Sashe 4
Yar Caskale Part 1 Complete Hausa Novel.doc · about 8 min read
ba,Ni dama tunda aka kawota Bata kwanta min ba Dan Haka yau sai kinsan kin taba salame". Shan gabanta Zuwaira tayi tana fadi'in"ah ah salame,gara ki Kira malam ki fad'a Masa,dan kin San Bai bamu izinin dukan dalibansa ba,Dan Haka Ni ba ruwana". "Dayalla gafara can tsohuwar munafuka,wato Dan ba miyarki aka zubar ba shine Zaki ce kada in daketa,ke uwar tausayi,harda wani yen yen yen! Mayam jeyi fata" tayi maganar tana kwaikwayon Wai maganar zuwaira.Dan haka saina daketa wallahi". Tsalle Zuwaira tayi taci d'amara tana fad'in" Ni Kuma zanga uban dazai tab'ata,miyace an zubar,Kuma ma ai akuyar lado ce ta zubar kibi akuyar Mana ki daka in gaskiya kike bi". Aikuwa Nan hayaniya ta kaure,yaransu ma suka shiga cikin rigimar,itako Maryam tana tsaye gefe tana kallonsu,ganin sai cacar Baki sukeyi sunki suba hammata iska yasata fad'in"mu in zakuyi kuyi dan Allah kubar sa Mana rai,nagaji da kallon tsohon yayi". D'aya daga cikin yaran malam me suna Idris ya kalli Maryam yace"A daina sa muku rai da me?" "Da fad'an Mana,in zasuyi suyi kawai musha kallo".Suna Shirin yin magana sukaji sallamar malam da gyaran murya,Nan da nan kuwa kowacce ta nutsu,dan duk bala'insu,to yanayi musu kwarjini kuma basayi a gabansa,Dan haka suka nutsu kowacce taja baya. Tsayawa yayi Yana Kare musu kallo kafin yace "Ku kuma lfy naganku tsaye kamar tab'are?" Zuwaira ce ta gyara tsaiwarta sannan ta ce,"wallahi malam gara da Allah ya kawoka,wai fa wannan 'yar kwiciciyar yarinyar ce,sabuwar dalibarka,ta shek'o da gudu inaga ko Kashi takeji,shine tsautsayi yasa tabi takan miyar da Yaya salame tayi,to shine fa tace yau saita Mata mugun bugu,shine na hanata nace tabari idan kazo ta fad'a maka,shine ta taso zata dakeni". "Ke uwar 'yan sharri!cewar salame,ni d'in ce nace Zan dakeki,to in dakeki ince na daki wa?" "Kin daki uwarki,shegiya Ni Zaki tambaya ma in kin dakeni kice kin daki wa? 'yarki ce ni ko k'anwar ki,in kina ganin damata ko zamu gwada ne.Jin hakan yasa salame fusata suka kacame da dambe.Su malam da ke gefe sai sukaja da baya,Dan wata mulmula da akayi da Zuwaira ji kake makkkkk an maka ta da k'asa.Ganin hakan yasa Maryam rugawa da gudu, ta dauko wata k'arama da wani sillen Kara tazo ta tsugguna saitin inda aka t ushe Zuwaira,ta shiga kid'a tana fad'in"jaruma! Jaruma! Baba Zuwaira jaruma! Wannan kid'an ya fargar da Zuwaira taji wani sabon k'arfi,aikuwa saita juye da salame ta shiga kintsimar ta,ganin haka yasa yaran sukayo caaa! malam ya dakatar dasu,Babu wanda ya raba su,malam ya Hana,saida suka gaji sannan suka Bari,bayan an daddaki bakin juna.Kuma har wannan lokacin maryam bata daina kid'an ba.Sai da kowacce ta koma gefe tana mayar da numfashi, itako Maryam ta janye fanteka gefe ta zuba musu ido bayan ta tallafe fuskarta da duka hannuwanta biyu. Shi kam malam baice dasu komai ba,illa zuwa da yayi ya kama hannun maryam yaja ta itako batare da Nuna tsoro ba ta bishi,Dan tasan dai bazai wuce ya daketa ba. D'akinsa ya nufa da ita,batare da yace da ita komai ba ya zaunar da ita Kan wani buzu dake gefe.Wata jaka ya jawo ya dauko wani daurin magani ya jawo wani kwano ya dauko d'aurin rubutu ya tsiyaya a Kofi ya hada da wannan maganin.Yakai wajen minti biyar Yana Kara tofa addu'a a ciki,sannan ya mikowa maryam yace ta karba tasha. Zaro ido waje tayi sannan tace"miyau d'in zansha malam?" "Wane irin miyau Kuma