← Book details So Ne Silar Faruwan Hakan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 43

Sashe 32

So Ne Silar Faruwan Hakan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kodama tun farko abinda ka same sa a banza ko ya bace bazakaji zafin batan sa ba, tunda ba Kai ka saye sa da kudin ka ba,anma da ace kai ka saye sa, kuma kafin ka same sa kasha wuyar neman sa,zaka samu ma'adani ne ka Adana sa bazaka taba saken dazai bace maka ba."

_Tabas ni Maimouna na gaskata maganar Sam baby,domin duk namijin da zai takarkare ya zuba maki rashin mutunci son ransa,ba tare da mace ta dau mataki ba,wly baisan darajar ta ba,sanan itama Bata San ciwon kanta ba,Dan da ta sani zata nuna Masa kuskuren sa ,Wanda gobe ko ya tashi Yi ya tuno sai gaban sa ya fadi,anma namiji ya zauna ya shuka Miki rashin mutunci wata harda zagin iyayen ta,wai kuma daga anyi Yan awani in ya sauko ki zauna kina washe Masa Baki kina dariya,Ina zaisan ciwon ki bare yasan darajar ki ,tunda ke Baki San ciwon kanki ba ,bare kisan darajar ki hum Allah sa mudace_

To wly Bari kuji ko ku yarda ko karku yarda ni a yau kunga wanan zuwan da Aïsh tayi bazata koma ba,kuma yanzu Zan je na d'auko kayan ta."

Tashi tayi ta zuri key ta fita daga falon Rai a bace,ta hau motar ta tabar gidan.

Sunsan ko sun tsayar da ita bazata tsaya ba,Dan sunsan halin ta in ta hasala ba Mai iya shawo kanta ,

Ita kanta Aï gidan nasa dama ya fice mata a Rai,kuma hakan da Sam baby tayi taji dadi,Dan ko ba komai tasan yau tanada gata.

Hakuri sukayita bata,ita ko Sam baby na zuwa security basu Hana ta shiga ba Dan sansan ta,sanan ogan su yace in sunzo a dinga barin su shigowa.

Shiga tayi zata huce d'akin Aï maganar da taji sama sama ce taji tana son sanin me ake fadan,a hankali har ta Isa falon Hanisa,suna zaune suna fira ita da safiya,labulan ta Dan bud'e yanda baza'a ganta ba,abinda suke fada ne yayi matukar Bata mamaki,waya ta d'auko ta fara d'aukan su videos
Safiya tace"ni wly naso ma ace yaron Nan ya kusanci kishiyar ki ,Kinga da sai mu d'auki videos shaida Mai k'arfi,tunda Kinga ba'a hankalin ta take ba,mun Bata maganin barcin da komai za'ayi da ita bazata taba sani ba,anma Kika ce Kar ayi haka,yanzu gashinan duk da yaga hotunan ya sake ta ,anma keda kanki kince yana wasi-wasi,wly da mun Bari anyi sex da ita da shida kansa zai jefar da ita waje,anma kinga gashinan,yau ko gobe sai kinji ya maida ta."

Cik'in hargagowa Hanisa tace"wly Bai Isa ba ,yanda nasa ya sake ta Nan da makircin da na hada mata,to Koda boka da malam sai nasa ya mata korar kare.,Dan ba zaiyu ace aikin da mukasha wuyar sa ba ya tafi a banza ba.
Ace duk wanan tugun da muka hada mata ya tashi abanza ."
Safiya ta dafa ta tana murmushin mugunta,tace "karki damu ai ko wanan baiyi ba inada wani malami sai muje gunsa Kinga shikenan sai mu Kara sa Masa tsanar ta,yanda shida kansa zai Kara mata saki biyun Kinga uku kenan ."

