Sashe 19
Yar Caskale Part 1 Complete Hausa Novel.doc · about 8 min read
wallahi da baki kawo kanki ba,in juninki bin bokaye to yau kin tadda gidan koya hankali,ni kinma taimaka min zan samu ku in ankon ummita(dan yanzu sun zama awaye),dan haka bari inzo gareki". Da sauri ta dakatar da tutun da takeyi ta tsarkake jikinta da hannunta ta bu ofa,inda ta hango zulai zaune ta zuba tagumi tana zaman jiranta.Da wata iriyar malkwa a ta taho tana juyi me kama da hajijiya,yayin data aura ankwalin kanta yadda zai zubo baya harta iso gaban Zulaiha,wadda tun fitowar Maryam da taga yanayin samfurin rawar ta mi e tayi bakin ofa amma bata fita ba,ta tsaya dai tana jiran ace arrr ta fece. Tana kallon Maryam nata lankwashe-lan washe harda hajijiya dasu juyi wanda daga arshe ta fa a saman gado.A hankali ta tako tazo dai-dai fuskarta tana le awa.Caraf idonsu ya sar e dana juna,yayin da Maryam ta tashi tana mutstsike idanu.Saida ta gama dai-daita zamanta akan gadon kafin ta kalli Zulaiha tace" lah Anty zulai kice kin iso,ai yau a gajiye nake dan kwana nayi akan aikinki,wancan ya hau wancan ya sauka,tun kusan arfe biyu indiyawa suka hau kaina naketa ti ar rawa sai yanzu suka sakeni. Sannu Zulaiha ta shiga jera mata,kafin cikin aguwa ta samu gefen gadon ta zauna tana jiran taji abinda Maryam zata ce.Sai da Maryam ta gama ja mata zare son ranta kafin ta kalleta tace"Zulai ko zakimin bayanin abubuwan da kika aikata game da zamantakewar ki a gidan aurenki,zan ji abubuwanne idan kin min arya to bazan miki aiki ba,idan kuma kin fa amun gaskiya dai-dai da abinda nagani da kuma abinda su tsurwata suka fa amin to zan taimaka miki". Zulaiha ta dade tana nazarin ta fa a ko karta fa a,amma jin ance in tayi arya za'a gane tasan kuma lamarin aljanu yasa ta karkakace tana tonawa kanta asiri,da irin malaman da take biya har takai aya.Jin tayi shiru yasa Maryam kallonta tace "duk naji bayanan ki ,kuma tsitaka tace zata taimaka miki amma fa aikin na da wahala sosai". Zulai dake zaune tana sauraron abinda Maryam ke fa i,tare da jin komai wahalar aikin zata iya,dan Maryam bata san abubuwan wahalar data aikata bane,tasan duk wuyar wanda Za'a ce tayi bazai kai na baya ba,dan haka cikin warin gwiwa tace"kada ki damu koma menene ni zan iya aikatawa matu ar ba kisan kai bane". Girgiza kai Maryam tayi sannan tace"Da farko dai aikinmu na bukatar sirri,ba kuma wanda zaki fa awa.Shara i na biyu kuwa kince min bakya girki sai dai ya siyo muku abinda zaku ci kullum,to 'yar tsiko tace zakiyi dakan sakwara kiyi sadaka dashi,kuma doyar da zaki daka ki tabbatar zata kai warya guda,ma'ana guda ari kenan,sannan nice zanyi miyar,bayan an saka hantar Giwa,sannan a samo fatar yaro ba ashi ,za'a samo farar macen uda wato zabiya,sannan za'a samo kan ba in ra umi guda dubu,sannan........"Dan Allah ya isa haka Ni kawai a fa amin ku in in bayar, ina ni ina samo duk wannan tarkacen da aka fa "To shikenan matawalliya tace zata au nauyin sa kanta ha ari ta samo miki muddin zaki biya,sannan shara i na gaba,Bama son muna aiki ana ata mana,ba'a ha a aikina dana wani,sannan babu katsalan dan,duk abinda kika gani kada kiyi magana a cikin gidan nan domin yin maganar zai iya jawo miki hauka tuburan,ki tashi