Sashe 1
So Ne Silar Faruwan Hakan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Copied
and
Compiled
By
Lady K
(KELLU BRAH MODU)
Yer BORNO
WhatsApp No:-08035507477
Yer Dakin Maimounah
Home of
Hausa and gyaran jiki novels Documents.
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞
💞💞💞💞
💞💞💞
💞💞
💞
*💖SO NE SILAR FARUWAN*💖
*💖HAKAN*💖
*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAHI AM*💋
*Ina kike Aisha Moh'd Barkindo wanan ma shafin naki 'ne*
*PAGE 1-2*
"Iye yar tsohuwa na tahi Sai n'a dawo, domin yau masoyina ne zai fara mana. "
Dariya Yar tsohuwar tayi, wada aka kira da iye daga ka ganta za takai shekaru sitin 60 à duniya, ta girgiza kai tace "Ai Allah shirya min ke, da wanan rashin kumya .
Tunda Ai ta kamo hanya take gudu gudu sauri sauri dan karta makara , idan kaga shirin ta zaka zata sabon kamu ce, sanye take da iniforme duk sun tsufa sundan fara yagewa ma, riga da wondo, yayin da tasa hijabi karami, ta kawo wani tsohon gyale ta d'aura à kugu, sai kace wada zata dambe, ta kara d'aura wani dankwolin atamfa à kai, bayan ta rataya wata tsohuwar jaka, yarinyar kyakyawa ce sosai, saide rashi ya sata ta zama wata munana, kamar yada ta saba kulum gudu gudu sauri sauri, à haka har ta isa scool din, kowa harkar gaban sa yake Anma tana shigowa aka fara nuna ta ga Yar mahaukaciya can, dan duk wanda yagan ta bazaiyi tunanin ba tanada cikakyan hankali Ba, su har sun saba da ganin ta haka, daidai zuwan ta aka shiga, itace à gaba, à hankali ya karaso cikin takun sa mai cike da nutsuwa da takama, tun kar ya iso suke jin kamshin turaren sa mai kamshin gaske da tafiya da imanin mai shakar sa, shigowa yayi cikin tamaka kamar ko yaushe yau ma yaci uban gayu cikin kananan kaya hada yar sarka karama ta gayu à wuyan sa, sanye yake da kaya farare, dogo ne fari jikin sa daidai shi ba kiba ba, shi ba ramame ba, hanuwan sa sanye cikin zobuna n'a azurfa da zinari.
Gayen ya hadu iya haduwa, yanada duk abinda mace zata nema à gun sa, kai gayen yanada kyau sosai.
Tun shigowar sa Aï ta saki baki tana kalon sa tana murmushi, yayin da take jin wani sanyi na ratsa ta ,ba ita kadai ba kusan ko wace budurwa kusan hakan suke ji saide sunsan ko sunsha giyar wake baza su samu ba.
À maganar sa ma abin sauraro ne a haka ya gama musu abinda ya kawo sa ya tafi..
Aï ta tashi zata bisa Safiya kawar ta ta lura da haka tayi saurin rike Aï . Taja ta bayan class tace "Haba Aï meye haka duk kin rude akan abinda kinsan bazaki samu ba. "
KO kalon Safiya batayi ba ta fincike hanun ta tayi Office dinsa, ya hadu iya haduwa yana zaune yana waya ga dikan alamu da budurwa, tsuru tsuru tayi har ya gama yamutsa baki yayi yana jin tashin zuciya yau wata guda kenan ya lura da take taken mahaukaciyar yarinyar nan ba wani fargaba tace "dan Allah ka ceci Rayuwa ta ka so ni wly zan iya komai a sonka". Saurayin kusan ji yayi tunda yazo duniya ba'a taba masa irin wanan raini ba, zagin ta yake uwa uba tare da korar ta kamar karya, haka Aï ta fita tana kuka Safiya ta tarbo ta, Aï ta kali Safiya da jajayan idanuwan ta tace "wly zan iya komai à kansa wly kinji n'a rantse zan iya shiga karuwan ci matsawar bai so ni ba.
