← Book details So Ne Silar Faruwan Hakan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 43

Sashe 34

So Ne Silar Faruwan Hakan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Pau Pau kake ji ya d'auke ta da mari ransa a matukar bace ya nuna ta da yatsa yace"ni Ansar nafi k'arfin wulakancin ga duk wata diya mace,macen ma kuma irin ki marar asali ,wada batada gata,ki sani Ina haka ne bawai dan ina sonki ba Saïdai inason kema ki dandani bakin cikin da n'a dandana,zina da auren ki ,ki fada min ban Kai namijin da zai biya miki bukatar ki bane,ni ba namiji bane da Zaki Nemi wani, ko yafini dadi ne,yanda yake magana Yana hargagowa yaja hankalin mutane dake gurin aka Dan fara musu taro,Sam ransa ya baci ya manta inda suke bayan bakaken maganganu da yake banka ma Aï da gori da tozarci ba abunda yake mata,Aï ko ganin taron da aka masu yasa hankalin ta ya tashi tunda take Bata taba ganin irin wanan cin mutuncin da wulakancin irin na yau da Ansar yake mata ba a bainar jama'a,gaban dubunan mutane.
Kuka ne mai k'arfi ya kufce mata,dan haka da gudu ta shige motar ta ,ta kuna a matsiyacin gudu ta tuka motar tabar gurin,shima ganin Yana mata magana tabar gurin ransa ya Kara baci,ya tada mota shima ya bita,gudu ne suke har na fita hankali bisa titi kamar masu gudun tsere,Aï ALLAH kadai ya kaita gidan su Sam baby,shima Ansar tana shiga da hancin motar ta bayan mai gadi ya bud'e shima ya shiga,bud'ewa tayi zata fita,shima ya bud'e tasa motar ko rufe ta baiyi ba,yazo ya finciko ta,juyowa tayi,tana kuka,da yatsa ya nuna ta yace"ba'a taba min wulakanci ba,Dan haka baza'a fara a kanki ba,ni nayi k'arfin duk wata yar iska yar matsiyata ,yar talakawa da zata nemi ta raina min hankali,nafi k'arfin ki dake da duk Wanda suka tsaya miki,in Banda ma ni mai zanyi da mazinaciya irin ki,wada Bata San darajar aure ba,ayau ina bakin cikin fara sonki a rayuwa,ai shi dama talaka duk yanda kake kyautata masa watarana sai ya nuna maka halin sa n'a akuyanci,duk yanda ka d'auke sa kakai sa inuwa wataran sai ya kaika rana,in Banda ma kadara Mai zai kaini gare ki,ga mata nan kala kala sai wada na zaba,kije nikam kin fice min ,kije kiso duk Wanda Zaki so kiyi karuwancin ki yanda Kika ga dama,nima ki barni na zauna da matata, stupid ."
Yana Gama fadar haka yabar wurin ya shige motar sa ya tada ta yabar gidan gaba-daya Aï ta durkushe a gurin ta aza hanu bisa Kai ta kece da wani irin mugun kuka,Mai ban tausayi."

Bayan kwana uku Alhaji Usman Mai dala akaci nasarar farkawar sa,anma abin Mamaki Yana farkawa ya fara Kiran sunan Yaya kulu Yaya kulu kina Ina Yaya kuluuuuuuu.

Aci gaba da gashi🍇
Maimou love😘
[06/07 à 15:01] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞
💞💞💞💞
💞💞💞
💞💞
💞

*💖SO NE SILAR FARUWAN💖*
*💖HAKAN💖*

*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAHI AM💋*

_sisters anji jiya Kuna cewa nayi mistake awajen sa number number jiya kamata yayi mutashi a 91-92_
_To ba haka ne ba ku duba dakyau ku gani number da nasa na jiya shine daidai 89-90 ki duba dakyau inajin kunai dai kukan Aï ya ruda ku_😂

*Page 91-92*

Sam baby Bata tsaya ko Ina ba sai office din Ansar ,an barta ta shiga,tana zuwa da salama ta shiga ,Ansar ne kwance Idanun sa sunyi jawur da Alamun ma kuka yayi,ga Khalid kusa dashi,tari ne ya Kara turnike Ansar Wanda tunda ya dawo daga gurin Aï yake yinsa,tari ne duk tare da jini da ya fito daga bakin sa,da sauri khalid ya rike sa ,Saida ya Gama ya amshin tissu din da ya zuba ma jini ,yaje ya yar a kwandon shara .

