Sashe 30
Yar Caskale Part 1 Complete Hausa Novel.doc · about 8 min read
Zuwa yanzu hankalinsu yayi matu ar tashi, musamman da umma ta kuma samun kiran yayarta akan zuwan Ummu Kulsum gida,bayan kuma ta sanar mata cewar ita a mota ta taho amma taji Maryam a jirgi ta taho,nanma ta faffa a mata magana son ranta.Wannan karon sam umma bataji zafi ba saboda tashin hankalin ina Maryam ta shiga,shi kanshi baban Maryam ya shiga damuwar da bai ta a shiga ba. Duk iriniyar yaro da saka bari da jawo magana gara yayita a gabanka da ace yayi a bayan idonka,tasan babu ko tantama fa an da suka yiwa Maryam in ne,tare da barazanar in tazo gida sai sun ata Mata rai,hakan yasa ta nufi wani gurin.Fatan su Allah yasa ba wani mugun ta ha u dashi ba ya hure mata kunne ta bishi ya cuceta,ko kuma ta ha u da mugayen mutane na zamani su sa ta nufi wani gurin. Ire-iren wa annan tunanin sukai ta yi,yayin da damuwa fal zuciya tasa su du ufa da addu'a . **************************** Tun fitar Laraba malam ya tashi ya lalubo inda ya ajiye wayarsa jiya da dare kafin ai masa aukar amarya. Malam Garba ya shiga kira,inda yana agawa baiko amsa gaisuwar dayake masa ba ya shiga fa "Wallahi ka fa awa uban Maryam yazo ya auki kayarsa,Inba haka ba kuwa zaizo ya auki gawarta,danma kada ace na fara shan jinine, wallahi dada kaina zan tsinke mata jijiya kowa ya huta,dan haka ka sanar dashi yazo ya arsa ai bani na halliceta ba da zan gyara mata hallaya,tunda haka Allah yaso ganinta sai su ha ura". Bai ko jira amsar da zai bashi ba ya gintse kiran,danma wai karya yi masa maganar da zata karya masa zuciya dan yasan halin yaron nasa. ***************************** Shi kuwa malam Garba baiyi asa a gwiwa ba yaje ya sanarwa da baban Maryam sa on malam,amma bai fa a masa maganar in da malam yace ba,yadai ce masa kawai Maryam na garinsu yaje ya taho da ita. Hamdala baban Maryam yayi kafin yajewa da Huwaila maganar,itama tayi farin ciki sosai,aikuwa ba ata lokaci baban Maryam ya hau shirin tafiya Jigawa a wannan safiyar. ***************************** Maryam sai da ta gama zaga gari kaf,har gidansu Iro mahaukaci taje ta tarar wai ya tsere amma taso yauma ta tsokano shi.Yawo tayi mai isarta,wanda sai kusan arfe biyu na rana ta dawo,tun a hanya take jin hankalin ta yayi gida,sai dai tsoron dukan babanta takeyi,dan indai na umma ne ta saba dashi, amma baba dukan mutuwa yakeyi,hakan yasa ta shiga tunanin mafita,amma harta iso gidan bata cimma matsaya ba. Turus tayi ganin babanta zaune a zauren shi da malam suna hira,gabansa ga kwanuka nan da alama ma harya ci abinci ya an huta.yi tayi kamar ta koma da baya sai taji Muryar babanta yana fa " Maryam mutan Jigawa ,wato daga Legas sai Jigawa ,Allah ya shiryamin ke kinji" a yanayin maganar tasa dayayi kawai sai ya bata tausayi taji zuciyarta ta karaya,cikin sanyin jiki ta ara so gabansa ta tsugunna sannan tace"Sannu da zuwa baba,dan Allah kayi ha uri wallahi ba......." Dakatar da ita yayi ta hanyar fa in "ba komai kinji maza shiga ki auko kayanki mu tafi naji na ha ura Allah yayi miki albarka". Da Amin ta amsa duk jikinta a mace ta mi e ta shiga gidan,Can gefe ta hango iyalan malam kamar masu zaman makoki,dan tun abinda ya faru