← Book details Yar Caskale Part 1 Complete Hausa Novel.doc Local reading mode
READING PART 3 OF 34

Sashe 3

Yar Caskale Part 1 Complete Hausa Novel.doc · about 8 min read

ban manta ba saina dake tan". Haka malam Shu'aibu ya daure bakin buhun,bayan ya yanka mata wani gurin,yace tasa hancinta dai-dai gurin,Dan ta dinga Shan Iska,Nan ya kinkime ta zuwa bakin motar. Malam Garba ya bude musu gidan baya yasata, shima malam Shu'aibu bayan ya shiga,yayin da Huwaila ke tsaye tana musu sallama da addu'a Allah ya tsare,tana Jin ba Dadi rabuwa da 'yar tata,badan rashin lafiyar Isma'il ba da da ita za'a ,Amma tana musu fatan sauka lfy da Kuma fatan samun shiriyar 'yar tata,ance kowanne yaro da kalar kuruciyar sa,to ita Kam ta Maryam ta dabance. Jin an tada motar Maryam ta saito bakinta saitin bular buhun tace"mama ke bazaki filin jirgin ba?" "Eh Zan biyo ku daga baya kinji mairo ta,ta fada tana goge kwallar data zubo mata. Haka aka ja motar suka tafi suna fatan sauka lfy. **** Da yake tsakanin Kano da jigawa ba wani nisa,Koda Tara tayi sun shiga garin,a irin hakan ne,malama Garba ya kalli malam Shu'aibu yace,"Amma fa munyi sauri,duk da ba wani nisa tsakanin Kano da jigawa,amma gashi har mun iso". Yana shirin bashi amsa,Maryam ta saito bakinta tace,"wace jigawa Kuma? Badai wadda nakeji a state and capital ba? Kenan a filing jirgin jigawa zamu tashi?"duk ta jero wannan tambayar tana jiran amsa....... _to readers Ku fada Mata gaskiya mana *Gaskiya Naga ruwan comments jiya,na Kuma gode muku masoya Allah yakara kauna,Ku tayani addu'a Banda lfy wlh* *Alkalamin khady* *_YAR CASKALE_* ( _Sanadin bakin uwa_) .* ____________________________________ KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ Sai yanzu suka San sun tabka katobara na ambatar sunan garin da sukayi,Dan Haka dukansu suka kalli juna da ido kafin malam Garba yace,"wato malam Shu'aibu,Inka fahimci wani abu, shi zuwa madina a biyo ta jigawa sai Mai babban rabo,yanzu dai kaga sunan fa garinmu na asali shine bakada suna,amma yaran zamani suke kiranshi da Kano,bayan Kuma in zaka shekara cewa a kaika Kano bamai ganewa,inhar ka fita daga garin,sai dai kace a kaika kanoma,Kuma fa Inka sake mutum Bai gane ba kace ya kaika Kano to lamari ya b'aci,Dan gidan wannan mashahurin d'an yankan Kai za'a kaika wato d'an kano,dan Haka gara kawai kayi zamanka inda Allah ya ajiyeka". Murmushi malam Shu'aibu yayi,danya fahimci inda zancen ya dosa,Yana shirin yin magana suka k'araso karamin kauyen,kofar gidan malam Jafaru mahaifin malam Garba. Jama'ar garin sunyi murnar ganin malam Garba,Dan haka duk alamajiran malam suka shiga murnar ganin d'an malam d'in,dan ko ba komai Yana kawo musu tsarabar lemo da biredi,kun San dai k'auye,duk k'in ka da biredi ko baka ci,to idan kaje k'auye ka kwana biyu,wallahi saika yi marmarin biredi Tunda motar ta tsaya malam Shu'aibu ya zagaya ya kwance Maryam a buhu,wadda ya zuwa yanzu ta jik'e da zufa,aikuwa Yana bud'ewa ta Fara rarraba ido,Nan idonta ya sauka akan tarin yaran da suka kewaye su.Zaro ido tayi kafin tace,"baba yana ganni cikin ba'kak'en fata,ba dai ta filin jirgin k'auye zamu tafi ba?" Dariyar data bayyana hak'oransa ya yi ,sannan yace,"ai gurin bita muka kawoki,Kinga Yara can dayawa" yayi Mata nuni da tarin yaran dake zaune duk rike da alluna,sannan yaci gaba,"muna hanya aka fad'a Mana sai mun Fara kaiki gurin bita tukun,Dan haka muka kawoki anan in kin Gama haddace komai saiku wuce kawai,lokacin