Sashe 11
Yar Caskale Part 1 Complete Hausa Novel.doc · about 8 min read
zaisa yanzu a ara gasa masa dan yaji da in cin abinda aka dafa masa,sai ma ya gama cin da inshi zaije yayiwa su salame rashin mutunci,danya lura yanzu sun raina shi wallahi.Cike da ladabi Laraba tayi masa sannu da zuwa,bayan ta idar da sallar ta,aikuwa ya amsa cike da jin da in siririyar Muryarta.Nan yasamu guri ya zauna a kan tabarmar da aka shimfida,babu ko jiran a gabatar masa da abinda ke kwanon yace" an taimakamin ki sake gasamin bakin nan kafin inci abin nan ko naji dama-dama". Cike da ladabi ta amsa da "Toh yalla ai"(cikin salon da mamanta ta koya mata,da sunan da yayarta tace ta dinga fa a masa dan jan hankali ewa tayi ta fice,yayinda malam ya bita da kallo yana kallon yanda kayan masarufi ke motsi Haka dai harta dawo da ruwan ta ajiye ta auko tsumma ta zauna gefensa,yayinda ta shiga ga sa masa a hankali tana masa sannu.Sai da ta gama ga sa masa sannan ta fito da lokon dake kan cinyar ta ta bu e.Kallonta yayi yace"Amarya ba'a barin man nan kuwa sai nazo kwanciya a shafa,dan kinga abinci ai baya ciyuwa da mai o a baki ko". Mayarwa tayi ta rufe tana murmushi,yayinda ta bu e masa murfin kwanon da amshin daddawa ya bugi hancinsa,nan ko ya jawo kwano tare da jawo dankwaleliyar tsoka yasa a baki.Tsananin azabar da yaji yasa shi ha iye naman tun bai gama tunawa ba.nan ma naman ya tsaya masa a wuya yasashi wata kwarewar data sa Laraba mi ewa da sauri ta bashi ruwa.Har naman ya wuce bai daina jin ra in a bakinsa ba,dan haka ya fuzge kofin ruwan ya kafa kai yana sha.Duk hankalin Laraba ya tashi,dan tsawon lokaci yana zaune ya jingina da bango Ya saki baki miyau nata dalala,nuni ya shiga yiwa Laraba da hannu akan ta kawar da kwanon kazar,aikuwa taja ta rufe.nan tayi tagumi dan bata da meke damun malam in ba. Sun jima a haka, kafin malam yasamu ra in ya lafa,nan ya juya ya kalli Laraba cikin ha e rai yace"Ke wannan wace irin dahuwa kikayimin,dake arin kasheni da raina kinji an karen yajin dake ciki kuwa?". "Dama Maryam ce....." Zuruf suka ganta ta fa akin tace"salamu alaikum gani Anty,an ragemun ne?" Baki bu e Laraba ta kasa magana,shima malam haka,har Maryam ta fita da kwanon basu sani ba,saida malam yace"ke kika kira wannan tauraruwa me wutsiyar?" "Ni ban kirata ba wallahi ,inaga dama tana kusa ne,jin na ambaci sunan ta shine ta auka ko kiranta nayi". Bai ce mata komai ba,sai zamewa da yayi ya kwanta,itama Laraba Batace komai ba,sai da suka auki lokaci a haka kafin tace" yalla ai katashi ka koma kan gado" laushin hannunta yasa shi lumshe ido dan haka ya mi e da kyar. Ita ta kama shi dan a halin dayake ciki ko abinci baya sha'awar ci,dan haka suka arasa akin nan fa labari yafara canza salo,domin duk yadda yaso kawar da kai abu yaci tura,haka dai fa malam ya runtse ido ya kawar da batun ramuwa ya fara lulawa duniyar masoya da Laraba. Gari ya waye duhu ya yaye,malam kam ya dangwali arzi in Laraba,ya manta duk wata damuwa,jinsa yake yi kamar ba wanda yakaishi kasancewa cikin farin ciki,dan jinsa yake kamar bai ta a kusantar irin wannan ba,dan haka tuni yayi watsi da batun aukar fansa....... _Kuyi manage,wallahi yanzu ma daurewa