← Book details Yar Caskale Part 1 Complete Hausa Novel.doc Local reading mode
READING PART 2 OF 34

Sashe 2

Yar Caskale Part 1 Complete Hausa Novel.doc · about 8 min read

ke faruwa. Itako Maryam ganin tafara gajiya gashi ta rasa gurin nufa kawai saita hango wata majallisar matasa,aikuwa ta nufi can tana fadin "ku taimakamin wayyo ni mahaukaciya ta biyoni",itako Rakiya Jin abinda Maryam ke fad'i yasata lailayo ashar tana Kara laftawa,tare da ikirarin idan har ta rik'e Maryam wallahi saita ga ta daina numfashi.Su kuwa matasan ganin yadda fuskarta tayi dumu-dumu da toka ga bakinta ya hadu ya hade,sai suka dauka da gaske batada lafiyar Nan ko sukayo kanta,ita ko Maryam ta labe tana mayar da numafashi. Sosai matasan suka shiga kiciniyar rike Rakiya,aikuwa ta shiga fizge-fizge,su kuwa sun sami abin bukata,nan wasu suka shiga lagudar inda yai musu a fakaice. Mijinta da karyo kwanarsa kenan yaga yadda ake tattabe matarsa,da sauri ya karasa ya shiga ture matasan yana zaginsu,nan suka kauce ita kuma Rakiya ta fashe da kuka tama rasa abinda zata yiwa yainyar nan,dan inta kamata saita ga ta daina numfashi........ _ina son inga comments din dazai girgiza ni_ *Alkalamin khady* *_'YAR CASKALE_* ( _Sanadin bakin uwa_ ) *NA* *KHADEEJA USMAN* *_(Real Tame Gari)_* ___________________________________ KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ___________________________________ *ALHAMDILLAH! ALHAMDILLAH!* *_AM BACK AGAIN_* Maimakon Maryam tayo gida data samu ta sulale,aikuwa saita bazama,itace wannan lungu,itace wannan layin,makaranta Kam yau islamiyya ta yafe ta,tunda dama yau asabar ba boko,islamiyyar yamma data safen duk yau bataje ba,tasan ko yau Mai kwatar ta gurin umma sai Allah,shine tace gara kawai ta cika laifinta ya cika cif ayi Mata dukan gaba Daya.(Illar sabawa yaro da duka kenan,komai yayi duka,hakan shi kesa yaro ya zabure yabar Jin tsoron dukanma,gara tun Yana d'an karamin sa ki Saba Masa da kallo ki banbance Masa dai-dai hakan zai fahimci kallon me yake nufi,kada kice komai yayi saikin daka,ki Bari ki Tara tukun,yadda idan Kika rikeshi yasan bazakiyi Masa da Wasa ba,zaiji tsoron gamuwar ku matukar kikace Zaki dakeshi.Allah yabamu ikon gyarawa amin.) A can gida tuni labari yazowa Huwaila,aikuwa yaran Rakiya sunyi rashin mutunci,Dan cewa sukayi a Miko musu Maryam sai sun jajjaga ta,Dan sunji labari tasa uwarsu gudu a titi,Kuma tayi sanadiyar fadawar babansu kwata.Sai da Huwaila tasa aka kirawo Mata malam Shu'aibu yazo ya basu hakuri,da kyar suka hakura suka bar kofar gidan. ********************* Ita kuwa Maryam tana Nan labe ta hango Rakiya da mijinta sun rungumo juna,Rakiya nata gunjin kuka,yayin da mijin keta Bata hakuri,Yana fado Mata irin nau'ikan azabar da zasu yi wa Maryam in sun kamata.Zugar Yara na biye dasu duuuuu! Kunsan Yara in sun samu abun kallo kiris suke jira.A hankali ko Maryam tayi tsulum ta afka cikin yaran ta wage murya da karfi tace,"mahaukaciya 'yar macukule! ,Take ko zugar yaran ta amsa suka maimaita,aikuwa harda tafi Nan ma wasu yaran suka Kara tittidowa,Nan da Nan ko Rakiya ta juyo,aikuwa idonta ya sauka Kan Maryam tana bada wak'a.Ai kuwa sata kwace tayo kansu,nan kuwa Yara suka watse,ta tsaya tana zage-zage tana neman maryam.Itako Maryam lungun gidan su taje ta labe, tana son shiga gida a ranta Kuma tana cewa mudun tsokanar ta Bai cika ba. ***. ******. ******. *** Sai da duhun magariba ya gabato,sannan tasa kanta zuwa soron gidan,dayake