← Book details Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 65

Sashe 9

Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

D'aukar handbag d'inta tayi had'i da gyara mayafinta kafin suka fito a jere.. Cikin zuciyarta tsantsan tsanar Maryama da uwarta ne zalla, tun yanzu gwara ta soma tunanin ways d'in da zatabi ta rabu dasu, musamman data tuna yanda yaran AT ke son uwar yarinyar, sannan ita kanta Sajida tana tsananin son yarinyar.... Kai dole ma yau taje d'aukan su makaranta don ta kuma ganin yarinyar sosai, tabbas ta ganta lokacin rasuwar Aysha amma sam tama mance kamannin ta, ko banza she feels at ease, don dai wannan yarinyar ne ai batada mastala, ta zaci wata babbar mace ce mai aji irinta Hisham ya gansu da AT d'inta... Da wannan tunanin ta isa jikin motar ta k'irar Accord...

****************

Da gudu Sajida ta k'araso ta rungume ta tana dariya take fad'in "Maryama don Allah kiyi hak'uri, wllhi Aunty Shemah ce ta kawo mu, sai surutu muke a motar shaff na mance da ke, sorry pls."

Harara Maryama ta galla mata kafin tace "Da nayi missing exams ai bakida damuwa."

Dariya Sajida tayi had'i da janyo kafad'an Maryama suka nufi bakin hall d'in tana fad'in "Ai da bakizo ba ma bazan shiga ba nima saidai nayi missing.." Da haka suka k'arasa don already an soma shiga.

*************

Zaune take cikin motar ta sai faman hangen ta ina su Sajida zasu fito take, burinta bai wuce taga Maryama ba.

Can ta hangesu suna tahowa itada Sajida, sai yanzu ta samu ta k'are ma yarinyar kallo. Chocolate ne in colour, don kai tsaye baza'a kirata bak'a ba sannan sam bata a layin farare. Shakka babu dukda uniform ne a jikinta zaka fahimci Allah Ya mata diri mai kyau, bata faye tsawo ba sannan ita ba gajeriya bace, irin mutanen nan ne da bature ke kira average, batada wani tsananin kyau sai manyan idanu da d'an k'aramin lips d'inta, sannan koda murmushi tayi kumatun ta suka d'an lotsa, wannan shine iyaka qualities d'in da Shema'u ta hango tattare da ita.... Wani murmushi ta saki don kuwa wannan ai ko makaho ya shafa yasan bata dace da AT ba, aima ruwa ba sa'an kwando bane, Babban goro sai magogin k'arfe, bayan k'aracin shekaru akwai rashin wayewa a tattare da ita, AT da ita ya dace, yanda yasha boko ya k'oshi ma bazai tsaya soyayya da k'aramar yarinya 'yar cikin sa irin wannan yarinyar ba. Dama bata tsaya damun kanta ba idan dai don wannan yarinyar ce. Abu guda da zatayi kawai shine ta dasa ma Sajida tsanar ta cikin ranta..... Muryar Sajida ce ya katse ta sanda suka k'araso tana fad'in "Oyoyo Sweet Aunt, ashe har kin iso."

Shema'u ta bud'e marfin mota ta tafi tayi hugging Sajida tana gogge mata fuska da hanki kafin tace "Na iso tunkan ku tashi My Sajee, kinsan I don't wanna keep you waiting, sabida banso ki wahala, yaya exams, me kike son ci..?" Ta k'arashe tana wani ware idanu tana sakar ma Sajida sassanyar murmushi.

Maryama dai jinin jikinta tasha, don harga Allah itakam sosai Aunty Shema'u ke bata tsoro, bata san dalilin hakan ba..... Tana cikin tunanin ta jiyo muryar Sajida tana fad'in "Maryama ga Aunty Shemah baku gaisa ba."

D'an murmushi Maryama tayi kafin ta rusuna ta gaida Shema'u. Da sakin fuska Shema'u ta amsa mata hannun ta still rik'e cikin na Sajida kafin tace "Okay girls mujen ku koh.." A sanyaye Maryama dai ta nufi backseat yayinda Sajida ta nufi front seat sai faman murna take tana fad'in "Wllhi Aunty don kece da tada Daddy ne sam sai ya mance damu, ina sonki Aunty yanda kike son mu...

