Sashe 9
Yar Caskale Part 1 Complete Hausa Novel.doc · about 8 min read
K'asa-k'asa ta amsa Masa sallamar,kun dai gane, irin kunyar Nan ta amaren asali,shikuwa malam kallon gefen ido yakeyi Mata,Yana son ya gano ta fuskar dazai fi samun nasara wajen aiwatar da kudirinsa.Ganin yanayin zaman datayi yasashi murmushi a zuciyarsa,aikuwa ya tattaro duk karfinsa ya had'o tun daga kuruciya zuwa samartaka da tsufa, ya daddage ya tuma tsalle ji kake timmm! Ya tima a cinyar laraba,amma Kuma sai me,ji yayi tana fad'in"subahanallahi malam lafiya? Ince dai ba tuntunbe kayi ba".Ji yayi duk lakar jikinsa tayi sanyi, sakamakon duba da yakai ga hannun laraba yaganshi kwance bisa hannunta kamar ta dauke jariri,ashe lokacin Daya tuma d'in Nan a hannunta ya fad'a Wani zunzurutun takaici ne ya ziyarce shi,cike da jarumtar daukar fansa kuwa ya mik'e,ya k'ara buga uban tsalle wannan karon iya karfinsa,nan ma aka Kuma na d'azu sai ji yayi ta cafeshi tana yunkurin kwantar dashi gefen gado kamar wani danta takuma cewa"malam kwanta ka huta,Dan ba mamaki fa jirine ke d'ibarka,Kar kaje ka fadi kaji ciwo sannu kaji bari in kawo maka ruwa kasha"Dai-dai ta Gama kwantar dashi ta mike da kyar ta dauki kofin silba sabo fil ta nufi waje Dan kawo Masa ruwan. Tsabar takaicin rashin nasarar sa a Karo na biyu,Bai San lokacin Daya Kama fatar hannunsa ba ya gartsa wa kansa cizo,sannan ya saki ya matso kwallar takaici.Yana a Haka ya hango inuwarta tana shigowa,aikuwa sai ya yanke shawarar bin shawara ta uku,ya mike da sauri ya sakko,sai da ya tsaya Nan ma ya tattale kafafu kamar zaiyi dambe,sannan ya saita hanyar Yana jiran ta taho.Itako kanta tsaye ta nufo kofar Dan shigowa,bama ta lura da malam dake tsaye ba,ita dai kawai taga kamar wulgowar abu, kawai sai ta d'an kauce,aikuwa wata iriyar sufa malam yayi waishi a nufinshi ya sai ta Koda dantsen laraba ne ya karyata a kafada tunda yaga tana da makaran Kare Kai a cinya,shiyasa ya kawo wannan farmakin ita Kuma cikin rashin Sani ta kauce wannan sufar da yayi aikuwa ji kake kummm rakwacam,fuskar malam ta daki simintin tsakar dakin,yayin da jerin kwallayen da langunan da akayiwa laraba suka biyoshi suka danne........... *Dariyata nafara yi tun yanzu,Dan nasan comment din dazan gani cikina Saiya kusa k'ulle wa Dan dariya.To masoyana Allah yabarmu tare* _sai kun Kara hakuri da yanayin typing din sai a slow wlh abubuwa sunyi yawa kudai ku Kara hak'uri_ *Alakamin khady* *_'YAR CASKALE_* ( _Sanadin bakin uwa_) *N *KHADIJA USMAN* ( _Real Tame Gari_ ) ____________________________________ KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ _Ha'kik'a Naga zallar soyayya ga masoyana,nakuma gode da addu'ar ku, wadanda suka Sami zuwar min gaisuwa ma nagode muku sosai da sosai ************************* Ya ilahi! Laraba ta furta cikin siririyar muryarta da zata ja hankalin malam da ita.Da saurinta ta karaso tana me kokarin d'ago malam d'in,bayan ta kawar da tarin fantekun da suka rikito Masa,malam tsananin azaba da rad'ad'in dayake ji,sunma hanashi yinkurin yin komai.A haka Yana hi har laraba ta d'ago shi. Tozali tayi da bakin malam dake yoyon jini,gashi tashin farko bakin ya haye yayi suntum,hakan ba karamin daga hankalin laraba yayi ba.Cikin yanayin damuwa ta shiga fadin"na shiga uku malam tashi muje gurin sule me chemist Kar jininka ya k'are". Malam dayake jin garama ya mutu ya huta,Dan shikam wannan shekarar