maryama,bakya ganin addu'a nayi miki,Dan haka yi hakuri karbi Kisha kinji mairoro" ya fad'a Yana Mata alamar rarrashi. Karba tayi takai bakinta da niyyar sha sai Kuma ta dawo dashi tace"tsakaninka da Allah malam ka wanke bakinka kafin kayimin addu'ar Nan?" Yak'e malam yayi yace "nawanke Mana baki gani ba tun safe nake asuwaki". "Tab da da asuwakin safe zaka tofeni wallahi bazan Sha ba" ta fad'a tana dungurar da kofin.Duk yadda malam yakai ga lallaba ta kin Sha tayi,hakan ko ya fusata shi,Saida ya dauko wata narkekikiyar bulala wadda yake maganin irin su Maryam da ita ya zuba mata,.Duk yadda ta Saba da duka Amma taji wannan bulalar ta dabance,aikuwa ta shiga canyara kuka,shi kuwa Saida ya tabbatar tayi laushi sannan ya kyaleta Kuma bayan ya tabbatar ta shanye rubutun,ya fada Mata da niyyar da zata Sha a zuciyarta amma sai cewa tayi a zuciyar tata"ka da Allah ya shiryeni". ************** Wannan dukan da malam yayiwa maryam Saida ya sata zazzabi,dayake kusan d'aliban suna da had'in Kai a wannan fannin Kuma ganinta k'arama yasa suka kula da ita.Babanta yayo Mata aike amma baizo ba hakan yasa ta samu k'arin wasu kayayyakin,wanda suke masu dadi,duk da take yarinya Amma ta lura da halin matan malam,Dan Haka saita Zama zakara me neman suna bada kwaya kaci tsakuwa,hakan yasa suka d'an Fara janta a jiki,duk da su a tsakaninsu babu wata jituwar kirki. Tun dukan da malam yayiwa maryam yasa ta nutsu,Nan shida kanshi malam ya Kira babanta Yana Masa albishir da ci gaban da aka samu,nan kuwa ya Nuna farin cikinsa har yake fadawa huwaila,wadda tace in an kwana biyu zasu zo suga Maryam din. ************************ Yau ta tashi da niyyar aiwatar da kudurin dake ranta,Maryam yarinya ce Mai ra'ayin rik'au,batada hak'uri Sam,duk da batada yawan shekaru,amma tanada akidar rama abinda aka Mata,sannan ga bak'ar mugunta a gun Yara sa'anninta,Sam batada tsoro ta Saba da duka da zagi,hakan yasa duk wani duka ko hargagin mutum baya tsoratata. **** Duk da irin kyautar datayiwa su salame,hakan baisa sun barta haka ba,Saida suka bi suka k'ara da wasu abubuwan a gabanta,Dan Haka tace Suma sunci bashi. Laraba me d'an bagalaje,irin narka-narkan matan Nan ne,saboda ma girmanta yasa tak'i auruwa,Dan gaskiya ita d'ince komai nata na musamman ne,hakan yasa dataga tak'i auruwa,saita Fara sana'o'i kala-kala,da sana'ar cikin gida takeyi,to kun San matan aure da cin bashi,yazamana idan mace taci bashinta,har gidanki har dakinki zataje ta jawo ki,in kin Bata kudinta kin tsira,in Kince Babu kuwa,Nan zata kamaki kamar 'yarta taita jibga,har sai anzo an kwaceki,hakan da takeyi ne yasa duk aka daina siyen kayan ta.Saita yanke shawarar komawa sana'ar yara,Kuma da biyar goma tana samu abinta.Tunda Maryam tasan da ita duk wani tattalin arzikinta ya Fara k'arewa a can. Yauma can ta nufa,tana zuwa kuwa laraba tahau washe Baki,Dan jininsu ya had'u Dana maryam,aikuwa ta tsugguna tana me kokarin bude murfin da aka rufe farantin d'an malele,Saida ta k'ara zambada yaji a iya Wanda zata iya siya,dayake yau batajin cin d'an ba galajen ,d'an malelen take sha'awa,kuma gashi yau yajin laraba yasha kafi zabo yayi chauuu dashi. Jin cikinta kamar ta shafa mota ga wani mugun kwadayi datakeji,ji take idan aka Bata farantin d'an malelen tana iya cinye shi.dan haka ta gyara zamanta saman wani d'ab karamin dutse tace,"Anti laraba kin San me?" Dai-dai tana make wata yarinyar data siyi d'an malele ta tsaya lasar