Shema'u murmushi kawai take tana driving kafin tace "Sweetheart anything for you, you and your siblings are my top priority... Faranta maku ya fiye min komai.." ta k'arashe maganar tana satan kallon Maryama datayi jigum a bayan mota ta cikin mirror.

Kashe AC d'in motar Shema'u tayi tana tara miyau a baki kafin tace "Baby ya sunan k'awar taki ma.?"

Sajida tace "Maryama Aunty. Baki ganeta bane, gidan Hajiya fah take."

Shema'u ta zubar da yawun bakinta kafin tace "Oh na ganeta, itace d'iyar Nannyn su Jamal koh, sannu Maryama, amma dai kina sure da body spray koh, kinsan fah kun zama 'yammata, idan baku kiyayewa wari zaku keyi duk yanda kuka shiga. Nasan My Sajee bata wasa da kayan k'amshi, kike k'ok'ari kina amfani da kayan k'amshi kinji Maryama, yanzu kiji yanda gaba d'aya motar nan ta hamame sabida shigowar ki... So nake ki gyara shiyasa na fad'a maki kinji."

Ba Maryama kawai ba harta Sajida saida taji babu dad'i abinda Aunty Shemah tayi, ta yaya zatace Maryama tana wari, bayan tsafta irinta Maryama, kai duk yayen d'alibai ma da akeyi ita take karb'an wacce tafi kowa tsafta... Kuma itakam sam bata tab'a jin wari a jikin Maryama ba tsawon shekarun da sukayi a tare.

Iya k'uluwa Maryama ta k'ulu, tsanar matan ya kuma shiga ranta, itace mai wari... A duniya babu abinda ta tsana irin wari, amma shine yau har ita akece ma me wari, tana son mutum d'an gaye, amma Sam banda Aunty Shema'u dukda gayu da take ji dashi..... Sajida ta d'an lek'o tana duban ta zatayi magana Shema'u tayi saurin fad'in "Me kuke son ci, ko a biya daku eatery ne, Maryama ko bakujin yunwa ne..?" Ta d'an juyo tana duban Maryama datayi zaune kurum cikin motar kafin tace "I hope dai ba abinda na fad'i bane ya b'ata ranki, kiyi hak'uri ni na d'auke ki ne kaman Sajida, duk abinda na gani na gyara zan maku both ke and Sajida tunda ku d'in tamkar sisters kuke, right my Sajee.?" ta k'arashe tana duban Sajida. Haba nan fah Sajida ta kuma jin dad'i ta kuma yarda lallai Aunty Shemah tana son su da gaske, tunda gashi soyayyar ta shafi har mutanen da suke so.

Murmushin yak'e kawai Maryama tayi wanda hausawa ke cema tafi kuka ciwo, Alla Alla take ta isa gida ta tambayi Hajiyar ta ko da gaske tana wari.

Marayama suka soma ajiyewa, tai masu sallama kafin ta fice ta nufi gate, a daidai k'ofa suka had'u da Buzu, nan suka tsaya suna magana...

Sajida tayi saurin rik'e hannun Shema'u dake saman steering wheel tace "Wayyo Aunty don Allah d'an tsaya.. " Ta k'arashe maganar tana kallon Buzu had'i da sakin sassayanyar murmushi, shiko sai magana yake da Maryama da alama cikin raha suke zancen.

Shema'u ta kafe Sajida da idanu tana karantar ta yanda take kallon Buzu kafin ta saki wata murmushi tace "Baby shi kuma wancan d'in waye. Your crush I guess?"

Murmushi Sajida tayi had'i da rufe fuska alamun jin kunya.

Shema'u ta murmusa sanda taci gaba da driving kafin tace "Sajee tsakanina dake babu wani kunya, ina so ki zama very free da ni, mu zama tamkar k'awaye, ki dinga fad'a min damuwar ki sabida bakida mahaifiyar data fini a yanzu, sannan yanzu ne kike buk'atar Uwa da zata guiding naki, tunda kin soma girma Sweery."