ya tabbatar a cikinta jarrabawar sa take, Yana Kuma da tabbacin guda uku ce,ta farko zuwan Maryam gidansa,na biyu auren laraba,na uku kuwa mutuwarsa ce,Dan Haka Yana jinta yai Mata banza ya kyaleta,illah kawai idan yaga zata tabashi Sai ya doke Mata hannu,hakan yasa ta fashe Masa da kuka. Ganin tana kuka ne yasashi cewa "Baki ma fara kuka ba tukun,Dan wallahi saina cika kudirina akanki".ganin bakin malam Yana rawa Kuma gashi Sam Bata fahimtar abinda take cewa yasata k'ara tsananta kukanta tace"nakuma shiga uku bayan wadda na shiga a baya,malam harshenka ya karye harka koma maganar gawa,wayyo Ni larabayye na mutu in malam ya mutu". Kallon ta yayi da sauri kafin jikinsa yafara mazari,kaddai laraba Mayya ce ta gano Masa mutuwar sa,shi Ina ma yataba Jin wani zance Wai na gawa,to kodai da gaske ne hasashen shi cewar mutuwa zaiyi,shiyasa har yafara warin gawa,shine Dan rashin hausa laraba tace Masa Wai zancen gawa.Da Gama wannan tunanin Nasa,Bai San lokacin Daya zabura ya makale laraba ba,wadda itama ta rik'e shi suka shiga rusa kuka,kukan da kowa da niyyar da tasa yake yinshi.Sun jima a Haka,inda laraba ta mike da kyar ta lalubo minsileta da tasa aka siyo Mata Dan tana shafawa a jikinta inda ke d'an Mata ciwo take shafawa saboda har yanzu gajiyar biki Bata Gama sakinta ba.Aikuwa jambaki tayiwa malam dashi,bayan tafi tudun leben ta shafeshi dashi,Wanda malam ya saduda yanzu badan Allah ba,Koda ya kalli laraba a kaikaice ya banka Mata harara kafin yace cikin zuciyarsa"Hummm ki gama wahalar ki yarinya,kwanton bauna zanyi Miki inta Miki kisan mimmike har saikin rame,duk wannan jikin naki wallahi saina maidashi kamar sillen kara" ya saki murmushi a zahiri,Wanda ya Kara kwab'e fuskar,laraba da karaf a idonta tace" sannu malam,kadaina Kuka haka,bari gobe da safe sai in dafa ruwa in gasa maka wurin sannu kaji mijina" Dammm! Kirjinsa ya buga,take yaji zuciyarsa tayi Masa d'aci,banda damuwa dayake ciki,daba abinda zai hana shi yiwa laraba d'an banzan Duka ya tattara ta a baro gobe yakaiwa iyayenta,amma yanzun ma Bari ya warke zai Rama ne. Laraba da kanta ta tallabi malam ta Dora Kan gado,sannan tajawo Masa bargo ta lullube abinta Dan taga Yana rawar sanyi.Shikuwa malam,sosai yaji dadin gadon, musamman da laushin katifa kirar zamani ta ratsashi,ga lallausan bargo da aka luntsume shi dashi,kawai sai yake Jin wani k'aramin nishadi,duk da kudirin dake ranshi na tarin daukar fansa.Laraba Bata Bari malam ya kwanta ba,Saida ta lalubo ciwo takwas ta bashi yasha, Bata San waya yadda shi ba ranar da aka kawota,da har zata jefa shi shara,sai Kuma ta bari dan gudun Kar a aiko cigiya,to gashi ma yayi Mata rana. Allah sarki baiwar Allah laraba,Sam kasa runtsawa tayi,tana kwance a katifar kasa,Amma ta zubawa malam Ido tana sharar kwallar tausayinsa.Duk abinda takeyi Yana kallonta sai Kuma yaji tabashi tausayi,Dan Haka ya rage yawan hukuncin da zaiyi mata,a Haka har bacci ya kwashe su. Tun asuba laraba tafarka danta d'ora ruwan zafi ta gasawa malam fuska kafin ya tafi masallaci.koda ta fito d'ibar ruwa,saita tarar gaba d'aya matan malam ba wadda randarta ke tsakar gidan,komai sun kwashe yau,hatta duwatsun girkin da sukeyi,bare Kuma azo maganar ice.Ashe dai Maryam tayi Mata dabara,da tace Mata jiya ta kawo a siyo Mata kananzir karta yadda ta dinga girki da ice,zatayi warin hayak'i,tunda ita 'yar gata ce,Kuma anyi Mata auren gata,to gara