← Book details So Ne Silar Faruwan Hakan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 43

Sashe 36

So Ne Silar Faruwan Hakan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mom tace" ya ta ,naji dadi da Zaki kwaci yancin ki,domin namiji baisan Yana son Abu ba sai ya kufce masa,ni na Baki dama kici gaba da zamanki har lokacin da ya Miki Zaki iya komawa gidan sa,ki kwaci yancin ki,Nan Mom ta Kara masu Nasiha ,ta tafi Aï ta rako ta ,anma ganin Ansar saida gaban ta ya fadi,shiko fitowa daga motar yayi suka Kura ma juna ido,ita tana mamakin yanda yayi rama Haka tun ba'aje ko Ina ba,shi kuma yana mamakin yanda yaga ta Kara Masa kyau."

Momy tayi gyaran murya tace "muje ko,Aï Kara salama tayi da Mom bayan ta d'auke Idanun ta a nasa ,ta juya Bata Kara ko marmarin Kara juyo wa ba,Dan a yanda ta gansa zai iya karya Mata zuciya......

Ansar abun tausayi Haka suka juya shida Mom.

Bayan kwana uku da dawowar Alhaji Usman Mai Dala ,yace zaiyi magana da tashoshin yada labarai,aiko dama suna jiran sa dama ba tun yau suke son yin magana dashi ba,kuma ga dama,Ranar Asabar,Alhaji Usman mai dala zaune gaban Yan jaridu, kasancewar shiri ne Kai tsaye ake ba inda ba'a gansa ba,Aï ce zaune,yau kawai taji tana sha'awar kalon tashar yada labarai,daidai an hasko fuskar Alhaji Usman Mai dala ,mtss wanan zancan siyasar nasu ne,har zata canza Tasha,anma abun Mamaki Wanda yayi matukar ruda ta shine,datijon da aka hasko,Mai matukar Kama da ita,sanan Mai Kama da kakar ta kulu,kur ta kura idanu ta maida hankalin ta akan TV ,Nan Alhaji Usman Mai dala ya fara jawabi,tare da Nuno wasu photos guda uku,das gabanta ya bada,da sauri ta Kara gusawa gaban TV Dan tabatar da abinda ta gani,abinda ta gani yayi bala'in girgiza tunanin ta gami da kwakwalwar ta,kurawa TV Ido ta Kara Yi zufa na tsatsaho mata,lokacin da taji mutumin ya ambacin mutanen,da kuma takaitacen tarihin sa na bacewar sa,da wata irin Kara Aï tace"kanin Kaka kulu ne,wly shine Wanda take bani labari ya Bata tun yana yaro,karar da tayi ya fito da Yan gidan,,,,. ,,,,,,,,,,,,,,,.,,,,,,,,,

Aci gaba da gashi🍇
Maimou love😘

[05/08 à 16:52] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞
💞💞💞💞
💞💞💞
💞💞
💞

*💖SO NE SILAR FARUWAN*💖
*💖HAKAN*💖

*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻
*(We are the Best writers among all writers*)📚

https://www.facebook.com/ANA-TARE-writers-association-2477871259112678/

*PAGE 97-98*

,,,,,,,,,,,,,,,Tv kawai take nunawa da hanun ta, bakin ta na rawa,hakan yasa su Sam baby suka Kai duban su ga TV babban mutumin Wanda yayi suna suka gani Yana bayani,da cigiya,tare da bada takaitacen labarin sa,su kansu Saida gaban su ya fadi,,,,,,,,,,,Dan idan aka ce maka Mahaifin Aï ne zaka yarda,lambobi ne aka fara badawa Wanda idan har akoy Wanda yasan d'aya daga cik'in wa'inda ake nema a wanan photon za'a basa k'yauta Mai tsoka,wato Aï ,da mahaifan ta ,sai kuma tshohuwa kulu. sune a jikin photon anma lokacin Aï tana goye baza'a iya Gane ta ba........

Cik'in sauri ta d'auki number sanan tayi saving dinta a wayar ta................

