Sashe 50
Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajiya data cakare cikin wata jan leshi mai duwatsu harda d'aurin ture kaga tsiya tayi, ta murmusa kafin tace "Allah sarki Attahiru nasan nasiha zai maki, shakka babu zaiyi kewarki sosai ni kaina nasan tsan-tsan SHAK'UWA CE a tsakanin ku,..." ta kuma murmusawa tana k'ok'arin maida k'wallanta kana tace "Duk tsiyan da kuka min a baya na yafe ku, b'oye ledar goro na, yau kuce da tsutsa gobe kuce ta rub'e duk don kar naci...." I zuwa lokacin idanun Maryama ma ya soma rau-rau, itama ta tuna wad'ancan lokutan.... Allah sarki Hajiya da Uncle zatayi kewansu domin kuwa ko Umminta bata shak'u da ita ba kaman yanda ta shak'u da Hajiya da Uncle.
Albarka Hajiya ta kuma saka mata, tasa hannu ta goge k'wallan da suka zubo ma Maryama kafin tace "Maza tashi kije ki koh nasan yana jiranki tunda lokacin d'aurin auren ya kusa."
Jiki babu laka ta mik'e ta nufi parlorn bak'i daga Maryama har Hajiya saida suka bawa mutane tausayi...
Tsaye ta hangesa ya bada baya yana fuskantar window, hannayen sa zagaye da bayansa, gabanta yayi wani irin mugun fad'uwa domin kuwa tunda take uncle bai tab'a mata kyau kaman na yau ba, kayan ya amshe sa ga wani golden brown hula zanna bukar da ya zauna akansa tamkar akan nasa aka k'era, kwantattun sumarsa wanda suke gauraye bak'i da furfura kad'an sai dai bak'in yafi yawa sun d'an fito ta bayan hular tasa, gaba d'aya k'amshinsa da k'warjininsa sun cika wajen.
Jikinsa ne ya bata tana wajen, a hankali ya kaikaito yana dubanta, tana sanye cikin leshi kalan hulan kansa wato golden brown da kuma yalwateccen mayafi fari k'al kalan shaddar dake jikinsa, har wani girma ta k'ara masa.
D'an saita kanta tayi had'i da yin sallama kana ta soma shigowa.
K'ak'aro murmushi Tahir yayi yana mai amsa sallamar tata ya k'araso saman Couch ya zauna, abincin da Sajida ta kawo masa ko bud'ewa baiyi ba.
Can k'asan carpet ta zauna kanta a k'asa. Gaidashi ta soma yi cikin sanyin muryar ta yana amsawa fuskar sa d'auke da murmushi, tabbas yau d'in d'iya ko ince k'anwar tasa ta canza masa gaba d'aya, ga wani kyau na musamman da wani daddad'an k'amshi da take.
Shiru ne ya d'an biyo baya kafin AT ya d'an muskuta ya ambato sunanta da irin sigan da ya saba kira.
Saida ta d'an d'ago ta dubesa kafin ta amsa, cikin sauri ta maida nata kan k'asa, itakam sai yanzu ta lura shiga iri guda sukayi da Uncle.
Tahir yaci gaba da fad'in "Tunda aka saka aurenki da Ashfaq ban samu zama munyi magana ba, sabida Hajiya ta tabbatar min kin zab'i Ashfaq d'in a matsayin miji...." ya d'anja fasali kafin yaci gaba "Ina so na kuma tambayarki kafin a d'aura auren, kin tabbata kina son Ashfaq....?"
Bugun zuciyarta ya k'aru, wayyo Allahnta yaya Uncle yake mata tambayar da yasan bazata iya basa amsa ba.
Shiru na wasu dak'ik'ai suka gifta.
Shi kansa mai tambayan k'irjinsa tamkar zata faso ta fito waje haka yakeji, addu'a yake kan faman yi Allah yasa kar ta amsa masa, shirunta sai yafi masa sauk'i akan amsawarta...