kawai ta nuna itama wata ce,kawai ta dinga girki a risho ta nunawa su baba salame ita wayayyiya ce.Shine ta bayar aka siyo Mata din ta zuba a rishon Dan dama da lagwani a jiki,Ashe zaiyi Mata amfanin kusa Dan a da ta dauka ba amfanin dazaiyi mata,duba da yadda taga tuwon gidan malam nada yawa,shiyasa,amma yanzu ta fuskanta ko a Dora ruwan zafi zai Mata mfani. Randarta ta ruwa ta bude ta debi ruwan ta shige d'aki.Cikin kankanin lokaci ta Gama dafa ruwan,ta tashi malam da kanta ta zuba ruwan a wata roba me Fadi,aikuwa cikin hikima da tattali ta shiga gasa malam,Wanda yake jinsa kamar jariri,saboda Jin sabuwar tarairaiyar dayake Samu,aikuwa sai a zuciyarsa tuni ya yanke shawarar karawa laraba tsawon Zama a gidan bayan yagama morewa.Haka ta gama gasa Masa,Kuma Alhamdillah yaji Dadi sosai,aikuwa a gida ma yayi sallar asuba,Dan Bai samu fita ba, Dan har yanzu kansa na Masa ciwo.Dan Haka Yana idar da sallar ya koma ya dada luntsume wa cikin katifar sa mahadi ka lotsa Tuni kuwa bacci yayi awon gaba dashi.Ita Kam laraba bata samu zarafin komawa ba,illa dauko kayan malam datayi Wanda jini ya bata,da kayanta da suka Baci lokacin data rungumeshi,ta zuba a bokiti,tana jiran gari ya ida wayewa a siyo Mata klin saita wanke su. Su kuwa su salame,kusan sa iya cewa cikinsu babu wadda tayi baccin kirki,kowacce ta so ta leko ta ga meke faruwa a dakin laraba,amma Sanin gidan gida ne mutane,yasa ba wadda ta fito Dan Kar taje a ganta,amma Kuma kowacce window da kofarta a hangame suka kwana.Lokacin da sukaji rakwacam din Nan k'arar zubowar kwanuka,kowacce matsuwa tayi taga meke faruwa amma sai suka dinga jiyo nishin malam,hakan ya Kara daga hankalinsu,a takaice dai ba wadda ta runtsa Dan suna son suga Taya za'a kashe arna(d'orawa Kai wahala). Da farko sun dauka kwashe ruwan da sukayi da Kuma itace da murhu sunyi nasara.Itako laraba wani dan gidan Zuwaira da taga zai fita da bokiti karami zai siyo Koko,shi ta bawa ya siyo Mata klin din. Kusan a tare matan malam suka fito tsakar gidan,yayin da kowacce ta shiga sabgar gabanta, amma kuma hankalinsu naga angaren akin Laraba,dan ganin me zai wakana.Itako Laraba bata ko bi takansu ba,tana son zuwa akin dasu Maryam ke kwana,amma Bata s dokar gidan ba,dan duk abin Laraba bata da abi'ar shiga shirgin daba nata ba,amma kuma kai inka shiga nata,tofa nanne ake kuturun bala'i,dan dan arar ka zatayi kamar uwar data haifeka. A gaban idonsu yaron yabata klin in ta shiga wanke kayan da shaddar ta da ta malam.Sai da ta gama ta shanya duk suna kallonta kowacce idonta ya sauka aka dabbaren jinin daya kama zanin Laraba ya i fita,aikuwa nan da nan zuciyar kowacce tayi ba irin,tare da cin alwashin cima malam mutunci idan ya fito. Shikuwa malam bai sami zarafin farkawa ba saida rana ta take,ya mi e da addu'a a bakinsa,yayin da yaga Laraba kwance tana bacci, ara mi a yayi da hamma,dan wata kafirar yunwa yake ji,ga kuma fuskarsa da gefen bakinsa daya hau,dan ma Laraba ta gasa masa jiya,ya kuma ji da in gashin,dan tanayi ne cike da salo,ga kuma wani amshi datake yi wallahi.Hararar ta ya shiga yi,a asan zuciyar sa yace ba amshi ba,saina gama zu amshin zan karairaya ki in ara dake gaba,ko ba komai ai na an more.Haka yasa kai ya fito waje,ya nufi akunan matan nasa.a zaune ya samesu,duk da suna zamani irin na kishi,amma hakan bai hana yau wani zumunci ulluwa a tsakaninsu ba. Koda yayi musu sallama ba wadda ta