← Book details Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 49

Sashe 7

Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Banji meh aka ce a ɗaya ɓangaren ba can yayi murmushi wanda ya ƙara ƙawata kyakkyawar fuskar shi.
“Barka da rana Mom”
“Eh ban jima da isowa ba, yea, I'll be there tomorrow morning in Sha Allah.... can't wait to see u Mom.... alright don't forget to prepare my favorite please....ohk bye Mom I love u” ya ƙarasa yana sakin kiss 😘 ta wayar sannan yayi hanging call ɗin.

(Ni Bhatool mamaki ya hana ni magana jin harshen Hausa a bakin wannan haɗaɗɗen guy Wanda Sam bai yi kama da Nigerians ba)

Phone nashi ƙirar Samsung ya janyo bayan ya latsa ta na tsawon five minutes ya ajiye ta kusa da Nokia ɗin tare da janyo Laptop ɗin shi.

GODIYA TA MUSAMMAN GARE KU ƳAN UWA NA ABABEN ƘAUNA TA DA KUKE ƘARFAFA MIN GUIWA A KOWANE LOKACI.....Seemah and Shaheeda! ALLAH YA ƘARAWA RAYUWAR KU ALBARKA.

FANS ƊINA NA LITTAFIN ƳAR IYA KUMA GODIYA TA MUSAMMAN A GARE KU MUSAMMAN MASU BIBIYA TA DA KUMA ZABGA MIN COMMENTS HAR DA MASU TAYA NI SHARING....ALLAH YA BAR ƘAUNA....

KU CI GABA DA BIBIYAR ALƘALAMIN DIAMOND LADY (GARKUWAR NAZARI WRITERS).

PLEASE COMMENT & SHARE.

[4/28, 8:18 AM] 💎Diamond Bhatool💎:

🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀

_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*

__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __

SHAFI NA ‘‘‘‘‘11&12’’’’'

Danne-danne ya fara almost 24minutes kafin ya aje laptop ɗin tare da phones ɗin shi.

Ƙaramar wayar shi da tayi ringing yayi picking tare da kara ta a kunnen shi. Ban san me aka ce ba a ɗaya ɓangaren can guy ɗin yace
“Alright, I'll be there now"
Daga haka yayi hanging call ɗin.
A hankali ya ziro kyawawan ƙafafun shi ƙasa tare da sanya takalmin dake bedside ɗin. Sauƙa downstairs yayi tare da buɗe door. Wani soja ne ya miƙo mishi manya-manyan leathers ɗin da alamau yayi order ne and it seems like abinci ne.

Kallon sojan yayi tare da faɗin
“Let me have one, the remaining is yours”
Kamar yadda ya umarta haka ya miƙa mishi tare da faɗin “Thank You sir” ba tare da nuna alamun ya ji shi ba ya koma yana rufo ƙofar.

A dai-dai dining area ya ajiye leather tare da wuce upstairs, ganin lokacin sallah ma yayi yasa ya shiga toilet, watsa ruwa yayi tare da ɗauro Alwala. Yana fitowa ya shimfiɗa praying mat tare da tada sallah.

Captain Alee Muhammad Naira Kenan, kyakkyawan matashi son kowa ƙin wanda ya rasa.

Ɗa na biyu wurin Gen. Muhammad Naira da kuma Dr. Rohmoh Isiaq.
Su uku Allah ya bawa iyayen su, Yaya Saleem shine babba, sai shi daga nan kuma Autar su Fauzah.
Daddyn shi Haifaffen jihar Adamawa ne bafulatani Usul wanda da ka gan shi zaka fahimci haka, Mom ɗin shi kuma daga India Daddy ya auro ta Lokacin sun je wani muhimmin taro ta maƙale masa ita ala dole sai ya aure ta. Irin kyau na Mom da kuma goyon bayan iyayen ta da ta samu kan batun yasa ya amince suka yi aure.

