Sashe 31
Yar Caskale Part 1 Complete Hausa Novel.doc · about 8 min read
dake kuna inji yasa suke samun haske a unguwar,hakan ne yabata damar hango fararen kayan dake jikinshi,duk da bata tantance yadi ne ko shadda ba.saboda ya juya mata gefe ne ba lallai yaga fitowar ta ba yasa ta ara sakin dariya a fili kafin ta shagi afa ta kama cilla ayar tana wani malkwa ewa ta isa gurin sa,inda tana zuwa ta tace dashi, "Sannu da zuwa ango na" Waigowa yayi dan jin Muryar sahibarsa wadda tunda aka furta an bashi ita ya tabbatar ya more rayuwa da mata,dan Maryam kam ba arya yarinyar ta ha u,yanzu ma fa ji wani salon magana da tayi amfani dashi wajen kiran sa da sabon suna,dan haka cike da farin ciki ya juyo yana fa "Yauwa amarya ta......" Sauran maganar tasa ta ma ale sakamakon ganinta da yayi a wani jirkice,shi yama kasa banbancewa akan lilo take ko kuwa,a dandagaryar asa take,da kallo ya bita yana son tantance abinda yake son tabbatar wa kansa,ah lallai! Ashe ba banza ba shi yasa mahaifin ta ya bashi ita wato dan yasan nakashshiya ce,wato nakasa ce ta sameta shi yasa ya bada ita sadaka,to ai koda yake nakashshe bai shirya auren irinsa ba,domin shi dirarriyar mace yake so,amma bari yayi maganin abun ya karta mata rashin mutun cin da zai sa taji tun yanzu dama bata sanshi ba,bare har tayi tunanin aurenshi. Wani gefen ya kalla da ban yana mai jijjiga kansa,kafin ya jawo sandarsa dayake ora guntuwar afar akai ya muskuta zuwa gaba.Hakan da Maryam ta gani ne yasata yin wani juyi tana fa in" ka gaji da tsayuwa ko albina?". Wani irin kallo ya watso mata,a zuciyarsa yana mai ara jin sabon samfurin rashin mutunci danshi sai yanzu ma ya ara lura da yanayin Maryam in, sakamakon juyin da tayi na yanzu ya tabbatar masa da tata lalurar nakasar ma mai hajijiya ce,dan haka cikin fa a-fa a yace, "Kinga dakata malama! Kada ki ara kirana kallabi,wato ma har lalacewa ta takai ki kirani da kallabinki? ah lallai,hakan ya nuna kenan koda munyi aure bazaki min ladabi da biyayya ba,dan bakida tarbiyya,saboda haka na fasa aurenki shikenan ai ko?". Yana kaiwa nan ya sauke ajiyar zuciya dan yasan ya gama da wannan matsalar cikin sau i,amma sai yaji muryarta tana fa in" kayi ha uri yaya Idiris ban san hakan zai ata maka rai ba,amma bazan ara ba masoyi". Ji yayi wata kibiyar ba in ciki ta soke shi,hakan yasa ya ara tattaro kaf ba en maganganun daya sani ya dinga ya awa Maryam ,amma ko alamun taji haushi bai gani ba,hakan yasa shi tattaro sandarsa ya fara mi ar hanya dan guduwa,amma sai Maryam ta fara walwali tana juyawa ha i da cangalawa tana binshi,ganinfa da gaske take binshi take tana yayi ha uri ya taimaka ya aureta nan fa ya ara sauri,itama haka. Ganin tana binshi tana ro onshi,daya ara gudu itama saiya ganta kamar wal iya ta kamoshi,hakan yasa yafara wala ihu yana neman taimako,aikuwa nan mutane dake jiran iris suka yo kansa suna tambayar lafiya? Maryam da taga hankalin mutane yayi kan Idi gurgu,tuni ta samu ta zame tayi hanyar gida tana dariya. Shi kuwa mutane nata tambayar shi ya i magana illa fa i dayake a taimakeshi mayya ce ta biyo shi,ganin haka yasa mutane suka auka ko gamo yayi,nan suka cicci e shi suka kaishi