← Book details Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 49

Sashe 18

Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi Halima tayi tace
“Yoh ai dole na san Ƴar Iya mai hannun ɓarna, ai naji ance ma taje birni, halan yaushe kika dawo?”
Duk irin tsiyar Ƴar Iya da yake nema take bata ce komai ba sai ma murmushi da tayi tace
“Jiya na iso, ammah nima na kusa yin auren ai tunda ƙawa ta zata yi, sai dai ina son ki min bayani akan gyaran da kuma maganin mata da kike magana a kai”

Halima ta gyara zama tace
“Babu damuwa zan miki bayani kamar yadda kika buƙata sai dai bari na kammala girka mana abinci muci, idan muka yi sallah sai mu fara bayanin don zamu kai zuwa gobe bamu gama ba. Tunda mai gidan baya nan ai zaku jima koh?”
Gyaɗa kai Ƴar Iya tayi haka nan A'i ma.

Halima ta tashi ta gyara wuta ganin ruwan ya riga da ya tafasa yasa ta wuce ɗaki ta ɗauko taliyar murji mai ɗan yawan gaske, zubawa tayi a tafasasshen ruwan daga nan ta gauraya da muciya.
Har taliyar ta dahu cikin su babu wadda yayi magana, da kan ta ta kwashe taliyar cikin matacin ta na ƙarfe.

Sai da ta soya manja ta ɗauko yaji sannan ta fito. A tray ɗin silver ta juye duka taliyar sannan ta saka musu manja da yaji, nan aka hau taliya aka cinye ta tsaf.....

(Masoya littafin Ƴar Iya ina matuƙar godiya da irin haɗin kai da kuke bani ta hanyar suburbuɗo comments don ƙarfafa min guiwa.
Ina godiya sosai ƙawayen Ƴar Iya, su AMEERAN MAMA, HINDATU HASSAN, da sauran da ban ambace ku ba, ina fatan samun haɗin kan ku har abada, Allah ya bar ƙauna.

ME KUKE TUNANI GAME DA ALAƘAR HALIMA DA ƳAR IYA?
MENENE DALILIN TAMBAYAR ƳAR IYA GA HALIMA?
SHIN WANE IRIN SALO NE ƳAR IYA TA DAWO DA SHI GALLARA?
MU HAƊU DA SAFE IN SHA ALLAH DON JIN CIGABAN LABARIN.
DUK AMSOSHIN KU NA TARE DA ALƘALAMIN DIAMOND LADY 💎, KU CI GABA DA BIBIYAR ALƘALAMI NA DON YANZU NE ZA'A FARA WASAN!

TAKU HAR KULLUM, DIAMOND LADY 💎

[5/5, 7:13 PM] 💎Diamond Bhatool💎:

🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀

_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*

__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __

SHAFI NA ‘‘‘‘‘29&30’’’’’

*ALEE POV*

Ana kaishi asibiti kuwa aka fara bashi kulawa, kwanan su ɗaya suka koma can gida da shi saboda yadda Ƴan jarida suke sintiri a bakin asibitin, ga kuma mutane kamar tururuwa safe, rana yamma, dare basu bar asibitin ba.

Kulawar da ya samu yasa cikin two days ya warke sumul da yake dama ciwon a iya jiki ne zuciyar na nan ƙalau.

Kowa nan da nan yake da shi kamar wani ƙwai, duk irin yadda yake takurawa ƙannen sa hakan bai sa sun gajiya wurin yi mishi addu'a ba. Musamman waɗanda suke jin kaunar shi daban cikin zukatan su.

Ɓangaren kulawar nan ba'a bar kowa baya ba, Granny, ƴaƴan ta, jikokin ta da sirikan ta musamman Nenne ga kuma Sarah da itama take iyawar iyawar ta, Allah these ko Allah zai sa Hamma Zaki ya so ta ne.

Ƙira kuwa ta ko ina, wasu na ƙiran Mom wasu kuma Daddy yayin da wasu ke ƙiran wani daga cikin ahalin suna tambayar jikin sa don tuni labari ya karaɗe Nigeria ta ko ina zancen ake.