nayi nayi muku zama aya_ alamin khady* *YAR CASKALE* ( _Sanadin bakin uwa_ ) *NA* *KHADIJA USMAN* ( _Real Tame gari_ ) *____________________________________* AINUWA WRITERS ASSOCIATION* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* " Kiyi maza ki shirya mana Huwaila,dan malam Garba yacemin yakamata muje da wuri,dan inaga malam in baida lafiya ne,yake son aje a auko ta tazo ta kwana biyu saita koma,saboda haka dan Allah kiyi sauri,shi Isma'il in ya shirya ko?" "Gani nan malam hijabi kawai zansa, Isma'il yana akin sa ai inaga ya shirya,dan tun azu yayi wanka". "Yauwa to yi sauri dan Allah kin san jira ba da A hannu ta fito da hijabin tana fa in"malam Allah dai yasa bawani abun matsayaciyar yarinyar tayi ba aka mana kiran gaggawa,amma ai kai kanka kasani babu yadda za'ai kwatsam ace azo a auki yarinya sama ta ka,bayan kai da kanka ka fa a cewa,malam in yace sai anga nutsuwar yarinya tukun,sannan ake bada damar tazo gida ta kwana biyu,amma ban sani ba ko ciwon ajali ne yakama tsohon tunda kace ya tsufa". Ransa a ace yace"wai ke Huwaila yaushe zakiyi hankali ne?haka jiya ma inajinki kina cewa Isma'il ma etaci la'ananne,shin ke wai har abada alkhairi baya fita a bakinki akan yaranki sai sharri,in sun lalace waye zai kaiki ba in cikin hakan,shashasha, wadda bata san ciwon kanta ba" ya arasa maganar yana me ficewa a akin. a baki tayi ta fa a a hankali" kaji malam da wata magana,da kuma bana tsawatarwa ace na cika sakaci,to yaran yanzu kana tsawatar wa ma ya aka are,bare ka zuba musu ido,to wallahi bada ni ba,inna kyalesu sakaka kuma a zagen" Tana kaiwa nan tasa kai ta fice a akin,tana saka makulli a ofar ta shiga kwalawa Isma'il kira,jin yayi shuru ya tabbatar mata da ya fita wajen baban shi, kenan ita ake jira,dan haka ta ara sa kulle ko ina ta fice ta damesu a waje suna jiranta.Dayake tasan ran mai gidan a ace yake,saita bu e baya ta shige abinta ita da Isma'il suka auki hanya..... Tunda asuba malam inka lura dashi zaka tabbatar yana cikin farin ciki,haka yabi duk ya tashi jama'ar gidan nashi dan suyi sallah.Ko yau a masallaci malam ne yayi limanci, yayinda tsabar farin cikin dayake ciki yasa yau har karatu da wa'azi ya gabatarwa da mazan auyen akan ri on aure. Wajen arfe takwas malam ya shigo gidansa,bayan yasa an sayo masa Lipton da Suger ,tare da uma- uman biredi ya shiga dasu gidan.Batare da damuwar komai ba ya ware iya na matansa kowacce,dan tunda akayi auren nan ya lura basa bawa Laraba abinci insun dafa(kunji fa malam sai yau yasan da hakan) Allah sarki 'yar marainiya bata ko damu ba,yanzu idan ya koma zaisa ta lissafa masa abinda ta kashe tsawon wannan kwanakin Duk wadda yabawa a cikinsu babu wadda tako kalleshi,shima bai damu ba,dan yasamu biskit in zuciyarsa,dan haka ya shige akin Laraba hankali kwance,baiwar Allah kun san dai yadda budurwa take duk girman ta in har Bata siyar da mutuncinta a waje ba,dayake zazza i take an ji,amma haka ta daure ta yi masa sannu da zuwa,ya mi a mata Lipton da Suger in,tare da lalubo sachet in madara da bombita(oh su malam an iya almundahana ashe )gashi maza tashi ki dafa mana shayi,sannan ki ha a da waccan yarinyar mairamu,dan itama tare damu zata