Sashe 33
Yar Caskale Part 1 Complete Hausa Novel.doc · about 8 min read
Washe gari ma daya koma gurin Maryam irin na jiyan ne ya kuma faruwa,dan da yamma yaje danta ganshi sosai a cewarshi. Shi kunyar Maryam har mamaki take bashi,yana tunanin dama a wannan zamanin akwai mace mai kunya haka,sai dai abinda bai sani ba,duk rashin ji irin na mace wata tanada kunya a wani angaren,kuma hakan bai rasa nasaba da rashin sabawar da tayi na tsayawa da maza,dan ita dai Maryam bata ta a saurayi ba,kuma wannan shine karo na farko data ta a jin son wanda yace yana sonta. Dayake Abbas mutum ne daba ruwanshi,kuma baida wuyar sabo,dayake yanada barkwanci shiyasa nan da nan yayiwa Maryam wayo,danya lura itama akwai zance,kawai kunya ke hanata maganar da sakewa,hakan yasa ya dinga ribatar ta harta dan fara sakin jiki dashi ta shagala,nan da nan kuwa ya shiga karantar da ita karatun soyayya,wanda yasa ta gane yadda malam da Laraba suka ji ...... alamin khady* *'YAR CASKALE* ( _Sanadin bakin uwa_ ) *NA* *KHADIJA USMAN* (Real ta maigari) *____________________________________* AINUWA RITER'S SSOCIATION ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* Cikin anin lokaci soyayya mai arfi ta shiga tsakanin Maryam da Abbas,wanda kowane angare ansan da batun har manya sun shiga maganar dan ansa ranar aure ma. Wata iriyar soyayya mai tsuma zuciyar wa anda ke yin ta,ita ke gudana tsakanin masoyan,tuni Maryam tayi nisa a karatun da Abbas ke koyar da ita. **************************** Biki na aratowa hakan yasa yau Maryam tana kwance bayan sun gama waya da Abbas wadda ta zame musu jiki yanzu,kusan kowanne lokaci yana ma ale da ita a waya,amma daya dawo gida yake kashe wayarshi,duk da tabizaron tasa wani lokacin bata dawo ba. Number Jazuli ta shiga nema amma bata samu ba,saita tuna a wayar umma ta ke, dan wannan wayar sabuwa ce fil Abbas ya kawo mata. Tashi tayi taje gurin umma ta kar o wayarta ta dawo ta kwanta tazo ta kuma kwanciya tana laluben number Jazuli. Bugu biyu kuwa ya auka yana fa "Hello". Saida ta an tashi zaune sannan tace"Salamu alaikum ya mijin mace biyu". Zaune yake a falo shi da su Ummu da Zulaiha suna cin abincin rana dan yau bai fita office ba,jin sunan data kirashi dashi yasashi fahimtar ko wacece,cikin mamaki da fa a fara'arsa kamar tana gabansa yace "Allah ya taimaki bokanya Maryam". Jin abinda ya kirata dashi yasata kyalkyalewa da dariya dan tasan yanzu yasan komai tunda taji ya kirata da wannan sunan. "Na'am sirinji kuma kifin gwangwanin wata ya keke?" Saida ya kalli gefen Zulaiha wadda ta kafeshi da ido jin sunan daya ambata,kawar da kanshi yayi kafin yaci gaba da magana. "Allah ya taimaki bokanya,gaskiya anwata Allah yayi miki albarka kawai zance". Dariya tayi kafin tace"Amin yayana mijin mace biyu.Ya su Anty zulai? Fatan suna lafiya?" "Wallahi duk lafiyarsu alau,ya kuma bayan saduwa? Fatan kin isa lafiya,dan mutunci na ragagge ne, wallahi ban samu time in kira ba,saboda Zulaiha ta kwanta ciwo duk hankalina ba'a kwance yake ba, amma yanzu Alhamdulillah! Kafin na kira kawai sai kika rigani kira". Dariya maryam in ta kuma yi kafin tace"Allah ya bawa Anty lafiya.Ina Ummu amarya kuma?" "Kin ganta nan,ko ince kin gansu nan sun sani a gaba suna ta min ura wai sai naci abinci nayi iba". Dariya