← Book details So Ne Silar Faruwan Hakan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 43

Sashe 40

So Ne Silar Faruwan Hakan Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Sam Aī taga masu aiki nata aiki,duk a tunanin ta Mr President bakin turawa zaiyi kamar yanda ta saba gani,kowa sai hidima yake, president ya sa a Kira masa Aï ya mata fada,sanan ya mata Nasiha ,dan bai taba haihuwa ba,daga shi har matar sa suna matukar son Aï kamar Yar cikin su.
Matar president ita ta shirya Aī ta Kira mai Make up dinta tayi ma Aï,ta fido mata wani farin less Wanda malakin Aï ne,kudin sa ma kusan dubu dari biyar yake,an mata dinkin Niger,ga doguwar sarkar zinari wada kudin ta zaikai kimanin naira million biyu,da aka sa mata,aka mata d'aurin dankwali na zamani,ga jan lale da aka Dan zana mata a yatsu kadai, kasancewar cikin ta yayi girma dogon zama ba nata bane.kai tayi matukar kyau,yanda kyanta ke kara fitowa sai walkiya take,tayi wani fresh ,ga cikin yayi bala'in yi mata kyau Kai abun Masha Allah.
Ita kanta da taga abin yayi yauwa,ta tambaya Shirin meye,ce mata akayi photo family za'ayi.
Ta yarda dan bata kawo komai a ranta ba,anma yanayin yanda gaban ta ke faduwa abun ya fara tsorata ta....
Ansar na durowa Niger a kasar Niamey akaje tarban sa da zuka zukan motoci na Alfarma sunkai guda Ashrin,shi kansa ya girgiza ,da wanan abu,Nan aka d'auko sa,tsarin Niger da rayuwar su yayi matukar burge sa,komai cikin tsari suke yinsa,ba kwaramniya,bai idda tsinkewa ba saida suka zo gidan shugaban kasa tofa,shi abin yayi matukar ruda sa,dan a tunananin sa ko batan Kai sukayi duk da way ba yafi nasu gidan bane,a'a tsarin ne yayi matukar ruda sa.........
[05/08 à 16:56] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞
💞💞💞💞
💞💞💞
💞💞
💞

*💖SO NE SILAR FARUWAN*💖
*💖HAKAN*💖

*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻
*(We are the Best writers among all writers*)📚

https://www.facebook.com/ANA-TARE-writers-association-2477871259112678/

*PAGE 106-107*

,,,,,,,,,,,,,,,,Masha Allah kawai yake furtawa,tun a k'ofa ake karama sa ana masa sanu da zuwa har aka masa iso uncles din Aï ya fara cin Karo dasu ,su biyu,suka rungume sa tare da ce masa (bienvenue Mon fils),ma'ana (welcome son).

Murmushi Ansar yayi tare da cewa( "Merci beaucoup") dan shima ya iya yaran French,nan suka rike hanun sa suka shiga dashi cik'in falo,waow ya furta a ransa, dan falon yayyi matukar tafiya da imanin sa,duk family din Aī sun tarbe sa cikin karama da mutunci,sunyi matukar jin dadin ganin sa,shima yaji dadin yanda suka tarbe sa,a cik'in ransa ko wata kumyar su yake ji,ji yake kamar a gaban su yayi ma Aï gorin asali,gashi ita har ma tafi sa family din masu wadata,domin har uncle uncle dinta sunada kudi, ba karamin mai kudi a cik'in su,daya shugabanin sojoji na kasa gaba-daya daya kuma minister ,ga kuma shugaban kasa,ga kakan ta,wanda ko ya sani acikin masu kudin duniya ,za'a iya jera sa a sawun su,wato Alhaji Usman Mai dala,anya zai iya hada idanu da Aï kuwa,dan kumyar ta yake ji sosai."

Wuri suka basa ya zauna nan suka fara gagaisawa,sai ga kakar Aï ta wajen uwa da kakanta,sun iso,kakar tace ",kardai har mijin nawa ya iso,ai nayi fushi bazan koma ba, dariya aka kwasa ita kuma ta rungume Ansar,kowa Yana dariya,shima kakan ya rungume Ansar tare da cewa"ai ki barsa kawai ba yayi sake ba,ai ni ga amaryar tawa can ta kawo kanta,ciwon so ya kawota har inda nake ."
Dariya aka kuma yi cik'in raha,ba'a jima ba shima shugaban kasa yazo suka gaisa,nan aka zauna saman dogon table,Wanda mutum arba'in zasu iya zama suci abinci,Ansar sai raba idanu yake yaga matar sa anma shiru,duk ya matsu ya ganta,(première dame) ce ma'ana(first Lady) ta danna wata kararawa,wada matsawar aka danna ta to duk wanda ke cik'in gidan yasan mai ake nufi.
A hankali Aï ta taso daga kwanciyar da take,gaban ta sai faduwa yake,kulum in an danna kararawar Nan ana nufin a taso aci abinci,hankali kwance take zuwa,anma yau ta rasa dalili ana dannawa saida gaban ta ya Fadi,a hankali ta sanya takalman ta,tasha kyau matuka,gidan yan boko ne,babu ruwan wani da suturar ka,dan haka bata damu da ta sanya wani gyale ba ko hijab kawai d'aurin dankwalin dake kanta kadai ta fito a haka ,ga katon cik'in ta da yayi bala'in yi mata kyau.

