Sashe 13
Yar Caskale Part 1 Complete Hausa Novel.doc · about 8 min read
Maryam suma a guje yayin da duk suka ru e suka shiga laluben inda zasu oye,daga can malam Garba ya shiga fa in"yo ta nan Shu'aibu,biyo nan angaren Inna salame".Suma su salame ganin mazan na gudu yasa suka shiga wurga ido dan ganin meke faruwa,aikuwa a guje malam Garba ya bangaje salame ,itama Zuwaira dake tsaye tana son ganin meke faruwa nan baban Maryam yayi gaba da ha arta,wadda saida tayi wani juyi kafin ta kifa saman randar ruwanta nan kuma kowanne ya shige aki ya banko batare da la'akarin ko wanne akin suka shiga ba. Da nufin yin bala'i Zuwaira ta ago,amma sai me.Ido biyu tayi da Iro daya shigo a guje yana muzurai hannunsa ri e da wata shar iyar adda tsirararta,na ya shiga raba ido.Ganin hakan da sukayi duka hankalinsu ya tashi, kafin kace me salame duk da tsufanta ta kama katanga ta haura,Zuwaira dayake tanada an jiki ka an ta mi a mata hannu itama tana fa in "yaya taimakamin nima na haye dan Allah kinji 'yar uwa". "Yau babu wannan zumuncin zuwai ,kowa yayi ta kansa ta ina na zama 'yar uwarki kedai nemi mafaka kinga nayi nan" Salame na kaiwa nan ta dira ta baya.Zuwaira na ganin hakan ta kama duru-duru,kawai saita nufi aton rumbun gidan ta bu e duk ayin dake cikin gero batayi tunani ba ta fa a ciki. Idon Iro ne ya sauka akan maryam,aikuwa ya zaburo yayo kanta,ta fice a miliyan ya rufa mata baya.Jikin Laraba ne yakama rawa,nan umma ta kalleta tace"ke kuma ultuwa me kika tsaya jira,ba ke kika ce duk wanda ya ta a Maryam zaki bashi kashin bala'i ba,to yau gata nan taje ta tsokano motsatstse sai ki je ki tare mata ai,dan wallahi Ni yanzu gida nayi ta taho daga baya tunda ita tajawa kanta,in Kuma kin kwatota ma tafi tare".Tana gama fa ar hakan ta nufi akin da taga mijinta ya shiga..... *Pls managed* alamin khady* *'YAR CASKALE* ( _Sanadin bakin uwa_) *Na* *KHADIJA USMAN* (Real tame gari) *____________________________________* AINUWA RITER'S SSOCIATION ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* Maigari ne zaune a gindin bishiya,tare da mutanensa ana gudanar da harkokin mulki irin nasu na masu sarauta. A guje Maryam ta tunkaro su,da yake gurin a kan kwana ne ya sa ita ce a kan gaba,dan haka ita suka fara hangowa.Ita in ma tsallen ta yi kamar yadda malam ya yi,ai kuwa sai ga ta ta tsallake maigari tare da tuge rawanin dake kansa. "Kaga irin marasa tarbiyya"cewar wani bafade da ya yi tozali da rantal in kan maigari.Maigari da ya kumbura yana shirin zartar da hukunci akan wannan mai babban laifin,kawai sai idonsa ya hasko masa Iro ya nufo su da adda tsirarar ta,kafin ma ya arasa magana tuni Iro ya iso inda suke,Hakan ya sa maigari fa owa daga kujerarsa.Iro ko ta kansa bai bi ba ya tsaya raba ido yana son ganin inda Maryam ta yi. Ya jima tsaye yana zare idanu,su kuwa duk gurin jikinsu mazari yake yi.Cikin tsawa Iro ya ce "waye ubanta a nan?" Maigari duk da bai san wa ake nufi ba amma haka ya daure yace cikin rawar murya"ai ita in shegiya ce" Zare ido Iro ya kuma yi,cikin wata tsawar yace" To waye baban babanta?" Wannan karon wani ne ya yi caraf ya ce "ai shima uban shege ne". "To shikenan tunda duk shegu ne,kai wannan" (ya nuna mai gari),kai ne babanta,kai kuma baban baban babanta".cewar Iro. " Mun ji mun amince mun kar i wannan kyautar" duka suka ha a baki. "To wa zan fara yiwa yankan rago a cikinku? Dan dama na ce tunda ta dakeni sai na yanka uwarta ko ubanta". Jin abin da ya ce ne ya sa su maigari ara tsurewa suka shiga ro onsa a kan ya yi ha uri.Ganin kamar suna da a tura shi ne ya sa maigari yin wata dabara domin ya zuwa yanzu ya fuskanci wadda ta tsokano Iro. "Kaga Iron Lantana ba dai kace harda uwarta ka ke nema ba?" "Eh in"Iro ya fa a yana zaro ido. "To maza shiga ciki,tana can ta goyata duk ka ha a ka yanka su gaba aya". Ai kuwa a guje Iro ya bi wata hanya ya shige wani gida.Su kuwa su maigari ba tare da ya sallami kowa ba suka hau kwasa a guje, shi ma bai damu ba ya tashi da sauri ya nufi bakin kasuwa ,a ransa yana me ayyana sai ya sa an nemo masa iyayen wannan yarinyar ya ci su ta ra. ************************* "Baban Isma'il bu ofar mana ni ce"cewar Umma dake tsaye tana bugun ofar akin da ta ga mijinta ya shiga. "Ke dai in kin ku uta ki yi ta kanki ,amma ni ba zan fito ba wallahi" ara bugawa ta yi ta ce "haba malam,yanzu dan abin kunya akin tsohuwar mutane ka shige,to ni dai wallahi na yi nan,dan ga shi nan a saman rufin akin da kake