Shewa sukayi suka tafa,Hanisa tace"madala da kawa ta gari badan ke ba da ban San halin da Zan shiga ba,badan ke ba da Sam ban kawo tunanin na kula ma kishiya ta makircin zina ba, gaskiya ke shu'uma ce.
Murmushi Sam baby tayi na gefan Baki lokacin da ta Gama video tsab,tayi Saving din video ta aje.
Wani sanyi ya ziyarci Zuciyar ta tace Alhamdulillah .

Hankali kwance ta tatare duk wasu Kaya na Aï , a akwati manya uku,ta zube kudi kusan millions biyu Wanda malakin Aï ne,bayan Wanda ke gare a account.

Fita tayi tasa su a boot ta fita.

Kiran Khalid tayi ta tambaye sa Yana Ina ,yace ga shinan office din Ansar ,tace ga tanan zuwa.

Alhaji Usman tunda ya farka yake faman Kiran kulu,Saida aka Masa alurar barci,yayi awa biyu Yana barci,Yana tashi take duk wani tunanin sa da rayuwar da yayi ta da tun kurciya da yanzu ta fara dawo Masa Saida komai Ya dawo Masa yayi salati ,Yana hawaye.

Doctor da ya shigo da shida doctor din Alhaji Usman Mai dala Wanda tun yana saurayi yake duba sa,Wanda sanadin fitowa daga gidan sa ne accident ya same su,Nan suka shigo Dan tunda aka kawo sa doctor din da aka kawo sa asibitin sa ya duba wayar Alhaji Dan ya Kira Yan uwan sa ya shaida musu,shine sai yaga lambar doctor din an rubuta yaya a jiki sai ya Kira ya sanar dashi a rude yazo asibitin.

Zuwa yayi ya dafa sa yace "Usman ka tashi sanu.

Kalon sa yayi yana hawaye yace"doctor ayau dai na tuna ahali na saide banida tabacin ko suna raye,mu biyu mahaifan mu suka haifa,har suka mutu Yaya ta kulu ita ta d'auke ni tana hidima dani,a lokacin tana budurwa ni kuma Ina secondry School ,, a lokacin shekarun iyayen mu biyu da rasuwa ,Yaya kulu ita ta d'auki nauhi na,tana so na sosai ,ita ke Yar sana'ar ta mu samu abin rufa asiri,da kuma abinda zata biya min Makaranta.

Watarana na tafi school shine a hanya ta ta dawo wa gida a wani lungu wasu masu bakar mota,Wanda nake tunanin masu garkuwa da mutane ne,suna gani na suka fito,suna tambaya ta wani gida shine na juya Ina tunani suka shaka min wani abu, tun a lokacin ban Kara sanin inda kaina yake ba, suka sani a mota, sukayi ta gudu Dani har suka fita Dani daga Niger gaba-daya,Ina tashi Naga muna tafiya a wani daji na kwala wani ihu,na Kama Mai tukin na shako sa ta baya,Ina ihu no su barni su sake ni,shakar da wanan dreba yaji yasa ya saki sitiyarin motar,Nan mukayi accident murfin mota ya bud'e ni na Fado kamar an jefar Dani su kuma suka fada a wani rame wuta ta kama,ni kuma ban fada a Ramin ba,na gangara bisa kwalta na bugu da wani dutse,anan ne wanan bayin Allah larabawa suka same ni ita da mijin ta suka kawo ni asibitin ka."

Aci gaba da gashi🍇
Maimou love😘
[06/07 à 15:01] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞
💞💞💞💞
💞💞💞
💞💞
💞

*💖SO NE SILAR FARUWAN💖*
*💖HAKAN💖*

*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAHI AM💋*

*PAGE 85-86*

Falo Ansar ya dawo yayi tagumi,yashiga zurfin tunani,me Aï take nufi dashi ne?
Ta sani cewar bazai iya juriyar ganinta ba a gidan sa kuma ba aure a tsakanin su.gashi shida ya kamata ace ya tsane ta anma wata wutar sonta ke kara ruruwa a zuciyar sa,dafe Kai yayi jin da yayi yana kara Sara masa kamar zai fado, lumshe idanu yayi ya kwanta saman kujera Mai zaman mutum hudu.