soron biyu ne,Haka ta sadada ta leka, dai-dai lokacin ta hango umman nata na bude robar ruwa danta zuba a buta,aikuwa sai taga ba ruwan,ji tayi tana fad'in,"oh ni 'ya su,Kinga a shefa ba ruwa a robar Nan,Allah sarki Isma'il ,sabo da ka Saba zubawa na dauka yau dinma diba kawai zanyi ashe babu,Bari idan nayi sallah nazo naja ruwan duk da ba amfanin Jan ruwa da daddare,Amma ya zanyi" Haka taja ruwan guga Daya ta zuba a buta,ta shiga bandaki,bayan ta fito tayi alwala ta shige daki. Maryam na ganin wucewarta ta shigo gidan tare da nufar gurin rijiyar,ta bude babbar jarkar ruwan ta shige,bayan ta jawo murfin ta Dan Dora aka ta zameshi tana Jin iska,take bacci ya kwasheta cikin kankanin lokaci. Saida Huwaila ta idar da sallar,sannan ta fito Dan Jan ruwan,so takeyi taja da wuri dan ma yaza ma dole ne,da Sai da safe zata ja,to tasan bukatar ruwan na iya tasowa Kuma dole dai rijiyar za'a bude aja komai dare. Tana zuwa ta bude rijiyar,Saida ta jawo ruwan sannan ta Mika hannunta ta Jaye murfin robar tana fadin" oh Kinga na Manta ma ban wanke robar ba,Haka dai zan hakura in zuba da safe a wanke,na ciccika Mana butocin kawai" dai-dai tana kwara ruwan cikin robar ruwan,Wanda yasa Maryam sakin ajiyar zuciya ta farka. D'an jimm umma tayi,Dan saita ji kamar an sauke ajiyar zuciya Kuma daga cikin rijiyar,amma sai Kuma tayi tunanin Kila kunnenta ne,Dan Bata Saba Jan ruwan dare bene,yasa ta Jin hakan,aikuwa ta Kara zura guga tana cewa"yau Maryam Ina tausaya Miki ,Dan ban ma San irin bugun dazan yi Miki ba,laifi goma da ashirin,Allah ya dawo dake gidan kafin babanku ya dawo zanci ubanki,Dan nasan idan Yana Nan nace Zan dakeki hanawa zaiyi,dai dai ta jawo ruwan ta Kara antayawa cikin robar,Maryam ta Kuma sakin ajiyar zuciya saboda sanyi,kun San ruwan rijiya lokacin zafi. Daurewa kawai umma tayi ta kara zura gugan,dan wannan Kar kam da gaske taji anyi ajiyar zuciya,hakan yasa zuciyarta Fara rawa amma wai ita jaruma saita dake,taci gaba da antya ruwan cikin robar,jin da maryam tayi ruwan na neman kawo mata wuya,yasata mikewa ta buga tsalle ta fito jagab da ita,ta zura a guje ta shige dakinsu. Wata kara umma ta saki tare da karanta ayatul kursiyyu iya karfinta,tana nan tsaye Kuma ta kasa sakin gugan yana hannunta,irin d'an dutsen nan na rijiya ya rike gugan Nan umma tawage Baki tana kuka da neman agaji. Mallam Shu'aibu da shigowar shi kenan ya hango matarsa na makyarkyata da sauri ya karasa Yana fad'in"subahanallahi! Huwaila waye ya fada rijiyar,bawai garin jarabar Taki Kika jefamin Yara rijiya ba,ya fada Yana fuzge gugan hannunta,Yana lekawa rijiyar,ganin da duhu ba komai zai gani ba yasa ya juyo a fusace Yana fad'in,kin mun shuru ki fadamin meyake faruwa! Cikin rawar murya da tsoro tace 'matashiyar 'yar ruwa ce ta fito daga rijiyar ta shige dakina". Tsaki yaja,kafin ya saki gugan ya nufi dakin yaran,a zuciyarsa Yana fad'in yaga ranar da Huwaila zatayi hankali. A kudundune yasamu Maryam da kayanta jikakku,tunda yaga Haka ya tabbatar da itace tayiwa uwarta haka.karasawa yayi inda ta kwanta kusa da Isma'il ya tashesu duka,Nan Maryam ta shiga rarraba ido,Bai nuna Mata wani bacin Rai ba,yace ta tashi ta cire kayan jikinta,aikuwa ta mike ta canza ,Nan yake tambayar ta ko taci abinci,Nan ma tace mishi ah'ah ,yasan za'a rina,Dan haka ya fita dakanshi ya fita kicin ya zubo mata,yace taci Yana zuwa. Yana fita ya tarar da Huwaila tsaye bakin kofar dakinta Taki shiga,Yana zuwa yaja hannunta