ko wani abun kike so halan”
An zo wajen, dariya tayi don ranta kafin tace
“Arɗo akwai fahimta Aradu, ƙwarai abu nake so”
Gyara zaman shi yayi yace
“To ina jinki Ƴar Iya, menene kike so haka?”
Itama sai da ta gyara zaman ta sannan tace
“Ina so zanyi aure ne”
Arɗo bai yi mamakin jin hakan ba saboda dama ita bata ga kunya ba duk da kasancewar ta jinin Fulani.
Dariya yayi tare da faɗin
“Masha Allahu, abu yayi kyau, ai haka ake so, shekaru sha uku ai kin ɗana ya kamata ki huta”
Murmushi tayi sannan ta fara magana
“To Arɗo ai ba iya maganar da ta kawo Ni ba, ba kuma ka tambayi waye mijin ba”
Ta ƙarasa tana fari da idanun ta.
“O oo ai dai kam, to wanene angon?”
Dariya tayi sannan tace
“Nima ban sani ba, sai dai yau ina so ka sanar bayan sallar magrib duk wani saurayi dake cikin Gallara ya iso fada ana neman sa, daga nan sai in zaɓa”

Cikin farin ciki arɗo yace
“To to to ai shikenan yanzu za'a sanar, wannan ai abun farin ciki ne”
Cikin ranshi yace “Zaa rabu da Bala'i da yardar Allah ”

Tun daga wannan lokaci Ƴar Iya ta baro fada bata tsaya ko ina ba sai gidan Iya.
Hajiya Iya lokacin tana kwashe tuwo taji shigowar shalelen nata. Kallon ta Iya tayi ganin farin ciki kwance a fuskar ta yasa itama tayi murmushi tare da faɗin
“A! Shalelen Iya har kin dawo yau ɗin”
“E Iya na dawo, yau kam farin ciki nake kuma zaku shiga in kun san dalili”

Cike da mamaki Iya tace
“Affafai! Halan kuɗi kika samo?”
“Yo Iya in kuɗi ne ai da sauƙi, to na kisa komawa birni saboda aure zanyi”
Farin cikin ya hana iya magana can dai tace
“Naji daɗi sosai, Shalele aure fa kika ce?”
“Eh mana Iya aure nace! Ko baki so ne?”
“A'ah Shalele na, Ni kuwa nake so kiyi aure baki ga duk sa'annin ki ma sunyi auren ba, basu har da ɗa ko ƴa”
Iya ta faɗa tana murmusawa.

Ɓangaren Ƴar Iya ma haka kawai take jin wannan auren a ranta, zata yi ko dan Iya sa Baffi su ji daɗi.

COMMENT, LIKE and SHARE FISABILILLAHI!

Ina matuƙar alfahari da ku masoya na, wannan shine wasa farin girki 😄 kuci gaba da kasancewa sa alƙalamin DIAMOND LADY 💎 don jin ci gaban labarin _Ƴar Iya_
Kuyi sharhi da yawa ɗin nan thanks alot.

[6/13, 7:21 AM] Diamond Bhatool💎🩷✍️:

🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀

_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*

SHAFI NA “““47&48”””"

Washegari da sassafe Mami ta shirya musu tafiya. Ta haɗa komai tun daga kan abinci har zuwa abun sha kasancewar tafiyar zata yi tsawo zasu kwashe kwana guda da yini kafin su isa.

Zuciyar Pretty tayi wasai, farin ciki kawai take Sweetheart zai so ta kuma zata mallake shi. Duk wannan shirin da suke Daddy bai sani ba, sai dai tun ranar da Pretty ta tayar mishi da gyambon dake zuciyarshi ya kasa sukuni, wutar ɗaukar fansa ce ko yaushe take ruruwa cikin ranshi.

Misalin ƙarfe goma na safe suka ɗauki hanya sai wajen Natoli aiki yanzu magani yanzu. Mami da kanta take driving nasu har suka yi tafiya mai nisa. Wuraren Azahar suka yada zango tare da cin abinci daga nan suka yi gaba babu batun sallah a ransu.
Chapter 28 · 0% Book details