← Book details Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 49

Sashe 29

Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har maghrib basu ƙara tsayawa ba sai da suka ga sun shigo wani ɗan ƙauye, hakan yasa suka yada zango ba tare da sun fice daga motar ba, a nan suka ƙara cin abinci suka sha abun sha. Mami da ta riga ta gaji ta koma seat ɗin mai zaman banza tare da kwantar da kanta, nan bacci ya kwashe ta.

Ba su suka bar ƙauyen nan ba sai da Asubahi sannan suka ƙara yankar hanya, sunyi tafiya sosai kafin suka kai ga wata hanya da ta rabe biyu, ɗaya abushe take ƙaraf yayin da ɗayar kuma alamun damshi da ni'ima suka bayyana tattare da ƙasar. Hanyar da ta bushe Mami ta umarci Pretty da ta ɗauka, babu musu ta yanki hanya.

Tafiya suke amma babu ko alamar ƙuda da ke rayuwa cikin wannan sahara, har sai da yamma tayi tukun suka fara hango hayaƙi na tashi, nan Mami tayi murmushi ta kalli Pretty dake tuƙi cike da gajiya sannan tace
“Kuka ya ƙare, Captain Alee zai so ɗiyata”
Ɗaga ido Pretty tayi tare da maida hankalin ta kan tuƙin da take yi tace
“Wayyoh! Can't wait”.

Daga wurin sukayi packing sannan suka fito tare da ɗaukar jakar kuɗaɗen sa suka zo dashi suna tunkarar wurin da hayaƙin yake tashi. Sunci uwar tafiya kafin su kai ga wani ƙatoton dutse wanda ke ɗauke da wani wankamemen kogo, nan da nan jikin Pretty ya fara rawa.
“Mami nikam mu koma”
Harara mami ta Banka mata
“Baki da hankali ma” ta faɗa tare da jan hannun Pretty suna tunkarar kogon.

Tun daga baƙin ƙofa suke jin wani sauti, shi ba kuka ba sannan shi ba dariya ba, a haka dai suka daure tare da kutsawa ciki. Wata mahaukaciyar tsawa mai razanarwa aka yi ana faɗin
“Ba'a shiga da ƙafar dama”
Da ƙyar suka shiga aikin yadda suka kiɗime. Suna shiga wata guguwa ta tashi yayin da wani duhu ya mamaye wurin. Can bayan waɗansu daƙiƙu haske ya dawo, guguwar nan ma ta ɓace nan da nan!.

Basu tsinci kansu ko ina ba sai a wani ɗaki wanda ke ɗauke da fatotin naman daji, kura ne, zaki ne, damisa ne! Da makamantansu. Tun daga nan bakin su ya mutu.

Can daga wata kusurwa ya fito, baƙi, jibgege mummunan gaske wanda fuskar shi ke ibi da ta shanu.....Natolu kenan! Suka ce sha yanzu magani yanzu. Cikin dariyar su irin ta rikaƙƙun bokaye ya zuba musu ido tare da zama gaban kayan aikin sa.
“Maraba da zuwa Hajiya Salima uwar ɗakin Ɗan Hambali”
Bokan ya faɗa yana murmushi
Sunkuyar da kai tayi don ta san dokar shi ba'a haɗa ido da shi.

“Kinzo ne batun ɗiyar ki ko, ba sai kin min bayani ba na ga zuwan ku tun jiya cikin madubi na, sai dai wannan aiki zai yi matuƙar wahala amma in kin sake kuɗi zai tafi dai-dai”
Shiru mami tayi boka yaci gaba da bayani
“Zai so ta, zai aure ta ammah kuma akwai wani abu da baya nunawa wanda da gani matsala ce, akwai abun da zai bayyana cikin rayuwar shi wanda zai zama katanga ga wannan aiki, har yanzu ban samu fahimtar menene ba ammah dai aure tsakanin ɗiyarki da yaron ba fashi”

Haka dai boka ya zance su su kuwa tsabagen farin ciki suka zuba masa kuɗin tare da fecewa abun su.

