← Book details Yar Caskale Part 1 Complete Hausa Novel.doc Local reading mode
READING PART 7 OF 34

Sashe 7

Yar Caskale Part 1 Complete Hausa Novel.doc · about 8 min read

shiga fadin"a shema Kaka sauri mukayi Dan Ina zuwa na tarar da innar laraban ma ta dawo daga kasuwa wajen siyen kayan gado ana debo kayan tarkacen Kuma a cikin gida,zuwana ba jimawa suka kammala shine muka taho gaba d'aya,a Nuna Mana d'akin saboda maza zasu shigo da kayan katako..........." *Team laraba gareku* *Wai Ina team malam ne,Ku fito a kafta* *Alkalamin khady* *_'YAR CASKALE_* ( _Sanadin bakin uwa_) *N *KHADIJA USMAN* ( _Real Tame Gari_ ) ____________________________________ KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ______ ______________________________ _Idan laraba ke Saku dariya,ni comment d'inku ke Sani dariyar wallahi,gaskiya ba abinda zance muku fans sai godiya, Allah yak'ara k'auna, Duk masu comment wlh Ina gani Kuma Ina godiya kwarai,masumin addu'a ma duk nagode_ ************************* Dan tsabar mamaki ma shi malam daina Jin zugi da rad'ad'in ciwon hannunsa ya daina ji.Ita kuwa kakar laraba ta kafa ta tsare tana Nuna inda za'a ajiye kayan, dai-dai k'ofar dakin data zab'awa laraba.Kusan duk kayan tare da laraba aka dinga kiciniyar shigo da su dan zumud'i.Saida aka shigo da kayan kaf,kafin Kaka ta kalli d'ayan saurayin tace" yauwa laminu,Dan Allah in kun fita ka biya gindin gawo shagon haruna me siminti,kace Masa yazo Nan gidan malam ja'afar ana nemansa". Da "toh" ya amsa Mata yasa Kai ya fice,sannan tasa wasu yaran cikin wadanda suka kawo kayan Suma tace su d'ebo musu ruwa a rijiyar gidan.Haka ko akayi nana da Nan suka cika musu robar sabuwa fil, aka shiga alwala Nan suka shimfid'a k'atuwar tabarma a k'ofar d'akin da suka za'bar ma laraba.Duk kowa da kallo ya bisu,yayin da matam malam suka koma gefe suna gunguni,Dan suna tsoron suce wani abu laraba tabi takansu,Dan sun lura tun d'azu ita kad'ai sai had'a zufa takeyi,da alama jira takeyi ace kule ta casss. Duk inda suka waiga neman Maryam ba Wanda ya ganta ko yasan inda ta nufa. *********************** Itako Maryam daga Nan ba inda ta nufa sai gidan su laraba,dayake Babar laraba ta ganeta saita hau washe baki tana tambayar ta ko me akeyi a gidan? Aikuwa Maryam ta karkace duk ta zayyano Mata duk abinda matan malam sukayi harda cewa tai Wai sunce laraba kuncen yunwa ce,gashinan ya Nuna a jikinta Bata samun wadataccen abinci,yanzu Haka ma sunce you bazasu bawa malam tuwon dare ba. Aikuwa a fusace mahaifiyar laraba tasa aka Nemo Mata Yara,Nan tasasu suka shiga kamo Mata zakaru da kaji,Wanda kusan rabinsu duk na laraba ne da ake Bata,Kuma dayake kiwon ya karbeta sai sukaita yawa ba'a ci bakuma Wanda ya Isa ya taba Mata,wasu su mutu ana gani Amma baza'a yanka ba. Saida aka kusa kame Rabin kajin,tabawa yaran kudi tace sukai bakin kasuwa gurin Idi Mai gyaran kaji ya yanka ya gyaro. Yaran Basu wani jima ba suka dawo dauke da gyararrun kajin,Dan yanada Yaran da suke taimaka masa.maryam cewa tayi zataje ta dawo saita kaiwa malam d'in. ************************ Shikuwa malam bayan idar da sallar la'asar Dan wani zazzabi ne ya rufeshi Dan ciwon hannun nashi,ga takaicin abinda ke faruwa ga Kuma matansa da suka rufe idonsu sukaita zazzaga Masa rashin mutuncin da tunda sukayi aure Basu taba Masa ko kwatan kwacin sa ba,gashi yanzu Haka Wai bwasu kawu Nan laraba suna nan suna