← Book details So Ne Silar Faruwan Hakan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 43

Sashe 31

So Ne Silar Faruwan Hakan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai Aï tasha kukan ta ,ta tashi,tayi d'akin ta ,rufe k'ofa tayi,ta d'auki waya ta kira su Sam baby a daidai lokacin ko duk suna wuri daya a falo ,suna zancan auren Sam baby , da Kam baby Dan Khalid yayi wuta,sanan kuma yan uwan sun amince Masa bisa ga wa'azi da wani malami ya musu,Kam baby ma a tare za'a hada auren su a rana Daya da sam baby ,ita Kam baby zata auri Ismael ,tsohon saurayin ta,zaky baby dai ce shiru,anma duk sun tatara harka karuwanci sunyi watsi da ita,tun wata abokiyar Hulda suke gida daya su suna wani b'angare daban acikin gidan Dan mafiya ya kwakule Idanun ta,da kasan ta aka tsinto gawar ta,anma shi an Kama sa suka tsorata suka bar karuwanci.

Aï n'a kuka bayan sun d'auki wayar Sunsa a speaka tace" na shiga uku cikin kuka,a rude ko wane ke tambayar ta abinda ya faru,tana kuka dak'yar ta zayana musu abinda ya faru.

Su kansu abin yayi matukar Bata musu rai,Sam baby ranta a bace tace" ai sai ki tataro kayan ki ki bar Masa tsiyar gidan sa,aikin banza kawai,mutum sai zuciya! shi daban Ina ne da ba zaiyi bincik'e ba kawai daga an kula makirci sai ya hau ya zauna an fada masa bakida gata mtssss.

Zaky baby tace "a'a ba za'ayi haka ba ,idan ita tasan wata ai Bata San wata ba,Aish inaso ki bud'e kunuwan ki dakyau kiji,dole ne kici gaba da zama a gidan mijin ki,kalon ta sukayi duka da mamaki ,a tare sukace ta Yaya ?bayan kinji ya sake ta."

Murmushi zaky baby tayi tace "hum dukan ku Baku gano abinda ni n'a gano ba,idan har Aish ta fito daga gidan ta kenan ita Hanisa taci galaba,sanan in har ta fito ba ta yanda za'ayi tasan makircin da aka kula."
"To da kike cewa haka ta ya za'ayi ta zauna alhalin Babu aure yanzu tsakanin su cewar Kam baby,.

"Zaman idda "

Kalon ta sukayi duka,har Aï da taji maganar wata iri.

"K'warai ko zaman idda zakiyi Aisha bayan kin gama zakiyi zaman cikin ki har ki haife sa ,tunda yace ba nasa bane ya Bari in kin haihu a gwada jinin su,sanan ki bar masa gidan sa.
Anma kafin wanan dama ce Kika samu da Zaki dinga shiga iri iri wada zata rikitar dashi,sanan ki fida damuwa a ran ki,ki fida tsoron sa,har yanzu cin ki da Shan ki yana karkashin sa,sanan yanzu da Kika bar auren sa daga shi har ita duk Wanda ya taka ki ki kwaci yancin ki,karki yarda Koda hanun ki ya Kara rikewa,anma Zaki iya yin shigar ki ko wace iri a cikin gidan kiyi kokarin ki gano wanan kulaliyar da aka kula miki,domin shairin zina da auren ki ba karamin Abu bane,shi kansa nasan bazai iya rayuwa ba ba tare da ke ba,Abu n'a gaba da nake so ki tsiro dashi shine,idan Kinga irin wanan ya kasa ya tsare a gida yana zaune Zaki tashi kisha Shirin ki kiyi kyau ki d'auki mota ki fita,sai kizo nan,wanan ma wani salo ne,karki yarda ya zazaro Miki idanu ki nuna tsoran sa kike tunda ya yarda Zaki iya abinda yake zargi yaje yayi ta yarda watarana shi zaiji kumya."

Waw gaba-dayan su jinjina ma Zuky baby sukayi,domin tayi dogan tunani,dukan su sun hau dokin zuciya sun zauna idan Aï ta dawo ai ba hakan zaisa su warware matsalar ba.