daren jiya sam basu da kuzari suna jiran hukuncin malam ne da zai yanke. aki ta samu laraba tana yiwa ayyaba fa an guduwar da tayi ana mata kitso,Da sallama ta shigo cikin akin Laraba ta amsa cike da fara'a. Ba ata lokaci ta nufi gurin data ajiye kayan ta dayake Laraba tasan da zuwan babanta kuma tasan yazo su tafi ne ta kalleta tace " Wai duk shirin tafiyar ne Maryam?" Murmushi tayi sannan tace"wallahi kuwa Anty Laraba". "Ai dai komai sauri kya tsaya kici abinci dai ko?" Dayake Maryam bata wasa da cikinta,samun guri tayi ta zauna batare data Musa ba,nan Laraba ta tashi ta kawo mata abinci,a zuciyar Maryam tana ta tunanin ikon Allah, ganin yadda Laraba keda kazar-kazar bata ko jin nauyin jikinta sam. Saida taci ta oshi kafin ta shiga yiwa Laraba sallama,wadda take jin kamar karsu rabu,itama Maryam in haka, ayyaba kuwa saboda azabar data sha ta kitso gashi ko rabi ba'ayi ba yasa taketa murnar tafiyar Maryam in.Suma matan malam sunyi sallama da ita,abin mamaki ciki babu wanda ya nuna mata wani abu,cikin mutunci sukayi sallama ta tafi zaure. A nan ta iske babanta inda ya mi e bayan ta ajiye kayan ta koma ta auko sauran,nan baban yayi gaba ita kuma ta tsaya sallama da malam,wanda ko kallonta baiyi ba,saida ta kuma maimaita ta zata tafi,a fusace ya juyo yana fa in "naji a sauka lafiya" Mi ewa Maryam tayi tace"Allah yasa baba malam" tana kaiwa bakin ofa taji ya kuma cewa"Allah ya raka taki gona" Ita dai Maryam bata ce komai ba harta arasa inda baban ya auki akwati ita kuma ta ri e dayar jakar tata da kuma hand bag inta. an mashin suka tara ya kaisu titi nan bada da ewa ba suka samu motar zuwa Kano,suna tafe baban Maryam na mata hira,dan yanzu hankalinta ya kwanta tasan babanta da sau in kai wani lokacin,in aka ureshi ne fa to nan jiki magayi,dan bai iya duka ba. ***************************** Sun iso gida lafiya, lokacin umma na tsakar gida tana tsintar shinkafar da zata dafa da dare. Sallamar da Maryam in tayi ne yasa umman agowa da sauri tana ajiye farantin.Baban Maryam ne ya biyo bayan bayanta auke da akwatin Maryam Hararar da umman ke aikawa Maryam in ne yasata sunkuyar da kai,cikin aga murya umma tace"kin kyauta abinda kikayi, Wallahi sai kin san kin......"ya isa haka Huwaila" ,baban Maryam ya katse mata fa an,kinga ke Maryam maza wuce ciki ki samu kiyi sallah kinji" . Ba musu Maryam ta shiga akinta da kayanta. **************************** " Kinga umman Isma'il nagama yanke hukunci harma nasamu baban yaron munyi magana dashi ya amince,sadaki kawai zasu bayar idan yaso duk wani abu yayi mata daga baya,gara bata gabanmu hankalinmu yafi kwanciya,amma bazai wuce sati biyu ba nan gaba za'ayi komai mu huta". "Nifa ban i ta taka ba baban Maryam,sai dai ina duba mijin daka za a mata da kuma yanayin gidan da zata zauna,kasan dai halin Delu gwamnan bashi,kuma ma kasan halin Maryam in ta ina tsoron abinda zai biyo baya,kaga fa Idi gurgu baida mutunci ko ka an". "To ai rashin mutuncin nasa na duba shi yasa ma nace zan bashi ita,dan shi zai daidaita mata sahu,yanzu ina ita Maryam in kirawo mana ita ma in sanar mata". Kira umma ta shiga walawa Maryam,ba jimawa sai gata tayi sallama ta shigo ta tsugunna ta gaishesu cike