← Book details So Ne Silar Faruwan Hakan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 43

Sashe 26

So Ne Silar Faruwan Hakan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hanisa ce zaune a falo ita da Mom sai cika take tana batsewa, cik'in kisa tace" Mom wly ni ba wai inajin haushin dan ta samu ciki bane a'a kawai yanzu in har ta haihu haka za'ayi ta zagin yayan dan uwa na ana cewa ga yayan karuwa nan,gata yarinyar batada Asali Mom ranar ma fa haka naji tana waya da wani kato,kuma wly Mom saurayin ta ne,wai tana ce masa yayi hakuri itama saboda dukiya tayi aure da ta samu abinda take so zata rabu da mijin ta,ta kwaso dukiya ta gudu tazo suyi aure."

Zaro ido Mom tayi,tace "kaji min shegiya ashe ba banza naji n'a tsane ta ba ,mu zata cuta,karki damu ya ta yau zanyi maganin abun yau sai ya sake ta."

Wani mugun dadi Hanisa taji tana kara zuga Mom.

Ansar yayi ma Aï salama cewar zaije gida ya lalabi Mom,ya ganar da ita, Aï ta masa fatan nasara sanan ta koma barci,yayima doctor magana a samu mai kula da ita zai dawo bada jimawa ba.

A sanyaye yayi Salama a falon ,Mom ta daga kai tana ganin shine tayi kicin kicin da fuska kamar bata taba dariya ba,dukawa yazo yayi,ya marairaice,nan ya fara rokon Mom yafiya yana mata rantsuwa cewar wly kulum in ya koma d'akin ta sai ya bata maganin Hana d'aukan ciki,ya tabata cik'in tun daran farko ta d'auke sa. Hanisa wani Haushin sa take ji kamar ta shake sa.

Nan yayita shawo kan Mom,Can sai ta dan yi murmushi tace" ba komai ,kaje ga abincin ka can irin Wanda kake so nasa an maka,shi kam hamdala yayi ganin mahaifiyar sa ta sauko,kira ne ya shigo a wayar Hanisa n'a Safiya,nan Hanisa ta d'auka ta fita waje tana jin haushi da bakin cikin Mom da Ansar.

Ansar duk da a koshe yake ganin Mom ta yafe masa har tasa aka dafa abinda yake so dan haka zaici dan ya faranta mata, cik'e da farin ciki ya rungume Mom yace"thanks Mom.

"Ba komai Son muje n'a zuba ma da kaina,tashi sukayi ta zuba masa komai sanan ta shafa kansa tace"son kaci dakyau bari naje nayi wanka kafin Daddyn ka ya dawo."

"To Mom a fito lfy."

Hawa saman ta Mom tayi tana murmushin mugunta,ta shige d'akin ta ta fada wanka,
wankan Mom sosai yake d'aukan lokaci dan takan kwashe awa daya tana wanka,.

Ansar ya d'auki abinci zai kai bakin sa kiran Khalid ya shigo nan suka koma kuma fira, Daddyn Ansar ne ya dawo,yayin da jiniya ta cika gidan,falo ya shiga da Salama ya hango Ansar saman diner yana waya,nan ya nufo sa,shima ya zauna, kusa da kujerar Ansar ya kashe waya yana murmushi yace"daddy barka da zuwa,kaga Mom tamin abinci mai dadi ni kadai."

