Sashe 23
Yar Caskale Part 1 Complete Hausa Novel.doc · about 8 min read
Maryam damar fitowa.haya in da Jazuli ya gani ne yasashi saurin arasawa kusa da gurin.A zaune ya iske Zulaiha ta baje afafu tana aura sakwara a leda,duk azabar nan bai sa ta karaya ba,yana shirin yin magana ya tuna da tace masa duk abinda yaga tayi a gidan nan cikin kwanakin nan kada ya tambaye ta dalili,dan haka yaja bakinsa ya tsuke ya bita da kallo,duk da magariba tayi amma hasken daya mamaye gidan saika auka rana ce.A haka Maryam ta ara so gurin itama taga yadda Zulaiha ta tara tarin dakakkiyar doya a baho,duk da kallo aya zakaima doyar ka ta tabbatar dakan amaja aka mata.Murmshin daya fi kuka ciwo ta sakarwa Maryam itama ta mayar mata dana mugunta,batare data damu da tambayar ya taga ba'aci ko rabin aiki ba,sannan ita wannan sakwarar ina za'a Kaita ? Dan taga dai babu ko alamun almajirai a unguwar da suke,sannan idan takai gobe tasan zata lalace,kai gaskiya tasa anyi almubazaranci,duk da batayi tsammanin Zulaiha zatayi duk abinda tace ba,da farko tayi niyyar tafiya sai taga idan ta kyale Zulaiha taci gaba da daka doyar nan gaskiya bata kyauta ba,bawai tausayin Zulaiha yasa tayi wannan tunanin ba,duba tayi da yadda wasu ke can ke bu atar abinda zasu ci,to ko Ayashe mai wanki ta layinsu ta ta a ce mata marabin data ci doya tun tana arama,ita koda tacewa zulai doya warya guda ta auka da ake cewa warya aya to a cikin waryar ake sayarwa ashe guda ari ce,gashi taga an kusa dake hamsin dole ta dakatar da wannan dakan,dan haka tace da Zulaiha"Yakamata ki bar dakan nan haka Anty zulai,ki bari zuwa gobe da asuba sai ki arasa zan ro ar miki sassauci". Jin abinda Maryam in tace yasa Zulaiha cikin alamun gajiya tace "kina ganin babu matsala idan na bari? Kuma wadda na daka in wa za'a bawa? dan kinga nan babu almajirai". Shiru tayi bayan tasa yatsa a baki ta kalli sama alamar nazari kafin tace"babu matsala za'a kai gidan marayun aljanu ne,ke dai yanzu ki ajiye inda bazai lalace ba,dan kin san su aljanu an shagwa a ne,duk da suna shegu hakan bai hanasu iskancin za ar abinci kamar ba'a gidan marayu suke ba". Sagale Zulaiha tayi tana jin tarihin aljanu gurin bokanya Maryam,"kenan a aljanu ma akwai karuwai?"ganin kamar Maryam in bata bu atar tambaya yasata yin gum da bakinta,ta dai ji da in sassaucin da uwar bokaye tayi mata.Ita ko Maryam tana gama magana ta juya ta nufi cikin gidan dan shi Jazuli tuni ya shige. *********************** A tsaye ta iske su da alamun ran kowa a ace yake,ta so tsayawa amma sai ta tuna miji da mata ne kuma sabon aure,Yakamata ta sakar musu mara suyi fitsari,shiyasa tayi niyyar wucewa amma sai taji Muryar Ummu tace........... alamin khady* *'YAR CASKALE* ( _Sanadin bakin uwa_ ) *NA* *KHADIJA USMAN* (Real ta maigari) *____________________________________* AINUWA RITER'S SSOCIATION ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* "Dakata aramar karuwa! Me ya ha aki da mijina?" Tabbas kalmar da Ummu ta jefeta da ita tayi matu ata ranta,domin ko ba komai tasan ita in bata jin magana ta ko wanne fanni,amma kuma bata iskanci ko masu yi tana musu addu'a Allah ya shirye su,ita ko ka an