Sashe 32
Yar Caskale Part 1 Complete Hausa Novel.doc · about 7 min read
lokacin Maryam keyin alwalar sallar la'asar yasa shi yimata fa an rashin yin Sallah akan lokaci,nan ta fa a masa aiki sukayi shiyasa ta makara yin sallar,ya fa a mata ta kiyaye nan gaba. **************************** Baki umma ta ri e cike da mamakin jin batun da baban Maryam in yazo da ita,cike da farin ciki ta kalleshi tace" kagani ko malam? Kaga ikon Allah ko? Da muna ta sauri da azar i ,gashi Allah ya kawo mata mijinta cikin ruwan sanyi,kuma ga yadda ka fa a malam daga ji yaron mutumin kirki ne". Cike da farin ciki ya kalli umma yace"ai Bama zaki tabbatar da hakan ba sai kinga dattijan waran da suka zo min,cike da kamala batare da ata lokaci ba suka nemawa ansu izinin fara zuwa zance gurin maryam,wallahi kwarjininsu yasa na amince dan naga dattako a tare dasu,dan haka ni na yarje musu yanzu ma Maryam in zaki kirawomin in mata bayani. Koda umma ta kirawo Maryam suka kora mata jawabi bata nuna damuwarta ba kamar wancan lokaci,dan haka suka shiga sa mata albarka.Tana fita nan ma tayi dariya tana yankewa kanta hukuncin abinda zata yiwa wannan in shima........... alamin khady* *'YAR CASKALE* ( _Sanadin bakin uwa_ ) *NA* *KHADIJA USMAN* (Real ta maigari) *____________________________________* AINUWA RITER'S SSOCIATION ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* A ranar baba ya sanar mata ba on zaizo,dan haka umma ta sata yin wanka da tilasta mata yin kwalliya ta musamman. Sosai tayi kyau duk da udirin dake cikin zuciyarta hakan bai hanata carka a kwalliyar da umma ta umarceta dayi ba,sai dai bayan ta gama kwalliyar ta auko aton hijabi tasa,wannan ma yana cikin shirinta. Sa on zuwanta ya riski su umma dan haka aka ara sanarwa da Maryam in yana waje yana jiranta.Tabarma umma tasa aka kai masa zauren gidan aka shimfi a masa tare da sa on Maryam in tana zuwa. *********** Da sallama Maryam in ta shiga zauren,yana zaune yana dannar waya yayin da hasken wayar ya haska kyakkyawar fuskarshi,wanda hakan yabawa Maryam in damar ganeshi,yayin da shi kuma ya amsa sallamar batare daya ago ba. Saida gaban Maryam ya fa i jin sassanya kuma kamilalliyar muryarshi. Jin har yanzu bata kuma magana ba kuma bata araso ta zauna ba ya ago yace" haba ranki ya da e,ko saina zo na kwanta kinbi ta kaina ne dan ki samu damar arasowa gimbiya ta". Kunyar da batasan tanada ita ba duk ta lullu eta,tunanin datazo dashi take ya fara canzawa. Ganin tayi shiru saima hijabinta data jawo ta rufe fuskarta yasashi tasowa,Sam bataji alamun takowarshi ba,illa jin da tayi amshin turarensa daya gauraye soron ya matso dab da ita,tana son bu e ido amma ta kasa, sakamakon makaman aikinta dake hannunta wanda data saki hannun suna iya fa owa asa asirinta ya tonu.Ganin batada niyyar bu e fuskar yasashi matso da fuskarshi dab da kunnenta cikin murya kamar ta mai yin ra a ya furta"ko banyi miki bane shiyasa bakya son kallon mummunar fuskata?" Nan ma shiru tayi illa kiciniyar janye jikinta da take sonyi dan matsawa baya,saboda yadda zuciyarta ke bugawa kamar zata fito waje. Zata iya cewa wannan ne karonta na farko data ta a jin wani abu dangane da a namiji,kuma wannan shine karo na farko data ta a tsayawa da wani namiji da sunan zance,dan Idi gurgu bata ma sashi a lissafinta. Ganin fa da gasken bawai zata bu e fuskar ba yace"shikenan bari na tafi tunda ko ba'a fa a ba alamu sun nuna ban samu kar uwa ba......" "Ah ah wallah......." Ta furta kalaman a guje,wanda sam bata shiryawa zuwansu ba illah jin fitarsu kawai da tayi. Ganin wannan kato arar da tayi yasa ta juya ta kwasa da gudu tayi cikin gida,nan kibiya ta fa o wato aya daga cikin kayan aikinta.Murmushi kawai ya saki tare da jin ta ara burgeshi,dan dama yayi al awarin bazai auri yarinyar da idonta ya bu e ba,kawai saiya auki kibiyar yana nazarin ko mai zata yi da ita oho.Sanin da yayi ba lallai ta dawo ba shima bai tsaya atawa kanshi lokaci ba ya fice a zauren cike da farin ciki. **************************** Alhaji Ibrahim Abbas Mainasara shine sunan mahaifinsa, an asalin asar Niger ne ,a wani