In ka hau facebook, IG har da Tiktok kowa abun da yake wallafawa a shafin sa kenan. Dr. Faruq ne yayi Video ɗin a lokacin da suke kan aiki. Ai kuwa a ranar da suka dawo ya wallafa Video ɗin a shafin sa na Facebook, Instagram, Twitter, YouTube, da sauran su. Kafin kace me kowa sai tofa albarkacin bakin sa yake. Kowa na yabawa wannan zarton matashi da yake aikin sa babu ƙakkautawa.

Comments ɗin wasu kuma bai wuce kan yanayin shi ba, wasu na faɗin wannan ai baindiye ne irin waɗanda ake nuna su a indian film ɗin nan. Ashe dai da gaske akwai masu irin ƙarfin nan. Kowa dai da abun da yake faɗa, ƴan uwa mata kuwa santi ne kawai ke jansu.

Videon nan fah tun da mata suka gani suka rikice, su ba jarumtar shi ce ta burge su ba kaɗai siffar shi kawai ita taja hankalin su.

Daga nan batun zai fara, Ƴan mata a ko ina a faɗin ƙasar mu Nigeria burin su yanzu bai wuce su mallaki wannan Lion ɗin ba. Ga kyau ga kuma jarumta.

Tuni ƴaƴan mommy da Daddy (Ina nufin ƴan gayu, shagwaɓaɓɓu ƴaƴan manya) suka fara yiwa iyayen su daru su fa ga wanda suke so, sun ji sun gani in Babu shi ba zasu rayu ba.

Ana wannan drama ne kuma hukumar sojoji ta ƙasa ta shirya gagarumin bikin cin nasara da suka samu bisa jajircewar Commander da ya jagoranci aikin wato Hamma Zaki.

Flyer na taron ma kar ku so kuga yanda yake trending a yanar gizo. Ai kuwa mata fa sunyi shiri tsaf don halartar wannan taro kowa da irin tata aniyar don jawo hankalin samɓalen saurayin nan.

(Wannan kenan, nimah gaskiya na haɗa sabbin kaya na don ina so nimah nasamu matsuguni a zuciyar Hamma Zaki na).

*ƳAR IYA POV*

Bayan sun samu cinye taliya da manja kowa tasha ruwa aka wanke hannu.

Halima tace “Toh sabbin abokai na, da farko zan fara amsawa Ƴar Iya tambayar ta.” tayi shiru tana maida duban ta ga Ƴar Iya.
“Tabbas akwai gyara na musamman da ake yiwa amarya idan zata yi aure. Wannan gyara kuma ana yin sa ne dai-dai al'adun kowa. Gyaran nan na da matuƙar muhimmanci musamman saboda shi kanshi ango ya son amarya tayi, yana don ya ji ta daban. Ana gyaran jiki, tun daga fuska zuwa ƙafa, gyaran gashi da kuma sauran gyararraki.

Kin gane, misali da zan baki yanzu saboda baki kai ɗaukar bayanan ba shine, kamar ke yanzu in Zaki yi aure, ni da kai na zan gyara ki fes, kinga fatar nan taki da gani Allah ya zuba mata kyau da haske datti ne kawai ya ɓata ta, To zan gyara ta ta koma fes da ita irin ta ƴan gayu ko ba komai ango ya gani zai yi mamakin hakan.

Sannan wannan bakin naki ma da kike gani in Zaki yi aure tas zai koma in yasha gyara ....”

Haka Halima ta fayyace musu gyaran jiki da ake yi.
“Sai kuma batun maganin mata, ku da yake ƙananan yara ne ba zaku fahimta ba amma dai zan faɗi muku abu kaɗan”
Halima ta faɗa musu batun sex idan anyi aure tare da muhimmancin da ayyukan waɗannan magungunan matan.