ma maza basa burgeta bare har takai ga ata rayuwar ta,kallon Ummu tayi taga yadda take wani huci kamar zata dake ta,dan haka tayi murmushin kinji haushi tace"yo banda abinki ga babban karuwi nan ki tambaye shi mana kya tsaya tambayar arama,kuma ma duk in kikaga karuwa da namiji ai kin san kwanan zancen,tunda kin tambaya kada kice na shiga ha in ki ban baki amsa ba,mun biya ta mashaya ne muka an kwal e mun so ma muyi tilldown kawai sai naga kada a yi miki laifi a matsayinki na amarya". Wata uwar ashar Ummu ta lafto ta makawa Maryam da Jazuli,dan idonta ya rufe,zugi da ra in da take ji a zuciyarta yasa ta kasa control in fushinta.Shi kuwa Jazuli tun farkon shigowarsa titsiyar data yi mishi da jifansa da kalmar Allah ya isa munafuki maci amana da dai sauransu ransa ya aci,dan ko Zulaiha da yake jin shakkar ta bata mishi wannan abin,duk tana lalla a sa,idan ya kula wata sai dai abin ya kare akan wadda ya kula in,amma bata ta a zaginsa ba,kuma bata nuna masa tana zargin sa ,shiyasa duk abinda yakeyi yake yinsa da taka tsantsan. Cikin hargowa tayo kansa tana fa in"ka gayamun gaskiya ne abinda ta fa a ko a'a? Dan in har hakane wallahi bazan iya ci gaba da zama dakai ba,dama Ni ba sonka nake ba inada wanda nake so,dan haka ka sakeni in kama gabana,idan yaso sai ka maye gurbina da ita karuwar taka!" Abinka da an duniya,yasan salon untatawa ta ko ina,dan haka yace da ita" Ai ba saina aure ta ba,tunda na fuskanci inka auro ka kawo anfi rainaka, amma in ka bari a waje akaci gaba da rayuwar bariki kowa ya gurje kowa yafi da in zama ai,da kike cewa bakya sona kika aure ni amma kina son ku i na ai,tunda baki nunamin ba kya so na ba da tuni na sake sabon lale tunda kuturu da ku insa ai alkaki sai na asan kwano". Maganar sa ta razana ta,dan ko da ta fa a masa haka ta fa a ne dan ta samu sassaucin abinda take ji,a yanzu data zo taji sanyin ra a bazata iya rabuwa da wannan daular ba, dan tasan wanda take so ko keke bashi da shi bare batun matsuguni,dama dai soyayya ce ta rufe mata ido yanzu kuwa ta gane.Amma duk da haka sai ta nuna masa kuskurensa kada ma ya ga damarta ya rainata,inta kama ko tafiya ne sai tayi wallahi,ai ba abin kunya bane dan ta dawo gida a matsayin ta na sabuwar amarya Gara aiwa tufkar hanci.Sosai suka shiga bala'i a tsakanin su wanda hakan yakai ga ran Jazuli ya aci harya kantarawa Ummu mari .Ita ko Maryam nata guri tayi,yayin da farin ciki fal ranta ta cika kudirinta na sanya sabuwar amarya Ummu yin yaji. ******************** Jirgin safe zata bi 7:30 dan haka tunda ta tashi bata koma ba,iya farin cikin shiga jirgi a karo na biyu ya hanata sakat,sai murmushi take yi ita ka ai,a haka ta tsinkayo Muryar Jazuli yana wala mata kira.Da sauri ta fito ta iske shi tsaye yana tambayar Zulaiha akan me ya same ta a hannu duk suka kumbura haka ,amma tayi mishi banza,dan jira takeyi tagama cika umarnin aljanu daga shi har sabuwar amaryar tasa ta karta musu samfurin rashin mutunci. Ko da ta ara so falon dukan su murmushi suka sakar mata,itama ta mayar musu tare da ce musu Barka da safiya.Jakar da Zulaiha ta gani ne yasata tambayar Maryam in ina zata?sai a lokacin Jazuli ke fa a mata