gida. ***************************** Ita kanta mahaifiyarta tayi mamakin yadda Maryam in ta shigo,ta auka zata ganta tana kuka da turjiyar ta fasa auren wanda aka bata,amma sai ta ganta da fara'arta tana fa in"lah umma har yanzu bakiyi bacci ba ashe?" "Ta yaya zanyi bacci Maryam? Wace uwa ce yarinyar ta na waje da sunan hira zata iya bacci,ai indai ba gani nai kin dawo ba hankalina bazai kwanta ba sam". Dariya Maryam tayi asa- asa sannan a zuciyarta tace"su umma an fara sanin darajar a ashe"amma a fili sai cewa tayi" Allah Sarki umman mu mai sonmu,kinga ma bamu wani da e ba yace wai akwai wani abokinsa da baya jin da i zasu je dubashi". "Allah ya bashi lafiya"cewar umma a takaice kafin ta kuma cewa"Wai ni Maryam kina ganin zaki iya zama da Delu kuwa? Ni wallahi sam wannan auren bai kwanta min ba,da malam zaiji ta tawa da ya ha ura da wannan auren,idan kuma ke in kina da wanda kike so ki fa a ya fito ayi dashi kawai zaifimin kwanciyar hankali........." alamin khady* *'YAR CASKALE* ( _Sanadin bakin uwa_ ) *NA* *KHADIJA USMAN* (Real ta maigari) *____________________________________* AINUWA RITER'S SSOCIATION ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* "To ni umma ina naga wani saurayi,ni wallahi ko ance ma ana so na bana tsayawa kulasu,dan duk yawancin samarin yanzu an iska ne". Girgiza kai kawai umma tayi,dan a yanzu bata bu atar wani dogon zance daga ar tata. Itama Maryam in bata ara cewa komai ba ta mi e ta nufi akinta.Harta kwanta kuma saita tuna bataci abinci ba,nan ta mi e taje ta zubo tuwon ta dawo akin ta zauna bakin katifarta.Harta zauna ta tuna bata ebo ruwa ba,nan ta mi e ta fita ta wanko hannu tare da ebo ruwan randa mai sanyi ta dawo akin ta zauna ta fara cin tuwon,tana ci tana tuna diramar su ta azu da Idi tana dariya harta gama taje ta matsi makilin a burushi ta fita ta wanko bakinta ta dawo ta kwanta. **************************** Tun a daren ranar mijin Delu wato baban Idi ya iske baban Maryam har gurin sana'arsa akan sun janye batun auren Maryam in,hakan ya aga hankalin baban Maryam,nan ya dinga basu ha uri amma fumfuris baban Idi ya i saurarar sa ya juya ya tafi,cikin hanzari baban Maryam yabi bayansa zuwa gida dan ya acewa ganin sa,dan haka sai ya bishi gida,to gara ma baban Idi,dan Delu tijarar fitar hayyaci tayi masa,dan harda ce wa Maryam mayya nakashshiya.maganganun ta sun ata ran baban Maryam sosai,dan sam bai fahimci inda ta dosa ba,saima yayi dana sanin abinda yayi niyyar yi,kenan dan sunga ya basu a a sadaka shine suke shirin wula anta shi,dan haka yanzu yaji koma yaya ne bazai ara yun urin aurar da Maryam ga kowa ba,illa wanda ya ganta yace yana so kuma itama tana sonshi.Da wannan acin ran ya koma wajen sana'arsa kuma koda ya koma bai jima ba ya nufi gida,bai oyewa umma komai ba ya sanar mata, addu'a kawai tayi da fatan Allah yasa hakan shi yafi alkairi. ***************************** Shirye-shiryen bikin ummita sukeyi a wannan watan,dan haka suketa tsara yadda abin zai kasance,da ku in data samu a Lagos gurin zulaiha da kuma Jazuli da su tayi bushashar ta,dan har an neman tallafin anko ta siyawa,dayake ta bawa umma ku in nan tayi mamakin yawansu kawai saita