Wai waye wanan gayen Ansar kenan dan gidan Président, shugaban kasa.
Yaro ne kyakyawa, kana ganin sa kasan ya sha nonon Fulani, domin baban sa da Momyn sa fulani ne kyawawa, auren soyaya sukayi, Mahaifin sa Abdoulkadir tunda ya taso yake son harkar siyasa, dan ya tashi da kudi basuda family sosai saï kanin sa Usman, suna Son junan su, dan tun suna yara iyayen su suka haifa kuma suka rasu, suka barsu da uwar dukiya, shi ke kula da kanin sa.
Abdoukhadir Ya Auri Amina
Auren saurayi da budurwa , yar wani tsohon minista ita kam yar dagin ce.
Auren su da shekara biyu suka haifi da Namiji Abdoul jalil suna ce masa Ansar,kyakyawa Son kowa kin wanda ya rasa, dogon yaro. Ansar tunda ya taso cikin gata yake sai abinda yake so yake yi, anma akoi sa da girman kai ,sanan baya Son wargi sai girman kai. Tunda ya taso à kasar waje ya gama karatun sa na bisiness, acan suka hadu da yar gidan kanin baban sa Hanisa, suke ma Juna so kamar su hade juna, har suka kamala ake shirin yi masu aure.
Ansar koda ya tashi course biyu ya karanta na koyarwa da bisiness kasancewar sa mai son koyar wa.
Iyayen na sonsa sosai kuma suna Son abinda yake so,
Shekara daya da gama course dinsa, aka hauda Mahaifin sa a matsayin shugaban kasa, wayo kuzo kuga farin ciki, anan ne Ansar ya kara daga kansa, yan mata na Son sa anma shi Hanisa ce hasken idaniyar sa.
.
Hakan yasa mahaifin sa yake tura Ansar makarantar gwomnati yayi basaja yaje yaga abinda ake gudanar wa, In har ana aiki da gaskiya..
Dan Ansar yana son koyarwa shi yasa ba musu yake yarda, yayin da yake lura da ko wane motsi na makarantar, à haka ne aka kaisa makarantar Karmu Secondary school GSS Karmu Sabo.
Yau wata daya kenan da farawa sa a à Makarantar wanan mahaukaciyar ta matsa masa. wai Ai itace mahaukaciya
Wacece Aï
Sunan ta Aisha, ya ga Malam Usman, Asalin su yan Niger ne, Usman buzu ne mai kyau sosai, tunda ya tashi yake Son rayuwar Nigeriya, kasancewar dangin sa yan daji ne suma ba mazauna ne ba, daga shi sai mahaifiyar sa kulu, nan ya tashi, yana dan kasuwanci ana rufa ma juna asiri da shida Mahaifiyar sa, watarana ya tafi wata ruga ta kauyan garin tessaou dake kasar niger, ya hadu da Laure bafulatana kyakyawa ya Aura, itama auren ta da shekara daya iyayen ta suka bar rugar dan suma ba mazauna bane, kuma basu fada ma yar tasu inda zasu koma ba, tunda laure taji haka tayi ta kuka, nan ta rungume mijin ta da surukar ta.
Auren su da shekara daya Malam Usman da Mahaifiyar sa bayan sun saida gidan su suka tatara suka dawo Nigeriya, Abuja nan garin yafi burge Usman nan suka samu mafaka, à.wata unguwa ta talakawa Karmu ,anan suka samu gida suke haya, Malam Usman à kasuwa yake sayo kanyan miya yana saidawa.
À haka suke zaune yau da dadi gobé ba dadi....
