← Book details Yar Caskale Part 1 Complete Hausa Novel.doc Local reading mode
READING PART 1 OF 34

Sashe 1

Yar Caskale Part 1 Complete Hausa Novel.doc · about 8 min read

Root Entry WordDocument 0Table Data *_'YAR CASKALE_* ( _Sanadin bakin uwa_ ) *NA* *KHADEEJA USMAN* *_(Real Tame Gari)_* ___________________________________ KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ___________________________________ *ALHAMDILLAH! ALHAMDILLAH!* *_AM BACK AGAIN_* *_Wannan buk d'in,sadaukarwa ne ga dukkan daukakin Marubuta na kainuwa writers asso...da Kuma masoya na a duk inda kuke a fadin duniya Allah ya barmu tare ya Kara Mana zumunci mu gudu tare mu tsira tare_* _Hussain ATK da dukkan masu taya mu posting din litattafan mu muna matukar godiya Allah ya saka muku da alkhairi ya barmu tare_ _Ban yarda wani ko wata su juyamin littafi ta ko wacce siga ba tare da izini na ba,yin hakan zaisa mu samu matsala Dan Allah a kiyaye_ ****** Sauri yakeyi kamar zai kifa,Dan ya na son yayi sauri yakai musu maganin. Malam shu'aibu kenan,cikakken bakano,asalinsa shida iyayensa 'yan Kano ne, a unguwar fanshekara,ya na da Mata guda d'aya da yaransu biyu,Isma'il shine babba sai mace *MARYAM* wadda ita ce karama yanzu ake goyo. Malam Shu'aibu da matarsa Huwaila,suna zaune ne a unguwar yamadawa,inda yake sana'arsa ta sayar da kayan marmari,dangin su lemo ayaba da dai sauransu.Huwaila macece Mai kirki da Sanin ya kamata,duk da cewar uban mijinta ya Dade da rasuwa,hakan yasa kullum Bata rasa abinda zata bayar tace akaiwa surukar tata,Dan malam Shu'aibu kullum Sai ya je gaida mahaifiyar tasa. Matsalar Huwaila fad'a da rashin lafazi,Sam bakinta Dad'i,ba ga wani ba ,Baga 'ya'yanta ba,malam Shu'aibu yasha fama da ita akan muna nan lafazi akan yaranta,amma Ta 'ki dainawa.Yanzu haka Maryam na da shekara goma yayin da Isma'il keda shekara Sha d'aya,Dan babu wata tazara tsakaninsu,Dan irin haihuwar nan ce ta zamani.Yanzu ma Isma'il ne ba lafiya,shine ta kaishi asibiti ,magungu Nan da aka rubuto,su ne malam Shu'aibu ya ta fi siyowa. Da sallamar sa ya shigo gidan,inda ya Fara jiyo hayaniyar ta tana fad'in"ai ke Kam anyi bak'ar matsiyaciya,ban San halinwa Kika kwaso ba,Danni kaf dangina babu Mai bakin Hali irin naki,sai dai ko can dangin ubanki Kika kwaso,ace yarinyar kullum sai kin Sani tsinin baki,da ace baki Yana Kara tsawo da yanzu nawa ban San inda yakai ba" Yarinyar dake tsaye idanunta feke ta tsare uwar dasu,babu ko alamun tsoro tace" Allah umma ko yanzunma bakinki ya k'ara tsawo ba kamar sanda na ke k'arama ba,Dan yanzu Kinga yadda bakinki ya koma",ta kamo le'benta na sama Dana k'asa ta jawosu. "Kinci kut......ta narka Mata ashar,Ni d'in ce bakina yake a hakan?" "Wallahi umma da gaske nake"ta fada kanta tsaye ."Zakici ubanki ne ,na rantse da Allah yau saina kusa kasheki a gidan nan". Jin abinda tace ne yasa Maryam din zumbura Baki ta nufi bakin kofa Dan fita daga dakin."wallahi Kika sake fita daga gidan Nan sai na farfasa Miki jiki,inba Haka ba shegiya uwata ta haifeni,Kuma jeki din in kina musu". Babu alamun tsoro ko ta fita daga dakin tana zumbura Baki tana gunguni,inda tayi kacibis da babanta tsaye a inda yake jiyo diramar su. Washe Baki tayi tana fadi'in ,"Lah baba! Sannu da zuwa,harka dawo daga siyen maganin?" Kama hannunta yayi Yana fad'in"yauw 'yar baba,laifin me kikayi ne naji mamanki na Miki fad'a?" "Kawai fa Dan tace na jire gida Kar naje ko'ina,shine fa Ni Kuma Ina Nan zaune sai