← Book details So Ne Silar Faruwan Hakan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 43

Sashe 9

So Ne Silar Faruwan Hakan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani kalar Kitso ne mai atashemn wanda ake yayi yanzu da ta jawo à wayar ta bai ma baza gari ba. Kowa yazo salon din sai yace masha Allah, Sara sai cika take tana bacewa zeey ce ta shigo Salon din, yar wani baban mai kudi ce, kuma Sara ke mata komai In tazo dan ta iya ,ai tana ganin kitson da Aisha take ta rude sai Aisha ta mata irin sa, murmushi
Jumai tayi da ita da Aï, tace "ba matsala Madame yanzu Za'ayi, ba bata lokaci Aï ta gama kitson har ta kama kan zeey, wayo Sara ta cika pam da wanan bakin ciki, Dan zeey indai tayi mata Kitso ko wani abu to fa sai ta samu kyauta. Ji tayi ya ta kurma ihu, Hajiya ma da tazo taga Kitso ta rude, tace "itama in sunje gida sai anyi mata ana ta dariya, sanan tace kawai Aï ta fara aiki, k'arfe biyar sai taje Restaurant, ita da jumai da lantana, wasa wasa fa ko wace mai ji da kanta taga wanan kitso sai tace à mata, à takaice duk à wanan rana saida Aï ta amshe mutanen Sara, bayan harara da cika da batsewa ba Abinda sara keyi, ya ta aza hanu bisa kai ta kwala ihu .

Rana daya Aï tayi suna SALON DIN, DUK mai ji da kanta in an gama mata Kitso in ta bada kudin Kitso sai ta ba Aï wani abu itama, Aï saida ta tara dubu biyar à ranar,na kanta ma'aikatan sai dariya suke ma Sara dan dama haushin ta suke ji, tana nuna komai ta iya sanan tafi kowa iyawa.

K'arfe biyar Aï, Lantana,da Jumai suka fida kayan Salon suka sa kayan su, sukayi salama da kowa sai Restaurant, à kasa suka tafi dan ba nisa. suna ta dariya Sara.

Jumai tace "Aisha yau kin mana maganin yar rainin hankalin nan, Lantana tace ni ai naji dadi wly, sam bata da mutunci yar rashin M ce, wanan da Ace yar wani ce a wanan k'asar da anshiga uku. "

Aï tace "hum ni ai tun da nazo naga yanda take min wani gani gani nasan bamun shirya da ita ba, Bata san ba nima shegiyar kaina ce."

Dariya suka sheke da ita, à haka suka karasa, lantana da jumai duk marayu ne, àsalin su yan kauye ne, dukan su wuyar kishiyoyin uwa ta fido su birni, shekarar su biyu suna aiki à k'arkashin hajiya, sunada fada
In ka taba su, Anma fa akoi shirme gare su, ba laifi sunada kyan su, tsayin kusan daidai suke da tsayin Aï, jinin su ya hadu d'à Aï, haka itama, ganin ruwan ta ne itama sai ta shige cikin su, gwanin sha'awa.

Suna fira suka iso katon Gurin cin abinci, Aï kam baki ta saki tana kalon gurin dakyar suka ja ta ciki.

Suna zuwa suka gabatar da ita suka canza kaya ,waw wanan ma riga da siket tasa wanan har sunfi wancan mata kyau, nan suka fara kai abinci ga masu shigowa, mayan masu kudi kam sai kalon Àï suke........

*Bayan wata daya*

Aci gaba da gashi🍇
Maimou Love😘💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞
💞💞💞💞
💞💞💞
💞💞
💞

*💖SO NE SILAR* *FARUWAN*💖
*💖HAKAN*💖

*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋

*Alhamdulillah jiki yayi sauki, anma fa saida nasha ruwa leda biyar, 😞nagode sosai da kulawar ku, masu kira masu min magana pc nagode sosai, Alhamdulillah jiki yayi sauki*

*PAGE 24-25*

*Bayan wata daya*

Gidaje biyun nan ko wane sai shirye shiryen biki ake,
Gidan Amarya Hanifa zaune take da kawayen ta, zuby, zeey, Rashida, sai zuga amarya suke, suma duk yayan masu kudi ne, zeey ta kali Hanifa tace "gaskiya yarinya bakiyi ba, ke ko irin shanawar nan bakiyi ba zakiyi wani auren takura mtsss ki wani zauna karkashin kato sai abinda yaga dama yayi dake tunda kina k'arkashin sa ,gaskiya Baby kin kwafsa."

Zuby tace "fada mata dai, yanzu wa ke wani ta aure ana shanawa, shifa namiji Bakin da ya aure ki tofa bakida iko da kanki sai abinda yaga dama, ma har aikin da yace Zai yarda kiyi Kina shiga gidan sa yace baisan wanan zancan ba. "

Rashida tace "hahh maza Kenan Zuma ne su saida wuta, saima ranar da ya kara aure. "

Wani tsale Hanifa tayi, tazo tsakiyar su ta rike Kugu tace"tabdi ai wly ni Hanifa nafi karfin ayi min kishiya, daga ni sai ni Wly Ansar yayi karya yace zai min kishiya yace "daga ni ba kari. "

Dariya sukayi suka ce a to sai kisan yanda zaki kara malake shi, Dan yanzu ba Wanda ke zaune haka .

,har mu da muke yan matan malake Samarin mu muke, dan haka karki wani tsaya biye ma Alkawarin da namiji."

Murmushi Hanifa tayi tace "ai tunda inada ku na huce takaicin da namiji"

Hahhh, dariya sukayi suka tafa, nan suka Ci gaba da tataunawa . .

