Sashe 6
Yar Caskale Part 1 Complete Hausa Novel.doc · about 8 min read
muddin baki Fadi gaskiyar abinda yake faruwa ba,Dan koma menene,to kece silar komai bakar munafuka" Hade fuska tayi jin ya kirata da munafuka,aikuwa saita kalli gefe tana gunguni. Nunata yayi da yatsa Yana fadin"wannan, wannan da gani uwarki tana zunduma ashar ta haifoki,Dan duk yaron da aka Haifa da Bismillah,bazaiyi abinda kikayi ba,Ni ba'ama taba kawomin makurar kangararru ba sai ke,Dan Haka ko ki fadamin gaskiya ko in tattara ki in maida ki gurin ubanki,tunda ba Dole sai a kanki Zan Sami lada ba". Jin yace zai maidata gida in Bata Fadi gaskiya ba,yasata Fadi a zuciyata"aikuwa wallahi bazan Fadi giskiya ba,tunda in ban fada ba za'a kaini gida,inje inci uban ummita Dan na rantse saina daketa".kawai sai gani sukayi ta mike ta rike k'ugu tace "yehhhh! Wani takalmi dake kusa da malam ya rarumo zai jefamata malam nuhu yayi saurin karbewa ya shiga bawa malam hakuri,ita Kuma akace ta zauna. Bayan ta zauna malam ya Kara had'e Rai yace" Zaki fad'a kowa yaji gaskiyar zance kokuwa?" Gyara Zama tayi, tai Zaman rak'uma sannan tace Zan fad'a yanzu kowa yaji,idan Kuma nayi karya a tambayi Anty laraba".Duka matan malam da harara suka bi laraba,sannan sukace "yauwa 'yar albarka yarinyar kirki Mai gadon fadan gaskiya,maza fad'i a gaban kowa yaji abin kunyar da malam yayi,Dan mun San bazaki yi Masa karya ba" K'ara muskutawa tayi sannan tace" dama um rannan ne da malam ya kirani yace Wai babana yace baida kudin dazai aikomin,amma shi ba matsala in Ina bukatar wani Abu in tambayeshi,sai nace Masa to Zan dinga tambayar ku in baya Nan,shine yace Wai ah'ah kada na tambayeku bazaku bani ba ko na tambayeku Dan son kudi Ne daku,shine na tashi Zan tafi yakirawo ni yace Wai idan nasan wata 'yar bazawara k'atuwa a garinmu inyi Masa kwatance zaije,Dan ya gaji da ganinku a bushe,shine fa nace Masa Ni duk wadanda na Sani a garinmu sirara ne,shine yace na tafi.To bayan kwana biyu sai ya kirani yace Ina zani nace Masa gun laraba inci danmalele,shine yace dama Yana nemana zai aikeni gurinta,Wai idan naje ince yace Yana sonta,shine na fada Mata daga Nan ta amince take kawo Masa abinci kullum ko Anty laraba?" Ta nuya akalar tambayar ga laraba,wadda sanyin Dadi yasa Banda murmushi ba abinda take zubawa,Wanda inba ka k'ura ido ba bazaka fahimci ma bakin nata bude yake ba,Wai Kuma har tana murmushi.Jin tambayar da Maryam tayi Mata danta k'ara burge malam,Dan gani takeyi duk ya shirya hakan ne cikin salon soyayya,Dan Haka ta lankwashe harshe da kashe murya tace"gaskiya ne,shiyasa ma nake sa masa onga a dukkan abincin da nake yimasa,danya cemin Yana son onga". Wannan karon kam malam ashar din gaske ya lailayo ya mike su malam nuhu suka rik'eshi Nan ko ya shiga fizge-fizge Yana son kwacewa,Dan shima ji yakeyi kamar ya kashe Maryam koya huta,Dan Haka ya shiga fadin"ku sakeni ala gafarta,ku barni in kakkarya yarinyar Nan inkira iyayenta Suzo su dauki gawar ta,Anya ma kuwa wannan yarinyar mutum ce,inko mutum ce da ganinta ba yarinya bace wallahi rikakkiyar wada ce kirar da can,Dan mu yaranmu na Nan Basu Isa su wassafa wadannan zantukan data fad'a ba".Yana kokarin Kara fizgewa sukaji hayaniyar mata duk kowa ya juya ga kallon bangaren da suka ji,suna jiran masu shigowa. Wata kyamu shasshiyar tsohuwace ta daddage ta rangada guda tana sannan tace"Alhamdillah yau nagodewa Allah Daya nunamin wannan ranar,jikata