← Book details So Ne Silar Faruwan Hakan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 43

Sashe 3

So Ne Silar Faruwan Hakan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saida Tayi mata ruwa uku, tukon tasa Ai ta gyara kanta, ita kuma zainabu taje gidan ta ta hado mata shayi mai zafi da kayan kamshi, sai Dan sauran biredi, tana zuwa Aï har ta sake kaya tayi sallah à zaune, bakin k'ofa Zainabu ta zauna ta zabga uban tagumi tana tausayin halin da yarinyar ta shiga da jarabawa kala kala, wane marar tausayin ne.

Shashekar kukan Aï shi ya dawo da Zainabu daga dogon tunanin da ta afka, zuwa tayi ta rungume ta tana bata hakuri.

Shikenan Anty Ni tawa rayuwar haka zata kare yanzu banida madafa, banida sauran gata, na rasa kowa nawa, har budurcin nawa ma saida aka raba ni dashi, nikam yanzu Rayuwa ta ba sauran farin ciki, wayo kulu kizo kiga yanda akaci mutuncin Aïn ki, na tabata da kina duniya ba'a isa ayimin hakan ba."

Gaba-daya ta rikice sai sabatu take , Zainabu tayi ta lalaba ta tana bata hakuri d'akyar tayi shiru tasha Shayin .Zainabu tace "Aï zaman ki nan hatsari ne kina ya mace gashi unguwar kowa yaki d'aukan ki, mu kanmu munso rike ki to anma bazaiyu ba domin d'aki guda ne damu, mai zai hana ki koma k'asar ku wajen dangin ku".

Cikin shashekar kuka Aï tace "wly nidai nasan à Niger suke anma bansan garin da suke ba, kulum Kulu nacewa zata fadamin suna garin da inda dangi n'a suke sai na hana ta fada nace ta bari ai da ita zamu watarana Dan haka fadar batada amfani, sau biyu naji tace iyaye n'a sun tafi dani tun ina shekara daya da kuma lokacin da nake da shekar biyu, tun daga shi da wayo na dai basu taba tafiya dani ba "

Kuka ne taci gaba dayi d'akyar Zainabu ta lalaba ta.

Sati daya Zainabu ke kula da Aï har ta
Samu sauki ànma har yau tana kukan bakin cikin rashin budurcin ta da taci buri akan sa.

À wanan lokacin ne aka aiko ma.

Zainabu cewar mahaifiyar sa dake suleja ba lfy, hankali Zainab à tashe taje tayi ma Aï Salama ta shiga mota ta tafi.

Kamar jiran tafiyar ta ake mai hayar gidan su Aï yazo Da maza yasa à fido duk kayan dake gidan su Aï haka ko akayi akayi ta fido tsuma ana zubdawa k'ofar gida, Aï da gudu tazo ta kama k'afar mai gidan tana basa hakuri anma ina, cewa ma yayi "ke yarinya ki kama gaban ki Dan bazan barki ba ai na ma yi hakuri yau wata daya Kenan da kudin hayar ku ya kare n'a mayi kokari, kai ku fido sauran kayan ku rufe min gida ni inada abin yi. "

Ba yanda Aï ta iya sai zuba ma sarautar Allah ido à haka suka gama fido komai suka kule gidan, mutanen unguwa nata basa hakuri ko kalon su baiyi ba yayi tafiyar sa.

Nan Aï ta duke tana kuka ,yayin da yan unguwa keta bata hakuri.

Haka ta d'auki kayan jiki da photos kulu da iyayen ta da suka d'auka ranar sallah ta saida wasu kayan ta bada saura tana kuka haka tabar unguwar kowa n'a tausaya mata anma basuda halin d'aukan ta dan suma basuda shi .

Aï haka tayita tafiya tana kuka yanzu shikenan batada sauran gata, shikenan rayuwar ta ta lalace an raba ta da budurcin ta.

À haka taje bakin titi wajen wata mai abinci ,Alhazai da yan gayu ke sayen abincin, ga yan mata nan da masu wanke wanke da masu zubawa, nan Aï ta zauna har hajiyar nan ta gama saida abincin ta, à hankali Aï taje ta mata salama ta amsa ,koda taje tace "Dan Allah hajiya ki taimake ni ko wanke wanke na dinga miki, nidai na samu wurin kwona da cin abinci. "

Hajiyar ta gama kalon Àï sama da kasa tace "yarinya yi hakuri ba irinku nake so à aiki ba ."

Ba irin rokon da Aï bata mata ba anma sam matar taki.

Haka Aï tabar wurin ta tafi, dare ya fara Aï bata san Inda zata je ba, haka tayita yawo har k'arfe goma n'a dare, wasu yan mata ta hango tsaitsaye bakin titi ,ba kayan arziki à jikin su ,karasawa tayi taji dayar mai kayan arziki tunda ita riga da wondo har kasa ne gareta tace "haba zaky Baby mufa munfi k'arfin mu fito mu tsaya nan saboda ko cikin karuwan mu daban ne, ai saide azo a same mu a gida, karki manta fa saboda hakan gidan mu daban ne mai tsari dakyau, Anma yau daya Dan ki bata ma Alhaji ki fito waje gaskiya ba girman ki bane, nidai nasan ba kudi kika fito nema ba tunda kinada sama da millions goma à accaunt Din ki ,,dan Allah kawa kizo mu koma gida. "

A hankali Aï tayi salama gurin su wani kalo suka mata daga sama har kasa sanan sukace..........

