← Book details Yar Caskale Part 1 Complete Hausa Novel.doc Local reading mode
READING PART 8 OF 34

Sashe 8

Yar Caskale Part 1 Complete Hausa Novel.doc · about 8 min read

idi na Shirin Kai duka,aikuwa caraf ta rike hannun Nasa,kamar ta samu gugguru ji kake rumus ta matseshi,Wanda yasa idi sakin ihun azaba.Zuwaira dake tsaye taga meke faruwa,da gaggawa ta shiga kad'a 'ya'yanta d'aki ta rufo har window duk da kuwa zafin da akeyi Bata bar musu ko kofar Shan iska ba.Ganin abinda ya faru ga idi yasa mamuda kallon salame yace,"Inna Wai dama zuri'ar gidan D'an lami k'ato baba ya d'auko?" Saida ta hadiye yawun takaici sannan tace"ai wadan Nan gara ma d'an lamin dasu,dubi fa yadda ta b'allamin hannun d'a kamar tasami karas,Dan Haka Kai dawo daga baya- baya tunda shi kaddara ta haushi ya had'u da mota k'irar bodi garin karambanin shi". Ganin yayar laraba tsaye tana huci yasa salame tahowa kamar marainiya tace"sannu Anty,ai Bai zaci Ku bane na dauka yaran da suketa lekowa ne Dan kartar kayan Amarya sunga sabon Abu,ashe kece cikin rashin Sani yakai Miki mazga" Ta fad'a tana karkarwa kamar wadda ruwa ya daka. "Itako yayar laraba cikin babbar muryarta tace"Ai na d'auka Hari ya kawo Mana dan anwa uwarsa kishiya zai kawo Mana wargi in Nuna Masa ko ni wacece". Cikin sauri salame tace" Haba shiya Isa,yaron da tun kafin zuwan wannan ranar shi kullum maganarsa d'aya umma laraba,har fad'i yakeyi yaushe wai za'a kawo musu ita Nan gidan shine fa nace Masa yau d'in nan,kin ganshi dayake ba girma saina jiki Wai yazo taryar Amarya,shine fa ya tsaya anan Yana korar yara ke Kuma kikayi Masa wannan cikin rashin Sani". "Hummm,ya kyauta" kawai tace,kafin ta sa Kai ta shige ta barsu anan,aikuwa kamar jira akeyi ta wuce Nan fa jama'ar kawo.amarya suka shigo duuuuu,wata cikin yayyen larabar itama batare data lura ba tabi takan idi dake kwance,garin zuwa gurinshi aka had'a da salame,Haka aka dinga bibbige su ana shigewa ciki,inda wasu ma takansu suke shigewa,tsabar azaba ma sun kasa ihun,yayin da mamuda tuni ya silala d'akin matarsa yayi luff. Cikin tsananin azaba salame ta tashi da kyar tana Kiran "idi tashi maza dokunan sun Gama wucewa".Da kyar ya bude idonshi ya kalleta kafin yace,"Inna har an Gama wasan sallar?"Kai dai tashi kawai Idi lallaba inkaika bangaren suwaiba ta gasama jikin ka". Haka suka rarrafa suka mike har zuwa bangaren matar idi itama Tasha dariya Jin sambatun da mijinta keyi. ********* A Haka aka jera kayan laraba,ko fentin Bai bushe ba,dakin kuwa yadau haramar warin fenti,Amma ko'a jikinta ,burinta a tafi a barta da malam d'inta,daga gefen dakinta kuwa aka kafa turken awakin ta kusan goma Sha biyu aka jeresu,kajima da akurkinsu aka taho,inda aka jera musu suma nasu gidajen har masu danyen goyo Maryam kuwa tana rike da fantekar kaji,taci taci har takai Mata Karo ,Dan Haka ta tafi dakinsu duk ta bawa 'yammatan da sukayi jugum-jugum suna ganin abinda ke faruwa.Kowacce Saida ta karba da aka Bata,sauran Maryam ta d'auka ta rike ta doshi dakin laraba dashi,inda laraba na hangota tajawo ta ta zauna kusa da ita,a takaice dai laraba ba wasu kawaye Maryam ce kawai,Dan auren kunsan na gaggawa ne.Kusan Zan iya cewa laraba ita ta Kori kusan mutanen da suka kawota,Haka dai kusan kowa ya watse aka barta da sauran yayyenta, fad'a suka yi mata akan ta rage wannan rawar Kan Kar malam ya rainata da sauran yaran gidan,Haka dai aka Gama Suma suka Kama gabansu,ko kallaon inda matan malam suke basuyi ba bare su