← Book details Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 49

Sashe 25

Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Neman halal ɗin ta ta fita, yau ma dai bata biya ta gidan su A'i ba saboda ita ta a can tana shirye-shiryen bikinta ne.

Tana fita ta fara zagayawa daga gidan dake maƙwabta da su. Da sallama ta shiga kamar dai ba Ƴar Iya ba.
“Salamu Alekum, ina mutan gidan ko sun fita ne”
Goggo hari dake cin ɗumamen tuwon dawa tace, “A'ah yau kuma mu aka tuna shalelen Iya?, Maraba lale iso muci ɗumame”
Zama Ƴar Iya tayi kan taburmar tana sinne kai. “Iy Aradu inna Hari yau ke na tuna, talla na kawowa sirikan ki, bari na shiga ciki”
“Tallen me kuma shalelen Iya?” Goggo hari ta jefa mata tambaya.
“Maganin mata ne, ku fa tsofin nan kun fiye tambaya, haka iya ma ta sani gaba da tambaya to Sarkin Aljanu da kansa ya koya min, kuma duk wanda bai siya ba Aradu mijin ta sai ya sake ta”
Ta faɗa tana miƙewa tsaye. Goggo Hari jin ambaton Aljanu da Ƴar Iya tayi yasa ba shiri ta bata hanya.
“Allah ya kawo kasuwa” Gaba Ƴar Iya tayi abunta ba tare da amsawa ba.

Lirwanu ɗan Goggo Hari na farko ya fito zai fita suka ci karo da Ƴar Iya. Dakatar da shi tayi ta hanyar faɗin “Mallam ka bawa matarka kuɗin siyan magani”
“A'a shalelen Iya ce?, Ya Iya ɗin tana lafiya”
Katse shi tayi da cewa
“Ba shi na tambaye ka ba in ka damu da Iyar ka je ka gaishe ta ai, mtsss ka bawa matar ka jaka biyu da rabi kaji”
“Toh toh babu damuwa” ya faɗa tare da bin bayan Ƴar Iya har suka isa, su Ƴar Iya ashe akwai hankali a bakin ƙofa ta tsaya jira, bayan ya fito ta tambaye shi ko ya bayar, da ya bata amsa ta barshi ya wuce ita kuma ta kutsa cikin ɗakin.

Ala dole haka tabi sirikan Goggo Hari duk suka siya tukun ta fito daga gidan. Tunani ta fara ina zata kuma nufa?
“Gidan Baba na!” ta faɗa tana murmurshi. Bata tsaya ko ina ba sai gidansu. A lokacin Inna Zaliha na zaune a kan kujerar zaman gida tana wanke-wanke tana rera ƴan waƙen ta. Ko sallama Ƴar Iya bata yi ba ta kutsa cikin gidan sai wani hura hanci take tana ɗaga shi sama, bakin nan yayi gaba kamar bututu.

Inna Zaliha da fuskar ta ke nuna tsantsan mamaki ta kalli Ƴar Iya tana yatsina fuska
“Ke kuma rasa kunya daga ina?”
Ƴar Iya bata amsa mata ba sai ma ƙoƙarin sauƙe kayan tallar ta da take.
“Wai ba magana nike maki ba?, Me Kika zo yi gidana?”
Duk rashin hankali irin na Ƴar Iya sai da ta tsaya ta maimaita me kike yi a gidana cikin ƙwaƙwalwar ta. Can ta kalle Inna Zaliha tace “Gidan ubanki ne ko nawa?”
Baki buɗe Inna Zaliha ke kallon Ƴar Iya tace “Eh ba shakka gidan ubanki ne kam..eh babu shakka haka ne”
Ƴar Iya ta harare ta tace “In baki sa na dawo gidan da zama ba, shegiya mai shegen baƙin hali da baƙar zuciya”
Inna Zaliha tuni ta tsure da zancen Ƴar Iya tunawa da sharaɗin da Bokan ta ya bata....hakan yasa tayi murmushi tana sunkuyar da kai.
“Wa ya isa ya hana shalelen Iya guda?, Yanzu dai me ya kawo ki maza ki faɗamin” Ta faɗa cike da ƙosawa coz zaman ta a tare da su akwai matsala.
Sai da ta gama shan ƙamshin ta tace
“Maganim mata na kawo miki ki saya, ai nasan kina amfani dashi”
“Maganin mata kuma Ƴar Iya?” ta watsa mata tambayar.
“Eh shi dai, ko kin fi so nayi ta maimaita magana kamar jaka?”
“Aah ba sai kin maimaita ba, wane iri ne”
“Irin wadda kike amfani da shi ki mallake min tsoho na har kika raba mu da shi gaba ɗaya, Aljanu da kansu suka bani wannan maganin bari kiji, Kuma in Kika karɓa bakiyi amfani da shi ba Aradu sai kin mutu, shegiya mai raba ɗa da uwa”
Cikin sanyin murya Inna Zaliha tace “Nawa ne?”
Ƴar Iya tace “Naira dubu biyu ne babu yawa, kuma zan dawo don kullum sai kin siya Aradu”
Zaro ido Inna Zaliha tayi tana kallon Ƴar Iya
“Dubu biyu fa kika ce shalelen Iya?”
“Eh haka nace!” ta bata amsa a fusace, “Kina amsar fiye da haka ma daga wurin Baba na ki hallaka a wurin ƙato ai”
“Shikenan yi haƙuri, bari na ɗauko miki kuɗi” ta faɗa tana miƙewa don ta ƙosa Ƴar Iya ta bar gidan zata shiga ɗakin taji Muryar Ƴar Iya “Ki taho min da dubu ɗaya zan biya na siya burodi”
Kamar inna Zaliha zata yi kuka haka ta amsa da to tare da shigewa ɗaki.

