← Book details Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 49

Sashe 42

Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da takaicin sauyin halin nasa ta juyo rai babu daɗi. Cikin ranta tana ayyana “Ba zai saɓu ba, dole ne ka dawo ƙarƙashina Captain. You're mine alone”.
Ba tare da ya juyo ya kalle ta ba yace “Ki haɗa kayan da zaki buƙata, in a day time zamu wuce Adamawa”
Baki sake take kallonsa ta ma kasa furta komai. “Me mutumin nan yake nufi?”. Cikin ƙarfin hali tace “Sweetheart kwana nawa zamu yi?”
Har ta cire ran samun amsar sa taji yace “Can zamu koma da zama”
“Kutumar uba!, Wallahi ba zata saɓu ba”
Ta faɗa tana riƙe kunkumi tare da jijjiga jiki irin ta tsumu da bala'in nan..

Bai kalle ta bare tayi tunanin yasan me take, saboda haka ta fice a fusace cikin ranta tana tabbatarwa kanta aikinsu ya ɓaci.
“Dole kuwa nasan yadda zanyi”
Mami ta ƙira take sanar da ita komai. Wani Ashar da ta kututtumo kamar bamagujiya.
“Amma wannan Allah yayi ƴan abu ta kazar uba, karki damu Daughter, yanzu ki nuna masa babu komai ki lallaɓa shi tunda ya dawo hankalinsa, ko bayan tafiyarki zan koma wurin bokan yayi masa babban aiki ke harda iyayen nasa ma”
Da haka ta fara haɗa trolleyn ta, komai na buƙata ta saka, ga yanzu damuwarta ma ɗaya itace ta cikin dake jikinta. Tana ayyana dole Captain ya amshi cikin ko kuma tayi aborting nasa.

Da haka ta haɗa komai ta zauna cike da zulumin komawarta Adamawa.

Washegari da safe ma sai da ya tashe ta tukun ta tashi, daga nan ya fita yana jin takaicin wannan aure nasa, sai da ya kammala komai tukun ya wuce yayi musu booking flight. Abinci ya biya ya siya daga nan ya ƙarasa gidan. Bai bi ta kanta ba har washegari. Ƙarfe bakwai dai-dai yaje ya tasheta saboda Flight ɗin 8 zasu bi, shi kam already ya gama shirinsa cike da haɗuwa da burgewa. A daddafe ta kammala shirin saboda zazzaɓi zazzaɓin da ya sauƙa mata. Tare suka wuce zuwa airport ɗin ba tare da wani ya cewa ɗan uwansa ƙala ba.

Ɓangaren Khairy kwana biyun nan bata san me ake yi ba, kowa tausayin halin da take ciki yake, Adda Salma Kam ta taro part ɗin granny tare da ita ake kula da Khairyn.

Flight ɗinsu na landing suka ƙarasa zuwa motar Hamma Salim da yazo ɗaukarsu. Kallo ɗaya yayi mata ya gano tana ɗauke da juna biyu, cike da barkwanci yace “Ke amarya zuwan farko da tsaraba”
Cike da duburburcewa tace “Ehm ah ehm yayan mu..” Bata Kai ga ƙarasawa ba ya katseta yana dariya “Kinga ba wani abu bane, baki ga basaraken mijin naki ma bai ce komai ba”
In banda ƙyaƙƙyafta ido babu abunda pretty keyi har suka iso. Shi dai Hamma Zaki ko kallo basu ishe shi ba. Bayan sun isa a part ɗin Mom suka sauƙa, babu yabo babu Mom ta tarebe su, Laraba aka sa ta kai trolleyn su Bedroom ɗin Hamma Zaki dake upstairs.Dawowar su Fauzah daga school yasa Mom ta umarce ta taje su raka ta ta gaida sauran mutanen gidan.