_(Ina ƙira gareku Ƴan uwa mata ku tuna cewa zuwa wurin boka haramun ne a musulunci, ku tuna duk wanda ya aikata hakan kuma toh ya aikata mafi girman laifi wurin Ubangiji kamar yadda Annabi Sallallahu Alyhi wa Sallam ya faɗa. Duk wanda ya halarci wurin boka to haƙiƙa ya kafurcewa abinda aka sauƙarwa Annabi Muhammad)_

_(Har ila yau iyaye mata ya kamata musan cewa ƴaƴan mu amana ce da Ubangiji ya bamu, ya zama dole mu kula da su mu kuma basu tarbiyya mai kyau kamar yadda yazo cikin Alqur'ani, haka nan annabi ma ya ƙara nanatawa Muminai a kan irin girman da amanar yaro take da shi a wurin iyayen shi!)_

_(Kada ki kasance cikin iyayen da zasu banzatar da yaran su, iyayen da basu damu da tarbiyyar yaransu ba! Kada ki kasance cikin su don kuwa ki sani Ubangiji zai tsayar da ke ranar alƙiyama ya tambaye ki a kan kiwon nan tun daga haihuwa, girman su zuwa mutuwar su? Wace rawa kika taka cikin rayuwar su?, Shin kin basu tarbiyya ko akasin haka)_

_Allah ya shiryar da mu sannan ya bamu ikon kiyaye amanar da ya bamu na yaran mu_

Tunda suka dawo tayi wanka ta huta washegari tabi Flight ɗin da zai kaita Adamawa. Tana isa ta wuce army barrack na su Hamma Zaki, tana isa ta tambayi office nashi aka nuna mata.

Dai-dai corridor na office ta tsaya tare da fitar da wata kwalba mai ɗauke da wani jan abu a ciki. Murmushi tayi tare da buɗe ta ta juye ta kaf a jikin ta, nan take wani irin mahaukacin ƙamshi ya tashi a wurin.

Sai da Pretty ta daidaita kanta sannan ta yi knocking, “Yes come in” ya faɗa cikin kamammiyar Muryar shi.
Shiga ciki tayi tana wani rangwaɗa shi kuwa hankalin shi na kan wata takarda da yake karantawa. Ƙamshin da ya bugi hancinsa ne ya dawo dashi daga duniyar tunani.

Murmushi ta aika masa tare da faɗin
“Hi Sweetheart!, Na dawo gare ka Please wannan lokacin kada kace a'a in ba haka ba zan iya rasa rai na”

Lokaci ɗaya ya ɗago da niyyar balbaleta sai dai ƙamshin da ya ƙara ziyartan hancinsa ya dakatar da shi.
“Say something sweetheart ko na koma?”
Samun kanshi yayi da jijjiga mata kai, murmushi tayi tace
“Alright bari na zauna”
Wuri Pretty ta samu ta zauna tare da kafe shi da Mayun idanuwan ta. Cikin ranta kuwa murna ce fal haka tayi ta masa zuba shi kuma ya kasa hanata sai ido kawai yake Binta da shi.

Lokaci azahar ya shiga toilet tare da ɗauro alwala yayi sallah Pretty kuma lokacin ta fice, abinci tayi musu order tare da dawowa. A nan suka ci har Yamma.

Lokacin tashinsa ma da yayi tare suka wuce a motar shi kowa sai mamaki yake ganin Captain Alee da mace. Wanda hakan ɗin duk shirin ta ne da kuma roƙon shi da tayi ya barta ta sauƙa gidansu.

Bayan sun koma gida Mom ta jima tana mamakin dawowar Hamma Zaki da mace! Haka dai sauran mutanen gidan. Ita dai Sarah Bata kula ta ba haka ta ishi mutane da iyayi da feleƙen tsiya.