Sam baby da tazo da Shirin Masa rashin kumya ta rama ma Aï Saida ta tsorata ganin sa a haka,hankali tashe ta jefa ma Khalid tambaya" me ya same sa?
Sauke nauyayar ajiyar zuciya yayi yace"saboda Yar uwarki ce ya shiga wanan halin."

Zama tayi Dan nesa dasu ,ta kale su daya bayan daya,sanan ta sauke ajiyar zuciya tace" Khalid!!!!!!!!!
Dago da Kai yayi ya kale ta ,domin tunda take dashi Bata taba Kama sunan sa ba,,Saida ta nisa sanan tace"a gaskiya bana Jin Zan iya auren ka dum gaban Khalid ya bada ,a take ya shiga tashin hankali shi kansa Ansar dake cikin ciwo Saida ya dago ya kale ta, girgiza kai tayi tace "domin ance idan abota tayi kamari Hali ma yakan iya zama daya,hausawa sunce abokin barawo barawo ne,kamar yanda abokin ka ke kalon wanan marainiyar Allah ,Yana cin zalunta ,Yana hukunta ta,Dan kawai itace farkon fara furta Masa kalmar so, duk yanayin da suke ciki a yau *so ne Silar Faruwan hakan*
Da badan so ba da na tabata a yanzu tana rayuwar ta tajin dadi,badan so ba Babu da namijin da ya Isa ya furta mata bakar kalma,anma yau abokin ka ke Kiran ta da karuwa,alhalin shine mutum na farko da ya fara yaga mata rigar mutuncin ta,Ansar Ina zaka Kai alhakin marainiyar Allah ,Ina zaka Kai hakin ta,ko wani yace maka Aisha zata kula da namiji da auren ta Kai Mai karyatawa ne,Koda ko ka ganta ita da wani zaka iya cewa asiri akayi mata,anma da hankalin ta bazata Yi haka ba,karka manta nida Yan uwa na sabon Allah muke,Babu yanda bamuyi da ita akan ta shiga,anma kulum kalmar ta guda ce shine muma muda muke Yi Allah ya shirye mu,Koda firar maza muke zaka ga ta rabe tana kuka ,tana Jin takaicin abinda Muke anma yau har kaga Abu ba tare da bincike ba ka yanke hukunci,shide Ansar baice komai ba baicin zuba mata Ido da yayi,Yana nadamar mugayen kalaman da ya furta ma Aï.

Video Sam baby ta bud'e wada ta d'auka ta su Hanisa saiga su far ana gani har maganar da akeyi komai ana ji,ta mikawa Ansar tace gashi ka duba.".

Ba musu ya amsa domin jikin sa yayi sanyi ,kalon video yake jikin sa na tsatsaho Masa da zufa,Yana Gama kalon video Nan ya Fadi a gurin a sume .