zuwaira ta leko ta tsokaneni ,Wai an barni tsaron gida harda min gwalo,Niko na bita har gidansu na Kama bakinta nai ta naushi irin yadda Naga rannan johnsina yayi dashi da omega,shi ne fa jini har Saida yayi tsartuwa,wallahi baka gani ba baba,da kyar aka kwaceta a hannuna,ashe dai nima jaruma ce,shine fa aka zo aka fadawa umma ,shine takemin fad'a" . Girgiza kansa yayi sannan ya shiga shafa kanta,"Maryam me yasa bakya Jin magana ne,anya kina son mu shirya kuwa? Kinga Ni bana son wannan yawan fadan da kikeyi sai kace ahlin shagon dambe,ke kenan make wannan jibgi wancan,to indai kina son mu shirya Kar in Kara Jin Haka kinji ko?" "Zan daina Amma suma ka fada musu su daina cemun _'yar caskale_ " "Naji duk zansa a tattara mun yaran in musu kashedi,muje maza kibawa ummanki hakuri". "Tab ai yaseen nasan Dana Bata daban Bata ba sai ta dakeni ,gara ma inki bayar war" tana Gama fad'ar hakan tayi waje da gudu. Girgiza kansa kawai yayi,Yana addu'ar Allah ya shirya Masa yaran Nasa,tare da matar tasa ma,Dan wannan abin na Maryam yasan yanada nasaba da bakin da Huwaila keyi musu,Dan tun suna kanana in sunyi Mata abu, kamar barna,sai dai kaji ta furta ,"Kai amma wannan yarinyar anyi tsinanniya,ko Kuma anyi matsiyacin yaro,da dai sauran irin wadan Nan kalaman marasa amfani,masu cutar da rayuwar yaranmu,su durkushe,in sun girma mu rasa dalili,alhali wani lokacin muke jifansu da wasu lafuza marasa dadi ,muna ganin kankantar su ko rashin tasirin su,Wanda wallahi komai kankantar zagi Yana taka muhimmiyar rawa a gurbacewar tarbiyar mu a yau. Da sallama ya shiga dakin,inda ya isketa zaune tana yiwa Isma'il fadan yatashi ya sha farau-farau koya danji dama a cikinshi. Saida yasami guri ya zauna sannan shima ya shiga lallabar yaron akan yasha,da kyar yasha kadan sannan ta balla maganin ta bashi, aikuwa saiga amai. "Kut......."ta lailayo ashar ta makamai,bakin matsiyaci,Dan kaga Ina lallabaka,shine kake dada wani langabewa,to Dan kut.........kada kasha ka mutu ma,Kai Ni Allah ma yasa ka mutu In huta da jaraba,yaro inata bin kanka na rasa inda Zansa kaina duk saboda ciwonka,amma komai aka baka saika amayar dashi,ni a wahale Kai a wahale,Dan bak'ar k'eta,Kai ba jinjiri ba ba Kuma d'an yaye ba,to wallahi daga yau sai dai ka mutu ,idan na K'ara baka wani abu magani ko abinci Allah ya tsinemun".Ta karasa maganar tana huci. Da kallo malam Shu'aibu ya bita,Bai ce da ita komai ba ya shiga lallaba Isma'il akan yatashi ya k'ara Shan kunun Koda kad'an ne yasha magani. Itako ta shiga hada kwanuka tana gyaran gurin tana masifa. ****** Misalin Sha biyu na dare,bayan ya tabbatar Daya yaran sunyi bacci,Dan shima Bai Dade da shigowa ba saboda yanayin sana'ar tashi.A zaune yasameta tana kokarin kwanciya. Saida ya samu guri ya zauna,kafin ya Kira sunanta,"Huwaila"! "Na'am mallam". "Ina son zamuyi magana dake,duk da ba wannan shine karo na farko ba,amma Kuma Zan iya cewa wannan shine kusan gargadi na karshe da zanyi Miki". Ganin kamar Yana maganar ransa a d'an b'ace yasata nustsuwa.Ganin da yayi ta maida hankalin ta akansa yasa ya Fara magana. "Wato abinda ke faruwa ne game da furucin ki Akan yaran Nan,anya kuwa Huwaila kina da hankali,kin San dafi da Kuma illar bakin uwa akan 'ya'yanta, mummunan furuci ko ba ga d'an daka Haifa ba,ai baida amfani,bare Kuma ace ga yaranki,tun yaran Nan na Shan nono nake fama dake akan ki gyara kalamanki akan su,amma abu yaci tura,yanzu furucin da kikayi dazu akan Isma'il,idan