Alee Matashi ne mai jini a jika, shekarun sa bazasu wuce 26years ba sai da yana da ƙirar jikin wani ɗan 30's ɗin. kyakkyawane ajin ƙarshe ga kuma uwa uba iya ɗaukar wanka. Duk da kasancewar shi youngest captain a Nigeria sai dai yanayin kwarjinin da yake da yasa colleagues nashi bashi wani girma na musamman, baya shiga abinda bai shafe shi ba haka shi ba ma'abocin yawan magana bane....miskili number 1 toh Yaya Alee ne shiyasa duk jarabar mata hardly kaga sun samu ko da kalma ɗaya ne daga bakin shi.

Main house nasu a can Adamawa yake, Uncle Suraj da Uncle Bello da kuma Daddyn shi duk a family house nasu suke. Rayuwar su rayuwa ce irin ta ƴan gayu kuma ƴan boko duk da kasancewar su Fulani ne, Granny kaɗai ke ƙaƙabewa al'adun su na Fulani.

Cikin familyn su kuwa babu wanda baya shakkar Hamma Alee....laƙabin da suka manna masa kan bayyanar da hakan “Zaki”.

Shi sam a rayuwarsa baya son hayaniya komai ƙanƙantar ta...in kaga yana dariya kuwa to tare da Areef ne son ɗin Yaya Saleem.

*Wannan kenan*

★★★★★★★★★

*ƳAR IYA POV*

Tunda suka ɗunguma cikin kasuwar ta fara tunanin me zata ci ne mah, dai-dai wata rumfa da Iliyasu ke saro bread yayin da sauran ƴan gari ke sara a wurin shi suka biyo. Yana ganin su ya cillo wani tsumma da yake goge daron bread da shi kan bread ɗin, All this saboda kada su Ƴar Iya su gani ne sai dai abu ya riga ya faru.

Kai tsaye rumfar suka nufa tare da faɗin
“Iliyasu akwai burodi ne?”
Cikin inda-inda yace
“A...aa..eh..akwai guda.. shida da suka rage”
Ba tare da ta ce uffan ba ta nufi wurin tsumman nan ta yaye shi ai kuwa A'i ta saki baki tana salallami.
“Innalillahi wai dama akwai burodin shine kace ƙwara shida suka rage, lallai ka cika ƙatoto kuma zungureren maƙaryaci”

Ƴar Iya kuwa tuni ranta ya soma ɓaci da halin ƴan ƙauyen nasu, kowa sai shegiyar rawar tsiya. Tsaki ta ja sannan tace
“Ni na kasa gane halin ku ƴan garin nan gaba ɗaya kun addabi jama'a da rowa, to kowa baƙin cikin ciyar da kai yake...Ni Autar Iya ina ganin jalala, to Aradu burodin nan duk ka juye man shi cikin buhu yanzu ka miƙo man” ta faɗa tana banka mishi harara.

Ba tare da ya musa mata ba ya juye bread ɗin baki ɗaya coz shine kwanciyar hankalin shi. Bayan sun ɗauki bread ɗin su suka wuce abun su sai gida Iya....babban buhu guda na bread suka sanya gaba sai da suka ga bayan shi tasss...ƙwara ɗaya suka bawa Iya wanda shima da ba don Iyar ta ɗauke shi ba da tuni sun gama da shi.

Da yammaci ne Baffi yayi baƙo, amininsa ne wanda suka yi karatun Allo da shi a tsangaya ɗaya sai dai shi Haifaffen garin Galdimari ne ammah a can Sakwa yake da zama.
Sun yi taɗi sosai da Baffi daga bisani ya tafi. Bayan tafiyar shi Baffi ya tunkaro Iya da batun da suka tattauna da abokin sa duk da cewa gabaɗaya kusan a kan Ƴar Iya aka yi shi.

