← Book details Yar Caskale Part 1 Complete Hausa Novel.doc Local reading mode
READING PART 12 OF 34

Sashe 12

Yar Caskale Part 1 Complete Hausa Novel.doc · about 8 min read

arba da Laraba ,a zuciyarta tana jinjina girma da udura irin ta Ubangiji,"Allah me halitta kenan" ta furta a zuciyarta,a fili ta shiga amsa gaisuwar da laraban keyi mata,bayan tayi musu nuni da gurin zama, Isma'il ma ya shiga gaisheta ta amsa mishi cikin sakin fuska kafin ta yun ura da niyyar mi ewa."Wash Allah "ta furta a hankali,Da sauri Maryam tace," Menene Anty?" Cije baki tayi kafin ta furta" Bakomai" ta arasa mi ewa da kyar ta je ta ebo musu ruwa.Nan ma da kyar ta zauna,duk umma na lura da motsin ta, amma saita kyale Ita kuwa Maryam sai hira take yiwa Isma'il tana tambayar shi ina 'yan layinsu,sannan ina su Rakiya? Nan take fa a mishi ai ita tama fasa zuwa madinan nan,dan ta tambayi su Hafsa (wa an da suke aki daya)suka ce mata ai ba'a zuwa Madina ta auye,nan suke fa a mata duk wanda taga an kawo shi nan,to kangararre ne,dan haka wayo aka mata dan a kawota nan in.Tunda taji haka tace itama saita nuna musu tanada wayo,badai ita za'a kai ba,to saita ce tafasa zuwa Madina a maida ta gida,kuma wallahi koya za'ai da ita bazata zauna ba. ************************ Tunda umma ta kalli Laraba ta fahimci inda matsalar take,dan koda take da iba gamai hankali inya lura zaiga yadda tafiyar ta ta sauya.Ganin da umma tayi maryam taja hannun Isma'il sun fice wai zasuyi sirri,nan tasamu damar kallon Laraba tace"Ni kam amarya in tambayeki Mana?" "To Innar Maryam" cewar Laraba dake rawar sanyin zazza i ka adan. "Mene ne ya jawo miki zazza i haka? Ko bakya kwana cikin gidan sauro ne?" "Ah ah,ai bama Musa sauro,kawai dai inaga dan....."sai kuma tayi shuru. Sosai Umma ta shiga nazarin ta,zuwa wani lokaci,sannan tace"kin gasa jikinki da ruwan zafi ne?"dan ta fahimci kamar abinda ya faru wannan ne na farko. Girgiza kai tayi a hankali tace"ah ah,dan ban san ma ana gasawa ba ai". Cike da tausayin ta,da kuma yaba tarbiyya irin ta yaran auye tayi,domin dai duk da ana kiransu da kidahumai to Gara hakan,dan yanzu wata wayewar da bu ewar idon basuyi ba. Kallon ta tayi sama da asa,taga yadda mazaunan nan suke,ta jinjina kai,to yanzu ya za'ayi a gasa wannan,dan ko bataga robar da zata auke Laraba ba,amma dai bari tasa a samo ta wankan jego ko zata yi,dan haka tace " a ina za'a samu baho irin babban nan na wankan jego?" Kanta a asa Laraba tace"ai inada shi,dan Innar mu ta siyomin tace wai mu fara tanadi ,robar tafi a wuya". "Tohhhh ! Umma ta fa a tana ri e ha a ,tare da mamakin abun,amma saita cewa Laraba ta auko robar.Haka ta mi e ta auko robar ta kawota gaban umma,umma ta shiga gya a kai a zuciyarta tana fa in"lallai wannan uwa tasan 'yarta dan robar ma kamar irar kamfani,dan kamar an auna larabar ne akayota fankaceciya.Mi ewa tayi tace" to ina madafin ku yake ?"a ora ruwan zafi". "Ai ni bana girki da ice Maryam ta hanani,sai da riho" Kallonta umma tayi tace au kema sunan mamanki Maryam kenan,lallai mama bata son 'yar nan tata tayi aurin haya i ko?" Murmushi Laraba ta sannan tace"Ah ah maryam fa 'yarki