Sashe 15
Yar Caskale Part 1 Complete Hausa Novel.doc · about 8 min read
dole jamilu yayi arfin halin tafiya dan bu ewa yaga waye. Yana zuwa cikin rawar murya yace" wa..ye?" "Ni ce" yaji ance. Jin kamar Muryar mace kuma ba cikin damuwa ba yasa shi zare sakatar ya an ziro kai sai yayi kaci is da farin abu zulum a asa,sannu a hankali yake bin asan da kallo har zuwa sama,nan yayi ido biyu da fuskar Maryam data bursune da farar hoda. Wata ara ya kwalla ya nufi cikin gidan da gudu yana kiran fatalwa....... alamin khady* *'YAR CASKALE* ( _Sanadin bakin uwa_ ) *Na* *Khadeeja usman* (Real tame Gari) _Mrs bello_ *____________________________________* AINUWA RITER'S SSOCIATION ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* "Kai jamilu! Nafa sanka da aryar bala'i a ina ka ta a ganin fatalwa bare har kace wai yanzu gata ka kuma ganinta" Cewar baban ummita dake gefe yana makyarkyatar jin an ambaci fatalwa,ba aramin ma jarumta ya aro ba daya tsaya yin wannan dogon sharhin. Suna shirin yin magana suka jiyo Muryar Maryam daga bakin ofa tana rafka Sallama. Dukansu shiru sukayi babu me jarumta ko alamar amsawa.Wata sallamar ta kuma kwa owa.Da kyar Raliya ta amsa murya na rawa"wa'alaikis....sa..la..m". Dariya Maryam tayi dan ta gane Muryar Raliya,ta kuma san ita ta goyata ta kaita zauren gidansu ta yar.Dan haka cikin 'yar ma e murya tace"yauwa Raliya dama ke nake ta jira tun azu kizo akai mu tare,dan tun jiya akaimin wankan gawa ance ana fitowa daga masallaci za'a kaini, shine nace bari nazo mu tafi tare tunda kin iya goyani can ma nasami me goyani,kai kuma baba kayi sauri ka fito aje kaini dakai.Dan Allah innar ummita kiyimin wainar gero ta sadaka,ki bawa ummita da Asiya sukai har gidan su Hajara awar nan tawa,kai kuma jamilu a baka ka kai har majalissu suyimin addu'a.." Jin shiru ba wanda ya amsa mata yasa tace "Raliya ko in shigo ki goyani daga nan?" Da sauri Rakiya tace"dan girman Allah kada ki shigo,ki bari in turo ta,gata nan ma zuwa". Kuka Raliya take yi tana fa in"inna wallahi ba inda zani,lahirar zan bita alhalin Ni ban mutu ba,tunda ke kika kashe ta ai ke Yakamata ki bita ku tafi". "Kinci ubanki! Cewar Rakiya,sharri zakimin,yaushe na kashe ta, ai a gabanku ta fa i ta mutu". Asiya ce tace"wallahi inna kece kika kashe ta,dan a gabanki muka zo muka same ta,kinga kenan tun kafin muzo ta riga ta mutu". "Yau naji Sharri da safiyar Allah,wallahi ko ku yadda bani na kashe ta ba,ko kuma nace ta tafi damu duka cikin kabarin, inya so a bambance a can". Jin ta ambaci hakan yasa jamilu yace"kinga Raliya tashi ki bita kafin ta shigo Mu ganta,dan wallahi baku ga yadda ta riki e ta koma kalar mutanen lahirar ba,ashe dama in an mutu haka ake komawa?". Maryam ce tace"In shigo?" Baban ummita cikin tsananin tsoro yace" Ka da ki shigo dan Allah,gata nan zuwa". "Wallahi saina shigo" cewar Maryam dake arin aga labulen akin.Cikin rashin sa'a hijabi ya ta iyeta ta afka akin gaba aya dai-dai gaban Rakiya". 