*Sameena Aleeyou Mrs*
[2:54PM, 3/4/2018] 鈥�+234 703 300 1537鈥�: 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊

*SHAK'UWA CE*

馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊

*08*

*漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�*

*_馃寛KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 馃_*

"My Sajee ina sauraren ki, go ahead fad'a min abinda ke ranki, nai maki alk'awarin I'll support a duk abubuwan da kike so, irin support d'in da uwa zata bawa d'iyarta, sabida bakida wacce ta fini." Shema'u ta fad'i sanda suke hawa babban kwalta.

D'an muskutawa Sajida tayi cike da jin k'arfin gwiwar fayyace ma Shama'u abinda ke zuciyar ta kafin ta soma fad'in "Aunty I'll be honest with you, ina fatan ki fahimce ni pls."

Shema'u ta murmusa had'i da gyad'a kai kafin tace "Ina sauraren ki daughter, don't hesitate pls kinji, kar ji d'ar d'in fad'a min ko meye, mother's daughter's talk muke yanzu so kar ki b'oye min komai, I promise to guide you to the right path insha Allah." ta k'arashe maganar in a serious tune, sai ka rantse iyakacin gaskiyarta kenan.

"Aunty,... Magana ta gaskiya ban tab'a son wani namiji ba kaman yanda nake son Buzu, tun lokacin dana soma ganin sa Allah Ya jarabce ni da son shi Aunty bansan yaya zanyi ya gane irin soyayyar da nake masa ba, farkon dawowar su unguwar Hajiya sam Maryama bata shiri dashi, idan ya mata magana ma bata amsawa, ni ce dai na dinga rok'onta kan ta bari ko gaisawa suna yi tunda kowa a layin yasan kirkin sa da son mutanen sa, da k'yar Maryama ta amince mun suka soma mutunci da Buzu har gidan Hajiya yanzu yana zuwa, sun saba sosai."

Shemah tayi murmushi kafin tace "Oh kice Baby na ta iya soyayya.?" Sajida ta d'an rufe fuskar ta.

Shemah ta kuma murmusawa kafin tace "Don't be shy, that's natural dear, at your age zaki sami first love d'inki dama, and ya tabbata Buzu shine masoyin ki. Amma meyasa ake ce masa Buzu, bashida asalin suna ne.?"

Girgiza kai Sajida tayi fuskarta cike da murmushi kafin tace "No Aunty sunan sa Haris, wllhi Maryama ce dai tasa masa Buzu sabida yana kiranta 'Yar Kunama, toh yanzu Buzu ya bisa, idanma kika shigo layin nan wani sa'in idan bakice Buzu ba baza'a gane ba,... Amma ai yaci sunan sa Buzu ko Aunty, kin gansa fari k'al kaman balarabe."

Shema'u tayi murmushi kafin tace "Aah gaskiya yaci sunan sa Buzu, sannan shida d'iyata would make a perfect couple, dukanku farare kyawawa..."

Wani murmushin jin dad'i Sajida tayi, har ranta taji dad'in furucin Aunty Shemah.... Muryar Shema'u ya katse mata murmushin nata sanda take fad'in "Amma kuwa kin tabbata babu wani abin tsakaninsa da Maryama.?" tayi tambayar idanunta naga kwalta.

D'an jim Sajida tayi tana dubanta kafin tace "SHAK'UWW CE kawai a tsakanin su, sannan Maryama tayi hakan ne sabida ni, don kinsan Daddy bazai bari na fara soyayya yanzu ba, kinsan shi allazi boko, mafarkin sa bai wuce nima na zama Likita kaman shi ba, ko fah waya Android bai bari mun soma rik'ewa ba wai sai mun kammala Waec, kiji fah Aunty, wake yayin haka yanzu...Shiyasa nake so tun yanzu a saba da Buzu harda Hajiya baki d'aya, tunda yanzu na kusan kammala WAEC d'ina ai zai cika alk'awarin sa ya mallaka min waya."
Chapter 9 · 0% Book details