kije,in kin amince da sharru an mu kizo a fara aiki........" *_BARKA DA SALLAH GA AUKAKIN MUSULMIN DUNIYA,INA FATAN KUNYI SALLAH LAFIYA_* ALAMIN KHADY* *'YAR CASKALE* ( _Sanadin bakin uwa_ ) *NA* *KHADIJA USMAN* (Real ta maigari) *____________________________________* AINUWA RITER'S SSOCIATION ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* Maryam ta jima a falo tana jiran fitowar Jazuli da Ummu amma shiru,a haka Zulaiha ta fito ta same ta cikin shiga ta ana nan kaya,three quarter sicket ne a jikinta,tare da wata riga ar ficika,siket in ya bayyanar da siraran waurikan ta,yayin da fuskar nan data ko e da beliching ta fito ra au da ita dan tasha jan jambaki. "Sannu anwata" ta furta.Maryam da duk zaman da takeyi na jiran abinci ne,domin ta saba a gida duk inda 7:30am tayi sun karya,dan haka a kasalance ta furta"Yauwa anty zulai harkin fito?" "Wallahi kuwa anwata,naga ke kinma jima da fitowa da alama". "Eh wallahi yunwa ce ta dameni,domin ban saba kaiwa har wannan lokacin ban karya ba,ko kin ha a abin karin ne?" "Ai Ni bana girki na fa a miki,nasan yanzu my sirinji zai fito bari ma naje na taso su,tayi maganar tana arin mi ewa,yayin da Maryam tabi bayanta da kallo,a fili ta furta 'yar shamula kenan.Tana gab da arasawa part in sukayi kaci us da Jazuli yana shirin fitowa.Sanye cikin wasu ruguza-ruguzan kaya na shan iska,fuskar nan washe kamar wanda akaiwa albishir da wani abun da i.Da kallo Zulaiha ta bishi tana jin wani zafi da tu in ba in ciki da wani kafirin kishi na taso mata,amma data tuna da batun boka Maryam da kuma yarjewa zuciyarta zata iya jure kowanne irin abu ne akan cimma muradinta.A yanayi na ba yabo ba fallasa ta arasa tana fa in"Barka da fitowa mai sirinji". Shafo gefen fuskarsa yayi alamun duniyar tayi masa da i,kafin cikin muryarsa ta jan hankalin matarsa yace"Yauwa my vitafoam fatan kin tashi lafiya". Saida ta balla masa hararar takaici a kaikaice kafin tace,Lafiya alau,dama tun azu anwata keta jiranka wai yunwa take ji".Takowa ya fara yi zuwa falon yayin da yanayin tafiyar tasa ma kanta abin kallo ne Masha Allah! Yana arasowa ya samu guri ya zauna irin zaman nan kamar ya dira,inda yana zama sai da kujerar ta motsa.Maryam kam har yanzu tanata ara jinjina mu'ujiza ta ubangiji tare da ara gode masa da ya yanko ta da tsada,dan gara zubinta akan na Jazuli da aka yankoshi da araha injita.Washe baki yayi ya shiga fa in"Ah sister ce kenan tunda safe take jin yunwa ko? Aimin afuwa kin san sabon ango". Maryam dake unshe dariyarta dan tana lura da Zulaiha da kallon da takewa Jazuli,cikin salon jan magana tace"Gaskiya ne yayana kaga kuwa yadda kake wani she in angonci". ara baje baki yayi yana arza dariyar basawa wanda ya ara sa Maryam sake magana tace"wallahi yaya jazuu da ace indiyawa zasu ganka da sun auke ka sun shirya maka Film". Cikin yanayin jin da in maganarta yace "Allah ko sister?" "Wallahi kuwa yayana, musamman ka fito a irin an daban nan na gidan boss".Gaba aya fara'ar fuskar sa ta auke yace"Bama a jarumin Film in ba wato a karen boss zan fito ko?" Dariya tayi ta gyara zama kafin tace"Ai kasan anfi son masu kalar mugaye kuma wa anda suka ware wajen iya shan giya da koken da kuma iya zu ar sigari tare da jan