Washegari ma tare suka fita coz tace mishi zata koma gida washegari ne ammah tana so ya tura iyayen shi a sanya ranar auren su. Kamar wani gaula kuwa ya sanar da Daddy da Mom, duk irin yadda Daddy ke son Hamma Zaki yayi aure kawai taji abun ya fita mishi a rai saboda yarinyar amma babu yadda zai yi tunda shi yake so. Ita kuwa Mom a matsayin ta na baindiya tasan sihiri iri-iri coz duk wasu shu'uman sihirhiru daga India yawanci suka samo tushe, a lokacin ta tabbatar ɗan ta yana cikin kogin asiri ne sai dai ta ɗauki alwashin ɓata aikin nan gaba saboda wani dalili.

Bayan Pretty ta wuce gida haka tayi ta damun Hamma Zaki da ƙira, dare, raba, safiya kamar jaraba, babu laifi kuma tana ɗagawa duk da cewa baya jin komai game da yarinyar kawai dai shima ya ji ya amince da buƙatar tata ce.

Su Dr Faruq sunyi mamaki sosai haka su Nenne, Mommah, granny Kai duk iyalen Muhammad Naira sunji a jikin su.

Bayan sati ya zagayo uncle Suraj da Uncle Bello suka je nema wa Hamma Zaki auren Pretty babu Musu aka basu don kuwa shi kanshi uban Pretty akwai wata ajiyar tsakanin shi da wannan ahali.

Wata guda aka sanya ranar bikin, tun daga nan Pretty aka fara shirye-shiryen bikin. Babu wanda ya nunawa Hamma Zaki rashin son auren nasa sai dai granny kullum sai tayi magana in yazo part ɗin ta, in kuma ya zauna har kuka sai tayi wai yaje ya nemo Ƴar mutunci ba wannan da ta haɗa rigima kwanaki ba.

Sarah kuwa babu ruwan ta coz yanzu ta riga da ta cire son Hamma Zaki cikin ranta, yanzu mutum ɗaya ne yake yawo cikin jinin jikin ta wato Captain Sulaiman wanda tuni ya isa gida har an fara shirin yin bikin al'ada irin na indiyawa.

Tunda ya diro ƙasar shi da Aunty Waheeda suka sauƙa a ɓangaren su dake cikin family house ɗin nasu. Labarin auren Hamma Zaki ya dirar musu a kunne su ma dai basu ji daɗi musamman da suka ji babu wanda ke son auren. Fatan Alkhairi tare da addu'oi kawai suka yi musu.

★★★★★★★★★★★★★

*ƳAR IYA POV*

Kamar yadda ta buƙata haka arɗo ya sanar da saƙon ta sai dai bai ce Ƴar Iya ke son ganin su ba.
Kafin kace me fada ta cika da samarin garin gaba ɗayan su.
Cikin nuna isa da taƙama tazo ta kama wuri ta zauna sannan tace da arɗo ya sanar da su dalilin taruwar su.
Gyaran murya yayi sannan yace
“To kamar dai yadda kuka gani an haɗa wannan taro na matasa ne ba don kowa ba sai Ƴar Iya, kuma dalili shine zata zaɓi miji cikin matasan ƙauyen nan” daga haka ya dakata yana maida kallon shi ga Ƴar Iya wacce take famar sake murmushi.

“To Ƴar Iya bismillah, ga su nan ki zaɓi duk wanda yayi miki a cikin su”
Sai da ta farfara ido kafin ta fara binsu ɗaya bayan ɗaya tana dubawa, ta shinshini wannan ta yatsina fuska tayi kallon banza daga ƙarshe dai duk ciki babu wanda yayi mata. Dawowa tayi ta zauna tare da yamutsa fuska tace
“Basu yi ba”
Arɗo yace “Shikenan kada ki damu zan gayyato samarin ƙauyukan dake kusa da mu zuwa gobe kinji? Ki kwantar da hankalin ki maza”
Jijjiga kai Ƴar Iya tayi tace
“Aah Arɗo ka barshi ai naga wanda yayi min ma ba sai an gayyato wasu ba”
Jin furucin ta yasa kowa fara zare ido yana sunkuyar da kanshi ƙasa. Cikin zukatan su kuma addu'a suke Allah yasa dai kada ta zaɓe su. Don kuwa babu wanda zai so ya auri Bala'i, a faɗar su ai Ƴar Iya saidai aljani.
Chapter 29 · 0% Book details