Wasu hawaye ne suke zubo Mata ,tana fadin" Alhamdulillah Alhamdulillah",tare da zubar da ruwan hawaye,tace"kulu kina Ina yau ga gudan jinin ki ya bayyana ,anma bakida ikon ganin sa,Koda ba'a fada ba wanan shine Dan uwan naki da kike nema,wayyo Allah nagode ma ,a yanzu da nake kukan rashin Yan uwa ,a yanzu Allah ya Aiko min dasu,Allah nagode ma,Allah ka Kara ma Annabi daraja."

Sujjada take tayi tana hawayen farin ciki.

Su Sam Baby ma,farin ciki suke,zama sukayi kusa da ita,suka dafa ta,Sam baby tace"sis sai ki Kira sa mana,dama mu ai fatan da muke kenan."

Girgiza kai Aï tayi tace "bazan iya neman sa ba a halin yanzu,nafi so agama hidimar bikin ku,tunda kunga Nan da sati daya ne,anma abinda nake so daku kumin Alkawari Koda Ansar ya Nemi sanin inda nake Kar wadda ta fada masa."
Kada Kai sukayi duka suna Mai Kara farin ciki,a ranar Aï tayi barci Mai cik'e da nishadi,marar misaltuwa."

Biki ne ya k'ank'ama gadan gadan,yayyin da Momy ta d'auko su Sam baby duka harda Aï a cewar ta ita zata zame musu uwa ,Bai kamata ba ace suna Yaya Mata Babu Wanda zai shige gaba a Al'amarin auren su.............

Dan ita Sam baby ko kadan batada sha'awar komawa kasar ta,yau in ta koma ma tayi me tunda ba mahaifiya.........Sam baby kuwa sai Dan uwan ta sani da ya shiryu yanzu Yana Yar sana'a sa ba laifi,da suka koma sun samu labarin Mahaifiyar sam baby dare daya aka wayi gari aka rasa ta,iyayen Ismail ko dama mahaifiyar sa ta rasu ,Mahaifinsa ma bai jima da rasuwa ba,shi yasa bai samu wani matsala wajen hanasa auren Karima ba,wato Kam baby, yanzu ya zama hamshak'ki,domin Mahaifinsa ya Tara kudin da shi kansa baisan addadin su ba,hakan yasa Ismail ya hada biyu yana karatun sa na doctor.
sannan Yana kasuwanci kassashe daban daban........
Duk da Yan uwan sa sunso su kawo matsala a auren sa a cewar su ya rasa wada zai aura sai karuwa!!!!!,yace yaji ya gani babu Wanda ya isa ya hana sa auren sa..
Kuma koma meye ai shi ya jefa ta cik'in karuwancin.
Wanan kenan...............

Momy Kam tunda suka dawo ta kawo masu gyyaran amare tace a gyyara mata yaran ta,Kai kace yayan ta ne wanda ta Haifa da ciki,dan har wani dadi Momy take ji Allah bai taba bata ya mace ba,gashi wayanan in tayi ai taimako ne,wannan abun da tayi ba karamin Kara Mata daraja da kima ba yayi a Idanun dubunan jama'a ,da kuma oga kwata kwata ,wato mijin ta,duk da zugar da kawaye suke Mata a cewar su wanan ai bata suna ne ,itakam saide tayi murmushi tace ta gode ,anma a yanzu babu wata alaka bare shawarar da zata kulla daga wata kawa,duk wada taji zata iya zata iya zuwa ta kama Mata tsare tsare na hidundumu.