hakan ta kasance wakeda asara,Kinga nidai inada damar k'ara aure,duk da kuwa bani da tabbacin Zan Kara haihuwar,amma ai daga ni har ke bamuda wata matsala mun tabbatar.Dan Allah na rokeki Dan girman Allah ki gyara kalamanki akan yaran nan,ke bama su ba har wasu yaran daba namu ba,shi yaro na kowa ne,addu'ar shiriya yakamata mu dinga yi musu bawai mugun Baki ba,Dan Haka Ina son daga wannan lokacin Dan Allah ki gyara lafazinki kinji Huwaila ta". Hawayen dake bin fuskarta ta share kafin tace"insha Allah malam bazan sake ba,nima sai bayan nayi sai abin yaita damuna,amma insha Allah Zan kiyaye". "Yauwa Huwaila,Dan Allah a dinga kiyayewa kin San shi harshe dafi ne me zafi,dan Allah bana so kinji". Gyada Kai tayi alamar toh,kafin ya jawo 'yar matarsa Yana me k'ara yimata nasiha cikin hikima. ************************* Tsaye take ta rike k'ugu gaban Rakiya me dambu,tana fad'in"baba Rakiya!wallahi daga yau bazan Kara kawo Miki karar ummita ba, jikinta ne kawai zai fada mata,gara ma kija Mata kunne Dan yaseen idan na kamata lallasar tishin yaji zanyi Mata,Dan karki ganta ma da tabo kice ban fada Miki ba,ki tanaji na magani tun yanzu".ta karasa maganar tana murguda baki. "Ke Maryam ki fita idona,Dan kaniyarki ni kikeyiwa rashin kunya,Dan wannan ba kashedin ummita Kika kawo ba,Ni kike jawa kunne a fakaice,Dan Haka anki ayi Mata fadan,ke ba'ai Miki fad'a ba sai ita,kinbi kin maida Mana Yara kamar jakai,kiyita lodar su kina musu bugun uwa da d'a,dama na fada duk ranar da abinki ya biyo takan ummita Ni Kuma ranar Zan gwada Miki Nima uwar zamani ce,shegiya fitinanniya". "Kenan bazaki Mata fada ba ko?" "Bazan yi matan ba,ta tsokane ki,gobe ma inta ganki Zan Kuma fad'a Mata ta tsokane ki,ai ba fin karfinta kikayi ba,Dan ma ita din saiwar sala ce, badan hakan ba,ai da inta rikeki ko kwacewa bazaki iya yiba,amma yanzun ma muje zuwa"ta karasa maganar tana bude tukunyar dambunta Dan ganin ko yayi,Dan so takeyi ta gama saboda yau ta d'an makara,dama yayar ummita ke fita dashi,wani Kuma ta sayar a gida,to yau Kuma gashi har ta shirya ita kawai ake jira,to iccen ne danye. Kwaaaaaaaaaaa! Taji saukar ruwa saman tukunyar dambun,Wanda tsabar ruwan Daya tumbatsa,har Saida ya antayo waje,ya leme murhun,toka tayo futar burtu tayiwa fuskar Rakiya fenti,tare da yiwa dambu decoration,Dayake bakinta bude yake sanda ruwan ya sauka a murhun,gaba Daya bakinta ya wanke da toka,inda hakoranta sun rikide sun koma ruwan tokar.Wata iriyar ashar ta narko,wadda tasa sauran tokar bakinta da bata Gama jikewa da miyau ba ta feso kamar ta zuki sigari,aikuwa a sukwane tayo Kan maryama dake rike da bakin bokitin k'arfe na wanka,Nan ko suka kasa tsere.mijin Rakiya da dawowarsa kenan daga kasuwa,Yana kokarin kafe kekensa yaga maryam ta fito a guje Rakiya ta dafo Mata,ya bude Baki kenan da niyyar ya Kira matar,gefen bokitin da Maryam ta rataya kamar jaka ya daki bakinsa,Nan take ya wuntsila daga shi har keken Nasa sai gashi a kwata,shima maimakon ya Kira sunan Allah ,sai ji kake ya runtuma ashariya,Yana me shafo bakinsa da jini ke d'iga,aikuwa ya shiga kiciniyar mikewa,duk da kansa dake Sara Masa,Bai hana sa Mara musu baya ba. Itako Maryam gudu takeyi iya karfinta,yayin da rakiya take biye da ita zaninta a hannu sai d'an under's din ciki Daya Sha bakar dauda. Sosai Maryam ke shiga lungu da Rakiya ga Kuma mijinta a baya,Yara da Basu San dalilin gudu ba suka dinga binsu duuuuu suna son ganin me
Chapter 1 · 0% Book details