← Book details So Ne Silar Faruwan Hakan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 43

Sashe 8

So Ne Silar Faruwan Hakan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan ta zauna tayi tagumi, bayan ta gama sallah, wayar ta ta d'auka ta kuna tunda à kashe take tunda tayi hatsarin nan, waya ç tecno k9 da Sam ta bata, komai akoi ciki, nan ta kuna message ne suka fara shigowa à wayar, à ciki ko duk nasu karima ne, suna tambayar ta ko lfy take, kiran Kam Baby tayi, kam Baby n'a ganin kira ta daka ihu ta kira sauran aka d'auki waya cikin murna suke tambayar ina ta shiga suna ta neman ta sunyi kewar ta, nan Aï ta fashe da kuka ta fada musu abinda ya same ta, sanan ta fada musu bazata taba karuwanci ba, ta gode da irin abinda suka mata, suma kuka suka sha tare da cewa ta musu addou 'a, suma Allah cire su, sanan suka ce tazo ta d'auki duk wata sutura da abinda tasan nata ne su suka bata ta rike su halak malak, tana kuka ta musu godiya, tare da cewa gatanan tafe.

Sosai suma jikin su yayi sanyi, anma ina su basu san ranar barin su ba, saide ma farin ciki da suka Aï, har cikin ransu suna Son ta, kuma sunji dadin barin ta harkar, ko ba komai zata tsira da mutuncin ta.

Aï ko tana gama kuka ta share hawayen ta, ta fito daidai Salau zaya fita da mota hajiya ta aike sa, da gudu Aï ta tarbo sa, yana wangale mata baki, domin jinin su ya hadu, tace "Salau Dan kakai ni wanan unguwar ta fada masa sunan unguwar tace kayan ta zai d'auka aiko yace ta shigo Dan hanyar yayi anma saide ta tare Dan acaba.

KO adaidaita ya maido ta tace ba matsala, à mota suna ta surutu, Salau har buga sitiyarin mota yake fira tayi dadi, suna dariya har suka kawo unguwar Maitama, saida ta sauka ta dawo da gudu tace "Salau wace unguwa ne bata san unguwar ba, inda hajiya take, me salau zaiyi bayan sakin baki ya zabga dariya, "yanzu ke ace kina kusa da shugaban kasa baki sani ba, federal capital Abuja ace baki Sani ba, tab, to bara kiji in fada miki nan inda kike kusa da shugaban kasa kike, gidan hajiya matar wani minista ne Wanda yanzu haka shekara sa daya da rasuwa kenan yabar hajiya da dukiya mai yawa, yanzu haka hajiya aminiyar First Lady ce matar shugaban kasa tun suna yara.dan haka yarinya kima Sani,indai kina tare dani to fa zaki sha labari tunda naga ke ba kamar sauran yaran hajiya ne ba yana gama fadar haka yabar Aï da sakin baki, nan dai ta shiga Gidan, aiko suna nan duka Dan dama fitar su ta dare ce.......

Tana salama falon da gudu suka tarbo ta suka rungume ta, suna ihu, bayan ansha fira da dariyar abinda Aï tayi. Bayan nan kuma suka taya Aï tatara kayan ta wanda duk wanda suka saya mata ne da kuma Wanda suka Bata, dinkuna masu tsada kuma sabi less da atamfa da shada sunkai ashrin, da takalma masu tsini suma Sunkai taki goma, sai kayan kwaliya, harda sarkoki da yan kune, da kananan kaya, kai masha Allah Aï tasha kaya kamar n'a lefe, akwati uku cif ta cika da kaya, sai dare zata tafi kowace ta bata dubu biyar biyar tare da Alkawarin zasu dinga zumunci Dan sun d'auke ta tamkar Yar uwa. Da kuka Aï ta fita Sam baby takai ta a mota har unguwar sukayi bank'wana ta koma Aï kuma ta shiga gida.

Bayan kwona biyu, à yau ne Aï ta shirya tsab cikin shirin ta na doguwar riga n'a atamfa dinkin ya mata kyau ta fito tayi b'angaren Hajiya domin yau zata fara Aikin ta.

À aikin Salon sam bazai mata wuya ba Dan tun bata kai haka ba ta iya Kitso n'a zamani,wani abin burgewa kanka kawai zata kala tasan wani irin Kitso zai maka kyau kuma tana maka saika yaba....

Aci gaba da gashi🍇
Maimou Love 😘💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞
💞💞💞💞
💞💞💞
💞💞
💞

*💖SO NE SILAR* *FARUWAN*💖
*💖HAKAN*💖

*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAHI AM*💋

*PAGE 22-23*

Salama tayi à baban Falon Hajiya sai yau taga haduwar sa da tsari,

Hajiya Hadiza matar wani minister man fetur ne Alhaji Sani yanada kudi sosai sunyi auren soyaya da hajiya Hadiza har takai su ga yin aure ,
Hajiya mace ce mai Son kudi, tana da fara'a, saide ko kadan batada mutunci akan kudi, kafin mijin ta ya rasu ya gina mata katon restaurant gurin cin abinci, da kuma katon Salon, wanda sai masu hanu da shuni ko yan karya su ke zuwa gurin.