Daga haka suka koma normal hirar su. Ƴar Iya tace
“Oh Ni Halima kika ce za'a iya gyara baki na?, To da me za'a ke gyara shi?”
“Ƙwarai Ƴar Iya Tun yanzu ma ki fara,idan kika samu gawayi, ko don ashe ku da kara kuke girki, to in kun tashi tafiya ga gawayi a nan sai ki tafi da shi.
Ki daka gawayin nan da gishiri da kuma lalle, sai ki daka kanunfari da kuma alimun ki haɗe da wannan dakakken gawayin, kullum sai durje bakin ki, ina tabbatar miki bazaki jima ba zai koma fes kamar farin wata”

Sai da dare ya fara duka suka yiwa Halima sallama tare da alƙawarin zasu ke shigo mata.

Ɓangaren Angel Ƴar Iya kam ba'a magana, haka kawai taji tana son yin sana'a cikin ƙauyen, tou yanzu tunda an mata bayani kan maganin mata shi ta yanke zata fara siyarwa ba tare da ta san menene da menene constituents na maganin matan ba.

Sassafiya kamar kullum Ƴar Iya ta tashi, bata, tana miƙewa ta fito daga bukkar ta, bata tsaya ko ina ba sai wurin kiwon Baffi, kashin shanu ta tsinta akan faifayin busa, ta hau kan turmi ta ɗaura shi bisa bukka.

Tana ɗaurawa ta diro tare da ɗaukar langa ta fice abun ta. A dai-dai gonar wani mutumi da yake kiwon tumaki da awaki ta tsaya. Ciki ta tsallaka saboda an riga an kewaye wurin da fence. Sai da Ƴar Iya ta kusa cika langar nan da kashin tumaki da awakin nan ta fito abun ta.

Gida taje shima ta ɗaura shi a sama daga nan ta ƙara fitowa, wannan karan ciyawa taje ta tsigo a buhu, ta sanya ta kamar yadda tayi wa sauran abubuwan.

Gidan su A'i ta wuce suka fita yawon su. Suna fitowa Ƴar Iya tace wa A'i
“Ke A'i yau kwaɗayin mangwaro da kashu nake yi, muje lambun Baba Haro mu ciro”
Bata Musa ba su ka ɗebi ƙafafuwan su suka wuce lambun Baba Haro. Sun ci Sa'a kuwa kamar baya nan har da murnar su don sun riga sun san Bala'in wannan tsoho, don duk maitar ka ko zata fito tayi rawa ba zai bayar ba.

Sai da suka kewaye ko ina suka tabbatar Baba Haro baya nan suka ɗale bishiyar kashu tare, suna tsinkowa suna ɗaurewa cikin kwalayen su. Da yawa suka tsinka sannan suka sauƙo suka ajiye ƙullin a gefe.

Basu tsaya ɓata lokaci ba suka hau bishiyar mangwaro. Tun akai suke Sha in sun sha sai su wullo ƙasa.

Suna cikin haka ko tarawa basu yi ba Baba Haro ya shigo lambun. A dai-dai lokacin ne kuma Ƴar Iya ta wullo ƙwallon mangwaron da ta lashe shi har ya zama fari sol.

Bai yi aune ba kawai yaji ƙwallon mangwaro akan sa. Duk tunanin shi irin wanda jemagu suka sha ne shi yasa bai samu ya duba ƙwallon ba.

Ba zato babu tsammani yaji wasu ƙwallayen har biyu da suka iso kan sa lokaci ɗaya.
“Ashh" ya furta tare da sunkuyawa ƙasa. Arba da lasassun ƙwallayen yayi ai kuwa ya ɗaga kai sama. Mutane biyu ya gani kan bishiyar mangwaron. Nan ya fara musu magana kan su sauƙo.
“Ku sauƙo yanzu ko na hawo na ci ubanku”
Dariya suka kwashe da ita Ƴar Iya tace
“Kaji tsoho da wani zance, har ya bani dariya...hhhhhhh..to ka hau ɗin mu gani ina zaka iya”
Chapter 18 · 0% Book details