faranti tace" sai kin fad'a mairo?" Gyara zaman ta kumayi sannan tace "Wai malam naji yace Yana sonki".Tsabar farin cikin Jin wannan kalmar me tsada yasa laraba ta saki Baki da hanci ta kasa motsi,illa jawo hannun yarinyar data make yanzu da tayi ta dan gwarar da ita,da kyar ta iya bud'e baki tace "cinye duka"Aikuwa yarinya ta gyara Zama tana washe baki,ganin haka yasa itama Maryam matsowa tana saka hannu suka hau cin d'an malelen,yayinda laraba take fad'in" taho farar yarinya me farin labari ki k'ara fad'a mun inji a wane kalar yanayi ya furta Miki Yana so na" "Um um Anty laraba, Bari in gama tukun"sam laraba tak'i barin Maryam ta sake da cin d'an waken,fad'i take ta taso inta Gama Bata labarin zata yi Mata Wanda yafi wannan dad'i,amma Sam Maryam tak'i bari.Ganin haka yasa laraba tasowa cak tayiwa Maryam daukar jarirai ta zauna ta d'ora ta bisa cinyarta tana fadin,bani labarin malam ja'afar d'ina ta fad'a tana karkada ido". "Nidai gaskiya Anty laraba ki daina marmar da idon Nan kina tsorata ni kamar fa zabi yar aljana haka Kika koma". Duk da taji haushi amma Dan Jin ance ana sonta ta maze tace to na daina fad'amin kinji,Dan in munyi aure da malam bazaki k'ara kwana d'akin Nan ba,sai d'akina kece 'yar tayin kwana na". "amma ba gado d'aya zamu rink'a kwana ba dai ko?" "A gado d'aya mana,ai Ni yanzu banida wadda ta fiki". "Har babarku da babanku?" "Eh Mana,yanzu dai tashi muje nayiwa malam girki me dadi,ki tafar mishi da shi". Aikuwa suka rankaya gidansu laraba,ranar ma danba galajen harshi kyautar shi ta bayar. Danwaken fulawa tayiwa malam,aka daka Masa had'ad'd'en yaji Wanda yaji onga,itama Maryam an sammata nata nana ta k'ara ci ta sud'e kwano sai kace me cikin zani. Cikin kwanukan da aka d'ebi shekaru ana tarawa Dan jiran ranar aure.Ciki aka dakko falleliyar langa aka zubawa malam a ciki ,har Maryam ta d'auka zata tafi saita ajiye.Da sauri laraba ta kalleta tace "tawajena ya akayi ne?" "Ba komai,kawai jinai bazan iya Kai Masa bane,abin yayimin nauyi" Da sauri laraba ta matso tana fad'in"haba 'yar d'akina ,taimaka kikai Masa,kice Masa Nima Ina sonsa ungo wannan ma,ta ciro naira ashirin ta Bata, aikuwa Nan da Nan Maryam ta d'auka ta fice.Laraba dake tsaye mamanta na tayata murna kawai saita buga tsalle,Amma abin mamakin ko rabuwa da k'asa batayi ba,illa mazaunan ta da sukayi sama da k'asa da Kuma teb'arta datayi rawa. *********************** Tana shiga gidan cikin sa'a ta Sami duk ahlin gidan a hallare,aikuwa gaban Zuwaira taje ta mik'a Mata d'anwake,Koda Zuwaira ta bude ta gani nasha-nasha da Mai,babu tambayar daga Ina,kawai tahau juyawa tahau kasaf ta shi,bayan ta jefa biyu a bakinta tana fad'in "um um um,gaskiya kowace tayi d'anwaken Nan ta kwararriya ce",Nan ta mikawa kowa ya d'auka. Saida kowa ya cinye ana sid'e hannu sannan salame ta juyo ta kalli Maryam,wadda Dan tsabar dadin da d'anwake yayi,an Manta da ita data kawo a rabo ko Bata ba ai ba,tana gefe tadau wani siririn Kara tana Wasa dashi a k'asa taji salame nacewa"'yar albarka Ina Kika samu uwar d'aki harta Baki wannan danwaken,Dan nasan wannan na musamman ne". Batare data d'ago daga abinda takeyi ba tace"budurwar malam ce" Wata irin kwarewa Zuwaira tayi,wadda tasata Fara kelaya Aman danwaken dataci,itako salame cewa tayi "wane malam din Kuma?" Saida Maryam ta d'ago wannan karon,harda cewa zuwaira,"sannu baba" sannan tace "malam Mana,Daya dakeni rannan a dakinsa,malam dai na