Basu taba haihuwa ba har Allah ya ma Alhaji Sani rasuwa ya barta da makudan kudi, Hajiya Hadiza Kawa ce a gun first lady matar shugaban kasa tun suna yara tare Suka tashi,dan ko yanzu haka suna zumunci, duk wata sabga in Za'ayi gidan Mrs Président Hajiya hadiza ake ba kwangilar yi à restaurant din su.

Hajiya hadiza farar mace ce mai ji da kudi tana da kyau ba laifi, ga baya, duwawu gareta sosai.

Da Salama ta iske hajiya zaune wuri ta samu ta zauna kasa bayan ta gaida hajiya, hajiya ta amsa fuska sake.

Hajiya Ruwa biyu Ce watarana tayi kirki, ranar da yan tsiyar ke kanta kuma ta iya jaraba da wulakanci taga damar ma ko ka gaida ta taki amsawa.

Fuska à sake ta d'auko wasu kaya kala hudu taba Aï, tace "kinga wanan dinkin ki ne wanda uniforme ne su zaki dinga sawa kulum in zaki gurin aiki, wanan coulor Orange din gasunan kala biyu ne, daya riga da siket ne, rigar Orange da siket da kuma wondo bakake ne, Dan haka hada su ake siket baki da riga Orange, dayan ma riga Orange wondo baki, su na aiki Salon ne kulum k'arfe bakwoy zaku dinga zuwa acan zaki sa uniforme din bana Son kazanta ki zama kulum cikin tsabta ,su kuma wancan kala biyu, Akoi siket da wondo haka tsarin yake riga kalar ja da siket bleu, shima wondon haka ne.
Dan haka muje sai ki fara gani yanda ake yi ko nan da sati ne kema sai ki fara, Anma à b'angaren salon mai kika iya.

"hajiya na iya kitso kala kala, sanan n'a iya wankin kai lokacin ina gida ina zuwa wani salon acan suna sani wani abun su biya ni, sanan n'a iya lale n'a zamani ina ma amare ma, anma kulu kaka ta ta hana ni à lokacin ."

"good"hajiya tace, yanzu muje

Muje sai ki gwada na gani à kan wata n'a gani à cikin masu aikin salon din.

Salau dreba ya jasu yana ta surutu har gaban wani katon salon, wanda duk gillas ne
Kewaye dashi, da farko in ka shigo gurin réception ne, sai ka Dan hau matatakala tunkon zaka kai ga katon wurin,Salon din ya hadu iya haduwa, yan aiki ne ko wace da uniforme din su sunyi kyau, ga mutane nan wasu wankin kai, wasu kuma Kitso n'a atashe wasu kuma ana dinka musu hular.

Hajiya n'a shigowa suka gaisa da client nan ta kira Sara daya daga cikin masu aikin, kuma suna gida guda da Aï, anma sam sara ita Aï bata mata ba, asali ma ta tsane ta saboda kyan ta, karasowa Sara tayi tace "hajiya gani."
Yayin da take harara Aï, kwafa Aï tayi tace "zaki Ci ibanki n e wly n'a fiki iskanci, tab yarinya Baki sani ba ne. Duk cikin ranta take maganar, Hajiya tace "yauwa ga Aisha nan zata gwada Kitso n'a atashe à kanki tunda naga kin kunce.

Kanki jiya, Ran Sara ya baci jin Aisha zata kama kanta, duk ga mutane nan anma sai ita , danewa tayi tace "wly hajiya kaina ke ciwo shi yasa ma na kunce n'a jiya tun bai tsufa ba, yayin da ta faki idon hajiya ta zabga ma Aï harara.

Jumai ce mai pédicure itama duk gida daya suke, anma ita tana Son Aï tun ganin ta da ita, dan d'aki daya ma suke
Tace "Hajiya ki bari ni ta gwada kaina, tunda nima n'a kunce kaina, kuma gashi n'a kadan ne, gashi ni mutane n'a ba yanzu suke zuwa ba ."

OK hajiya tace bayan tace su d'auki abin karin kitson leda daya suyi tana sama, in Sun gama zata gani. Hajiya
Ta haye sama inda Office dinta yake, jumai taja Aï ta kaita inda suke sake kaya tace "kawas sake kanyan ki kizo ki tsantsara min na wuce sa'a "

Dariya Aï tayi dan itama Jumai ta kwanta mata tace "hahhh karki damu kawas dan zamani ma kuwa zan miki, suka tafa, nan Aï ta fida rigar ta tasa uniforme dinta riga da siket, siket din sai bai ida zuwa kasa ba, kayan Sun kama ta hakan sai ya bada wani sityl mai tsari mai kyau, hula ta d'auka itama orange à kayan take, tayi kyau matuka, kamar ka sace ta ka gudu. Takalma kanana ne na roba, gaskiya ta hadu, ta d'auki wayar ta ta fito ,waw kaf gurin ba wada bata burge ba, acikin salon din harda maza masu aikin, idanu kawai ke kanta kowa n'a fadin tubarkala, banda Sara da ta buga uban tsaki,. Aï tayi wani juyi tace yan hasada da bakin ciki saide haushi. " 'nan jumai ta zauna Aï à tsaye ta fara tsantsara mata Kitso Dan dama kan à wanke yake, tun daga kama kan kasan ta kware à hankali mutane suka fara zuwa, ai sai kalo ya koma gun Aï ganin yanda take tsara Kitso cikin sauri da kuma kwarewa.
Chapter 8 · 0% Book details