Saida ya d'an kuma yin gyaran murya kafin yace "Ko a shari'a shirun budurwa is acceptance.... Masha Allah, Allah yayi maki albarka.... Allah Ya baku zaman lafiya mai d'orewa tareda......" kasa k'arasawa yayi sai d'an murmushi da yayi wanda yafi kama da yak'e kafin yaci gaba da fad'in "Maryam, ki sani koda ace kinyi aure we're still your family, duk wani rashin fahimta ko na cin zarafi ko na wani abu makamancin haka don't hesitate to tell me right away kinji, you can always count on me..... I'll always be there kinji koh...." ya k'arashe cikin rawar murya wanda hakan yasa Maryama ta d'ago tana dubansa, take ta gano sauyawa da idanunsa sukayi...
K'walla ne suka ciko idanunta cikin sauri ta sadda nata idanun k'asa.
Saurin daidaita kansa yayi had'i da d'an fuzar da iska kafin ya soma mata nasiha mai ratsa zuciya wanda ba Maryama kawai ba harta shi AT d'in saida yaji zuciyarsa na neman karaya.....
Ganin tana hawaye yasa sa soma lallashinta yana fad'a mata idan tana so zaisa Ashfaq yake kawota wajen Hajiya kullum ko kuma shi yaje da kansa. _(Ni kuwa Sameena nace, inaga dai AT ya mance Maryama aure zatayi zata zama mallakin wani shiyasa yake fad'in haka... Lol)_
Ita kanta Maryama statement AT d'in saida ya sakata nishad'i, yana kallon yanda take murmushi har cikin ransa yaji dad'i.
Duban abincin gabansa yayi kana yace "Toh Maryamar Hajiya ayi serving Uncle na k'arshe koh..."
Murmushi tayi cikeda kunya kafin ta k'arasa gabansa ta soma bud'e warmers d'in, sai bin zanen lallen hannunta da kallo yake, flowers d'in sunyi kyau sosai, take yaji zuciyarsa na k'una, wai duk wannan lalle domin Ashfaq tayi su... Saurin kawar da kansa gefe yayi don hakan ne yafi masa sauk'i.
Bai k'yaleta ta tafi ba har saida ya d'an ci abincin, Maryama kuwa gaba d'aya ta kasa sakewa dashi.
Wayar da Hisham ya ringa damunsa dashi ne yasa sa dole ya mik'e ba don ya gaji da kallon Maryama ba don yasan daga yau zata zama mallakin wani....
K'ura mata idanu yayi kafin ya fice sannan yace "Zanje na bada aurenki Maryam.."
Kasa ce masa komai tayi sai kallon tausayi data bisa dashi, he's acting strange, gaba d'aya Uncle ya canza mata.... Muryarsa ta jiyo yana fad'in "Bazaki min fatan Alkhairi ba..?"
K'ak'aro murmushin k'arfin hali tayi kana tace "Allah Ya kaika lafia yasa ayi a sa'a..." ta k'arashe kaman zata kurma ihu.
Murmushi ya sakar mata da gefen baki kafin yace "Ameen..." Daga haka ficewa yayi cikin sauri.
Maryama tabi bayansa da kallo lokaci guda da durk'usa saman gwiwoyinta tana kukan da batasan dalili ba.
Shema'u da isowarta kenan taga AT ya fito daga parlorn bak'i ga kuma takalmin mace a wajen, cikin sauri ta nufi parlorn k'irjinta na bugawa da sauri da sauri.
Turus ta tsaya ganin Maryama durk'ushe a wajen na kuka, saida ta bita da wani mugun kallo kafin ta k'arasa ta dafata tana fad'in "Haba Amarya yaufa ranarki ne, kuka bai kamace ki ba."
Jin Muryar Shema'u yasa gaban Maryama ya yanke ya fad'i cak ta had'iyi kukanta, Ji take kaman Aunty Shema'u ta fahimci sabida Mijinta take kuka.
Lallashinta Shema'u ta ringayi tana watsa mata mugun kallo, duk yanda taso Maryama ta fad'a mata abinda ke damunta Maryama ta kasa fad'a mata....
Kallo kawai Shema'u ke binta dashi, Jakar uba!! Ai sai yanzu ta lura AT da Maryama anko sukayi. Wani k'atutu ya tokare mata mak'oshi, ita kad'ai take huci tana watsa ma Maryama kafiran kallo.. Allah sarki Maryama kanma batasan tanayi ba.....
*************
Taro yayi taro, uban gayya kurum ake jira a gabatar da d'aurin aure, Ashfaq dasu Dr Bilya su Dr Nicolas da sauran abokanayen aikin su tuni sun sami hallara.