ma yarinyar ta k'ara girma ko?" Ya karasa maganar Yana shafa kanta,kafin ya kamo hannunta suka fito,yayin da suka doshi rumfar da malam Jafaru yake. **** Duk abinda yakamata ayi Kuma su Sani dangane da zaman Maryam anyi,Kuma Alhamdillah duk malam Shu'aibu ya gamsu,bayan sun gama ganawa akace a dauki jakar Maryam a shiga da ita ciki.Duk k'iriniya da rawar Kai da Kuma son ke ta hazo na Maryam Saida ta zubda kwalla da babanta zai tafi,bayan yayi Mata nasihan ta daina rashin ji da sauran k'iriniya,ta tsaya tayi haddarta Dan ta kasance a 'yan tashin farko.Haka suka rabu bayan ya bawa malam kud'i yace a dinga bata intana bukatar wani abun.Kuma itama ya zaro nera goma sabuwa fil ya Bata,hakan ya d'an sanyaya ranta. **** Bayan an shiga da kayan Maryam itama ta shiga gidan malam.Babban gida ne irin na k'auye Daya kunshi bangarori da dama,matan malam biyu,yayin da duk yaransa maza ne baida 'ya mace ko d'aya.D'akin da aka Kai kayan Maryam,d'akine da akayiwa kanta irin wadda akeyiwa almajirai maza,sai dai su abin birgewa harda katifunsu.kuma dakin duk da na kasa ne amma a lailaye yake da sumunti,Kuma an shimfida musu katon buhu,inda kusan duk Mai gata a cikinsu ita keda katifa,wasu Kuma bargo,wasu Kuma tabarmi,daki biyu ne irin hakan,yaran matasa ne 'yammata,sai Kuma irin su Maryam d'in,dan gaskiya kusan sune ma kanana. ***** Matan malam akwai iya salame itace uwar gida kasancewar mahaifiyar su malam Garba itace matarsa ta farko ta ladan noma Allah yayi Mata rasuwa da dadewa,a yanzu dai salame uwar gida itace yaranta duk manya maza,Dan malam Garba shi kadai ne mahaifiyar sa ta haifa.Sai matarsa ta biyu Zuwaira,ita ma yaranta duk mazan ne,amma kuma sune kanana,duk da ta daina haihuwa,autanta bazai wuce shekara 8 ba. Zaman gidan malam Garba shima zamane na kishi,irin kishin kauyen nan.sam matan Nan basuda mutunci yaran da aka kawo irin su Maryam,su keyi musu shara da wanke-wanke harda girki.Idan kaga suna haba-haba da yarinya,to sunsan 'yar masu dashi ce,iyayenta in sunzo suna musu abin hasafi,Kuma in an kawowa yarinya kayan dad'i suna sammasu. Tun daga kawo kayan Maryam da suka bude sukaga kayane na dangin irin namu ya ku bayi,Nan suka hau gatsine-gatsine,basuyi Mata wata tarbar mutunci ba. *****"************"****** A d'an wannan lokacin zamu iya cewa marayam ta sake,dan ba ruwanta da bakunta,sa kanta da tayi a zata keta hazo,yasa bata fara Nuna Hali ba,Kuma Bata Fara halartar karatun ba,tunda litinin aka kawota,malam yace ta huta zuwa asabar saita Fara daukar karatun. A iya wannan kwankin Maryam ta Fara fahimtar halin matan gidan,tazama mage Mai kwanciyar daukar Rai,saika rantse Bata San wani abu Wai shi rashin mutumci ba. Yau aka tashi a dakin su Maryam anyi sata,aikuwa Nan fa gida ya kacame aka shiga tone tonen kaya,dayake yarinyar da akawa sata,wata 'yar kaduna ce,Kuma 'yar masu dashi,sosai su Zuwaira suke karuwa da ita,hakan yasa sukafi kowa zakewa akan abin,nan ko suka shiga bincike kayan kowa,ganin Basu samu ba yasa salame tsayawa ta rike k'ugu tace" Ni fa gaskiya abin Nan akwai abin mamaki,tunda muke cikin almajiran malam babu Wanda yataba Mana sata,nidai inaga wannan yarinyar" ta nuna Maryam" inaga sata ta addabi jama'a da ita shiyasa suka dungumo ta suka kawota gun malam,Wanda shi kowacce tantariya a cewarsa zai iya da ita,to ai Sai ya zo yayi Mata kafi,tun kafin ta Gama damu". Dafe kirji Maryam tayi tare da zaro ido tace,"Ni d'in ce barauniyar ko wata?" Zuwaira ce tayi