ce tazowa Maryam amma saita gimtse tace"ah lallai ai gara suyi maka haka,wannan abu kana tafiya kamar zaka karye ni kaina naso nabasu shawarar su baka maganin iba dan ka cicciko ko ramar nan ta ace". Yasan magana ta fa a mishi amma saiya shareta yaci gaba da tambayar ta bayan rabuwa nan dai suka gaisa harda Ummu.Itama Zulaiha kar a tayi suka gaisa, abin mamaki kuma dukansu babu wanda ya nuna mata wani abu,itama kawai saita bisu a haka suka gaisa harta sanar musu biki ya taho ,nan suka mata al awarin zasu zo da yardar Allah. *************************** _A gurguje_ Amarya Maryam tana ta shan gyara tako wane angare,yayin da umma tasa ake ta gyareta gyara na musamman ,dangi da an uwa duk sun fara hallara,wani abin burgewa harda su Anty laraban malam,duk da tana da aramin jaririnta hakan bai hanata zuwa bikin ba,malam kuma sai ranar aurin aure. A ranar kuma da yamma sai ga Zulaiha da Ummu harda Jazuli,wannan abu yayiwa Maryam da i,maimakon ma awaye sai su ukun suka zama awayenta Laraba,Ummu Kulsum, Zulaiha,a ranar akin da zasu kwana nan Maryam itama tace zata kwana,aikuwa ansha hira ba kama hannun yaro,anan Zulaiha ke bada labarin wuyar da tasha bayan tahowar Maryam,nan take sanar mata sai da ta kwanta asibiti,daga nan ta fahimci aikin bokaye wani lokacin duk bogi ne, yadda da abun zaisa kaga kamar kaine keda riba,daga baya ta fahimci ta tabka kuskure,shine ta nemi gafarar mijinta da kishiyarta, yanzu haka suna zaune abinsu lafiya basu da wata damuwa. Ansha dariya kuwa,nan itama Laraba ta hau bada labarin yadda akaita kaftawa da Maryam,har yadda akayi aurensu da malam. Nan ma dariyar suka dinga she awa,itama Ummu ta bada labarin aurensu da yadda Maryam tayi mata,nanma suka kafta dariya harda Maryam Kusan raba dare sukayi ana hira kafin kowa bacci ya kwashe shi.Ita ko Maryam ba batun bacci,domin kuwa Abbas ne ya kirata sukai ta soyewa abinsu,koda ta tambayeshi ina matarshi, yace ta tafi wajen gyaran jiki sai gobe zata dawo,haka suka ci gaba da hira har saida yaga asuba ta kusa sannan yace ta an kwanta kafin a kira sallah,nan sukayi sallama cike da kewar juna. ******************************* Yau aka aura auren Maryam shu'aibu tare da Abbas Ibrahim,akan sadaki Naira dubu ari cif, Alhamdulillah aurin aure yayi jama'a sai dai fatan Allah ya sanya alkhairi ya bada zaman lafiya. Kowanne bangare na cike da farin ciki,duk da ba wannan ne karo na farko da family in gidan Alhaji Ibrahim Abbas suka fara taron biki,domin gida ya cika dam da an uwa da abokan arziki. Itama Aina'u a nata angaren ta shirya nata bikin,sam bazaka ce ita zafafawa kishiya ba,da farko abin bai dameta ba,amma yau sai take jin abinda bata ta a ji ba akan Abbas in ba,kishinsa take ji matu a amma sai taketa arin dannewa dan kar wasu daga cikin an uwanta dake ganin ita taja aka mata kishiya su sami damar amayar da abinda ta fuskanci suna son fadi tun azu,shi yasa ta danne abun a ranta taketa sabgoginta kamar babu abinda ke damunta. Dayake Abbas bamai son bidi'a bane bai wani damu da ayi ba,akwai dai aramar liyafar da suka shirya a gidan in an kawo amarya. Yau shi kanshi baban Maryam yana cikin farin cikin da bazai misaltu ba,yayi godiya ga Allah har bai san adadi ba,yayiwa Maryam nasiha da zama da kowa lafiya,da umartar