Dariya Daddy yayi yace"son ai nima yunwa nake ji,bari n'a dana nima,dan abinda ya koro ni kenan,Ansar n'a dariya shi ya zuba ma daddy duk Abinda Mom ta zuba masa,daddy n'a hada yawu yace "waw wanan abinci daga ji zaiyi dadi,tare suka suka daga cokali suka Kai bakin su,suna ci,waw abincin yayi dadi cewar Ansar,nan suka ci gaba da ci,yayin da gaba-dayan su suke jin wani irin sauyi a jikin su,Mom ce ta fara saukowa tana farin ciki dan tasan wata kila zuwa yanzu Ansar yaje aiwatar da saki, Hanisa ma a daidai lokacin ta gama waya ta dawo falon,daidai saukowar Mom ta dafe kirji da k'arfi tace n'a shiga uku,daga daddy har Ansar suka juya ganin matan nasu take sukaji wani irin abu,tamkar an buga musu guduma a tsakar Kai ,yayin da sukaji ,wata irin tsanar matan su ta dirar musu,daddy take yaji tsanar Mom ta shige sa,shima Ansar wata irin tsanar Hanisa ta dirar masa,a take ko wane ya kali matar sa kusan a tare kowane yace n'a sake ki,
Daddy yace ya Saki Mom ,shima Ansar yace ya saki Hanisa,daidai shigowar hajiya Balki domin ta fada ma Mom abinda boka yace game da maganin Wanda ta manta bata fada ba,tayita neman layin Mom ta fada mata bayan ta koma gida da ta tuna anma kira yaki shiga,kwatsam ta shigo falo taji wanan Mumunan abun,Mom da Hanisa kusan sankarewa sukayi wuri daya,zuciyar su n'a wani irin bugawa.

Aci gaba da gashi🍇
Maimou Love😘
[17/05 à 03:13] Maimouna Matar Abdoulaye😍: 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞
💞💞💞💞
💞💞💞
💞💞
💞

*💖SO NE SILAR FARUWAN💖*
*💖HAKAN💖*

*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAHI AM💋*

*PAGE 71-72*

"Daddyn Ansar lfy la kuwa ,ko ka samu matsala ?

Cewar Mom
Daddy rai a bace yace "lfy uwarki,nace n'a sake ki Saki biyu ki barmin gida na."

Nan kusan a tare suka rubuta suka basu takarda shida dansa,wani ikon Allah daga daddy har Ansar babu Wanda ya tambayi junan su dan me akayi haka.

Sai ma fita da sukayi gaba-daya daga gidan kowa yayi hanyar sa,Daddy da escort dinsa suka je airphore suka hau jirgi dan dama tafiya gare sa n'a wani taro a kasar waje da zakayi, a yanda yake jin zuciyar sa game da Mom ko ba wanan tafiyar baya fatan sake haduwa da ita.

Ansar kam Asibiti yayi Rai a bace,dan shima sam bai kaunar ya kara ganin Hanisa.

Mom tsaye take tana kalon takarda tare da sakin da aka mata ,ita kam Hanisa kuka take sosai,Mom ita abin tsoro da mamaki da ban Al'ajabi suka tarar mata ,ta ya akayi haka.

Hajiya Balki ta duka har kasa tana ba Mom hakuri cik'e da dana sani,anan take fada mata abinda boka yace,sanan bata san cewa ba Hanisa ba ba itace Aï ba dan sunan ta ta Bada.

Mom kuka ya kufce mata ,tace Hajiya Balki kin cuce ni Allah ya isa tsakani n'a dake,wly Allah ya isa dama abinda kike so kenan kina bakin cikin ni inada aure ke bakida ,Allah ya isa kuma sai n'a d'au mataki a kanki, shegiya mai sufar Yan wuta......"

Ran Hajiya Balki a bace ta tashi ta wurga ma Mom wani mugun kalo tace"a'a ke Malama kimin shiru da bakin ki,ba ke kika kira ni ba ina zaman zama n'a Kika ce a aiwatar da aiki,ni n'a tursasa ki ne,inajin shawara n'a baki kuma ba matsa miki nayi ba cewar ki d'auka,shine har Kika samu damar zagi na,to kinyi da diya,mai Kika kare ni dashi, dadin abun inada abin hanu n'a ban dogara da kowa ba,dama ai Ance duk Wanda yaki sharar masalaci dole zaiyi ta kasuwa,ke kin isa ki ja da Allah,ni dama yar abi yarima asha kida ce ko yau Kika ce naje gurin wani Malamin ko n'a kaiki cass zan kaiki."

Tana gama fadar haka tayi tafiyar ta.

Mom kam hanu ta aza bisa kai,yayin da take kara jin tsanar Aï.

Kamar daga sama Mom taji Hanisa n'a mata Allah ya isa tare da tsine mata,dama Hanisa in Rai ya baci bata san abinda take fidowa daga bakin ta ba.
"Allah ya isa tsakani n'a dake ashe dama munafuka ce ke ni kike so a fida ba Aï ba kike fakewa da ita,sai yanzu n'a gane bakin ciki irin naki,Ana munafurci Ana nuna Ana son mutum ashe karya ce bayan sa ake son gani.