gari mai suna damagaram,neman ku i ya kawo shi Nigeria kuma sai Allah yayi ana na zamanshi yake dan harya ha a iyali.Abbas shine aya wallin wal namiji ga mahaifinsa,domin Alhaji Mainasara yanada mata hu u cif,kuma kowacce tanada yaranta amma duk mata ne sai amaryarsa ce kawai mai suna zahra'u ta haifa masa a namiji,itama kuma daga nan haihuwar ta tsaya mata cak,sunan mahaifinsa yasa masa wato Abbas, hakan yasa duk gidan basa kiransa da sunansa hatta shi kanshi mahaifin nasa sai dai su kirashi da Alhaji baba. Zaman gidan Alhaji Ibrahim zamane mai tsabta cike da yalwataccen zaman lafiya,kowa na mutunta kowa,yaro yana girmama na gaba dashi,hakan yasa suka samu cikakkiyar tarbiyar da kowa ke sha'awar ha a zuriya dasu. Alhaji baba wato (Abbas ) ya taso da kulawa da kuma tarin soyayyar an uwa da kuma ta iyaye daga kowanne angare.Hakan yasa ya taso cikin shagwa a da gata,wani abun kam ko yayi ba'a kwa arsa,sai dai hakan baisa ya zamo mara tarbiyya ba. Alhaji Ibrahim an kasuwa ne shi sosai,shiyasa ya ora Abbas ma akan wannan harkar kuma Alhamdulillah an samu yadda ake so,dayake dama digiri insa biyu a fannin kasuwanci sai abin yazo da sau A yanzu haka Alhaji baba wato Abbas yanada mata guda aya da yarinyarsa guda aya daya sanya mata sunan mahaifiyarsa wato Fatima,amma suna kiranta da Aliyah,Abbas bayada niyyar ara aure a tsarinsa,domin yana zaman lafiya da matarsa amma a bisa dalilin barinta tayi rayuwarta yadda taga dama,domin a cewarta babu namijin da zai tauyeta wai dan yana aurenta.Sam matar Abbas batada kishin mijinta,dan in kaga yadda take barinsa ko yadda awayenta ke mu'amala dashi da sunan mijin awa sai abin ya baka mamaki,wannan abin ya an basu matsala a aurensu idan an duba yadda suke rayuwa cike da son juna,matsala ta biyu ga matar Abbas shine yawan fita,itadai ba ma'aikaciyar gwamnati ba,amma kullum bata rasa uzurin fita,kamar a dangin ta ne kawai ake biki ko suna,hakan yasa annen Abbas mata suka sa mata ina zaki biki,daga ina kike suna .Tun tana tambayar Abbas har takai sai dai ya dawo wataran ya tarar bata nan,yanzu ma harya saba,da farko abin baya damunsa,amma dayake yanzu suna da yarinya kuma gashi harta tasamma shekara biyar,sam bata samun kulawar data kamata,tun yana neman mafita ya samu ar aiki mai k ula da ita,duk babu wani dace,daga ballagaza sai kazama,hakan yasa ya gaji ya daina samo masu aikin yayiwa Aina'u magana akan ta tsaya ta lura da tarbiyyar arta,amma ta nuna itafa akan yarinyar bazata fasa fita ba,dama ya isheta a cewarta,saita auki yarinyar ta kaita gidansu,gashi dama tayi planning Wai sai Aliya ta shekara takwas za'ai mata kanwa ko ani.Dole ya ha ura suka ci gaba a haka,to yanzu kuma labari ya canza salo,domin idan dare yayi ya bu aci ha inshi sai tace ta gaji,yo ba dole ta gaji b tunda an wuni ana garari,koda ya nuna mata shifa zai ara aure gaskiya,sam bata nuna damuwarta akai ba,hakan ba aramin mamaki ya bashi ba,amma saiya shanye abunsa,Daga nan ya fara neman yarinyar da zai aura,amma duk wadda ya gani sai ya gano makusarta,kuma saiya ga ta fiya wayewa da bu ewar ido,danshi duk a ganinsa hakan yasa Aina'u take yawan yawon ba gaira ba dalili. Musbahu mijin da ummita ta aura abokinsa ne da sukayi karatun secondary tare daga nan kowa ya kama gabansa,to dayake suna zuwa old boys anan aka kuma ha uwa abotar ta kuma ulluwa harya halarci aurin aurensa da kuma sauran shagulgulan da akayi,dan ba laifi shima Abbas an bidi'a ne .To anan ya yalla ido yaga Maryam tun farkon bikin.Batare da ata lokaci ba yafara bincike akanta,yasamu shaidar tantirancin ta da tayi a unguwa na jan magana,shi abinma saiya sashi nisha i,domin duk a cikin abinda akace tayi babu inda akace tayi sata ko kuma tana kula maza,hakan yasa ya ara jin tarin soyayyarta,batare da ata lokaci ba yaje ya sanarwa da mahaifinsa batun,bayan kuma yasan gidan ya sanarwa da iyayensa akan yana son aje a nema masa izinin fara zuwa zance. Sam bai samu matsala da iyayensa ba,saima farin ciki da suka nuna akan auren da zaiyi ko zai samu Aina'u tabar wannan jarabar yawon. ****************************