Su Mom Kam nacan ana shan love an jima ba'a hadu ba.

Hanisa kam ganin Ansar ya tafi yasa taja jiki tayi d'aki Dan yanzu tsoron Aï take ,Dan tasan zata iya jibgar ta.

Bayan ta Aï tabi da harara ,tare dajan tsaki tace "munafuka kawai."
Hanisa d'aki ta koma ta Kira Safiya ta fada mata cewar Aï Bata tafi ba fa.

Wani irin kunci Safiya taji yayin da wani turirin bakin ciki da kishi suka taso mata lokaci guda ,danewa tayi dak'yar tace kibari gobe in Allah yakaimu in munje wurin Aiki munyi maganar ,wanan maganar ba ta waya bace."
Kafin Hanisa tayi magana Safiya ta kashe waya,Dan wani irin Hali ta shiga itafa yanzu Allah na gani bayan kudi da take so na Ansar hada shi karan kansa take so,saboda yanda Hanisa ke fadar sa ,cewar jarumi ne bisa gado zai iya Kai awa daya bisa mace ba tare da gajiyawa ba,ga nata da ko minti daya cikake baya yi zai kawo,itako irin Maza kamar su Ansar take so."

Ya salam da auren ta,haba ke kuwa yar uwa mai zai kaiki bayana sirin kwanciyar ki da mijin ki,hakan bai kamata ba koda kuwa ga matar aure kike bayana ma haka,sirrin mijin ki sirin ku ne ke kadai keda mijin ki,idan mijin ki halitar sa ce hakanan in kinga Zaki cutu Zaku iya raba auren Allah ya hada kowa da daidai shi,karki yarda ki jefa kanki wata hanya,idan kuma ba halitar sa bace sai ku tashi ku Nemi magani.bawai kina hangen mijin wata ba da auren ki,ko kiyi tunanin shiga wata hanya daban da ta saba ma mahalacin ki,diyawa yanzu matsalar da mata ke fuskanta daga mazajen su kenan,anma sun kasa tashi neman magani,saima tunanin bin wasu mazan daban Wanda ba nasu ba , ko kaji ance inason miji na bazan iya rabuwa dashi ba,to kinason mijinki tsaya Nan so yakai ki mahalaka.
Allah sa mudace.

Hanisa kam bakin ciki ke nukurkusar ta dan haka ta hada kwayoyin samun barci ta kwanta,Babu tunanin yima mijin abinci,dama kuma ba dabi'a ta bace.

Aï kicin ta shiga ta hada lafiyayan abincin ta,tuwan shinkafa da miyar danyan kubewa da Tasha Naman rago,da man shanu,ta hada juis na cita,taje tayi wankan ta ,tashirya,cikin doguwar riga ta barci ba mai nauhi ba,anma ta kama ta,kusan ma surar ta Ana gani ,komai na jikin ta yaji ,duk namiji lafiyaye yagan ta sai yaji wani Abu ya tsirga mishi,Bata sa pant ba bare bra. Bata sa dankwali ba sai wani ni'imtacen kamshi dake tashi akowane lungu da Sako na jikin ta . haka tazo falo ta zauna ta kuna TV ta tashi ta zuzubo abincin ta dama bakin iya cinta tayi sai kamshi yake ,ta zubo juis,zama tayi ta fara ci ko kadan kamar ba wata damuwa a cikin ranta,anma kuma kasan zuciyar ta ita kadai tasan mai take ji game da makircin da aka hada mata,har yayi sanadiyar sakin da aka mata.
Ansar da yaga har anyi Kiran Sallah magariba iyayen sa basu fito ba ,ya tafi masalaci har Isha can yayi kawai ya huce gidan sa.
Chapter 32 · 0% Book details