N'a gode ma Allah da n'a zubar da cikin d'anki da yanzu an barni da wahala,sanan ki fada ma tsinanan d'anki ya saki yazo koda k'ofar gidan mu ne sai n'a halaka sa munafuka tsohuwa kawai."

Tana gama fadar haka ta higi jakar ta da takarda tabar gidan Rai a bace.

Wohoho Mom kam gaba-daya busoshin kanta suka kunce kwakwalwar ta ta daina aiki komai ya tsaya mata cak, Hanisa ce ta mata haka ta zage ta , Hanisa da ta d'auka tamkar yar cikin ta, yarinyar da ta fifita fiye da danta ma,take ta fara da n'a sanin abinda tayi ma Aï,domin ko tantama babu Alhakin yarinyar nan ce ashe Hanisa har cikin danta ta zubar ,wayar daddy ta kira a lokacin yana shirin shiga jirgi,ya d'auka Rai a bace yace"wly wly Kika sake kira n'a mai raba mu hum,sai nasa an rufe min ke , sanan ki tabata kin barmin gida n'a,ko minti goma ban yarda ki kara ba." Yana gama fadar haka ta kashe wayar.

Tashin hankali da ba'a sa masa rana,ranar Mom ta gansa ,dan saida ta kusa zama tamkar mahaukaciya.sai dumi take ita kadai.

Kuka taci har ta gode ma Allah sanan ta tashi ta hada kayan ta ta d'auki abinda zata d'auka tashiga mota tabar gidan,masu tsaron ta zasu bita ta tsayar dasu tare da cewa bata bukata.........

Sai mamaki suke ,yau gidan ya hargitse, Président guda Rai a bace,dansa ma haka ga sarakuwa,ga itama hajiyar first Lady.hum Allah kyauta.

Hajiya a mota sai kuka take,ace kamar ta godo godo da girman ta taje ma iyayen ta da takardar Saki,ai abun da kumya,bazata iya ba,dan haka ta nufi wani katon gidan ta Wanda akoi komai a ciki,acan ta koma,ta dawo da Yan aikin ta biyu amintatu suka zauna ciki.

Ansar kam ,yana isa asibiti a gadon da Aï ke barci ya haye bayan ya rufe d'akin da key ya rungume ta ,take yayi wata irin ajiyar zuciya,nan ya samu shima barci ya d'auke sa.

Bayan awa biyu Aï ta farka ta gansa tayi mamaki,anma kuma sai tayi murmushi ,dole tasa ta koma barcin dan kar ta tashe sa taga kamar yana jin dadin barcin.

Bayan kwana biyu da jinyar Aï aka Salame su anma abin Mamaki sam ya kasa tunawa da Mom bare ya neme ta ,ko ya kira ta,ko yaje gidan.

Aï ta warke ras,komai tana yi da kanta,yayin da take Mamakin rashin jin motsin Hanisa a gidan,kasa hakuri tayi ta tambaye sa ita,ransa in yayi dubu to ya baci,jin an ambaci sunan Hanisa dan haka fada ya dinga mata,tare da kashedin kar ta kara Kiran koda mai wanan sunan ne a gidan sa,ita kam abin ya bata mamaki,sai tayi tunanin ko Hanisa ta masa baban laifi ne,anma bazata tambaya ba ,dan tsakanin miji da mata sai Allah.

Bayan sati daya ,Mom duk ta lalace tayi baki,ta rame,kulum cikin istigfari take,yayin da shiko Ansar sai a yanzu ya tuna da mahaifiyar tasa.

Sorry Bana jin dadin yin typing sai a hankali😂

[05/06 à 13:21] Maimouna Matar Abdoulaye😍: 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞
💞💞💞💞
💞💞💞
💞💞
💞

*💖SO NE SILAR FARUWAN*💖
*💖HAKAN*💖

*NA*✍
*MAIMOUNA MARAR ABDOULAHI AM*💋

*PAGE 73-74*
Chapter 26 · 0% Book details