Aci gaba da gashi🍇
Maimou Love😘

💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞
💞💞💞💞
💞💞💞
💞💞
💞

*💖SO NE SILAR* *FARUWAN*💖
*💖HAKAN*💖

*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

```18decembre 2018,
60ème Anniversaire De la proclamation de la République du Niger```

_Yan Niger barkan mu da Sallah_

*PAGE 7-8*

"lfy dai malama ?
Dayar ce mai magana mai suna Samira suna ce mata Sam baby tace "kinyi shiru muna tambayar ki ?

Cikin rawar murya Aï kamar zatayi kuka tace "dan Allah yan uwa ku taimaka min wly à yanzu banida kowa duk iyaye n'a sun rasu, sai nida kaka ta itama ta rasu gidan da nake ciki na haya ne yau mai gidan ya kore ni wly tun safe nake tafiya na rasa Wurin barci, dan Allah ku taimaki rayuwa ta."

Dayar ce mai suna Zakiya suna ce mata zaky Baby, tace "ya sunan ki ?

À hankali Aï tace sunana "Aï"

Wani kalo suka ma juna suka bushe da dariya sukace "Aï. Ay ba suna bane, meye sunan ki na gaskiya ?

"Sunana Aisha"

"Nice Name"

Cewar Sam Baby .

'D'auko kayan ki muje' cewar zaky

Sami ko murmushin dadi tayi tunda yar uwar ta bazata zubda musu ajin su ba, tayi murna da zuwan Aï ko banza ai ta zama silar hana Zaky tafiya.

À wata mota mai kyau baka suka nufa, Sambaby ke Jan motar yayin d'à zaky ta zauna wajen mai zaman banza, Aï kuma ta zauna gidan baya. Tayi tsuru tsuru tana tunanin halin Rayuwa tabas duniyar nan sai kana da shi akeyi dakai in bakada shi kai ba kowa bane itakam zata shiga duniya, me take takama dashi yanzu budurci ne kuma an raba ta dashi 😭.

À haka tana hawaye sukazo daidai wani gida madaidaici mai matukar kyau.

Gidan ya hadu sosai, gidan b'angare biyu ne daya b'angaren wasu masu zaman kansu ke zaune suma yan mata yyin da suke gasa da su sam baby.

Mai gadi ya bud'e musu suka shiga gidan wajen motoci b'angaren su Sam Baby mota biyu Ce gami da ta sam baby uku ce, sam n'a paka mota duka suka fito Aï sakin baki tayi tana kalon tsaruwar Gidan, sakin baki da hanci tayi tana kare ma gidan kalo ,Zaky ce ta janyo ta suka shige cikin falon .waw falon kansa yayi matukar haduwa ba karya, kujeru ne na alfarma masu kyau saiti daya, sai labulaye masu matukar kyau da tsada, b'angare daya katuwar plasma ma ce TV ta bango sai mayan photon su ,su uku, sai katon karpet da aka shimfida mai kyau na alfarma.

Wata matashiya budurwa ce mai kyau zaune bisa daya daga cik'in kujerun sanye da kananan kaya fara ce tana dana waya, domin kaf din su daga Sam baby har Zaky duk farare ne .

Ta zaunen ce ta daga kai ta kali zaky tace "au hajiya an dawo kenan nawa aka taya ko ba'ayi kasuwa ba"😂

Harara Zaky ta zabga ma ta zaunan tace "wly Kam baby ki kiyaye ni fa mtsss ."

Dariya dai ta zaunan ta kara kecewa da ita ,sai lokacin idanun ta suka sauka kan Àï da take tsaye ta cukwuikuye jakar ta sai piki piki take da idanu yatsine fuska Kam Baby tayi sanan tace" wanan fa ta nuna Aï.

Murmushi Sam tayi tace "zaki sani yanzu .

Tashi tayi ta ta kawo ma Aï kaza taci ta koshi sanan tasha juis.

Bayan ta gama Sam tace "muna so muji tarihin ki."

Take idanun Aï ya fara ruwa nan ta basu duk labarin ta harda Son da take ma ansar da cin mutuncin da ya mata da fyade da aka mata hakika sunyi matukar tausaya mata ba kadan ba .

Zaky ta share kwola tace à yau tsakanin mu ba boye boye dole kowa ya fadi asalin tarihin sa ..

Da farko dai kamar yanda kuka sani ni sunana Zakiya, ni haifafiyar yar Niger Ce ,mahaifiya ta su biyu ne ga baban mu ,mahaifiya ta itace uwar gida, à lokacin suna zaman lfy da mijin ta kafin kawar ta salima tazo taci amana ta shiga tsakanin mahaifiya ta da mahaifi n'a kulum cikin muzguna ma mahaifiya ta yake ita kuma mai hakuri ce bata cewa komai sai addou'a à haka har ya auro Salima kawar ta, shigowar ta gidan ta kara hura wutar tsana tsakanin mahaifina da mahaifiya ta, à haka ne aka samu ciki na wanan cikin yasa Salima ta kara hasala ba yanda bata yi ba ta zubda cikin Allah baiyi ba, à cikin kangin bautar gidan mu mahaifiya ta ta haife ni, akoi wata tsohuwa yar uwar mama ta ita tazo tana mata wanka jego tun ina jaririya ta Salima kemin matsi da atargu, saide aga inata kuka à rasa dalili, kai har zaman yayanka ni da reza matar nan tayi ba imani, ko kuma ta azani bakin gado mai rumfa ta matso dani in ta faki idanun mutane in fada.
Chapter 3 · 0% Book details