B'angaren Aï kuwa zuwa yanzu aiki ya mike komai ta iya, restaurant ya kara cika, saboda Aï, duk da bata ba ko wane namiji fuska, namiji guda ne ke makale à zuciyar ta, wato Ansar. Kulum da pic dinsa wanda ta sace Office Dinsa take yawo.

Ta murmuje ta kara kyau, da yake tana samun cima mai kyau, Sai tayi wani fresh da ita , yau ta shirya, da ita da kawayen Nata su Lantana, har ta fito taji yau sabon Son Ansar ke shigar ta bazata iya tafiya ba ba tare da ta kali fuskar sa ba .ta d'auko photo ta tafi dashi direct Salon suka nufa.

Misalin k'arfe tara na safe mutane sun Cika salon din, kowa yayi shigar sa, ta kayan su na aiki Aï yau riga da wondo tasa, dan haka sai ta makale photo Ansar à wondon ta, anma bai ida shiga ciki ba.

Yau zeey Hanifa Amarya da Zuby suka zo Salon Din, zeey ta zauna Aï ta fara tsefe mata kai, yayin da Hanifa ta hakimce Sara n'a tsefe mata kai itama,. Kowanen su na taunar shingam, Aï bata San me yasa ba, Anma koda taga Hanifa gaban ta ke faduwa , tsinkar kunce Kitso ce ta fadi gaban zeey Aï ta duka zata d'auka carab idon zeey yakai ga pic din dake aljihun Aï ta zaro photo tana kura masa idanu, tace "what, Ansar wani kalo ta watsa ma Aï .

Hanifa Jin an ambaci ansar çikin wata mahaukaciyar zabura ta tashi tayo gurin, Zuby ma bayan ta ta biyo.

Please kuyi maleji

💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞
💞💞💞💞
💞💞💞
💞💞
💞

*💖SO NE SILAR* *FARUWAN*💖
*💖HAKAN*💖

*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAHI AM*💋

*PAGE 26-27*

Hanifa na zuwa ta k'arbi pic din ta duba batayi wata wata ba ba ta Zabga ma Aï mari, dafe kunci Aï tayi cikin kunar rai itama ta maida martani, har guda biyu ras tayi ma Hanifa.

Haba ai su Zeey Na ganin hakan suka tarar ma Aï, lantana da Lami ransu à matukar bace suma suka shigar ma Aï, kowa yaja daya daya, Àï da Hanifa ta yada Hanifa tana jibga kamar me ,lantana da zeey, zuby da Lami, su Aï su suka Ci galaba akan su Hanifa ba wanda ya raba,saida su Aï suka musu tas, hahhhh su zeey girman birni ba'a saba da wahala ba kuma ba'a iya fada ba, ba k'arfi, yau su lantana sunsha miyar kauye ai ba'a gwada musu k'arfi, Sara ce tayi kiran hajiya ta fada mata sai murna take, Dan tasan korar su Aï za'ayi daga d'aki dan ka'idar wurin ne indai ma'aikaci yayi fada da customers tofa kora ce.

Hajiya na zuwa rai a matukar bace ta raba su ta fara fada jin abinda ya faru, Hanifa ajigace tace "hajiya wly sai na batar da yaran nan a doran kasa, uban wa ya basu photo miji n'a, hajiya bata gane ba, rai bace ta kali Aï tace "ke ki fada min Me akayi ne"?

Ba kumya Aï tace "wai kawai dan sunga photon saurayi n'a shine suka fara duka na. "

Baki galala suke kalon Aï.

Hanifa waya ta d'auka bugu daya tace "kazo salon din hajiya ina jiran ka.

Daga can OK kawai yace.

Minti da basu kai biyar ba sai ga jiniya, ya shigo da salama, kasancewar ya d'auki hajiya kamar uwa dama yasan salon din yashiga kai tsaye cikin takama da isa ya kara kyau sosai, kai tsaye inda yasan ake mata gyara ya karaso ganin mutane tsaitsaye sai cacar Baki ake yasa ya karasa kai tsaye, Aï ta fara ganin sa saida gaban ta ya fadi, ganin yanda ya kara kyau ga kwarjini, tuna haduwar su ta k'arshe tayi, gaban ta ya fadi dum, Dan tasan yau mai kwatar ta sai Allah.

Yana zuwa à dan rude ya isa Gurin da Hanifa take ya rike hanun ta yace "baby keda waye hakan ?

Rai bace Hanifa tace "kasan wanan, hanun ta ya bi yaga Wa take nunawa, Àï ya gani saide bai gane ta ba domin Aï yanzu ba ta da bace wanan ta waye tasan kan duniya, yace "ban santa ba. "

"Hum Baby Dan kana gaban ta ne zaka ce baka San ni ba, anma ba komai zamu hadu ne ranar da na tare cewar Aï ta fada a dake, yayin da ta kura ma agogon hanun sa ido, ga kamshin turaren da bazata taba manta sa ,gaban ta ya fadi dum kara tabatar wa da zargin ta, anma dakewa tayi , sai yanzu ne Ansar ya gane ta, kasa magana yayi Dan ta kule sa, itako Hanifa ganin haka ta gaskata maganar Aï, jakar ta ta d'auka ta huce fuuuu suma binta sukayi baya. Ansar tsabar takaici ya nuna ta da yatsa yace "wly da na aure ki gwara na auri jaka. "

Ya kali hajiya yace "wly Mama indai wanan nan take aiki bazan kara miki magana ba, baki san karuwa bace mai lasisi duk abinda ta fada miki karya take. "

Hajiya fa ranta ya baci, duk sai taji ta tsani Aï, ta nuna Aï da yatsa tace "ke Aï kije daga yau n'a kore ki, dama tsintaciyar mage bata mage

.
Chapter 9 · 0% Book details