Mom ce ta Kira su Aï d'akin ta dadare dukan su Harda zaky baby ita da ba aure zatayyi ba,duk da itama minister na Sam baby tunda Sam baby tace tabar karuwanci a lokacin Zaky baby Bata Bari ba sai ta hada su,hakan yasa kullum sai yayi ma Zaky baby maganar aure da Alkawarin in har ta aure sa bazai Kara bin matan banza ba,shima dole tasa shi Shiga wanan harkar saboda matar sa Sam batada ni'ima bare dadi,gashi idan anje wanjen sex sai tayi dakas shi zaiyyi kidan sa yayi rawar sa.to yanzu dai zaky baby tace ya bari tayi shawara ,Nan Mom ta fara masu Nasiha kamar haka.
Yayana na d'auke ku tamkar yayan da na haifa,ku bud'e kunnuwan ku dak'yau ku saurare ni,wanan Nasiha ce a tare da shawara, nasan dai kunsan abinda ya faru Dani akan zugar kawaye na banza Wanda na tabata badan ni matar wani ce ba, da ba wadda zata rabe ni,dan Haka shawarar da Zan Baku shine na farko
A yanzu karku manta nauhi ne zai hau kanku,zakuyi rayuwa ne k'ark'ashin mazajen ku,zaku zauna ne inuwa daya,ku zama Abu daya,duk Abinda mazajen ku suka gindaya muku matsawar bai sabawa dokokkin Allah ba to kubi,,,,,,,,,,, Auren ku ya zama domin neman yardar Allah kukayi ,ba Dan Tara abin duniya ba,,,,,,,,,,,,,,,,
Ku zama masu ruko da Addini a gidan miji,,,,,,,,
Kada ku zama masu k'auracewa shimfidar miji,ku zama masu matukar biyaya ga mazajen ku,ku zama kwararu wajen iya girki kala kala , kwaliya,tsabta,kada ku zama masu rainuwa a cikin duk Abinda mazajen ku zasu baku,akoda yaushe ku zama masu godiya da sa Albarka a komai kankantar abinda Mai gida zai Baku.........
Ku kula da abinda mazajen ku sukafi son ci safe,Rana ,yanma ,dare... Kuso dangin mazajen ku da iyayen su,karku zama masu kyashi Akan abinda mijin ku Yama Yan uwan sa,,,,, ,
Ku zama masu ma mazajen ku Addou'a a lokacin zuwa aiki da sauran su,ku tausasa kalaman ku yayin yima Mai gida magana,karku yarda kuyi sa'insa wato kace nace da mazajen ku,ku zama masu yin shiru yayin da mazajen ku suke muku fada,ku zama masu yawan basu hakuri,Koda ko Baku aikata laifin da suke muku fada ba akan sa,,,,ku rike sirrin mazajen ku,ku kiyayi Hulda da mugayen kawaye ,karku yarda ku dinga fita ba tare da yardar su ba ,ku zama masu kula da HQ dinku,Dan shi tamkar Ido yake baya son wargi,.........

Haka Momy taci gaba da musu Nasiha sosai, sanan ta sa musu Albarka sosai sukaji dadi,Dan har kuka sunyi ,Dan yau daya sun samu mai musu fada

,cikin farin ciki suka mata godiya tare da musu Alkawarin insha Allah zasuyi aiki da abinda tace musu.sanan suka koma d'akin da aka basu."

Zaky baby tace"Aïsha Kodan karamci da Abinda Mom tayi ya kamata ki koma ma Ansar ban hanaki ba idan kinje gidan sa ki Masa."
Murmushi Aï tayi tace"karki damu Zan koma ne ai anma ba yanzu ba,ganin tayi nisa yasa suka rabu da ita,kwantawa tayi ,tayi lamoooo,tana tunna yanda taga mijin ta lokacin da ya Fadi sume,runtse idanu tayi ,yayyin da taji Zuciyar ta na bugawa pat pat , shaukin mijin ta take sosai,ji tayi an Bata Tim a ciki, murmushi tayi ta shafa cikin ta Jin danta ko yarta sun fara motsi......

Ansar a gida duk ya rame ,kulum da rashin Aï yake barci,baida wani sukuni,kulum a d'akin ta yake barci,karewar ta ma da rigar barcin ta yake barci ya dukunkune Yana shakar kamshin ta.

Daky'ar Khalid ya Fido sa daga gidan washe gari dasafe,yace ya tashi suje wurin Amare suna gidan Mom harda Aishan sa tana can wajen Mom ,Jin An ambaci Aisha yasa ya juyo ya Kara kalon Idanun khalid Dan ya tabatar da maganar sa, Kai Khalid ya kada Alamun gaskiya ya fada,cikin Jin dadi ya tashi yayi wanka ,ya shirya cikin shada fara, yasha ado ,farin sa ya fito,anma kana ganin sa kasan Yana cikin rashin lfy,Dan duk ya rame fitowa yayi sai kamshi yake Khalid na tsokanar sa da wai ango Aisha , murmushi kawai yake masa ,suka Shiga motar Khalid ya tuka suka nufi gidan su Ansar,sai murmushi yake zaiga abar kaunar sa,gidan suka Shiga ,Ansar sai mamakin shige da ficen mutane da yake gani.
Chapter 36 · 0% Book details