zata amarce,Dama nayi alkawari Ni zanyi Mata gara,Dan tunda laraba ta Fara girma nake tarin kayan gararta,Dan so nake duk mijin Daya aureta yasan ya auri 'yar gata,yanzu uwatata ta aikemin laraba tayi miji Kuma mijinma na gwadawa sa'a wato malam Shu'aibu Mai abin mamaki,Dan Haka muka tattaro duk kayanta gasu Nan mun kawo,inya so tayi zamanta har zuwa ranar da za'a daura aure,kaga kafin ranar ma tasaba da matan ka an k'ulla zumunci,in Kuma yanzu kake bukatar a daura mu ashirye muke" ta karasa tana Kara rangada uwar gud'a,wadda tasa duka matan malam hasala suka juya suka kalli malam,Sai dai me? Leme suka ga malam Dan tun maganar tsohuwa ta farko ya sulale ya Suma,nanko laraba ta tare kayanta,yanzu Haka ma kansa Yana cinyar ta tana yarfa hannu da matso kwalla......... *Gareku team laraba* *Team Maryam* *Team matan malam* _A kafta_ *KU bani comment kuga posting,KU hanani kuga d'an Karen dankarewa* _mura nakeyi,irin Mai gigita mutum din Nan shiyasa na kasa katabus_ *Alakamin khady* *_'YAR CASKALE_* ( _Sanadin bakin uwa_) *N *KHADIJA USMAN* ( _Real Tame Gari_ ) ____________________________________ KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ _wallahi jiya da yau na Kuma Shan dariya,Naga alamar akwai masu halartar bikin malam da laraba_ Masha Allah Ina yinku fans Dina fiye da yadda ma kuke yina ************************* "Yau na shiga uku Ni salame,me Zan gani haka? Dama idan kaje zance akan katifar gargajiya ake d'oraka,wayyo ni Allah dauki Raina na huta da ganin wannan abin kunyar,ga 'ya'ya ga jikoki amma malam nashe-nashe akan cinyar mace Ku tayani gani jama'ar musulmi".ta karasa maganar tana d'ora hannu aka tare da razga sabon kuka.Itama zuwairar nata jidalin ta Fara da Kuka,Nan ko jama'a suka Sami abin kallo hatta 'yan kawo gara. Kukan laraba ne ya k'ara jawo hankalin kaka tace"mun shiga uku,daga maganar aure sai takaba,aikuwa Koda malam ya mutu laraba takaba tahau kanki Dan sai kinyi Masa kin Sami wannan ladan".Jin an ambaci malam zai mutu yasa laraba canyarewa da kuka,Wanda yayi sanadiyar farfadowar malam,Dan ji yayi kamar an busa Masa usur a kunne.Wata kyakykyawar mik'a yayi,danshi ya d'auka duk abinda ya faru mafarki ne,jin kansa a lallausan filo yasa ya dad'a bankarewa Yana addu'ar tashi daga bacci,tare da wage Baki Yana hamma yasa hannu ya rufe Baki Yana shirin mikewa idonsa ya sauka Kan Zuwaira dake huci.Ganin hakan ne yasa yafara karewa kowa kallo Dan tabbatar daba mafarki yakeba.k'okarin ja baya yakeyi yaji ya dunguri abu da sauri ya juya aikuwa sai ji yayi laraba tace, "Alhamdillah gishirin zuciyata Allah ya karbi addu'a ta Dana dinga yi cikin zuciyata,wallahi malam daka mutu yau Nima mutuwar zanyi" ta k'arasa maganar tana marmari da ido alamun kuka. Maryam dake gefe tayi caraf tace"in Allah ya yarda ma bazaku mutu ba saikun haifi Yara 'yan lukutaye inta taba musu kumatu ana Mana hoto a irin wayar babana".Wata irin fyaud'a malam yakaiwa Maryam Yana daga zaune,aikuwa ta goce ya maki kasa,a zuciye ya shiga fad'in"wallahi Maryam idan Kika shiga hannuna sainayi gunduwa-gunduwa dake" Tana dariyar shakiyanci tace"kaga ko sai ayi miyar biki Dani,ransa ne ya Kuma hasala ya k'ara yunkurawa Yana fad'in" wannan wadar yarinyar kisan gilla shi yafi dacewa dake a halin yanzu". "Haba masoyi"yaji laraba tace, kalmar data sashi makalewa jikin bango,itako tana matsowa tace"Ni bana son kayiwa Maryam komai,dan 'yar arziki