'yar dubaidar Rakiya irinta mutan da,dataci jeren su an Chaina da silbobi kai harda tangaran,abin tsautsayi baban ummita garin ya mi e ya gudu aki ya bugeta,dan dama an tokare asan da ana nan duwatsu ne,aikuwa rakwacham duk ta fa o musu.Ita ko Maryam tunda ta yalla ido taga ta fa o dai-dai afar Rakiya,aikuwa ta zura hannu taja yatsan Rakiya da duka suka kacame da ihu,dan duk har ma ota ana jiyo su.Ihun su ne ya jawo hankalin wani ma wafcin su mala Gali da tun azu daya dawo daga masallaci yake jiyowa , kasancewar gari ya waye rass kuma ga ihun yanzu yafi na azu yasa ya shigo gidan yana kwa a sallama.Maryam ce ta mi e tana shirin fitowa malam Gali ya nufo akin yana fa in"malam ummaru wai meke faruwa ne nake jin koke-koke?" Jin Muryar malam Gali yasa baban ummita kiciniyar fa in"yauwa malam taimaka ka fara mana karatun Alkur'ani fatalwa ta shigo gidan nan". "Subahanallahi! Fatalwa a ina kuma?" Dariya Maryam tayi data mi e tsaye tace"Wai fa nice fatalwar Dan basu da wayo,sune fa suka......(nan tabashi labarin duk abinda ya faru)sannan taci gaba da fa in"Ni kuma shine nace wallahi saina tsorata su,Ni ban ma yi niyyar ce musu Ni fatalwa bace,sai da naga jamilun Rakiya ya zura da gudu yace wai fatalwa,shine nace tunda sunfi tsoron fatalwar bari kawai nace nice fatalwar,da niyyata ince ni Aljanace". Jin hakan da ahlin Rakiya sukayi,yasa suka sami arfin gwiwar fara ture abubuwan da suka danne su dan su kama Maryam su marka e ta.Ganin sun yuun ura ne yasa Maryam yi musu gwalo ta sulala a guje har tana bige malam Gali. ************************* A Guje ta shigo gidan tana tana ri e da hijabin a hannu.Kasancewar yanayin na damuna ne kuma yau an tashi da matsanancin zafi yasa suka shimfi a tabarma dan karyawa.Yayin da baban Maryam ke yiwa umma fa an garin ya Maryam ta fita bata sani ba,yana tsaka da yi mata fa an ne Maryam in ta shigo. Da kallo babanta ya bita batare daya ce mata komai ba,sai dai ga dukkan alamu wannan kallon ya bambanta da irin wanda ya saba mata a duk lokacin da tayi laifi.Umma ce ta daka mata harara sannan tace"In kin gaji da yawon barba ar taki na sanyin safiya ki je kiyi arwalla kizo ki karya a kaiki makaranta".Jin da baban Maryam yayi wai ashe ma ko sallah batayi ba ranshi ya ara aci,bai ce dasu komai ba ya mi e ya fice,ita kuma Maryam tayi abinda umma tace tayi. ************************ Ransa a matu ace ya shigo gidan. aki ya shiga ya fito yana dube-dube ya nufi akin su Maryam.A hannu ya fito da bulalar wadda gadan-gadan ya nufi inda Maryam ke zaune tana shan shayi,baiyi wata-wata ba ya shiga shimfi a mata dorinar da dukkan arfinsa. Tashin hankali umma ta shiga,dan tunda take dashi bata ta a ganin fushinsa kamar haka ba bare har takai daya yiwa yaran irin wannan dukan.Duk yadda taso kar ar Maryam abin yaci tura,domin kuwa dataje ha awa yake yi har ita.Sai da yaga Maryam tun tana kuka da ihu harta kasa sannan ya kyale ta ya nufi Isma'il shima cikin acin rai ya shiga tafkarshi.Kukan su daya arewa tare da kururuwar umma ya jawo hankalin makusanta gidan suka shigo.Shima Isma'il da kyar aka kwace shi ,yayin da tsabar acin ran da baban Maryam ke ciki yasa ya kasa magana,wanda ganin hakan da wasu sukayi yasa suka jashi zuwa waje. yar wata ma ociyar su data shigo ta rarrashi umma itama data ke kuka,haka tasa Maryam da Isma'il a gaba tana kuka suma sunayi,sai zuwa can ta tashi ta ora musu ruwan umi.yau hatta Isma'il umma ce tayi mishi wanka ta gasa musu