nemi guri ta ajiye batare data ta a ba.Sauran data iba su take ta facaka dasu. **************************** An shiga satin biki su Maryam babbar awa,duk wani shiri anyi shi,kuma Alhamdulillah biki ya ayatar,dan yauma ake shirin kai amarya,dan a yanzu haka ma motoci ne jere aukar amarya. ************ Tunda suka fito yaketa nan nan da ita,ya kasa ya tsare burinsa ta shiga motarsa,dan gaskiya bazai oye yadda yake jinta ba tun ranar paty'nsu na farko daya yalla ido ya ganta ta tafi dashi,yanzu ma sai ari yakeyi danya tabbatar ta shiga motar shi.Ai kuwa yayi nasara dan a motarshi aka auki amarya da wasu tsofaffi biyu sai ita Maryam in a gaba. Tunda suka tafi babu wanda yayi magana sai kukan ummita dake tashi,Maryam da haka kawai ta tsinci kanta a yanayin jan aji sabon salo tayi gum da bakinta har suka iso gidan amarya. Ba laifi gidan yayi kyau sosai a dai tsarin ginin mai rufin asiri kuma ginin zamani,a haka har aka shigar da amarya ciki da dai sauran abinda Yakamata kafin kowa ya kama gabansa aka barta da awayenta.Suma basu jima ba dan dare ya fara yi suka ma amarya sallama suka fito har Maryam.Yana tsaye jikin motarshi ya jingina bayanshi hannunsa ri e da waya yana daddanawa,bazakace ga kamminsa ba, saboda yanayin gurin akwai duhu, motoci uku ne a tsaye a wajen da alama dama jiran ammatan sukeyi,cikin sa'a babu wadda ta nufi motarshi sai Maryam ,wadda batayi tsammanin sauran basu biyota ba har saida ta bu e gidan baya ta shiga tana cewa"Ni dai na kama guri na kowaccen ku ta nemi nata.....sauran maganar ta ma ale sakamakon jin ya shiga motar a mazauninsa na driver,maida kallonta tayi ga waje ta hango su suna arasa shiga mota, bata gama dawowa ba taga sun ja matocin sun tafi,shima ya kunna motar batare da yace da ita uffan ba yaja suka tafi. Tsintar kanta tayi da fa uwar gaba amma ga mamaki ta kasa cewa komai har suka iso ofar gidansu Ummita ya tsaya. Bu e murfin motar tayi ta fito batare data shiga gidansu Ummita ba,nan taji aya daga cikin awayen nata na kiran sunan ta suna fa in sai da safe ta amsa musu da Allah ya kaimu nan ta nufi gida cike da sanyin jikin da bata san musababbin hakan ba. Shi kuwa tunda yaji an ambaci sunanta ya shiga maimaita sunan,bayan ta tsallaka hanyar ya fito ya an yi taku ka an dan yaga gidan da zata shiga,nan ya hango ta ta shiga gidan da yake kyautata zaton nasu ne,sai da yaga shigar ta sannan ya koma da baya ya auki motarshi ya tafi cike da okin ganin gobe in Allah ya kaimu. ***************************** Yau ta taya umma aiki ta gaji,dan kwana biyu bata samu zarafin tsokano wani ko wata ba,dan sosai umma tasa mata ido yanzu kuma ta dage da addu'a bisa nasihar da baban Maryam yayi mata,hakan yasa yanzu duk tayi sanyi ,yauma an kwanukan su ajiyayyu duk sunyi ura,shi yasa ta ebo su da niyyar wankewa,sai Maryam in ta tayata suka wanke har aka juyawa umma jeren akinta yayi rass dashi,basu gama aikin ba sai bayan la'asar hakan yasa tayi wanka ta aura alwala dan yanzu bata wasa da Sallah a an kwanakin nan,tana alwalar baba ya shigo. Da ganin yadda fuskar sa ke auke da murmushi kasan yana cikin farin ciki,da alama yaji wani labari ko kuma kasuwa tayi kyau. Ganin sai wannan