ce,Ina sonta,in munyi aure ma gurina zata dawo da Zama ko darling?"ai Duka muatanen gurin kowa baisan sanda ya rungume Dan uwansa ba Jin kalmar da laraba ta Kira malam da ita.Shiko malam tsayuwar da tayi akansa ne Saiya ke ganin kamar giwa ce tayi Masa rumfa,Dan son ta kauce ya shiga furta"kwarai kuwa ai gurinki zata zauna" Jin dadin kalaman malam yasa laraba muskutawa ta zauna a gefen sa batasan da hannun malam a gurin ba,Dan inda ta yanka zata zauna ta dauka bazata kusanta kwarai dashi ba,ai kuwa ji kake kurusssss hannun malam yayi k'ara yayin da malam ya kwalla wata siririyar k'ara,itako Laraba Fadi take,"oh Kunga na zauna akan Kara ban lura dashi ba",ta fada tana muskutawa gefe Dan Jaye Karan,aikuwa tayi ido biyu da hannun malam Wanda malam din ya zuwa yanzu kwallar azaba ce kawai ke shatata,su kuwa mutane tunda hannun malam yace b'asss kowa ya zaro ido yakuma rasa bakin magana. Cikin kidimewa laraba ta yunkura ta tashi danta matso gun malam sai ji tayi yace"kina k'arasowa Ina tsine Miki albarka" ya k'arasa maganar Yana yiwa malam nuhu alama dasu zo su d'aga Masa hannun sa.Cak laraba ta tsaya takasa motsi,yayin da Kaka tace" kul 'yar Nan,danki samu albarka muka kawoki gidan nan,Dan Haka duk abinda yace kada kiyi to ki bari,Dan bama fatan kiyi zawarci,Dan Haka zauna Nan idan Nan yake son ganinki" aikuwa sai laraba ta koma ta zauna,yayin da duk ahlin gidan malam dama makotan gidan na sauran bangarori suka shigo,Dan Jin gudar da kakar laraba tayi,yasa sukazo Dan ganin meke faruwa,nan suka iske wannan lamari Suma suka tsaya kallon t.v ,Dan haka kowa ya Kama k'unshe tashi dariyar,Dan hatta matan malam Saida suka Dara wannan karon,duk da takaicin dake cin zuciyarsu. Inda Allah ya taimaka Malam labaran ya iya ire-iren wadan Nan gyaran shiya duba hannun malam ya tabbatar karaya ce,Nan yace Bari yaje ya kawo kayan gyara.sam malam ma yarasa me zai yi, yau dayasan inda zaiga 'yan Boko Haram ,ba abinda zai hana Bai damka musu Maryam sunyi gaba da ita ba,inyaso yacewa ubanta ta gudu,Yana wannan tunanin ya juya ya kalli barayin da laraba take,yaga yadda ta kwabe fuska kamar taci sabulu,sai Wani kyafkyafta ido takeyi,Dan tunda taji Wai tajiwa malam d'inta ciwo duk hankalin ta ya tashi.dan Haka ta kwab'e fuska tana matsar kwalla. Koda akazo ana gyaran,Saida aka Kori yara,Dan malam sosai ya zage Yana ihu,Haka itama laraba kukan takeyi iya yinta,su kuwa matan malam Allah ya k'ara kawai sukeyi,itako Maryam tana daga gefe Banda dariya ba abinda take yiwa malam,inya d'an bud'e ido ya ganta,Saiya yunk'ura da niyyar maketa sai rik'eshi,da Haka har aka Gama gyaran,yayin da dangin laraba sukayi jugum-jugum Wanda hakan ke k'ara sa jinin malam hawa,amma Kuma idan yakai duba ga tarin buhunnan da aka shigo dasu,Saiya ji Kuma labari na neman sauyawa.Haka dai aka zauna shiru. Ganin la'asar tayi Kuma lokacin sallah yayi yasa masu yi suka yunk'ura da niyyar yi,amma matan malam duk suka tattare butocinsu da Kuma kayan ruwansu,suka ce babu Mai tab'a musu.Hakan yasa sauran matan gidan sukace Suzo bangaren su su yi ,amma Kaka tace ai sunfi k'arfin wulak'anci,yanzu zasu Nuna su ba matsiyata bane. A cikin wasu daga cikin wadanda suka rakota tace wata taje ta karbo musu butoci a gidansu Laraba,aikuwa ba'a wani jima ba sai jin tsayuwar mota sukayi a k'ofar gidan,Dan Haka cikin aka shiga kwada sallama Nan Kaka na Shirin yin magana saiga wadda ta tafi kawo butoci ta