ta shiga tittirjewa,ganin tana cijewa ya juyo yace "Wai miye haka ne Huwaila?ba fa na son sakarcin banza wuce muje,Dan Yara na baro wurin Ina son magana ne dake a gaggauce". Ganin ya shige ciki Bai Kuma dawo ba yasa tayi shahada ta biyo shi,ta samu guri ta zauna tana waige-waige. Bai kulata ba yace,"dama ba komai ya dawo Dani ba sai akan Maganar Maryam, Huwaila bazan boye Miki ba,komai ya faru da yaran nan kece sila, wallahi na tabbatar bakinki ne,gashi yanzu kin samu a damuwa,kullum maryama da kalar tsokanar da zatayo,a tsokaneta Kuma ta jawo magana Nan ma,ba babba ba yaro duk Kan me uwa da wabi takeyi,gashi Bata Jin tsoron ko mu iyayenta Dan kin Gama horar da jikinsu da duka,tasan bazai wuce muma dukanta zamuyi ba intayi ba dai-dai ba,Kinga yanzu abinda ya faru dazu,yanzu Haka maganar da nake Miki mijin Rakiya ne yaje da yaranshi maza manya har gurin san'ata sunce wallahi idon su idon Maryam sai dai wata ba ita ba,na rasa abinyi da kyar aka Basu hakuri suka bar gurin.To shine nake fadawa malam Garba abinda ke faruwa shine ya bani wata shawara yace in Kai Maryam almajiranta kawai". Da sauri Huwaila ta d'ago ta kalleshi tace,"wace irin almajiranta Kuma malam ? Wai ma Isma'il kake nufi ko wa? Dan Naga dai shine namiji Kuma maza ake kaiwa almajirci ba Mata ba". Murmushi yayi kafin yace ," Maryam dai nake nufi kamar yadda Kika ji,malam Garba yace babanshi Yana da almajirai Mata,idan yarinya ta gagara to shi ake kaima,sannan Kuma cikin yardar Allah sai kiga yarinya ta kimtsu ta samu ilimi,sannan bawai bara sukeyi ba,zamu had a Mata kayane kamar zata boading school,shima Kuma acan gidansa ana Basu abinci Dan suna mu'amulla ne kamar yaran gidansa,Ina gudun abinda Maryam zata jawo Mana ne Nan gaba in mun barta Haka. Nanfa ya shiga gayawa Huwaila muhimmancin Kai Maryam makaranta. "Naji malam na Kuma gamsu,amma kasan fa halin Maryam,kana ganin bazata iya dawowa ba?" "Kada ki damu na shirya yadda za'ai tafiyar,Kuma yace min garin lungu ne can jihar jigawa ne". "Shikenan malam, Allah yasa karshen wahalar kenan" "Amin ya amsa,kafin ya mike Yana fadin ta hadawa maryam kayanta kala biyar,Dan da asubar nan zasu tafi a motar malam Garba. Haka ko akayi Daya tashi dawowa ya tahowa da Maryam harda robar almajirai,dasu gari da dakaken kuli magi dadai 'yan wasu abubuwan bukata na 'yan makaranta ********* Asubar fari suka fito aka tashi Maryam Huwaila ta sallara mata wanka,itadai Bata cewa komai,ana shiryata ana Mata nasiha. Gani sukayi malam ya fito da zundumemen buhu yace"maryama ta taho ki shiga Nan kinji" Make kafada tayi alamar ah'ah,Nan ya shiga.lallabata harta yarda ta zura kafafunta tace"baba kasheni zakuyi?" Zaro ido yayi yace "injiwa yace Miki kashe ki zamuyi?" "Gashi Nan zaku je ku jefani a ruwa". "Ah ah,madinan Nigeria zamu kaiki ki sauke farali,shiyasa muke son mu boyeki anan,kar Yara su ganki suce Suma sai anje dasu,bayan ke kadai ce 'yar gata...." Bai gama ma maganar ba,yaga ta shige buhun tana fadin"to ummana Allah ya kaddara saduwar mu,nidai yau Zan hau jirgi" sai Kuma ta fitoda kanta tace,"to amma baba a maleji zani ko Kuma a booth,da Naga za'a Sani a buhu?" "Ai a kujerar boye Zaki shiyasa,Dan Haka ma Zan yanka Miki inda Zaki dinga Shan iska bakida matsala kinji". Komawa tayi tana fadin,baba k'ulle bakin buhun muyi sauri Kar jirgin ya tafi,amma Allah ya taimaki ummita,da nace wallahi saina mata dukan tsiya,amma yanzun ma idan na dawo indai
Chapter 2 · 0% Book details