Kai amarya kamar yadda akeyi bisa al'ada.An bar Amarya dai ita da Maryam inda suna fita tace Maryam ta Bata fantekar kajin Nan ta ajiyewa malam inya shigo saita bashi.Koda maryam ta Mika Mata fantekar kaji taga saura kad'an saiko ta shiga tambayar ta cikin masifa wayaci Naman da akayi Dan malam? ,Kai tsaye Maryam tace "ni ce",aikuwa a fusace Laraba ta yunkura tana fad'in,"kin San muhimmancin malam a gurina kuwa Zaki tab'a abinshi,to wallahi sai kin San kin ci Naman Nan" Murguda Baki maryam tayi sannan tace"Allah in Kika dakeni wallahi saina sa malam ya sakeki" Jagwab laraba ta koma ta zauna cikin marairai ce murya tace" waya ce Miki dukan ki zanyi,dama zaunar dake zanyi akan cinyata fa,amma tunda bakya so shikenan na Bari ,yi hakuri,inma Bata isheki ba cinye na bar Miki duka ma". Mika Mata k'aramar fantekar maryam tayi,sannan tace, "ah ah ungo ajiye Masa Ni na k'oshi tana kaiwa Nan ta juya tana fad'in " Anty laraba amaryar baba malam Saida safe" Wannan karon laraba Bata dakatar da ita ba,Dan dama so takeyi ta tafi ko malam d'inta ya shigo.amma harta gaji da jira ta bingire da bacci. ********** Shi kuwa malam yak'i zuwa dakin laraba ne Dan ciwon hannunsa,yafi son idan ya warke komai ma ayishi ta Kare,Dan wallahi Saiya karyata ya rantse,Hakan yasa har matansa ba Wanda yake shiga d'akin ta,duk yadau fushi dasu *_'YAR CASKALE_* ( _Sanadin bakin uwa_) *N *KHADIJA USMAN* ( _Real Tame Gari_ ) ____________________________________ KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ _Hak'ik'a ke d'in ta musamman ce,kamar yadda kike ta musamman a wajena, comment d'inki ya k'ayatar dani sosai nakuma ji Dad'i,tare da addu'ar Allah ya barmu tare.Wannan shafin sadaukarwa ne gareki Hafsat garkuwa besty na kiyi yadda kike so dashi kinji tawan_ ************************* Abu kamar Wasa,sai ga malam ya shafe tsawon kwanaki Bai ko lek'o cikin gidan ba,sai dai kawai ya aiko musu da abinda zasu d'an yi cefane,dayake ma kun San cefanen k'auye sauk'i gareshi.Dayake garar laraba duk kayan hatsi ne shiyasa ba wani kayan ta'bawa,hakan yasa dole matan gidan in sun dafa su bawa laraba nata,duk da salame dai na bayarwa ne kawai Dan gudun abinda zaije ya dawo.Itakam Zuwaira Dan tattalin lafiyarta ne,haka Kuma duk 'yan mata d'aliban malam suna zuwa gaisheta kullum,harda masu biyo Maryam a d'an tab'a hira,Dan Maryam kamar itace angon ma,laraba ba yadda batayi da ita akan ta zo su dinga kwana ba,amma tace bazata kwana ba,ita Maryam a cewarta indai ta kwana gado d'aya da laraba to kwananta ya k'are, Dan tasan juyi d'aya laraba zatayi sunanta ya Zama marigayiya Maryam.To a fannin 'ya'yan malam dai mamuda ma biyayya yakeyi shida matarsa da yaransa,hakama Idi,to itakam Zuwaira kadaran kadahan,dan harga Allah akwai tanadin datayiwa laraba,Dan saita zaneta ciki da bai d'inta,shiyasa bata nuna wani abu sosai.Itama salame hakan ne a ranta,dan haka haka tayi likimo itama. ******* Abu kamar Wasa,Saida malam ya shafe tsawon kwanaki bai ko leqo gidan ba,abin yayi matuk'ar damun laraba,inda tasami Maryam a tace taje tabawa malam hak'uri,aikuwa k'iri da muzu maryam sai tace bazata ba sai laraba tayi Mata d'anta malele,Haka zata zage tayi Mata ,inta fita saita dawo tace malam yace tayi hak'uri bak'i yayi ne,Haka kullum laraba ke siyawa malam kayan dad'i tace Maryam takai Masa,aikuwa Maryam tasamu abinda take so,tuni ta dinga cinye abubuwan tana zuwa ta tsarawa laraba kalamai, tace malam ne yace ta fad'a Mata,a haka har