shiii......"Sada allahul azim ar uwa me kike karyawa dashi a kawo miki"ya fa a dan son katseta daga zayyanar datake yi a gaban Zulaiha,amma ko yarinyar nan anyi hegiya,wato dan taji yace baya son matarsa tasan yana an afe-afe da kore-,kore harda zu e-zu e shine take son Tona masa asiri,saboda taji yace baya son Zulaiha ta sani".Daga yanayin daya katseta yasa ta fahimci ya gane inda ta dosa,a zuciyarta tace "Ni wallahi ko ni kaina wani lokacin tsoron kaina nakeyi na zama wata iri kamar wadda akaiwa asiri saboda tsabar rashin son ganin ana zaune lafiya".A zahiri kuwa cewa tayi"To nayi shiru yayana tunda na fahimci baka son a sani,nidai ku bani duk wani abu daya danganci abinci ba ruwana da za ar kala". Ummu ce ta fito sanye cikin shigar doguwar riga ba a,bakin nan yasha lipsglows anata baza amshin amare.Wani wula antaccen kallo Zulaiha ta bita dashi,tana shirin yin magana suka ha a ido da Maryam tayi mata alama da tayi shiru,ba dan ta so ba sai dan cika umarnin bokanya maryam.Itako Ummu dan ta tura wa Zulaiha haushi dan tana da labarin ta a gun mamanta yasa ta arasawa kujerar data ga Jazuli akai 2 seater ce amma ya kusa cinye abarsa, an gurin daya rage nan ta nemi yiwa kanta matsugunni dan bala'i da sa kai saida ta kutsa ta zauna.Sai da ta sa alo hannunta a wuyansa tare da kwantar da kanta a kafa arsa kafin ta wana ido ta kalli angaren da Zulaiha take zaune data cika tayi fam tace," Ina kwana Anty" Bata amsa mata ba,illa aiko mata da wata banzar harara da tayi,itako ko'a jikinta ta ta e baki,dan ya zuwa yanzu tana jin zata iya goggaya dako wace irin mace akan kifin gwangwanin ta,domin al awuran daya mata iya daren jiya sun isa su canja rayuwar ta itada 'yan uwanta,dan haka itama ta aikewa da Zulaiha tata hararar,wadda hakan yasa zuciyar Zulaiha tasowa tazo iya wuya, musamman yadda taga Jazuli na shafo hannun Ummu dayasha lallen amare. A zuciye Zulaiha tayi magana tace" Jazuuuli ina son a kawomin doya warya aya".Cike da mamakinta ya kalleta jin ta kirashi da ainihin sunansa wanda a tsawon zamansu har ya manta ma lokacin da zai ce ta kira sunan shi,sannan gashi tace a kawo mata doya har warya guda.Yana tsaka da wannan tunanin yaji ta katseshi tace"ko bazan samu bane insa a kawomin da kaina?" Girgiza mata kai yayi alamar ah'ah,ya kalli Ummu Yace"Amarya aukomin wayata in kira makel yaje ya samo doyar."Mi ewa Ummu tayi cike da kwarkwasa ta fara tafiya,Maryam dake zaune tana jinjina lamarin kishi irinna wasu matan tunda Ita dai bata ma san meye soyayyar ba bare kuma tasa ran sanin kishi,dan haka ta dinga dariyar mugunta a zuciyarta.Dawowar Ummu ne ya dawo da hankalinta inda taji tana cewa "gashi my ginger".Dariya ce ta wacewa Maryam inda cikin salon jan magana tace"Amarya duk a cikin love in ne ko kuma kin shawu ne an an afa na safe,dan naji kin fara sakin layi,da alama babbar kwalba ya kawo me zafi,tunda naji ana kiransa da ginger,ince dai baki sha i abar ba wannan......"Kaiiiii taji Jazuli ya fa a da arfi,hakan ya katseta,amma kuma ko da ta waiga sai taga bada ita yake yi ba a waya yake wannan hargagin.Shi kuwa a nashi angaren yayi hakan ne dan katse wannan yarinyar,ashe haka take da an banzan surutu,daya san batada sirri da bai fa a mata