_Dayawa mutane abinda bamu gane ba,ada idan namiji ya saki mace zata tsaya zaman idda a gidan sa,domin addini ya halata,zakuga ko wani Abu ya shiga tsakanin su daga baya mijin yayi nadama su maida auren su ,ko kuma ke mace in kece da laifi sai kiyi kokarin gyarawa,kuma shida kansa zai lura da hakan ya maido ki d'akin ki ba tare da kowa ya sani ba,to idan kinada matsala da mijin ki shi idan baiyi bincike ba ke ki zauna kiyi mana,anma yanzu zaka ga diyawa manta ke ja a sake su kuma Ana sakin sun ja Kaya Riki Riki sunyi gida,wai zuciya Ace tunda ya Kore ni to me zan tsaya Yi a gidan sa,yake Yar uwa idan har kinsan kece keda kuskure ki tsaya ki gyara ta hanyar zama kiyi karatun ta nutsu ki daina yin abinda baya so ,kiyi abinda yake so indai har sakin bakai uku ba ,zakiga kun daidaita Allah sa mudace Ameen_

Sosai Suka kara mata da Nasiha da nasu salon nan taji Zuciyar ta tayi sanyi,tayi alkawarin kuma insha Allah da yardar Allah duk masu hanu a kula mata makirci Allah zai tonu asirin su.

Wanka tashiga tayi duk da tana cik'in damuwa mayuka ta shafa masu kamshi,ta Nemo wasu riga da wondo masu kyau tasa,Dan cikin ta yadan fara fitowa wata hudu,anma sai ya mata kyau kwaliya tayi simple tasa turaruka masu matukar kamshi da sanyaya zuciya,taje gashin ta tayi ta sake sa har gadon baya sai kyali da walkiya yake bakikirin gwanin sha'awa ,takalma tasa kanana masu kyau ta fito daga d'akin falo baba ta nufa direct TV ta kuna ta zauna ta aza k'afa daya Kan Daya tana kalon wani indiya film na soyaya.

Hanisa ce ta fito da kwarkwasa yau ranta fari tas kuma tasan zuwa yanzu Aï ta bar mata gida dan haka taci kwaliya zata nufi wajen Ansar a cewar ta wai ta kwantar Masa da hankali.

Anma me turus taja ta tsaya sakamakon abinda ta gani,ranta ne yayi bala'in baci,tace a ranta meye ma'anar hakan ?
Meye kuma wanan nanatatar yarinyar take min a gida? Batada amsar tambayar ta Dan haka

Cik'in bala'i ta karaso falon kugu ta rike tace"ke Maya meye kike min a gida bayan an sake ki😡"
In kuda kenan kunyi magana to Aï ta kula ta ,yi tayi kamar bata san da wata halita a kusan ta ba,cikin bala'i Hanisa ta hargago zata shako wuyan Aï wata kara Aï tayi tace"kul kul karki fara Dan kinsan yanda nake da ma da akoi auren mijin ki a kaina ban raga Miki ba ,bare yanzu da nakeda incin kaina nayi abinda naga dama,dan haka karki soma."

Duk wanan maganganun da take akan kunen Ansar da ya fito Jin hayaniya,shi kansa da tace ada tanada aure yanzu batada Saïda gaban sa ya fadi,jiki sanyaye ya karaso gurin ,ganin Aï zaune tasha ado Saïda ya hada yawu ,dakewa kawai yayi take wanan pic din ya Fado Masa a Rai cikin kunci yakai duban sa ga Aï yace"ke me kike yimin a gida?
Wani kalo ta Masa uku saura kwata,tace "ya ban Gane me nake maka a gida ba,me ko Zan maka ,na zauna ne zaman idda da kuma abinda ke ciki n'a ,ina haifewa kaga da nabar gidan Ka ba sai na tsaya Bata lokaci ba sai muyi auren mu da kwarto na kamar yanda kace au n'a manta Ashe kace ciki ba naka bane,to kayi hakuri in yazo duniya sai mu tantance Dan kai ya waye akoi asibiti."
Runtse Idanu yayi domin wani irin daci yaji maganar ta ta masa,wani tashin hankali ne ke kara ziyartar sa,kasa magana yayi yayi ficewar sa,yabar gidan gaba-daya,Hanisa n'a Kiran sa tana cewa "au tafiya zakayi bazaka Kore ta ba,zaka wani tafi Ina ko juyowa baiyi ba,Dan in ya tsaya Zuciyar sa n'a iya bugawa a rasa sa..