Saida 'yan guzirin kud'in da laraba tayo ya k'are,aikuwa ta aika Maryam gidan su.Da farko abar Laraba hanawa tayi,da Maryam ta dawo ta sanarwa laraba abinda Innarta tace,sai laraba tace taje tace Mata in bata bata ba zata dawo gidan wallahi tayi zamanta.Hakan da uwar taji jiki na b'ari ta dauko kud'i tabawa maryam tace takai Mata,gobe ma in sun k'are ta aiko,aikuwa Maryam tasami abin nema,kusan kullum saita je gidan su laraba tace a bata kud'i inji laraba ko ta dawo gida,ita Kuma uwar a 'yar ribar sana'ar da takeyi zata dauka ta bayar tana mita a zuciyarta.Maryam na fita zata tafi bakin kasuwa,itace cin ganda, ragadada, d'an bagalaje,cofe da acama,Kai duk dai kayan kwalama,gashi ta dinga wa laraba wayo tace ta dinga wa malam farfesun kaji kullum zai k'ara sont.Aikuwa ba b'ata lokaci laraba ta shiga kashin kajinta tana dirjewa malam Maryam na kwamushewa a cikinta. ******************************* *K'URUN KUS* Yau malam an warke sumul,Kuma yau tun safe Daya tashi yake k'ullawa da kwancewa ta hanyar dazai bi ya karya cinyar laraba,shin wane salo zaiyi Mata ya karyata a shammace,dan so yakeyi taji zafin daya zarce shi Wanda yasha.kasancewar baida lfy tsawon lokacin ba Wanda ya fita karatu,dama jira yakeyi Saiya warke rass ya rama karayar sa,sannan ya Kira uban kowacce ya zo ya d'auki 'yarshi.Ita Kuma Maryam Saiya tabbatar Daya Gama azabtar da ita ta yadda iyayenta ma said sun mance kamannin yadda suka haifeta,sai dai in sun dauko hotonta su tuna,sannan zaice Suzo su dauketa,ko yaje tasha yabada sakonta kawai a kaita gida.Kai Bari ma yakira su tun yanzu,dan a yau yake son ya kaddamar wa da Laraba ita Kuma Maryam gobe da safe,Dan Haka ya shiga lalaubar wayar d'ansa malam Garba,bayan ya d'aga ya sanar dashi ya sanar da mahaifin Maryam gobe Yana son ganinsa da gaggawa,Nan malam Garba ya amsa Masa da toh sannan suka gaisa,danshi baida labarin auren da mahaifin Nasa yayi. ***************************** Wanka sosai malam yasha,kafin ya baza turarensa irin nasu d'an d'uri mai kamshi.Kan Nan yasha aski ga Kuma gyaran fuska daya Sha,abin gwanin sha'awa.Dan ya kuntatawa matan nasa,bisa yadda suka ki yadda dashi a baya,suka dinga zuba Masa rashin mutunci,Dan Haka ya daura damarar ramawa shima. Kusan duk Wanda ke cikin gidan yau Kam ya San malam na cikin nishadi, inda ya tattara 'yan jikokinsa,ya raba musu alawa ya Kuma Basu sabulai yace su kaiwa iyayensu Mata,cikin Wanda ake kawo Masa yake ajiyewa. Sai da ya gama lekawa gaba Daya dakin matan nasa,Wanda dukansu Babu wadda yasami kyakykyawar tarba,in Banda ba'kak'en maganganu,shi dai murmushi kawai yayi ya fice Yana musu sallamar Saida safe. **** Tun shigowar malam Maryam tayi sauri taje ta sanar da laraba, kasancewar kowacce bandakinta a bayan d'akin ta yake, yasa laraba saurin tafiya tayi wanka,cikin sa'a kuwa harta Gama shiryawa ta bad'e jikinta da turarenta kala biyu,Habiba da balila ,aikuwa saita hau tashin kamshi ga kamshin da dakinta keyi irin na amare Tunda ya doso dakin ya had'e ranshi,dan so yakeyi ya aro rashin tausayi da rashin imani ko iya na yaune kawai ya gwada su Kan Laraba.Ita kuwa Laraba tana zaune gefen gadonta,yayin da taci adonta cikin shaddarta aikin wuta kalar lemon green light,sannan Tasha bakin mayafinta,abinka da bakin mutum,saita fito tayi dass da ita wallahi, musamman da bakin Nan yasha jambaki kalar anti daba,ga Kuma jagirarata data Sha da jar jagira abin dai zasshawa,kwaliyyarta kirar zamani.
Chapter 8 · 0% Book details