yana aye kwano zai shigo".ji kake kararaf ana kiciniyar bu ofar duka akunan,yayinda jin maganar da umma ta yi ya sa har malam Garba fitowa ba shiri. Dariya umma ta sa duk da halin da suke ciki ta ce" ba gashi yanzu kun fito ba,da ina ta magiya abu ya faskara,to ni dai malam na yi gaba sai kun taho dan wallahi ba zan zauna a auki rayuwa ta a garin da ba nawa ba,dan haka ni nayi nan" Ta arasa maganar tana nufar angaren Laraba dan ta auki jakarta. Turus suka yi dukansu, ganin Laraba tsaye tana ta rokon malam a kan ya bu ofar amma ya ce ba zai bu e ba.Maryam da tun azu tana ma ale a soro da sauri ta araso tana fa in"Baba malam yi sauri ka fito gobara a akinka na zaure" Ba shiri malam ya bu ofa har yana tuntu e dan sauri, saboda ajiyar sa da duk kadarar sa suna wannan akin, su ma jin abin da Maryam in ta ce ya sa suka rufawa malam baya.Zuwai dake cikin rumbu jin an ce wuta itama tayo tsalle ta fito ************************* Dukan su zaune suke an sanya Maryam a tsakiya sai raba idanu take.kowa huci yake yi musamman malam da ya zuwa yanzu duk wata martaba da Maryam ta samu a gurbin zuciyarsa ta goge,dan haka ya kalli su baban Maryam har da zabga musu harara a fakaice sannan ya ce" Da farko dai ba sai na ce komai ba game da wannan yarinyar, dan ku iyayenta kun fini sanin matsalarta sannan kuka yayibo ta kuka kawomin ni wato ga mai matattarar 'yan iska kangararru.Dan haka ina son kafin na yanke hukunci mai zafi a kanta inyi muku wata tambaya". Baban Maryam ne ya samu zarafin cewa " Allah gafarta malam ai mana afuwa dan Allah,dan wallahi zaman yarinyar nan a nan ya fi mana kwanciyar hankali,domin mu mun ga ci gaba a zaman nata". Malam ne ya ara muskuta zamansa sannan ya ce " tabbas kam an samu ci gaba da lalacewar ta ba,domin yarinyar nan tunda ta zo ban ta a ganin ta yi wani abun arzi i ba,kullum da kalar bala'in da za ta jawo". "To amma Abban Maryam ba kai kace min malam in ya fa a maka an samu ci gaba ba Maryam ta nutsu?" cewar maman Maryam. "Tabbas haka ya kirani ya fa amin". "To inaga lokacin aljanuna ma aryata sun hau kaina,dan haka nake wani zubin in suka zo yini nake bana cikin hayyacina,amma yanzu abu mafi sau i shi ne,ku tattara ta ku tafi da ita gida,nayi muku al awari daga nan zan dinga jifanta da addu'a, dan ita bata fa uwa asa banza,kuma ko ina akwai Allah". Maryam da da i ya kasheta ta ce" Baba malam Allah Ya yi maka albarka idan na tafi zan yi kewar ku wallahi,amma zan dinga mafarkin ku". Da sauri zuwai dake zaune ta kasa cewa komai tun azu saboda aikin susa da take yi ta ce" Bama sai kinyi mafarkin mu ba, mu ma dinga yin naki". "Ai ba ma wanda zai dinga yin mafarkin wani a tsakaninmu,sai kace wasu mayu,kunga ku tashi kai Garba kar dare yayi muku a hanya" cewar malam. Laraba dake zaune jikinta a sanyaye tace"to amma yalla ai inta tafi ni kuma da wa zan dinga hira kuma wazai dinga bani shawara?" Dariya zuwai ta sa tana fa in" abin dariya wai yaro ya tsinci ha ori,sai ki koma saida anta malele ko zaki kuma samun wata sha-sha-shar irinki" "Ni kike cewa sha-sha-sha?" "Ke in mana ,ko da wata ne bayan ke". Zuwaira ta fa a cike da masifa A harzu e kuwa Laraba ta hun ura,ba tare da tunani ko tsammani ba zuwai taji an fya e ta da kasa ai kuwa ta hau ihu,domin zauneta kawai Laraba ta yi ta fara murzar ta". Malam dai ya san arfi bazai kwaci zuwai ba,kawai sai ya kama ro on Laraba amma ta i ji.Ganin haka yasa Maryam matsowa ta ce" Allah Anty idan baki aga ta ba zansa Baba malam ya sake ki".Da sauri suka ga Laraba ta zame daga kan zuwai. Kowa da kallo ya bita,yayin da malam a ufule yace"ka ga irin tsiyar tata ko? Matata ma ita ke iko da ita bani ba tunda ita ce ta haifeni za ta sa na sake ta,to tun kafin ma lokaci ya ure ku tashi ku tafi,ke kuma in ta tafi kada ki sake jin maganata kiga idan ban sake ki in ba da gaske". Maryam kam bata ara bi takan kowa ba taje ta auko jakarta tana fa in"Baba zuwai sannu ki gasa jikinki sosai.Anty Laraba ni tafiya zanyi sai mun kuma zuwa,ina addu'a Allah yasa ki haifi 'yar kulullu ar yarinya me kama dake,itama ta dinga irkar mutane". Ba irin ha urin da baban Maryam bai bawa malam ba,amma ya ce bai san zance ba sai an tafi da maryam.Haka suka fito da ita da kayanta,yayinda mutan gidan dake nan duk suka rakosu bakin mota. alibai irin su maryam kuwa duk sunji ba da i da wannan tafiyar ta Maryam ,Laraba ko kuka ta kama yi amma ita Maryam ko a jikinta suka shige mota ita da Isma'il da mamanta,wadda