karya da ita,dan yarinyar na yaba da hankalin ta ba tun yanzu ba,bari ma in kirata mu an ta a hira kafin shayin ya dahu tunda naga a madafin zamani kike girki" ya arasa zancen yana me fitowa ofar akin,daga nan ya shiga kwalawa Maryam kira"Maryama! Kina ina mairamu?" Ya shiga tambaya yana daga bakin ofar Laraba. Daga cikin akinsu ta amsa masa,ta fito sanye cikin kayanta masu kyau da hijabin ta.Sai da ta ara so gabansa ta an tsugunna tace"Gani Baba malam" Washe baki yayi kafin yace"yauwa 'yar albarka taso dama neman ki nake yi shigo ciki kinji" ya fa a yana me juyawa ya shige ita kuma Maryam ta mi e tabi bayanshi. Zuwaira da salame dake can gefen akunan su da yau in nan suka tashi da sabon ha in kai, kowacce saita ja dogon tsaki suka saki dariya a tare suka tafa. ************ Gefen tabarmar malam ya nuna mata ta zauna,aikuwa tasami guri ta zauna,tare da aro ladabin kunama tayi shiru.A haka har larabar malam ta kammala ha a shayin aka kawowa kowa nasa,nan ko Maryam ta zage tasha abinta,dan saiya zame mata abin marmari,dan tunda tazo bata sha ba,danma ita in hamburin hayam ce,ba ruwanta da za ar abinci, komai in zaiyi Mata maganin yunwa to tana maraba dashi. Bayan sunsha sun oshi nan fa malam hira ta arke,ya shiga bawa su Laraba labarin samartaka da irin gararin da yayi lokacin dayaje almajiranta,ita kam Laraba wani farin ciki take ji ,wai yau itace da miji suke hira.Yayin da ita kuma Maryam sam hankalinta na ga gida,danta matsu a zo a tafi da ita taje taci uwar ummita .Tana shirin tambayar malam shin yaushe su babanta zasu zo? Kawai sai taji ihun yara suna fa in, ga yaya Garba! Ga yaya Garba na kano.Aikuwa a zabure ta mi e tayi waje,yayin da sukayi ido hu u da babanta suna gaisawa da wasu mutanen ofar gidan.A dai-dai nan ta ga Isma'il na arin fitowa daga motar.Da gudunta cike da murnar ta ta nufeshi,shima da sauri ya fito,a nan kuma taga ummanta itama ta fito aikuwa da gudu ta canza akala ta nufeta, tare da fashewa da matsanancin kuka,itama umman saida zuciyar ta tayi rauni,hawaye suka fara zubo mata na ganin 'yar Tata da tayi.Haka suka rungume juna,kafin malam Garba yayi musu jagora zuwa cikin gidan. Koda malam ya gansu ya nuna farin cikinsa,dan yanzu duk abinda ya shafi Maryam to yana daraja shi,dan shi Sam Yama manta shiyace Suzo su auki 'yar su. angaren su salame ya musu jagora,yayin da suka shiga akin salame,amma sam babu wadda tayi musu koda kallon arzi i,hakan yasa jikin umma yin sanyi,ganin hakan da malam yayi ne yasa yakama yin ya e tare da cewa"Maryama idan sun gama gaisawar maza ki raka su akin amarya kinji" yafa a yana me juyawa ya fice,dan su gana da mahaifin Maryam Batare da ata lokaci ba kuwa Maryam tace"Umma tashi in kaiki akin Anty Amarya dan ita tanada kirki,amma yanzu tsofaffin matan Baba malam sun koyo rashin mutunci". Jin furucin na Maryam yasa umma jin kunya,ta kalli salame dake du e tana le ashin gado,kome zata auki oho,bata bi takansu ba har Maryam taja hannun Isma'il suka Umma ta bisu a baya,har zuwa akin Laraba. A kwance take kan tabarma, dan zazza i takeji,hakan yasa koda suka shiga da kyar ta iya agowa ta amsa musu,dan ciwon da kanta keyi.Jinjina kai Umma tayi datayi