Ashfaq yayi kyau cikin shigar sa ta angwaye, tunda ya hango AT gabansa ya yanke ya fad'i. Hisham ma kallo yake kan faman bin Tahir d'in dashi yanda yake kan faman gaisawa da Jama'a.
Zama AT yayi bayan sun gama gaisawa dasu liman aka soma k'ok'arin gabatar da abinda ya tarasu....... Kaman daga sama sai jiyo sautin jiniya suke gaba d'aya ya gauraye unguwar tako ta ina... Dama auren a farfajiyan babban masallaci ne, gaba d'aya jama'a aka soma mik'ewa ana hange-hange da kalle-kalle... Gaban Ashfaq yayi wani irin yankewa ya fad'i, suka kalli juna shida Baffah Yawale.... Kafin su sami zarafin magana sai gani sukayi tirk'a-tirk'an motici na alfarma suna shigowa...
Kankace me Mopulawa sun soma durowa daga motocin su suna ba ma uban gidansu tsaro...
Mamaki ya cika mutanen dake wajen ganin mataimakin shugaban k'asa ne sukutum a wajen, wasu a nasu tunanin shima gayyatar sa akayo....
Ashfaq da ya kasa furta komai sai huci da yake ga wani irin gumi dake karyo masa, ya kasa gasgata abinda yake gani, kenan Daddy bazai tab'a k'yalesa ba...
Kallo guda VP ya watsa ma Baffah Yawale wanda dama sam basu shiri kana yace "Ina Haidar....?"
A'a gaba d'aya mutanen wajen sun rasa gane meke faruwa, AT kam ko motsawa daga yanda yake ya kasa...
VP ya cakumo kwalan rigar Baffah yana fad'in "Yawale ka fad'a min ina Haidar...."
Haidar da tuni idanunsa sun kad'a sunyi jazir ya k'araso ya fincike hannun VP 'yansanda suka yunk'ura zasu kai mai duka VP yayi saurin dakatar dasu kafin yasa hannu ya fincike hular Ashfaq nan gashin da yake sakawa a kansa ta zame tabi hular asalin halittar sumarsa ta bayyana...
Murmushi Daddy yayi idanunsa sun kad'a sunyi jazir kafin ya d'auke Ashfaq da wata lafiyayyar mari wanda yasa tuni gashin bakin da yake mak'alawa ta fice ta fad'i k'asa, gemun ma tabita lokaci guda.... Asalin kalan fatarsa ta bayyan sosai....
Mamaki ya cika mutanen dake wajen.
VP yaci gaba da fad'in "Kayi kad'an Haidar, har kana tunanin zaka b'ace min a cikin k'asar nan.... Yau na tabbata zakaji zafin ka tara mutane a kunyata ka kaman yanda kamin a baya..." ya juyo yana duban Baffah Yawale kafin yace "Kai kuma ka saurare ni." Ya dubi 'yansandan sa yace "Ku d'auko min Haidar..."
AT dake tasye idanunsa sun kad'a sunyi jazir k'arasawa yayi ya cakumo babban rigar Ashfaq yana jijjiga sa yake fad'in "Who are you...? Wanene kai? Me kake nema daga wajena....??? Answer meeee!!!!!"
*Sameena Aliyu Mrs*
[8:53PM, 4/5/2018] +234 806 652 0501: 💘💘💘💘💘💘💘💘
*SHAK'UWA CE*
💘💘💘💘💘💘💘💘
*41*
*©Sameena Aleeyou...✍🏼*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*OMG! Just unbelievable, wai dama haka SHAK'UWA CE keda masoya... Hayam just.... Speechless guys❤❤ Allah dai ya bar k'auna, ina sonku gaba d'aya da zuciya guda 💘*
Jijjiga sa AT yake da iya k'arfinsa yana fad'in "Ka amsani nace, tell me who you really are...?"
Yanda yake huci yana fitar da gumi dole mutum yaji tsoro idan yaga yanayinsa...
AT yaci gaba da fad'in "I trusted you.... I even introduced you to my very own Family.... K'arewa na d'auki babban treasure ina yunk'urin damk'a maka amma ka rasa me zaka min sai butulci.... Why! Why!! Just tell me whyyyy...!!!!"