LIKE PLEASE

[5/18, 10:52 AM] 💎Diamond Bhatool💎:

🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀

_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*

__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __

SHAFI NA “““41&42”””

Dubu uku cas Inna Zaliha ta ɗauko tare da damƙawa Ƴar Iya tana zuba godiya. A yatsine Ƴar Iya ta amshi kuɗin sannan tace
“Idan Baba na ya dawo kice masa inji ni ya bani wasu kuɗaɗe za'a yi bikin ƙawata daga nan kuma nima za'a yi nawa ba daɗewa.
“to to zan faɗa masa, sai anjima”
Harara Ƴar Iya ta Banka mata tare da ɗago daron ta ta aza shi bisa kayin ta, nan ta fice abun ta tana murna. Ganin tayi ciniki yasa ta yanke shawarar komawa gida ta adana kuɗin ta.

★★★★★★★★★★★★★★★★

*PRETTY POV*

Yammacin yau Laraba Pretty ta shirya kaima Sweetheart nata ziyara bayan ta binciko bayanai game da shi.

Sanye take ciki wasu expensive English wears, Wanda suka ɗame ta sosai, surar jikin ta ana gani kamar dai babu. Kitson attachment da tazo da shi ta sa aka sauya duk da ta kashe kuɗi mai yawa kafin ayi mata, ƙwaƙuyayyen kan nata ta ɗaurawa wata cap na gashin doki tare da gyara ta tsam, nan sai ka rantse gashin ta ne.

Fauzy ce ta mata makeup wacce ta mayar da ita mutum-mutumi, in ka ganta babu abinda zai hana ka guduwa, hankali kwance ta fesa uban turare tare da yiwa ƙawayen nata alama da suzo su wuce, suma da shigar tasu babu gwanda, sai dai ita sumy Abaya ta saka tare da rolling veil.

Cikin motar kuwa Pretty farin ciki ya hana ta sukuni, zata ga Sweetheart ɗin ta, babu abunda ke tashi sai sautin waƙar India tuni ta manta duniyar da take.

Dai-dai Gate ɗin gidan General Muhammad Naira suka yi horn, gateman ya buɗe, sai da suka kai dai-dai parking space suka yi parking motar. Ba tare da sun fito ba suka tsaya ƙarewa motocin dake wurin kallo, ga kuma tsarin gidan da tuni ya tafi da su.
Pretty da ta tuna mai ya kawo ta ta ce “Babes wanne part ɗaya zamu shiga ne?”
Fauzy tace “Mu shiga na farkon idan ma ba nan bane ai za'a tura mu wani”
“ƙwarai yadda Fauzy ta faɗa haka za'a yi” Sumy ta amsa mata.

A gadarance cike da yauƙi suka fito daga motar tare da nufar entrance na part ɗin. Ganin door ɗin a buɗe yasa suka kutsa kayuwan su ciki. Ƙamshin da ya daki hancin su kaɗai yasa su lumshe ido, bisa latsa-latsan kujerun suka yiwa kansu masauƙi.

Ganin babu wadda ya ko gifta yasa Ishy faɗin “Pretty wai zaman me muke yi ne?, Letz just get in mun tsaya a nan babu mai fitowa fa” Sumy kam da kallo ta busu don tuni gidan ya matuƙar burge ta, sai taji inama ace tana da wata alaƙa da gidan. Su Fauzy ma dai zuciyar nan a cunkushe ana bawa ido abinci.

“Assalamu Alykum” sallamar Fauzah da ta doki kunnuwan su yasa su waiwayowa don ganin waye”
Mutuwar tsaye taso yi ganin baƙi a parlourn Mom, baƙin ma Christian, sai da ta hango Sumy tukun taga ita kamar musulma ce. A hankali ta ƙara sa tare da faɗin “Ina yinin ku”
Murmushi duka suka yi mata tare da faɗin “lafiya ƙalau a tare”
“Bari na sanar da Mom tayi baƙi to”
Daga haka bata jira amsar su ba ta wuce bedroom ɗin Mom.
“Good evening Mom.... I'm back oh sorry u've visitor outside”
Cike da mamaki tace “Visitors kuma Fauzah, su waye”
“I don't know them but it seems like Christians ne, suna jiran ki” ta ƙarashe tare da nufar hanya zata fice.
“Wait Fauzah, ask Laraba to bring something for them, Ina fitowa”
“Ok Mom”

Kamar yadda Mom ta umarce ta haka ta wuce ɓangaren su Laraba ta sanar da ita saƙon Mom kafin ta wuce bedroom nata ta cire uniform tare da yin wanka. Sai da Mom ta ƙara kusan five minutes ta fito sanye cikin kayan al'adar su, sari ce blue wacce tayi matuƙar ƙara bayyanar da kyau da kuma izza irin ta Mom ga kuma kyakkyawar kwantacciyar baƙar sumar ta da ta zubo da ita ta baya.

Jin takun takalmi yasa duka suka waiwayo..... idanuwan su suka zaro tare da sakin baki kowa na ayyana abun da ke zuciyar sa. Cike da mamaki ganin duk ciki babu wanda ta sani yasa ta ƙara ƙure su da ido ko zata tuna su. Su kuwa kallon da Mom ke jifan su dashi ya sauƙar musu da shakkar ta na lokacin.
Chapter 25 · 0% Book details