Amatukar tashin hankali sukayi kan sa,Da k'arfi Khalid yace "bani ruwa "
Da gudu taje firge ta d'auko ruwa masu sanyi aka zuba ma Ansar ,ajiyar zuciya Ansar ya sauke tare da tashi ,dishi dishi ya fara gani can ya sauke Idanun sa akan Khalid da Sam baby hawaye ne masu zafin gaske suka fara zubowa a kumatun sa,cikin k'arfin Hali ya tashi Yana kuka,"Hanisa kin cuce ni Allah ya Isa tsakani na dake,wly bazan taba yafe Miki ba Allah ya isa😭kuka yake kamar karamin yaro,can kuma kamar an tsikare sa ya tashi zurmut key na mota ya Zara ya fita da sauri,Khalid na kwala Masa Kira anma Ina Yama car key har ya fice daga harabar filin ma'aikatar, Khalid ma a rude yace "Ina key din motar ki ,basa tayi Dan jikin ta yayi sanyi amsar key din yayi yaja hanun ta suka fito suma,shi ya tuka motar ya Mara ma Ansar baya,Ansar sosai yake zabga uban gudu bisa titi
Bai tsaya ko Ina ba sai gidan su Sam baby Yana zuwa ko motar Bai sanya a acikin gidan ba ya fito,buga k'ofar yayi Mai gadi ya bud'e kamar zarare da gudu ya shiga gidan,salama yayi Aï dake falo ita kadai ,sauran suna d'aki ,ita tana zaune tayi tagumi,ji tayi mutum ya Fado bisa kanta,ya rungume ta kam,kuka ne yake gadan gadan kamar ba namiji ba,cewa yake"Aïsha Dan Allah ki yafe min wly shairin shaidan ne,duk Abinda nace dake wly ba har cikin zuciya bane,Dan Allah ki yafe min,kuma ni Ansar ayau Ina Mai shaida Miki na maida ke d'akin ki,daidai shigowar Khalid da Sam baby,dasu zaky baby,duk sunji wanan kalaman nasa,Ido ya daga ya kale su yace "ku shaida ni Ansar na maida matata Aishatou."

Wata irin zabura Aï tayi tare da ture sa ,ta tashi tsaye cikin bala'i tace "ka sani wly Ansar ko Kaine Dan Autan maza na barka har abada,Mai za'ayi da Miji irin ka ,Wanda baisan darajar iyalan sa ba,Mai baza sirin sa a titi,wly ni ka fice min a rai ,ka sani ni ban maidu ba,sanan Ina Gama idda zanyi aure na eheeee."

Wani irin zabura shima yayi Yana aika mata da wani irin kalo Mai cik'e da tsantsar tashin hankali,ya nuna ta da yatsa yace"wly ko sama da kasa zata hade Babu Ubanda ya Isa ya shiga gona ta,sasauta murya yayi ya gurfana a kasa,ya rike gwiwoyin ta yace"na roke ki da girman Allah Dan hasken Alkur'ani,dan Allah ki yafe min,ki dawo gida na mu zauna na Miki Alkawarin rike ki amana,bazan taba barin kiyi kuka ba,."

Murmushin takaici Aï tayi tace dadi na da gobe saurin zuwa karka manta a baya ka yaudare ni da kalaman ka ,anma a yanzu wly baka Isa ka yaudare ni ba,da mugayen kalaman ka ba,wly Ansar a yanzu haka ganin ka da nake a gaba na ji nake kamar na shake ka,na tsane ka tsana mafi muni,karka manta me zakayi da mazinaciya ,Yar iskar ,marar gata,marar dangi,kaga ai kafi k'arfin ta,ni da zaka taimaka ka Ida sa min sakin biyun da naji dadi,Dan da inyi rayuw dakai a yanzu na kwamace na Kare rayuwa ta ba aure,I hate you I hate you Ansar,tana Gama fadar haka ta ruga da gudu ta shige kuryar d'aki, shiko Ansar tarin sa ne ya tashi dandanan ya rike baki,sai ga jini,Yana zubowa,take kansa ya fara juya Masa jiri ya fara dibar sa,take ya fara ganin duhu duhu,anan take ya Fadi gurin ,Jin sa ganin sa suka d'auke lokaci guda,ya Fadi a gurin tamkar gawa ,Hankulan su a tashe sukayo kan sa......

Aci gaba da gashi 🍇
Maimou love😘
[06/07 à 15:02] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞
💞💞💞💞
💞💞💞
💞💞
💞

*💖SO NE SILAR FARUWAN*💖
*💖HAKAN*💖

*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋

*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻
*(We are the Best writers among all writers*)📚

*PAGE 93-94*
Chapter 34 · 0% Book details