← Book details Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 65

Sashe 61

Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gyad'a masa kai tayi cikin sauri, Haidar yayi saurin tsare mai adaidaita baima san yawan kud'in da ya damk'a ba Maryama ta shige ciki a tsorace... Yayi masu addu'an kariya kafin shima yasa hannu ma d'an acab'a ya d'ale....

*************

Napep d'in su Hajiya tana shigowa layinsu AT ta hangi Sajida sun shige motar Buzu har wani rirrik'eta yake...... Ai a tamanin taceda mai adaidaita "Yaro mubi bayansu, mubi bayansu nace, jikata ce tsinanne zai lahanta min ita..."

Cikin sauri mai adaidaita yace "Toh Baaba an gama, gaskiyarki ne kam gwara ki tsare mutuncin jikar ki, irin wad'an nan gurb'atattun samarukan lalata 'yanmata kawai suke....

Ko zarafin amsa sa Hajiya bata samu ba idanunta k'yam kan motar Buzu yanda yake kwasan gudu da jikarta Sajida cikin motar.....

**********

Da taimakom Allah suka samu wutan ya mutu, AT gaba d'aya fatarsa tayi ja, bak'in hayak'i duk ya rina masa fata... Dole aka kawo masu d'auki daga Teaching Hospital....

Kai tsaye CCTV FOOTAGE na cikin asibitin ya bud'e ya soma dubawa domin shima kansa bai yarda wutan ba kunnata akayi ba, don tafi kama da kunnata akayi... Duk abinda ya faru a asibitin tun daga safiya ya soma gani....

Har isowan Hisham saida ya gani, wani ikon Allah basiran Hisham gaba d'aya ya shafe bai yi hacking cameras d'in ba kodashike sam bai zaci asibitin bazata k'one gaba d'aya ba...

Jiri ya fara neman kada AT ganin Hisham na fito da gallons d'in petur ya nufi cikin Store dasu yana gani ya saka su a last store kafin ya fito parlorn yana fashewa da wata irin dariya.... Tashin wutan saida yayi jifa da Hisham gefe, wutan bata biyo ta parlorn yanda Hisham yake ba sai ta shige cikin asibitin cikin ward d'in majinyata... Hisham kwance a wajen sai k'ok'arin janye rigarsa data rik'e k'arfe yake ya kasa ga hayak'i ya soma gauraye wajen.....

Kasa ci gaba da kallo AT yayi sai hawaye dake kwaranyo masa, yak'i aminta ma zuciyarsa cewa Hisham ya gani, Hisham dai his very own best friend wanda ya zame masa tamkar d'an uwa.....

Cikin wani irin huci yayi jifa da computer d'in, hawaye na bin k'uncinsa ya fito ya nufi store d'in magunguna, su KB na ganinsa ya nufi wajen sukayi saurin take masa baya, sabida sun razana da ganin yanyin nasa...

Yana isa ya daki k'ofar da hannunsa yaji zafi.... Cikin sauri KB da Alonso suka jawo k'arfe suka bugama k'ofar nan ta bud'e... Hango Hisham da sukayi kwance a k'asa yayi mugun d'aga masu hankali, cikin sauri suka k'arasa kansa suna k'ok'arin ceto rayuwar sa...

AT kuwa yana k'arasowa ya finciko Hisham ya kai masa wata wawan naushi a hanci wanda saida yasa sa bud'e idanu babu shiri tamkar d'an maye.. Alonso da KB gefe suka matsa suna kallon ikon Allah, yau Dr AT ne da Dr Hisham a wannan yanyi..

Dukansa AT yake da iya k'arfinsa hawaye na bin k'uncinsa yake fad'in "You Animal I'll kill you, you're despicable wllhi Hisham sai na kashe ka..."

Da k'yar su KB suka janye AT ganin na shirin aika Hisham lahira...