Bayan shekara uku da zaman su sun saba da mutane, anan Laure ta fara laulayi, Malam Usman da mahaifiyar sa sunyi murna sosai, nan ake tatalin laure, har lokacin haihuwa yayi suka haifi yar su Aisha, Suna kiran ta da Ai, yarinya mai kyau ta gado kyau gaba da baya uwa uba tana girma dirin ta na karuwa, doguwa ce, anma ba çan ba jikin ta dan madaidaici. Hakoran ta masu kyau farare da wushirya tsaka ,in tayi dariya dimple Dinta sai sun lotsa.
Fara ce tas, kai in na tsaya fada muku yanda take da kyan ta masha Allah bata lokaci ne Dan Allah ya bata
Saide Ai tunda ta taso masifafa ce, sosai bata d'aukan raini, saide In tayi shiri watarana ya ka zabga da gudu, ya Yar kauyen kayau.
Ko mahaukaciya
Anan tayi Primary school, ta fara secondry School karmu, tana da shekaru sha shida iyayen ta suka rasu à sanadin Accident zasu Je Niger ganin dangi, duka suka mutu à mota.
Wanan abu ba karamin taba kulu da Ai yyi ba, sai daga baya suka fawala ma Allah .
Aci gaba da gashi🍇
Maimou Love😘
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞
💞💞💞💞
💞💞💞
💞💞
💞
*💖SO NE SILAR* *FARUWAN*💖
*💖HAKAN*💖
*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋
*PAGE 3-4*
Tun daga wanan lokaci kulu ke kula da jikar ta, su ke kula kayan miya daga gida suna sayarwa, dashi suke biyan mai hayar su, duk da bashida mutunci ko kadan, dan ya taba watsar da kayan su lokacin da baban Ai yana raye dan sun d'au lokaci basu biya ba, mai gidan yazo yasa aka masu watsi da kaya saida wani Mai kudi yazo bada zaka, a ciki ya bada kudin hayar na shekara biyu, to tun daga lokacin suka samu saukin abun.
Ranar da ansar yazo makarantar a matsayin Malamin da zai koya musu Mathemaque a cikin wanda zai koya má harda su Aï, ranar farko da yazo class din su ya fara koyar wa, cikin shigar Sá ta kananun kaya bakake, sun masa kyau matuka, shirin ya fido da ainahin kyan sa, a ranar Aï a makare tazo, tana zuwa ta shigo, bata ma lura da malamin ba, tsawa yayi mata, ta zabura ta juyo, nan yace "ke wace irin daba ce, class din ta uban ki ce da zaki shigo lokacin da kika ga dama, fada yake tayi kamar zai doke ta, anma duk wanan fadan Ai bata ma san yanayi ba, ta tafi duniyar shauki, ji take in ba wanan gayen ba ita kam saí rijiya, ganin bata ma san yanayi ba yasa yasa wani abu a hanuwan Sá kamar safa ya jata kiiii saí waje yana kaita waje ya yar yana toshe hanci tare da kara yi mata fada, ransa duk a bace.
Ikon Allah ranar duk fadan Aï kasa magana tayi jin wani bakon tabaco na shigar ta game da wanan Malami, yan ajin nasu sunyi mamakin Aï bata d'au mataki ba, kasancewar bata barin ta kwona, koda ko malami ne, wasu suna cewa taga ba wurin wasa bane, kowa da abinda yake cewa.
Tun lokacin ta tsiri zuwa Office dinsa tace dashi tana son sa, shi kuma ya mata wulakanci. Dan in akoi abunda ya tsana to itace ,in bama raini ba mai zaiyi da talaka irin ta,mai zai tsinta a jikin ta, kazama, munana.
Wanan kenan,
Safiya kawar ta ce, itama iyayen ta ba masu hali bane saide rufin asiri, tana iya kokarin ganin Aï ta saitu anma abin yaci tura, so ya rufe mata ido, taki ganewa cewar ansar ko mai gadin gidan su ya huce ajin ta, a cewar sa.
Ci gaban labari.