A hankali ta tako ta sauko daga bene,tana Dan bata fuska cikin shagwaba,ta karaso kusa da first Lady tace"Momy wly bana jin yunwa,anma nasan in ban fito ba sai kin cika min kune."
Duk cik'in shagwaba take maganar sam bata lura da wanda ke gurin ba ,dan kusan su duka haka take musu,dan suna ji da yar su suna sonta sosai."
Dariya first Lady tayi tace"to ai kece saida haka ,domin in ba haka na miki ba bazaki fito ba,zauna ko a baki kike so sai na baki a baki, dariya aka sa Kaka tace "tofa yau kuma salon da kuka zo dashi kenan,ku kulum da kalar naku akayi dariya,sanan Aï ta fara gaida uncle uncle din nata,wayo Allah lokacin da ta sauke idanun ta akan fuskar Ansar ba karamin faduwa gaban ta yayyi ba, Kara murza idanun ta ta Kara yi, ta tabatar da shi dinne,kalon kakar ta tayi ,sai kakan ne nata yace"ja'ira to ai mijin ki ne,dama shine bakon ."🤣 Dariya aka kuma yi,tsaye take anma cik'in shok ,sakaka yayi yana kalon ta ,dan ba karamin kyau ta masa ba,ga cik'in da kulum yake mafarkin sa. shima Ansar kur ya kura ma farin cikin sa ido cik'e da kewa,,,a hankali dukan su suka hada idanu tare da tashi gaba-daya suka bar gurin dan sun gama cin abincin su.

Aï sai juyawa tayi taga ba kowa, cik'in sanyin jiki ta juya zata bar gurin ,da zafin nama ya tashi ya riko hanun ta tare da dukawa,idanun sa cik'e da kwalla yace"haba kalbi kiyiwa girman Allah wanan horon ya ishe ni,ki duba yanda na dawo saboda ke, gaba-daya bana jin dadin duniyar idan bake a tare dani,dan Allah ki sasauta min,kodan ciwon Zuciyar da na kamu da ita a dalilin ki idanu ta waro a matukar tsorace ,yace"yes gaskiya na fada miki, inada ciwon Zuciya da hawan jini,kalbi har kasar waje daddy ya fitar dani saboda ciwo na ,wly kalbi a yanzu nasan daraja da kimar ki ina sonki wly koda wasa bazan kara sake na miki wani abun da zai bata miki rai ba,dan Allah kalbi ki dawo d'akin ki kizo muyi rayuwar mu cikin Jin dadi."
Aï ko dama ta jima da yafe masa dan tasan zuwa yanzu ai ya gane kuran sa,,dan haka cik'in tausayawa tace"Ansar kayi Alkawari bazaka Kara k'watank'wacin abinda kayi min ba,Ansar ka cutar da rayuwa ta ,babu furcin da yafi taba raina kamar yanda kaso shegenta min dan ciki na,wanda a lokacin ko gama halitar sa ba'a gama ba,tashi yayi cik'in zafin nama ya hade bakin su dan gaba-daya ji yake kamar tana zuba masa garwashin wuta a jikin sa da take wanan maganar.........

Sosai yake sarafa bakin ta , dak'yar ta kwace bakin ta ,tana raraba idanu tace haba" hub baka ga a falo muke ba."

Ransa fari tass yace "dan Allah maimaita abinda kika ce plz"
Langwabe kafada tayi a shagwabe,tana jin wani son mijin ta tare da tausayin sa yana shigar ta......
Kalbi na miki Alkawarin bazan kara maimaita abinda na Miki ba,Zan baki farin ciki,
"Plz muje d'akin ki in ba so kike muyi abin kunya anan ba,jan hanun sa tayi dan dama gidan hawa shida ne,ita kadai ke hawa na biyu,kakanin ta na kasa ,dan haka ta jasa sukayi d'akin ta,suna shiga ya rufe k'ofar da key,wani irin kamshin dadi yaji ya buge sa a hanci,daga ji yasan na matar sa ne kuma kamshin yayi matukar missing dinsa, d'akin ya gama ma kalo komai na rayuwar duniya akoy,zama yayi bisa gadon Yana kara kalon tsarin d'akin,wajen firge dinta taje ta hado masa fruits a plat,ta d'auko juis din da take hadawa tazo ta kawo masa,amsa yayi ya amshi kayan ya rungumo ta."
Chapter 40 · 0% Book details