Hisham ya tsuguna saman gwiwoyinsa yana tarin azaba... AT yaci gaba da fad'in "You're unbelievable, Hisham bansan kai meye a gareni ba, duk shekarun nan ashe kanada shirin da kake yi akaina, you're not Human Hisham kai ba d'an adam bane.... You'll rot behind bars and pay for what you did..." Ya k'arashe yana kuma yunk'ura zai capko Hisham...

Mik'ewa Hisham yayi yana layi yana nuna AT da yatsa yake fad'in "You're a coward AT, baka san su waye masu sonka ba bakasan su waye masu k'inka ba, abunda zan fad'a maka sai yafi komai d'aga maka hankali..." yasa hannu ya share jinin da ya gangaro daga bakinsa kafin yace "Aysha ba a had'arin mota ta mutu ba.... She was killed by your wife Shema'u, her very own sister..."

Girgiza kai AT yake yana duban Hisham yake fad'in "You gone insane, baka san me kake fad'a ba, hatred ya cika maka zuciya shiyasa kake magana marassa kan gado...."

Hisham ya fashe da dariya kafin yace "Shema'u ba iyaka abinda tayiba kenan, ta kashe Maama Juu sannan ita ke yunk'urin gurb'ata tarbiyan Sajida and lastly k'anan yaranka rayuwar su na cikin had'ari domin maganar da nake maka a yanzu zata kaisu..... Za'ayi masu fyad'e gaba d'ayansu daga Ni'ima har Jamal, so if I were you I won't waste time here zan tafi ceto rayuwar yarana..."

Bai kai aya ba AT ya kuma kai masa wata wawan naushi yana fad'in "You imbecile I'll kill you...."

Alonso ya dubi KB yace "Buddy let's call the cops let's go..." KB ya gyad'a masa kai suka fice a tamanin...

Hankad'e AT Hisham yayi yana dariya kafin yace "You miserable Coward na fad'a maka sai na karb'i land d'in mahaifina, it's mine... Snann idan kana ganin abinda nake fad'a maka k'arya ne nasan idan ka gani bazaka k'aryata ba...." Daga haka ya zaro wayarsa a aljihu yayi playing videon da Shema'u take k'ok'arin kashe Aysha...

Tamkar gunki haka AT ke bin Video d'in da kallo..... Momma da ahigowar ta wajen kenan itama daskarewa tayi had'i da k'unshe bakinta da duka hannayen ta biyu...

*Saminah Aliyu Mrs💖*
[8:57PM, 4/5/2018] ‪+234 806 652 0501‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘

*SHAK'UWA CE*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*49*

*©Sameena Aleeyou...✍🏼*

_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_

Sosai hankalin Maryama ya tashi sanda ta isa makarantar su Jamal aka sanar da ita cewa Aunt d'insu tazo ta d'aukesu, idanunta sukayi rau-rau lokaci guda bugun zuciyarta ya k'aru... Innalillahi kawai bakinta ke furtawa, gaba d'aya ta birkice ta rasa wanne zatayi.... Wayarta dake hannunta ne yayi k'ara wanda hakan saida ya firgita ta, tana ganin Ashfaq ne tayi saurin d'agawa lokaci guda ta fashe da kuka tana fad'in "Ya Ashfaq basu nan Aunty Shema'u ta d'auke su... Wllhi ta d'aukesu..."

Haidar ya dubi commissioner of police kafin ya girgiza kai yace "Sir sun baro makarantar na tabbata wajen Daddy na suka nufa...." commissioner ya gyad'a kansa kafin ya dubi ASP yayi masa alama da hannu... Sara masa ASP yayi domin tuni ya gane me yake nufi kafin ya wuce cikin sauri..

Wayar Maryama Haidar ya kuma dannawa kafin yace ta jira shi a wajen yana zuwa yanzu.... Commissioner ta wagan sa kuwa tuni sun d'auki hanyar guest house d'in VP..