Tun acikin mota dreba na Jan sa yake tunanin magangun Aï,"ina bazai yuba wly s'aide ki mutu ba aure ,babu Wanda ya Isa ya aure ki sai na dandana Miki kwantank'wacin bakin cikin da Kika dandana min ". Ya fada da k'arfi dreba kam tsoro abin ya basa ya juyo yace"yalabai lfy dai?

Wani kalo ya wurgo masa tuni dreba yasha jinin jikin sa yayi shiru.
A haka suka karasa gida yana zuwa ko daidai tashin Daddy boye damuwar sa yayi suka shiga d'akin daddy da shida Mom da salati dady ya farka, Idanun sa suka sauka bisa Kan n'a Mom yace"a'a yadai Mom Ansar wanan kalon fa."
Ya fada Yana murmushi,hamdala daga mom har Ansar sukayi sanan suka fada ma dad abinda ya faru ,anma suka boye masa da Mom ce,sukace wata kawar ta ce take son sa ita ta zuba magani a abincin Dan ya saki Mom ,har saki ya shiga,wanan karyar ko Ansar ne ya hada ta ,ya Hana Mom dinsa fadar gaskiya,Dan kar rayuwar auren iyayen sa ta tagayara.
Anma indan ta Mom har ga Allah taso yasan komai.

Daddy ya girgiza da maganar take kuma ya maida auren sa da Mom suka rungume juna,cikin shauki cikin kumya Ansar ya bar musu d'akin, b'angare daya damuwar sa ta yaye,sai ta Aï dake dawainiya dashi.

Aci gaba da gashi🍇
Maimou Love😘
[06/07 à 15:01] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞
💞💞💞💞
💞💞💞
💞💞
💞

*💖SO NE SILAR FARUWAN💖*
*💖HAKAN💖*

*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAHI AM💋*

*PAGE 89-90*

Sama sama suke jiyo kukan mutum Dan haka kusan a tatare suka fito,gaban su Saida ya Fadi ganin Aï a durkushe,tana kuka kamar ranta zai fita,kamata sukayi suka rungume ta ,suna dadaba ta ,Alamun rarashi.
Janta sukayi suka shige da ita falo ,ruwan sanyi suka Bata Tasha ,tana ajiyar zuciya,.

Nan suka so Jin ba'asi Bata boye komai ba ta fada musu.

Zaky baby ta fara magana tace "a gaskiya duk da laifin sa yafi naki kema kinada laifi,kinsan cewa har yanzu in ba Gama idda kikayi ba bakida incin kula wani,haramun ne,kuma ko baya ga haka keda yake zargi dama me yakai ki kula wasu mazan,duk da kinyi ne Dan ki Bata ransa,Kinga kenan kin basa damar da zai yarda da abinda yake zargin da kinyi kenan."

Kuka ne ya Kara kufce ma Aï ,Dan wulakancin da Ansar ya mata a yau Bata tunanin akoi ranar da zata yafe masa."

Sam baby dama tafi saurin d'aukan zafi,tace "tun farko banso wanan zaman ba nata na gidan sa ba,saboda namiji idan mace tafi nuna Masa so yafi Yi mata wulakancin da yaga dama,tunda Bata San ta zage ba ta kwaci yancin ta ba,wly tun farko Ansar Dan yasan Bai wani Sha wahala agurin auren ta ba,Bai kuma Sha wahalar shawo kanta ba,yagan ta a arha ai dole yayi haka,anma da ace an gara sa wly bazai Bari ko da Wasa ta kufce Masa ba.
Chapter 31 · 0% Book details