Sai dai suka je kowanne sashi sai dai gaisuwar mutunci basu samu daga wurin Pretty ba, daga ƙarshe sashen granny suka wuce. A lokacin granny na gaban Khairy wacce ta farka, abinci take bata sai gocewa take ita kuma granny sai famar sannu take aika mata.

Isowarsu ko sallama babu, ita kanta granny Bata san da shigowarsu ba har sai da Fauzah tace Granny Khairyn ta tashi?”
Juyowa granny tayi yayin da idonta ya kai kan Pretty da ta hakimce tana wani hura hanci.
A faɗace granny ta dubi Pretty tace “Ke Kuma fa Malama? Daga ina?”
Fauzah ce ta rufe bakinta da hannu cikin ranta tace “Shikenan granny ta ɓata” a zahiri kuma tace “Granny Aunty Nabila CE fa matar Hamma Zaki”
Baki granny ta kama tace “Ah ai dole, ashe dai kece, zakiyi fiye da haka, to rasa kunya tashi ki bani waje tunda ba'a koya miki ɗaa a gidanku ba”
Daga haka ta juya tana maida dubanta ga Khairy tana ƙara jera mata sannu. Sai da ta saisaita kanta kafin tace “Yi haƙuri Hajiya naga kina bawa yarinya abinci ne shiyasa, ina wuni mun same ku lafiya?”
Ɗan sanyi granny taji ta juyo babu yabo babu fallasa tace “Shikenan lafiya ƙalau” sannan ta maida dubanta ga Fauzah “Ke fauziyya raka ta ina kula da yarinyar nan, sa dawo ita da mijin nata ai”.

Pretty Kam danne fushinta tayi ta wuce ta koma part ɗin granny tana tunanin yaya zamanta zai kasance a wannan gidan? Dole ne tayiwa tufkar hanci don ba zata juri iskancin wannan ahalin nasu ba. Tunawa da wannan yarinyar da tsohuwar ke wani tarairaya kamar jaririya tayi “Tsaki taja tana shigewa cikin Bedroom ɗin da aka ajiyeta.

“Wow!” ta furta, “Kai komai nasa daban ne, ina sonka Captain, ina sonka sosai Captain!”
Haka tayi ta bin frames ɗin dake ɗakin da kallo sai yaba irin kyan da mijinnata yayi, “Tabbas nayi sa'ar samun Captain matsayin mijina, tabbas zan tsaya da anyi sabon aikin nan na kula don cikin cousins ɗin nan nasa masu kama da aljanu zai iya ƙyasa wa”, fuska ta ɓata tana wucewa Toilet ɗin shi.

Bayan ta fito main parlourn ta dawo, da yake babu kowa duk sai taji zaman ya ishe ta saboda haka ta fara chat abunta.

Tun fitar Pretty granny ke sauƙe bala'i kamar tana gabanta.“Ho ni Shatu, wannan wace irin mata ce?, Yo ai nayi mamaki ma, in Banda iya shege tazo ɗaki na kuma tana buɗe min hanci kamar wando,mtsss marar tarbiyya ko ina ya shiga sai ya nuna. Ai dole na nemawa maza mata don baya zama da wannan mai zubin shaiɗanun”

Kamar daga sama taji Khairy na faɗin “Granny ruwa zan sha”
“Yi haƙuri ɗiyar arziƙi wannan shashar duk ta ɓata min rai, karɓi ki sha abunki”

_To ga Pretty a Adamawan Yola fa, Mami Kuma tace za'a sabunta aiki, ga kuma ƙudurin granny ma, uwa uba ya kuke tunanin tashin Khairy?, Kasance da alƙalamina don jin yadda zata kaya._
_Comment and share please_

[8/24, 9:35 AM] 𝙳𝚒𝚊𝚖𝚘𝚗𝚍_𝙱𝚑𝚊𝚝𝚘𝚘𝚕💎: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IWQW3ytbVc611XLon2sn66

🌸🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀

Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*

SHAFI NA “““71&72”””

Kwana biyu suka shafe a gidan, Pretty dai damuwa tayi mata yawa sosai, gabaɗaya bata samun kan mijinnata, saboda haka yasa ta fara tunanin aborting cikin don babu yadda za'a yi ma ta fara cewa cikin nasa ne saboda kwatakwata ma sau nawa ne suka tara?. Dole ta samawa kanta mafita don ba zatai sakacin rasa kyakkyawan mijinta ba.