jiki. ************************* Baban Maryam ne zaine da kuma umma,gefe guda kuma mahaifiyarsa ce zaune saman kujera cike da dattako.Kallon umma tayi tace"Huwaila yau naji abinda ban ta a ji ba daga bakin mai sunan malam(daya ke bata fa in sunan baban Maryam ,saboda sunan surikin ta ne dashi,wato sunan kakansa),kin bani mamaki,ina yabonki sallah zaki kasa alwala.A ce da hankalin ki da tunanin ki ace tsawon wannan lokacin kina aibata yaranki,kuma a haka kike tunanin ace yaranki sunfi na kowa nutsuwa da hankali,burin ko wacce uwa ace anta ya zamo nagartacce, wanda ya ginu da tarbiyya ingantacciya.amma ko da uwa tana arin bawa anta tarbiyya kuma tana masa addu'a, matu ar ba zata tsaftace harshen ta akan yaranta ba,to wallahi bazata ta a ganin yadda take so ba,domin dai kamar kina tufka ne tana warware wa,babu amfanin tsayawa dawo da abinda ya wuce,amma kisani banji da in abinda naji ba gaskiya,dan haka na ro eki da girman Allah,bazan so ganin zuriyata ta tarwatse ba,dan haka ki dinga kiyayewa idan rai ranki ya aci,sannan ki yawaita yimusu addu'ar shiriya.kai kuma malam babba,ka dinga kiyayewa da irin dukan da zaka yi wa yara,dan irin wannan sai kazo kayi abinda za'a zo ana dana sani,Shi kanshi yawan dukan ma bashi da amfani yawan nasiha da nunawa yaro wannan ba dai-dai bane,kaza shine shi ne Yakamata kayi,ka dinga tara laifin yaro rana aya kayi mishi hukuncin da idan ya tuna dashi a duk sanda zai aikata wani abu mara kyau,zai san gamuwar ba kyau,amma ba ko yaushe duka ba.Haka dai tayi musu nasiha mai ratsa zuciya.Kamar yadda na fa a muku acan baya,umma tanada kirki da kyauta,haka ta samu abin bawa baba da zata tafi. Kusan wannan dukan da baban su Maryam yayi musu yasa an sami sau in abubuwan da suke yi,dan yanzu baya sakar musu fuska sosai,dan haka suke jin tsoronsa yanzu. Ita ma Umma ta rage kaso mafi yawa na hayagagar da take yi akan su Maryam in.Cikin anin lokaci aka mayar da Maryam makaranta,shima Isma'il sosai baban ya sa ido akanshi, kasancewar. Basu da lokacin zama duk suna makaranta yasa aka samu sau in abubuwan da dama. Baban Maryam da kanshi yaje har gidansu Rakiya ya basu hakuri gaba aya,dan dama ranar da ya yiwa Maryam wannan dukan, malam Gali ne yazo yake fa a masa abinda ke faruwa. ************************* A yayin da muke tafiyar da rayuwar yau da kullum cikin farin ciki ko akasin haka.Kwanakin mu nata tafiya tare da lokacin mu.wasu abubuwa sun faru,ciki harda shurawar lokaci,yayin da Maryam ya zuwa wannan lokacin idan ka ganta zakayi mamakin ita ince kuwa.Duba da yadda ta kasance,zamu iya kiranta da yarinya mai matsakaicin tsawo,ba fara bace haka kuma ba zamu kirata da ba a ba,tana da kewayayyiyar fuska tare da madaidaitan idanu,wanda fuskar ke auke da hancinta tare da bakinta irin namu,zan iya cewa a dai jinsin mu na ba ar fata kuma Hausa Fulani , muna iya kiranta da kyakkyawa amma ba can ba. A tsawon wannan lokacin zan iya cewa wani abu dai ya ragu game da Huwaila,sai dai fa bakin nan na nan,dan kun san ba'a iya canza wa mutum zuciya sai dai a fa a masa da baki ko zai gyara. A wannan lokacin kam zagi da baki bamu san iya adadin da yaran suka sha ba,wanda har baban ya gaji ya zubawa Huwaila ido.I zuwa yanzu shima