itace ta hanani girki da ice" "Wai kina nufin Maryam dai dana sani?" Gyada kai alamun ita. Dariyar takaici umman tayi,tabbas mai hali baya fasawa amma inba haka ba,yanzu Maryam yazatayi da wannan rushe shiyar idan ta tsokano ta,to a yadda take gani ko ita da Baban su Maryam in ai sai sunci aniyar su gurin ta,dayake ma da sau i dan taga akwai jituwa a tsakanin su,sai dai ta lura Laraba girman ne kawai ba wayo.Haka dai tasa Laraba ta kunna risho aka ora ruwan zafin. A ban akin Laraba umma ta ha a ruwan bayan takai robar,sannan ta ce Laraba ta tashi taje ta fa a mata yadda zatayi cikin hikima. Umma na zaune kusan minti goma taga laraban ta shigo akin kanta a du e.Umman ce ta kalleta tace "har kin gama gasa jikin naki?amma dai ba baki shiga ruwan nan da kyau ba,inba haka ba du-du-du mintinki nawa,dan haka maza ki auko bokitin a ara zuba wani,in kin tsaya son jiki kece da wahala,dan kar kiga mijinki tsoho,su maza kullum jinsu suke kamar sabbin yasa,dan haka maza mi o a ara wani ruwan". "Dama ba in shiga nayi ba ina zama ne sai robar ta fashe" "Ta fashe fa kikace?"umma ta fa a tana zaro ido waje alamin khady* *YAR CASKALE* ( _sanadin bakin uwa_ ) *NA* *KHADIJA USMAN* _Real Tame gari_ *____________________________________* AINUWA WRITERS ASSOCIATION* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* "Oh ni Huwaila,tunda roba ta fashe ya zamuyi? Gashi dai ba abin a samo daro ba ya au zafi duk kibi ki one,garin neman gira kuma a zo a rasa ido,ya muka iya,kawai auko butar ki babba a zuba ruwan ki kama ruwa,gashin dama ai shine dai-dai tunda muna son ruwan ya shiga ciki ya gasa miki ciwon,to kodai aramin tiyo zamu samu a zira a bakin botar sai kema kisa ko ruwan zai shiga? Kai nan ma ba dabara bace,kinga kawai kawo butar a zuba kar ruwan ya one". Ita dai Laraba kanta a sunkuye Batace komai ba,har Sai da akace ta mi o buta ta shiga ta auko.Sai da umma ta ha a mata ruwan ta sanar da ita yadda za tai sannan ta bata ta nufi ban dakin.Ita kam umma al'ajabi take tayi,a haka har larabar ta kuma dawowa ta ha a mata wani ruwan ta ara watsawa ********************** Suna nan zaune ba wata hira suke ba a tsakaninsu,sai ga malam ya aiko da Isma'il da kayan miya da ledar taliya, kasancewar yasan su salame sun koyo azzalumin rashin mutunci,yasan bazasu bawa uwar albarka koda ruwa ba.Duk yadda Laraba take ji,haka ta daure ta tashi ta ora musu taliyar,maman Maryam ta so ta bari amma tace zata iya.Koda ta kammala a kwano mai kyau nan ma aka zubawa malam,suma Baban Maryam nasu daban aka zuba musu shida malam Garba.Maryam kam atan dabo tayi,sai da kowa yaci ya oshi sannan ta dawo gidan.Isma'il ya gama cin abinci kenan,ya ago ya kalleta ganin ta fa akin a guje ko sallama babu tana haki"Ke Maryam shi ne kika gudu kika barni kin san ban san gari ba ko?, Badan gidan nan bai da wuyar ganewa ba ai da na ata". Humm yaya Isma'il ai dan baka san ina naje bane shi yasa,da ko cewa nayi kazo muje bazaka ba,Anty Laraba ai kin san gidan su maraba da wari ko?" "Eh mana gidansu Iro mahaukaci". "Yauwa can,to dama rannan ne fa da na je ta wajen layin,kin san wai aureshi ake yi,ni ban sani ba