*********

D'an napep gaba d'aya ya cika Hajiya da surutu ga traffic ya raba tsakanin su dasu Buzu.... Hajiya bata san sanda ta shiga sille sa ba, ita gaba d'aya tama rasa wani hanya suka nufa ga gari ya canza ko ina flyover.... Kaman ance ta kalli gefen hagu nan ta hangi Buzu na shiga wani guest in....

Talle k'eyar mai Napep tayi ta shiga nuna masa motar tana fad'in "Kaga mu shiga gidan karuwan can da ya shiga, maza muje nace idan bakayi sauri ba kuma ka bani..."

Mai napep ya shiga sosa k'eyarsa yanda Hajiya ta talla masa mari yana fad'in "Baaba bafa gidan karuwai bane Hotel ne...."

A harzuk'e Hajiya tace "Uwar otel ne ma, yo me ake a ciki banda bad'ala da b'arna ko kaga masu kamun kai a wajen ne inyi...." ta k'arashe tana huci...

Mai napep dai bai kuma cewa komai ba domin kuwa Hajiya ta zarce tunanin sa, duk son surutun sa dole yayi shiru....

********

Girgiza kai AT yake yana naman zubewa k'asa.... Murya na rawa yake furta "No... no, wannan ba gaskiya bane, No no no.... This can't be happening......" ya k'arashe yana dafe k'irjinsa dake barazanar rabewa.....

Momma kuwa tuni ta zube a k'asa sumammiya.....

AT yayi kan Hisham zai kai masa duka Hisham ya ciro bindiga a bayan wandon sa yayi pointing AT dashi, kan kace me ya harba masa a kafad'anshi yana wata irin kafiran dariya yake nuna AT da bindiga d'in yake fad'in "I've always known you to be a coward, be a man for once AT, ka kalle ka bazaka iya komai ba saidai kallo da ido....." ya kuma fashewa da dariya yana kallon AT dake durk'ushe rik'e da wajen da ya harbesa jini na zuba yana cije baki.. Da k'yar yake fad'in "You're an Animal Hisham.... Wllhi sai ka girbe abinda ka shuka....."

Hisham ya kuma fashewa da dariya ya k'araso yanda AT yake ya kai masa naushi a hanci nan AT ya fad'i k'asa ga zafin bullet ga jini na kan zuba.... Dariya Hisham keyi yana nuna sa da bakin bindiga yake fad'in "Tashi ka rama.... Da zafi koh nasan da ciwo, zan maka kisan gilla bayan na wulak'anta k...... Bai kai aya ba yaji sauk'ar katako a gadon bayansa..... A tare shida AT suka juyo suna dubanta ba kowa bace illa Momma, hawaye na bin k'uncinta tana rik'e da katakon da gani zaka gane k'arfin hali kawai tayi amma tana jin jiki..

Ganin Hisham ya nufi Momma yasa AT yayi ta maza ya mik'e ya kai mai naushi wanda saida yasa Hisham ya fad'i akan fuskar sa.... Duka AT yake masa irin dukan huce takaicin nan.... Bai ko kula da jini dake bin hannunsa ba sai dukan Hisham da yake tamkar an aiko sa, baka ko ganin fuskan Hisham jini ya rufe gaba d'aya... A haka su KB suka iso da polisawa suka taddasu, da k'yar aka k'waci Hisham hannun AT domin kuwa ya kusan aikasa lahira.... Take akayi arresting Hisham 'yansanda

AT bai daina fimcika yana so a barshi ya k'arasa Hisham ba....

KB na rik'e AT yana fad'in "Dr you're bleeding pls ka bari ayi treating naka..."

Girgiza kai kurum AT yayi yana nunawa KB Momma dake durk'ushe a wajen rik'e da k'irjinta sannan yace "KB just take care of her... My children need me... I've to go... Kar ka damu I'll be fine, bazan iya tsayuwa a nan ba alhali rayuwan yarana na cikin had'ari..."

Da k'yar ya k'arasa gaban Momma dake dafe da k'irjinta idanu rufe, jin ta ambato sunansa a hankali..
Chapter 61 · 0% Book details