ta da tayiwa mijinta biyayya da kishiyarta.Duk abu irin na Maryam yau kam daban take,dan yadda take saita baka tausayi,tayi laushi tu us,abin har ba'a cewa komai. Yamma nayi jikinta ya ara sanyi,musamman da awayenta da an uwa suka dawo daga gurin jere,suka sanar da yadda gidan Maryam in ya tsaru,koda suka je da kayansu ma da baba ya taka muhimmiyar rawa akai sun tarar da shima angon ya zuba mata kaya masu kyau da tsari. angare biyu ne a gidan na Aina'u da ita Maryam in.kowacce akuna hu u ne a angaren ta falo biyu babba da arami.A babban Abbas ya zuba kujeru dan haka an uwa suka sa mata nata a falon arami,kayan gadon ma an sa mata a aya da in,abin gwanin ban sha'awa. Hankalin Maryam ya tashi jin motocin aukar amarya sun fara zuwa.Ummanta ta ame tana kuka mai ta a zuciya,itama umman haka,da kyar aka raba su aka sa Maryam taje tayi wanka,haka wata a cikin family in su ta zage tana zanawa maryam kwalliya,duk da anayi tana hawaye hakan bai hana an arasa ba. Tayi kyau na musamman,ga wani fitinannen amshi da take fitarwa,a haka aka kamata aka kaita har gaban ummanta da Abbanta suka kuma mata nasihar ha uri da rayuwar da zata shiga. Suma an uwa sun ora da nasu nasihohin,ita dai Maryam banda kuka ba abinda take,a haka Isma'il ma ya shigo sanye da farar shaddar shi dayasa da safe wajen aurin aure.Abin mamaki hannun Maryam ya kama kowa ya bishi da kallo,nan suka koma akin da iyayensu suke,nan ya tsugunna itama Maryam haka,cikin muryarsa data karye ya shiga ro on gafarar su. Dukansu jikinsu yayi sanyi,yayin da farin ciki ya cika zuciyar baba,ji yakeyi kamar mafarki yakeyi, Allah maji rokon bawa,tabbas yau Allah ya kar i addu'ar shi dayake yi kullum. Cikin farin ciki ya tashi ya kamo hannun Isma'il,cike da farin ciki ya shiga fa "Na yafe maka,na yafe muku yarana! Allah yayi muku albarka ya ara shiryar daku da dukkan an musulmi". Cike da farin ciki ya rungume shi,yayin da ya ara juyowa ga Maryam yaci gaba da sanya musu albarka. ***************************** An kawo amarya cikin gidanta lafiya,yayin da su Hajiya Laraba hankatama suna daga gaba.Kallon gida da aki kam ayyaba ansha kallo,duk da tsaruwa irin na gidansu Zulaiha,hakan bai hanasu zagewa su karewa ko ina kallo na gidan ba. Sai da aka fara biyawa da ita gidan iyayen mijin kafin a wuto da ita gidanta.Kamar yadda al'ada ta tanadar ankai ta angaren uwargida Aina'u,sun samu tarba ta mutunci daga kowane angare tare da fatan zaman lafiya . Zuwa goma kowa ya watse an bar Maryam ita ka ai.Jin ba kowa saita yaye lilli in fuskarta tana arewa akin kallo. Sosai yayi mata kyau,tana kuma jin farin cikin wai nan gidanta ne kuma kayan mallakinta ne. Duk da dare yayi haka wasu daga cikin an uwan Abbas suka zo suka sake shiryata ,tare da yi mata kyakkyawar kwalliya da kaya na musamman. Family house aka kuma nufa da ita, kasancewar dare ya fara yi shi yasa babu manya duk sun tafi su ora kafa unsu su huta,sai taron matasan mata da suka sha gayu wannan tana wane waccan. Gurin ya tsaru duk da acikin gida ne,wajen zaman da aka tanadar musu su uku aka nufa da ita,Ango Abbas da uwargida Aina'u ne zaune sai kujerar da babu kowa ita ke nuna alamun ta Maryam ce. Sai da aka zaunar da ita sannan ta samu zarafin sauke ajiyar zuciyar da har saida Abbas ya jiyota. an