da ladabi,wanda duk suke mamakinta,dan sun lura tunda ta dawo daga balaguron da tayi wata sabuwar nutsuwa take ji. Babu ata lokaci baban ta ya shiga sanar mata hukuncin daya yanke akanta,ya kuma fa a mata wanda zata aura.Duk sun zuba mata ido suna son jin ta bakinta,amma sai suka ji tace,"ba komai ba duk abinda kuka yanke babu damuwa zaku sameni mai bin umarninku,tunda kunga na dace da Idi gurgu na amince zan aure sa". Dukan su cike da mamaki suka kalleta har baban yana tunanin ko dai ya fasa mata wannan auren ne,tunda yaga ta nutsu,sai kuma wata zuciyar tace dashi gara dai ayi matan yafi.Albarka yasa mata kafin yace ta tashi ta tafi,tana fitowa ta shige akinta tana dariya asa- asa a fili ta furta "zakuga Idi gurgu baba......." alamin khady* *'YAR CASKALE* ( _Sanadin bakin uwa_ ) *NA* *KHADIJA USMAN* (Real ta maigari) *____________________________________* AINUWA RITER'S SSOCIATION ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* 9 Misalin arfe 8 na dare Maryam na kwance saman katifarta tana game mai maciji a wayar umma Isma'il ya shigo. Cikin muryarsa data koma ta mashaya yanzu ta bu e ta ara girma yace da Maryam" ke dayalla malama tashi ki kawomin abinci yunwa nake ji". agowa tayi tayi masa kallon sama da asa kafin taja tsaki ta mayar da kanta ga abinda takeyi batare data tanka masa ba. Cikin zafin abinda tayi masa ya lailayo wani uban zagi ya maka mata,aikuwa itama ta mi e daga kwancen da take ta lailayo kalar nata mai tsadar ta afka masa.Sanin da Isma'il yayi ko sunyi fa a ba abinda zai tsinta saima shi yasha wahala hannun Maryam in,dan sun saba fa a kuma duk lokacin da sukayi yayi arin dukanta haukace masa takeyi,domin duk abinda ta rarumo buga masa takeyi,yanzu haka yanada tabonta sun kai guda uku da aka masa inki,da alama yarinyar ba ita ka ai bace. Ganin ta mi e tana kutuntuma masa ashariya tare da ikirarin suzo su daku yasa shi nufar ofar fita yana tanga i da fa an gaggo a kofa.Umma dake sallar isha'i tana jiyo su,amma kafin ta sallame ta fito Isma'il ya fice. Girgiza kanta kawai tayi tare da yiwa yaran nata fatan shiriya,sannan ta nufi kitchen in dan duba ko Isma'il in ya auki abinci,karya auki na babansu.Ta fito kenan yaro yayi sallama,inda ta amsa masa sannan yace"Wai ana kiran Maryam inji Idi gurgu". an jimm umma tayi kafin tace da yaron"je kace tana zuwa" nan yaron ya juya ya fice. Maryam dake kwance duk tana jiyo abinda akeyi ta mi e tsaye cikin sauri ta tattaro abinda zata tattara sannan tayi saurin saka hijabi ta nufo ofar akin. Kicibis sukayi da umma itama tana shirin shigowa sai Maryam ta anja baya ka an, da kallo umma ta bita tana fa in" ina zuwa kuma naga kina wannan saurin hak?" "Kiran da akemin zani umma". Wani kallon tuhuma umma ke binta dashi,amma sai ta share kawai tace,"kibi dai a sannu wannan rawar kan naki ki ajiye shi gefe". Da sauri ta ra a ta gefen umman nata ta fice tana fa in "to umma bama da ewa zanyi ba ai yanzu zan dawo".Tana jiyo ummanta na fa in "oh ni asu! Wannan yarinyar dai Allah ya shirya". ***************************** Jingine ta hangoshi shi jikin dakalin ofar gidansu,inda ta saki murmushi ganin yadda yayi tsayuwar,dayake bakin layin nasu akwai masu sana'ar