anyi musu rasuwa ne kakar Maryam in babar mahaifinta ce ta rasu.Ta'aziya ta shiga yi mata,dan sam bata ji da in tafiyar Maryam in ba a wannan lokacin,dan haka ta mike tace wa Maryam in ta zo tana son ganinta. Koda suka shiga akin na Zulaiha ta marairaice wa Maryam tana fa in inta tafi waye zai rabawa aljanun sakwarar,sannan sauran aikin wa zai arasa mata,karkacewa Maryam tayi tace" kada ki damu Anty zulai,na riga na kammala miki aikin ki,ita wannan sakwarar da kika daka ki barta haka ta isa,amma zaki dakawa mai martaba tashi guda aya,sai dai ita da mazaunan ki zaki daka,ki buga tsalle kiyi zaman da aro har doyar tayi laushi,shikenan aikin ki ya kammala,Bama kishiya ba,ko mace jinjira aka haifa yaje Barka bazai auke ta ba,dan haka ki zuba ido ki jira sakamakon wahalar ki". Sosai Maryam ta kalamance Zulaiha,wadda ta ara bu e jaka ta kwararawa Maryam abubuwan arziki,itako da i kamar ya kashe ta dan ganin ta samu abinda bata ta a tsammani ba cikin sau *********************** A inda suka barshi a nan suka dawo suka same Shi,sai dai yanzu a zaune yake kuma yana yin fuskarsa ya canza kamar da alamun acin rai,ganin su yasa ya aro murmushin dole amma zuciyarsa cike da mamakin halin mata,dan shi duk ahalinsa ba wanda yake shiri da Zulaiha,amma sai gashi ita da Maryam har aki ake shiga,bai ta a ganin Zulaiha tayi girki ba,amma wai jiya harda kunna icce tayi girki ya tambaye ta tace abincin sadaka tayi.Ganin kamar lokaci na urewa yasashi cewa Maryam ta tashi driver ya kaita airport,jirgi ba kamar mota bace.Haka ko sukayi sallama batare da tabi takan Ummu ba,ita ko Zulaiha ganin haka yasa ta ara yadda da Maryam,tare da tunanin tazo tayi gaggawar dakawa mai martaba tashi sakwarar. Koda suka fito tuni driver na cikin mota yana jiran ta,suna zuwa Jazuli ya bu e mata gidan baya ta shiga,ya le o tare da mi a mata ku i 20k yace tayiwa an gidansu gaisuwa,sannan kayan da suka siyo jiya suna but in wannan motar cikin jaka.Godiya tayi masa kafin ta kalli driver'n tace masa "kunna motar muje kaji"dan jinta takeyi kamar mafarki,wai yau itace a bayan mota za'a kai filin jirgi,wato duk abinda take gani a film da novel Ashe anayi a zahiri,bata ankare ba tana duniyar tunani taji arar bu e get in gidan alamun suna shirin fita.Da sauri ta dakatar da driver'n kafin ta zuro kai ta walawa Zulaiha kira dake tsaye tana son ganin ficewarsu tare da murmushin samun nasarar da tayi. Calai-calai ta ara so gurin harda an gudunta,lamarin da yabawa kowa mamaki kenan,daga Jazuli har ma'aikatan gidan.Tana zuwa tace "ga ni anwata ko kina bu atar wani abin?" "Ah ah Anty zulai ta Yaya Jazuli ato,dama kawai kiranki nayi dan nayi wani tunani ne,da farko banyi niyyar fa a miki ba,sai dai alherin da kikai min ne sai naga bari na fa a miki gaskiya.Dama wallahi Ni ba boka bace,kawai haushi kika bani Ni kuma na azabtar dake,idan kika sake kika daka sakwara da mazaunan ki kamar yadda kike shirin yi kika je kika karya kwankwaso wallahi ba ruwana,direba muje" Wata ara Zulaiha tayi,tare da zaburowa ta biyo motar da har ta fice daga gidan,dayake Jazuli yana kusa ta zabura zata fice ya ri ota,yayin da ita kuma Maryam ta zuro kai ta