sai naga an aureshi jikin bishiya, ina zuwa nace mishi sannu yaya,sai naji yace min yauwa,nace laifin me kayiwa me gari yasa aka aureka?sai yace min babu komai,tsabar zalunci ne,shine nace masa idan na kwance ka nawa zaka bani? Shine yacemin biyar,Nikuwa na kwance shi,ina kwance shi kuwa ya ri e Ni,yaita zabgamin igiyar nan,da kyar aka kwaceni,shine ban fa a wa kowa ba nace saina rama,dana san yau zan tafi shine nace nasami bulalar malam atuwar nan dayace yana dukan masu kunnen ashi da ita na oye,yauma ina zuwa na tarar dashi a aure, na kuma cewa in kwance ka? Yace "eh" na ce,idan na kwance ka nawa zaka bani? Yace ari,shi ne nace masa Ni kuma zan baka ari biyu kana so? Ya cemin "eh" shin Ni kuwa na fito da bulalata na shiga zabga masa,Allah yau ba kalar kukan da Iro baiyi ba,da farko ba wanda ya fito sai daga baya baban su kandala ya fito shi ne ya ganni ya biyo ni,wallahi da kyar na sha" ta ara sa maganar tana mayar da numfashin gudun datayi. "Na shiga uku na lalace! Dama har yanzu Maryam baki daina halin ba? Malam fa cewa yayi kin kintsu kin zama kamila mumina,ashe arya ne,ai ni dama nasan da kamar wuya wannan matsayaciyar ace cikin anin lokaci wai ta nutsu,to wallahi yau sai dai abin ya are akanki,mahaukacin da kika tsokano abin sai dai ya tsaya akan ke da kika jawo,ni kinga ma tafiyata, in an gama lallasa ki a kawomin ke nayi jinya,'yar iska kawai". Laraba dake tsaye jin abinda umma ke fa i,dan haka ta tattaro jarabar ta ta da ta can tace"Ai wallahi indai ina nan ba wanda ya isa ya ta a maryam,ba dai Iro bane kawai,to yazo ni zan lallasa shi,Ni na ma warke,Maryam jeki ki ara tsokano shi,yazo wallahi saina ci hancin babarsa". "Oh Ni Huwaila ! Nikam naga abinda yafi arfina, ah kice malam mazahabar caskale ya kawo ki bawai ki shiryu ba,kidai ara tamba ewa da lalacewa,dan haka tashi maza gara ma mu koma gidan nasan yadda zanyi ki daina wannan hatsabibancin,tunda gashi har da masu irar katafila ke tare miki fa a,ba dole abu yaci gaba ba tunda kunsa zalunci a harkar, kije ki tsokano ananan iba,ita kuma ta marka e miki su,to kinga tashi maza musan nayi". Haka t kama hannun Maryam tana fa in taso 'yar jaraba ai banga ta zama ba tunda kika tsokano motsatstse". "To ai ban auki jakata ba umma" "Ba bu ata ki barwa wasu almajiran ita,tunda baza'a rasa masu bu ata ba". "Dan Allah Innar Maryam ki barta karki tafi da ita kinga itace awata,kuma ita ke bani shawara a komai,na rantse ki kyaleta duk wanda ta tsokano Ni zan tare mata". Numfashin takaici umma taja sannan tace,"kice Maryam ba koyon tarbiyya aka kawo ki ba kawai an kawoki koyon CASKALE,to wallahi bada ni ba,gara ki koma gabana duk abinda zakiyi kiyi shi da a gaban idona". Da matsiyacin gudu sukaga malam ya shigo,yayin da ya buga wani uban tsalle ya ketare kan Maryam ya afka akin Laraba ji kake bamm ya banko ofar.Salame da Zuwaira na zaune kofar daku nan su su na aikowa su Laraba harara a fakaice dan suna jin duk abinda suke fa a.laraba ta bu e baki da niyyar tambayar malam sai ji tayi anyi ciki da ita amma bata fa i ba sai dai ta motsa daga inda ta ke.Malam Garba ne da baban
Chapter 12 · 0% Book details