“Iyar Shalele dama wata magana nake so muyi da ke”
“Toh ina sauraron ka, Allah dai yasa lafiya”
“Lafiya ƙalau....damah ɗazu Amini na Shehu ai baki dai manta shi ba?” kai ta ɗaga shi kuma yaci gaba.
“Toh shine muke tattaunawa akan matsalar Yarinyar nan mai sunan ki, toh ya bani shawara wacce ina kyautata zaton in mun bi ta zamu samu nasara da Izinin Allah kuma la'alla yarinyar ta daina wasu daga cikin halayen ta”

Ganin Iya ta tsura mishi ido tasa ya ɗan dakata yana kallon ta.
“Ammah baka tunanin haka Allah ya halicci yarinyar ne?, Ba ma wannan ba wace shawara ne kuka yanke kai da shi Malam Shehu ɗin?”
Sai da Baffi ya gyara murya sannan ya ce
“Malam Shehu ya bani shawara kan kai takwarar ki makarantar kwana, idan har bata ganin na kusa to za'a samu sauyi, kuma a can zata ƙara sanin rayuwa tunda mutane ne iri iri idan muka ci Sa'a sai tayi koyi da wani daga ciki”

Jimm Iya tayi ta rasa abun faɗi can tace
“Ammah baka tunanin in taje can ma tayi musu halin ne?”
Murmushi irin nasu na manya yayi sannan yace
“A'ah bana fatan hakan, fata na ta samu sauyi cikin rayuwar ta, itama tayi rayuwa kamar yadda kowa yake yi, ina da tabbacin ba haka ainihin yarinyar nan take ba saboda na sha yin mafarkai iri-iri game da ita ba a irin wannan yanayi ba”

Hawayen da ya zubo masa ya goge, tuni zuciyar Iya ta karye don zata iya ƙirga sau nawa taga hawayen mijin nata saboda ba ƙaramin abu ne zai taɓa zuciyar gwarzon mijin ta ba.
“Shikenan Ni kam duk hukuncin da ka yanke zanyi maraba da shi, fatan mu bai wuce samar wa jikar mu ɗaya tilo salama a rayuwar ta ba. Saboda haka sai a fara shirye-shiryen tafiyar ammah ina ne za' kai ta?”
Iya ta jefawa Baffi Tambayar.
“Can wani gari ne wai Sakwa, akwai makarantar kwana to can za'a kai ta”

Cikin sanyin guiwa Iya da Baffi suka gama hirar su daga ƙarshe suka tsaya kan kaiwa Ƴar Iya makaranta.

A daren Iya ta siyo sabulun wanka da kuma alimun har da soda da kanwa...ta haɗo da dutsin kaushi. Bayan ta siyo bata wuce gida ba sai da ta nemo Ƴar Iya cikin ƙauyen suka dawo.

Kallon tuhuma Ƴar Iya ke bin Iya da shi tana ƙara wari idanuwan ta waje.
“Lafiya Iya kika ɗauko ni ko dai wani abu ya samu ne”
Murmushi Iya tayi tace
“Jika ta kuma Shalele na birni nake so kije, shiyasa na bi kasuwa na siyo kayan gyara ko baki son zuwa birnin?”
Caraf tace
“Tab ɗijam, Aradu ina son birni Iya, baki ganin irin kayan da suke sakawa ga ginin su masu kyau ba irin bukkokin mu ba”

Ta faɗa tare da nuna bukkokin su da yatsa tana yamutsa fuska. Cikin zumuɗi Iya tace
“Toh ke a ina kika san birni ke da iyakar ki ƙauyukan kusa da mu ne”
Kallon baki da wayo ta jefi iya da shi tana banka mata harara tace
“Kiji Iyar nan, toh bari kiji in gaya miki a gidan kallo ne a can Zubo, idan naje sai na laɓe ina kalla...Aradu Iya kin ga wasu kyawawan samari kuwa?”

Murmushi Iya tayi ganin ba zasu samu matsala da shalelen ta ba tace
“Toh ai kema zaki zama irinsu musamman in Kika je kika yi karatun boko”
“Miye kuma boka Iya, Ni ba zan yi tsafi ba” ƴar dariya iya tayi tace
“Bokoooo nace ba boka ba”
Ganin Iya na mata dariya yasa ta ɓata fuska tare da miƙewa zata fice, kamota iya tayi tana faɗin
“Yi haƙuri shalelen Iya, boko shine karatun Ƴan birnin, kuma tunda suna burge ki ai zaki yi shi ko?”
Kai ta gyaɗa tunda ita yau ta fara jin kalmar boko a rayuwar ta.
Chapter 7 · 0% Book details