← Book details Yar Caskale Part 1 Complete Hausa Novel.doc Local reading mode
READING PART 34 OF 34

Sashe 34

Yar Caskale Part 1 Complete Hausa Novel.doc · about 7 min read

waigowa yayi ka an tare da kama hannunta wanda laushinsa yasashi lumshe idanu kamar mai jin bacci ya kuma bu esu tar akanta,kyau sosai yaga tayi masa,yayin da ya kafeta da ido babu ko iftawa yana jin wani abu na fizgarshi zuwa gareta. Gyaran Muryar da aketa yi ne a loudspeaker yasashi yayi firgigit ya dawo hayyacinshi ,yayin da gurin ya kaure da hayaniya an uwa musamman abokan wasa suka shiga yi masa tsiya daga inda suke. Duk yadda Aina'u taso daure zuciyarta akan abinda ya faru saida walla ta zubo mata. Dama haka mata keji? Dama haka kishin yake? Tunawa da tayi wata anwar mamanta data mata nasiha tace idan taji irin haka ta kama karanta Lahaula wala uwwata illah billah.A take kuwa ta kama maimaitawa a zuciyarta,zuwa wani lokacin harta ji zuciyarta sakayau. A wajen yanka cake ma ansha shagali,dan Abbas cewa yayi duk sai sun bashi a baki,ai shi yanzu an gata ne tunda yanada mata har biyu. Ita kam Maryam kunya duk ta isheta,sam bata saba ganin irin hakan ba,jin abin takeyi kamar mafarki,batayi wannan wayewar ba,yau itace cikin an gayu masu ji da kansu.Bisa dole dan kar taji kunya a rainata,ta shiga bashi,dan tsabar ara salo harda yankowa ta nufi bakin Aina'u dashi,bisa dole Aina'u ta bu e bakinta,nan kuwa guri ya au tafi,dan Maryam in ta burgesu. ***************************** Alhamdulillah taro ya tashi lafiya, a daren an mayar da amarya akinta,angonta ya shigo kamar yadda kowanne angon da sukayi auren soyayya ke shiga akin amarya sa. Sun gabatar da komai kamar yadda addini ya koyar damu,kafin nan kuma labarin ya sauya she a zuwa sabon karatun dayake son fara koyar da ita. Yau dai kam hatta ni Real ta maigari nasha kira,umma baba,har cewa takeyi "Isma'il kazo ka ceceni gurin wannan bawan Allahn da ba'a halicci tausayi a zuciyarsa ba,dan Allah kafin kazo ka tabbatar kasha wi-wi yadda imaninka zai ragu ka ramamin". Saida ya samu nutsuwar daya mance tsawon lokacin da rabon daya samu irinta,wadda ta ara shiga cikin tarahin rayuwarsa a karo na biyu.Tunawa da daren farkonsu shi da Aina'u yasa shi shafa kwantaccen gashin dake gefen fuskarsa har zuwa gemunsa na rashin kunya daya fara ajiyewa. Kusan shi ya taimaka mata ta gyara jikinta,inda ta dinga nannarke masa,ganin kusan asuba yasa shi aura arwalla itama yasa tayi,duk da zazzabin daya zubar mata lokaci aya hakan baisa ya barta ta kwanta ba har saida akayi sallar asuba,nan yaja su jam'i dan idonsa fal yake da bacci ga gajiya,suna idarwa kuwa suka haye gado ya jawota jikinshi sai bacci mai nauyi. ****************************** A shirye tsaf suka fito zuwa falon nasu, murmushi Abbas ya saki ganin saman teburin cin abinci sha e da kuloli, ko ba'a fa a ba yasan aikin mama amarya ne,wato amaryar babansa,duk da ta tsufa a gidan ,amma har yanzu sunan da suke kiranta dashi kenan,dama tun jiya tace ya bata mukullin angaren nasu, dan bata son a zo a damesu da bugu. Sosai ya zage ya ibi abincin sinasir ne da miyar agushi data sha naman rago,sai farfesun kayan ciki da kuma ruwan tea.Ganin Maryam ta tsaya wasa kunya ta hanata ci yadda ya kamata,yasa da kanshi ya takurata yana bata har saida taji ta oshi tukun ya barta. A ranar kam Maryam taga soyayya,tasan ta shigo rayuwa mai da i,ji takeyi kamar ba itaba,duk Abbas ya mantar da ita kewar gida a iya yinin wannan ranar,sai take ganin wautar wasu ma'auratan da zasu dinga fa a ,dan gani takeyi babu abinda yakai rayuwar ma'aurata da i,ita a ganinta ma meye abin fa a ai ba abinda Abbas zaiyi mata ya ata mata rai(Ni ko nace rai dai Maryam muma da haka muka auka). Su Anty Laraba da dai sauran duk sunzo yi mata sallama,inda ta ha a musu goma ta arziki,suka rabu ana kewar juna. ***************************** Yau ya cika kwanaki bakwan shi zai koma bangaren Aina'u,ya gwada mata yadda zaiyi missing inta,har take jin ina ma ita ka ai ce keda shi,dan itama yau wani abu take ji data kasa banbancewa (nan ma nace kishi ne A ranar ya tara su yayi musu nasiha ma ratsa zukata, ya kuma ro esu dasu zauna lafiya da juna shine kwanciyar hankalinshi. Sun tabbatar masa da zasu zauna lafiya da juna da yardar Allah ya kuma ji 'da ****************************** Zaman gidan Abbas zamane ake yi na kishin birni,dan sam Aina'u baka gane abinda ke ranta,wani abin mamaki yanzu sam ta rage wannan masifaffen yawon har Aliyah ta auko ta dawo gabanta,inda Maryam ta zama uwar Aliya,Dan itace akinta.Hakan ba aramin da i yayiwa Abbas ba. Wani abin farin ciki da jin da in dukansu matan nashi suna cikin laulayi ne,sosai murna da farin ciki suka kasa oyuwa a gurin Abbas,kowa a gidansu yasan da batun cikin,hakan yasa matan nasa duk suka zama an lele gurin iyayen Abbas Maryam taje gida a tsakanin nan,farin cikin da baba da umma sukayi ba'a magana,tunda umma ta fuskanci Maryam nada ciki ta fa awa baba shima ya dinga murna. Dayake yanzu sana'arsa ta da a bun asa, dan sari yake bayarwa. ****************************** Yau maryam na zaune a angarenta,taji ta gaji da zaman,tunda yau Aliya na makaranta,dan haka ta tashi ta nufi bangaren Aina'u. Zaune ta isketa da ba uwa suna hira.Ganinta yasa Aina'u fa a fara'arta tana mata sannu dan ganin yadda take tafiya da yar,duk da itama hakan take yanzu. Amsa mata tayi ganin da ba uwa tace. "Bara naje na kwanta Anty tunda naga kinyi ba uwa". Da sauri Aina'u tace"kinga zo kiyi zamanki ai ta gida ce,duk aya ne". Dayake tana bu atar hirar saita zauna tana in,aikuwa nan ba uwar ta ha e rai,da sun ha a ido da Maryam in saita sakar mata harara,ganin hakan yasa Maryam sakin murmushi. Ganin abin ya arewa yasa Maryam fa i a zuciyarta" bari dai nayi maganin wannan shegiyar". Tana ago kai suka ha a ido kuwa ta kuma sakar mata hararar,aikuwa Maryam ta kwa e fuska tare da dallaro mata harshe kamar mai gwalo.sunyi haka yakai so biyar,hakan yasa zuciyar ba uwa fara karaya,sannan jiki ya fara rawa,dan ta fara tsorata da yanayin Maryam in,dan sai taga ba haka takewa Aina'u ba,hakan yasa ta kuma kallon Maryam in amma bada salon harara ba,nanma sai gani tayi ta ara dagule fuska ta wur ile idanu fiye da azu,ba shiri ta suri jakarta da mayafi tana sakin ara. Aina'u ,da bata san meke faruwa ba a ki ime ta mi e tana" fa in lafiya?" Bata ko bi takanta ba har takai bakin ofa tana fa in "na shiga uku mayya "ta fice a guje,ita ko Maryam ta kama dariya yayin da Aina'u ta rasa abin yi kawai saita koma ta zauna tana tunanin to wace mayya kuma?. ****************************** Yau Ahlin gidan gaba aya suna cikin farin ciki, sakamakon haihuwar da Aina'u tayi na a namiji,shi kanshi uban gayyar yama rasa inda zaisa kanshi dan murna sai yiwa Allah godiya. Ranar suna aka sha shagali yaro yaci suna Ibrahim sunan baban Abbas suna kiranshi Daddy. Wata aya tsakani itama Maryam ta tashi da na uda,tasha wuya ba ka an ba,kafin itama ta haifi yaronta namiji shima mai kama da Abbas din. Maryam ta ara sanin darajar uwa,dan cewa tayi da tasan haka ummanta taji gurin haihuwar ta da batayi duk abinda tayi a baya ba. In kaga Maryam a wannan lokacin bazaka ce ita bace, tayi la was da ita. Ranar suna anyi shagali abin har ba'a magana Abbas yayiwa kanshi takwara,suna kiran yaron da Sultan. Haka rayuwar taci gaba da gungurawa da da i ba da i,abubuwan ci gaba na samuwa,komai ya sauya rayuwar tayi musu dadi kowanne bangare. Cikin shekara biyar kawai Abbas ya tara iyali,dan haihuwa matan suka dinga yi kusan a tare hakan yasa shi farin ciki da godewa Allah. Gashi matansa suna zaune lafiya ba fa a ba tashin hankali. Umma tayi nadama ta kuma fuskanci bakinta shi ya jawo duk abinda ya faru a baya.yanzu haka Isma'il ya kintsu inki ma yakeyi na mata. *_TAMMAT BIHAMDULLAH_* _A nan na kawo arshen wannan labarin na ar caskale ina ro on Allah daya sa mu amfana da darasin dake ciki, kuskuren ciki kuma Allah ya yafe mana amin.Sai mun ha u a littafi na mai suna ASHFAT, wanda zai zo muku da sabon salon da baku ta a ji ba,littafin ASHFAT zai zo muku da abin mamaki,domin na tanadeshi tun kafin ku fara neman shi,ku dai kada ku bari a baku labari,zaku sameshi akan Naira ari 300 kacal,ga mai bu atar sa saiya tuntu i wannan number 08103271722,ko kuma 08092924299 Kada ku manta REAL TA MAIGARIN NAN CE DAI_ alamin khady < > p r t v x > r t v v x SummaryInformation DocumentSummaryInformation WpsCustomData TECNO LD7 WPS Office Normal Times New Roman Times New Roman Calibri Calibri !%),.:;>?]} $([{ 24f87296d8244dfca0c5668f9b39083e
Chapter 34 · 0% Book details