caraf tace,"uwar wace bakuwar zuwa da bamusan halinta ba inba ke ba". Hawaye Maryam tafara yi sannan tace" Ni d'in Nan 'yar Karamar yarinya Dani Ina Zan iya wani sata,Kuma ma idan nayi satar abinda kukace Ni da Banda aljihu Ina Zan boye,wallahi tunda kukaimin sharri da banyi ba ma nayi d'in". "Dan ubanki mu kike murgudawa Baki,sharri zami Miki ko me?" Maryam dai batace komai ba illah kuka data Fara yi, a zuciyarta tana jin ita Tama fasa zuwa makkan tunda akayi haka,gara azo a koma da ita gida tama yiwa ummita dukan datace zatayi Mata. Haka dai aka karaci tujarar aka gama,shi malam ma baisan abinda ke faruwa ba. ***** Ranar asabar kuwa kamar yadda Maryam taga kowa nayi itama Haka tayi,duk da ta tashi da kewar yayanta Isma'il da Kuma mamanta,tace ba yanzu zata tuna babanta ba,su din dai ta damu dasu da son gani,Dan tasan yanzu da umma ta lakada Mata duka yafi a kirga.Ina sonki ummana ta furta a hankali.Dayake duk kusan 'yammata ne shiyasa bamai bi takanta bare har ya tabota. Yau su Maryam an hallara a makarantar,rumfar malam ta cika,Yara da manya,dayake ya hada da yaran gari suna zuwa daukan karatun. Kamar a boko Haka malam ya dinga wa Maryam interview,bai samu komai ba,illah fatiha,Dan itama da kyar takaita,yayi mamaki kwarai,inda yasata ajin Yara aka Bata allo da aka rubuta basin mi'a ra,aka ce ta Fara da nan. Aji-aji abin nasu yake cikin tsari,Dan Haka ajin Yara aka kaita,duk da itama yarinyar ce,amma tafi son akaita cikin manya,aikuwa nan Saida ta bayyana a fuskarta Bata so ba. Tana zaune amma ba karatun take ba,wata yarinya dake bayanta,ta bude murya tace "malam ga wata Bata karatu". Aikuwa malam ya zaburo Yana fadin "wacece?" Nuna Maryam tayi,aikuwa ya tsulawa Maryam bulala,har Saida yayi Mata bulala biyar,Yana jaddada Mata Nan ba gurin Wasa bane.Kema dagas Maryam babu ko hawaye, aikuwa ta rasa me zatayi wa yarinyar ta huce,Nan ko ta dage ta gallara Mata mintsini,yarinya ko ta callara ihu,ko kafin malam ya juyo wata ta bude Baki da niyar Kai Kara ita data kusa da ita,aikuwa ta Maryam ta ankara,ta Kama kawunansu ta gwara,Suma ko kukan suka saka,Nan da Nan tahau rankwashin yaran da Kuma gwarawa wasu kawuna,kukansu ya karade ko'ina Wanda ya jawo hanakalin malam d'in,dama sauran wadanda ke karatu. Ganin malam yayo gurin da Dan ganin duk yaran sun rude yasa ta kwasa da gudu tayi cikin gida,Wanda tana shiga dai-dai salame ta gama miyar dumamen tuwo,Dan jiya miyar karewa tayi,shine malam yanzu ya Aiko yace a bashi dumame Dan hantsi yayi yunwa yakeji,shine salame gimbiya tace yadan dakata Babu Miya za'ai sabuwa,yace to a kada Masa miyar kubewa,aikuwa tana saukewa Maryam na shekowa,akuyar dake tsaye bakin danga ta zabura tayi ciki da miyar Maryam na bayanta,aikuwa har wani salo miyar ta bayar gurin zubewa ji kake lemmmmmmmm........ _nagode da addu'arku Alhamdillah,Ina sonku sosai fans,Naga comment dinku ya girgiza zuciyata,da yasa nayi Mana addu'ar Allah yakara kauna. *Alkalamin khady* *_'YAR CASKALE_* ( _Sanadin bakin uwa_) *N *KHADIJA USMAN* ( _Real Tame Gari_ ) ____________________________________ KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ "Kam balastin!" salame ta furta a fusace,hakan ko ya j awo hankalin Zuwaira dake d'aki tana magana da yaranta.Dukansu tsaye sukayi suna kallon maryam,wadda ta tsaya wuk'iiii tana kallon kowa.Ganin hakan yasa salame yo kanta tana fad'in"yau Banga shegen Daya Isa ya hanani cin uban yarinyar Nan
Chapter 3 · 0% Book details