jiransa Wai maihaifiyar laraba ta aika musu akan shi malam din Yana son ganawa dasu,shi yasa abun ya hadu yayi Masa yawa. Malam nuhu dake gefensa ya kalleshi Yana nazarin malam d'in,da tun d'azu yaketa faman tunani yace" ala gafarta malam,Wai meye gaskiyar wannan maganar ne, Dan ni abin ya dauremin Kai,domin Naga kamar akwai alamun gaskiya a maganar yarinyar Nan,Dan Inka duba yarinya ce k'arama da batayi giraman da za'ace ta iya had'a irin wannan abun ba,Dan Haka ka fad'a Mana gaskiya musan abinyi mu sallami wadan can dangin turun tun kafin abin nasu ya motsa Dan kasan dai asali" "Wannan Haka yake" cewar malam labaran,gara ayi duk abinda ya kamata,dan banza bata kai zomo kasuwa" Jinjina Kai malam yayi wato ma kowa ya yarda kenan ko? Lallai baya raba d'ayan biyu yarinyar Nan Maryam tana da nasaba da jinsin arnan farko,wadanda Basu San ma da Allah ba,Basu tuna mutuwa bare su San da hisabi,Kuma duk yadda akayi daga k'aramar hukumar munafukai yarinyar Nan ta fito,dama ana cewa kano ta dabo tumbin giwa, Koda me kazo an fika,tabbas ya yadda,Dan gashi yau yaga yarinya ma k'arama ta fishi gulma da sharri da had'in husuma.Tabbas yanzu ya lura bashida wata mafita illa kawai ya amincewa auren laraba ,badan komai ba sai Dan shima ya rama karyashin datai,Dan shi ba mutunci ma wallahi a cinya zai karyata,ita kuwa maryam Kiran ubanta zaiyi yazo ya d'auki abarsa,Kai bama ita ba dukkan yaran dake gurinsa kowa yazo ya zo ya d'auki 'yarshi inya so ma yaran su koma fashi da makami ba abinda ya shafe shi,Dan an maida shi matattaran 'yan iska da yarinya ta Fara kangarewa sai a d'auko a kawo Masa,to shima ya kile yanzu ba wadda zai k'ara dauka,Maryam duk ta jamusu. Baiko bi takan su malam nuhu ba ya fita yana me cije baki,Dan ciwon da hannunsa yayi masa,a zuciyarsa kuwa,Yana kissima yadda zai Kama kashin laraba yai Masa karayar wulak'anci. A Haka ya fito ya samu kawun nan laraba su biyu.nana yace musu ai shi ya tura a kirawosu Dan Yana son a d'aura auren sa da laraba yau d'in nan.dukansu hamdala suka shigayi,daga bisani yace Yana zuwa.bai wani jimaba a d'akinaa na zaure ya fito da kud'i a hannunsa ya damkawa malam nuhu yace ya k'irga.Koda yagama k'irgawa yace" dubu ashirin ne cif" Gyada Kai malam yayi kafin yace" wannan sadakin laraba kenan Ina son kaimin walicci" Batare da gaddamar komai ba ko ya amsa da na'am. Nan suka dunguma zuwa masallaci,aka Kira liman da Dan sauran jama'a Nan take aka daura auren malam ja'afar da laraba,aka sadaki naira dubu ashairin lakadan ba ajalan ba. Tab zamusha biki alkur'an *Alkalamin khady* *_'YAR CASKALE_* ( _Sanadin bakin uwa_) *N *KHADIJA USMAN* ( _Real Tame Gari_ ) ____________________________________ KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ _fans Ni da ku,ba'asan Wanda dariyar zata jigata ba,ku Kuna dariyar laraba,Ni Ina dariyar comment d'inku,gaskiya ba abinda zace,kun bani nishadi dai-dai iyawarku Allah yabar k'auna ya k'ara zumunci amin_ ************************** Tuni labari ya iso cikin gidan an daura auren laraba da malam.Aikuwa Nan k'aramin bala'i ya tashi,domin kuwa su salame rashin mutunci kawai da ruwan bala'i sukeyi.Ita kuwa Kaka Koda haruna me siminti yazo,ce Masa tayi dama fenti suke so ayi musu,ba Bata lokaci ya fad'a Mata kudin,Babu ko neman ragi ta Lalo su a lalitar ta ta damka Masa da cewar yayi sauri fa.yana fita kuwa yaje shagon say Nuna kwarewa irin tasa da