Khairy ma dai har yanzu babu wani kyakkyawan cigaba da za'a yi magana sai dai takan bi duk wanda yazo dubata ne da ido, babu wanda aka bari a baya wurin bata kulawa.

Yau Litinin, a kuma safiyar nan ne Pretty ta shirya zuwa asibiti don aborting cikin da wanda ake tunanin nasane bai sani ba. Sassafe ta tashi ko jira ya tashe ta bata yi ba ta nufi toilet. Wanka tayi ta shirya cikin wasu English wears sannan ta feshe jikinta da turare tana jiran zuwansa don tashinta kamar kullum. Around 5:58am ya shigo ɗakin da niyyar tashinta, ganinta zaune yasa yayi yunƙurin juyawa sai dai da sauri ta isa gare shi, cikin wata yaudararriyar murya tace “Good morning sweetheart”
Bata yi zaton zai amsa mata ba yasa ta buɗe baki don sanar da shi zata hospital sai taji yace “Morning” hakan ma ya faɗa ne cike da mugun jin haushinta.
“Sweetheart dama ina son zuwa hospital ne bana jin daɗi”
Sai da ya kusa fita ya juyo yace “I'll call the family doctor, zai zo ya duba ki”.
Cike da jin haushinsa tace “Wallahi sai naje, sai dai ka kashe ni, shegen baƙin rai, mami zata yi mana maganinka ne”

Ko da suna breakfast da yake tare da su Mom ne, da wuri ya miƙe saboda kallon da take aika masa. Fitowarsa cikin uniform ɗin da suka matuƙar dace da shi yasa Pretty jin daɗi. Sai da ya fita bayan Daddy ma ya miƙe, Fauzah ma ta fita ɗauko school bag nata ta kalli Mom cikin ladabin ƙarya tace “Mom, dama ina son zuwa shopping ne don siyo abunda bani da shi a nan”
Kawar da mamakinta Mom tayi tace “Kin sanar da shi mijin naki?”
“Eh ah dama na faɗa masa sai yace wai driver zai kaini”
Mom tace “Shikenan, zuwa 10:00am sai ya miƙa ki”
Bata iya ɓoye farin cikinta ba har godiya tayiwa Mom wadda ya matuƙar ɗaure kanta.

Alhamdulillah, yau tun safiya Khairy ta tashi kuma Alhamdulillah da warginta ta tashi. Murna wurin granny kamar tayi rawa. Darun da ta tasa wai zata je school yasa granny yin fushi, bata so hakan ba saboda haka tace ta haƙura.

Ko da Pretty taga motar da za'a kaita sai da ta saki baki, cikin ranta tace “Bazanyi sakaci na bar wannan daular ba, dole ka dawo nawa Captain” umarni ta bawa drivern ya kaita wani private hospital Mai kyau. Bayan sun isa ta shiga, card ta yanka daga nan ta zauna a reception tana jiran layi yazo kanta. Ba'a jima ba kuwa aka kira sunanta “Nabila Ali Naira” da sauri ta shiga don ganin likitan. Bayani tayi masa a kan abinda take so, da farko cewa yayi it's illegal Kuma basu yi a nan, daga baya ya amince tare da tambayar ta cikin wata nawa ne?, “3months” tace masa, Magungunan yayi prescribing daga nan ta fita pharmacy ta siya. Tana kammalawa tace ya kaita shopping mall. Pads ta kwasa sai wasu abubuwan saboda rufe baki da cewa shopping taje.
Chapter 42 · 0% Book details