Kuma son janyowa kansa kasuwa,harda had'o me kala biyu Kuma na musamman da a ganinsa zai haskaka d'akin,wato yellow da Kuma dark blue ,Haka ya tattaro yaransa suka d'unguma gidan malam aka hau haramar fente d'akin laraba batare da b'ata lokaci ba. Duk masifar da matan malam keyi ko a jikin laraba,domin farin ciki kawai ya cike Mata kowanne gurbi na jikinta,babu wata kusfa da bacin rai zai samu zarafin shiga,Dan Haka ko kallonsu batayi ba.Ganin Kuma anata fenti ya k'ara hasala su,Nan fa salame ta aika a kirawo yaranta idi da mamuda a can gidan biredi su zo su lakadawa su laraba dukan tsiya. ************************* A can gidansu Laraba kuwa,duk an aikawa yayyenta dake gidan aure,Jin kanwarsu ta auru duk suka dungumo zuwa gidan,batare da b'ata lokaci ba tab ashe laraba ba ita kadai bace hankatamar ba,sai dai duk ta fisu girma,Dan abun kamar bin bi akayi shi,wata tafi wata,to ita laraba sai nata yafi nakowa. Cikin matan kawunansu laraba wasu masu hankalin ciki suka zo da kyar da lallabawa suka tafi da laraba gida,akan anjima zasu zasu kawota kamar yadda al'ada ta tanada.Da kyar laraba ta bisu Saida Kaka ta lallaba ta tukun. Bawani mashahurin gyara sukai Mata ba,amma dai a kauye Kam ta gyaru. Shikuwa malam tunda aka d'aura aure aka nemeshi aka rasa,abinda Basu Sani ba kuwa malam wata hanya ya yanka ya Miki daji,Saida ya tabbatar yayi nisa da gari Kuma ba Mai ganinsa ya labe jikin wata bishiya kawai ya rushe da kuka.Sai da yayi me isarsa yaji har kanshi yafara ciwo tukun yayi shuru ya shiga tunanin hanyar dazai bi ya azabtar da Maryam kafin ubanta ya zo ya d'auke ta,haka kawai taja Masa,'yan kudaden Daya ajiye dan noman bana dazaiyi gashi tasa ya fito dasu,Shidai yasan aure sunna ne,shiyasa ma ya auri har Mata biyu,Kuma harga Allah su kadai sun isheshi,su kadai yaga zai iya ciyarwa da 'ya'yan da Allan ya bashi,amma gashi tsabar rashin mutunci irin na yarinyar Nan,tasa shi auren dole,in ba iskanci ba,ai da alama babanta Mata d'aya gareshi,meyasa Batace ya auri laraba ba sai shi,gashi dama yanada labarin bala'in cin abinci irin na gidansu Laraba da sukayi gado gun babansu,Wanda Koda ya tashi mutuwa sai a akori kura aka dauke shi ga tsayi ga kiba.shi yanzu babbar damuwarsa ba dama ya saki laraba,dan ana Masa kallon mutunci,Yana wa wasu wa'azi akan zamanta kewar aure aikuwa shi yanzu baya Bari asamu wata baraka daga gareshi ba. Tunawa yayi da uwar garar da aka kawo wa laraba,sai Kuma yaji kaso mafi yawa na damuwarsa ya ragu ,kawai bari zaiyi su kusa Gama cinye garar Saiya Fara gallaza Mata azaba da kafarta ma zata gudu.da tunanin wannan mafitar ya goge hawayensa ya nufo cikin garin,inda Yana zuwa ya iske jama'a cike suna jiransa danyi Masa Allah ya Sanya alkhairi, kasancewar sa babban mutum da kowa ke ganin kimarsa. ********************************* Kusan a gidan malam akayi shagali,Dan kusan Nan gidan dangin laraba suka tare,Wanda hakan yasa suka Dora babbar tukunya,aka shiga shagalin girki.hatta da awakin laraba haka aka kwanto su da kajinta,tace duk gidan malam ta nufa da abinta. Sai wajen karfe 9pm ma sannan aka samu zarafin Kai amarya,inda sai kaje kudaje haka jama'a suka dunguma gidan malam,yayin da idi da mamuda suke tsaye tsakar gidan suna jiran 'yan kawo amarya Suzo Dan su basu San fa laraba babansu ya auro ba. Famkam-famkam babbar yayar laraba ta shigo da sallamar ta, dai-dai
Chapter 7 · 0% Book details