← Book details Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 65

Sashe 3

Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai su Momma suna shigowa wani sabon kuka ya kaure, Maryama ta k'arasa da sauri ta rungume Sajida data koma tamkar gunki ganin mahaifiyar ta kwance saman gado bata numfashi idanunta a rufe ruf ga kuma mahaifin ta rungume da ita yana kuka wanda bata tab'a ganin hakan daga garesa ba... Tuni su Jamal da Ni'ima sun k'arasa wajen suna kuka, cikin sauri Ummi ta d'auke su ta fice dasu...

Da k'yar Hajiya ta janye AT daga jikin matar sa. Su Dr Hisham sai kai komo ake sai ka rantse aminin arziki ne. AT rungume mahaifiyar sa yayi yana kuka sosai yana fad'in" Hajiya Aysha ta tafi.... Ta tafi ta barni... " Hajiya ta matsi k'walla tana rik'e dashi take fad'in" Kayi hak'uri, kayi hak'uri Attahiru, kayita karanto innalillahi kaji....." Momma ta k'arasa kan d'iyarta sanda za'a fita da ita, tana kuka tamkar ranta zai fita... Sam babu wanda yabi takan Shema'u dake kwance d'aya d'akin...

Tana kwance tana tunani taji an tab'a k'ofa... A tamanin tayi saurin sakin jiki irin ta mai jinya ta rufe idanun ta...

Dariya ya kwashe dashi kafin yace " Bud'e idanun ki abinki ba wad'anda kike tunani bane. " Ya k'arashe yana mai zama gefen ta..

Bud'e idanunta tayi kafin ta dubi Dr Hisham tace " Ina AT, yanacan yana kuka akan gawar matar sa koh?"

"Keda kika sani, yana can yana rungume da ita da k'yar aka b'anb'are su, kaman a bisne su tare... " Hisham ya fad'i sanda yake warware drip d'in k'aryar da aka d'aura wa Shema'u.

Shema'u tayi k'wafa kafin tace "Aysha dukda ta mutu wato sunfi sonta, AT da yaranta suna tareda ita, Momma da banida kowa sai ita itama tana can tare da ita,.." tayi wani murmushi mai cike da ma'anoni kafin tace "Yanzu ne zan kafa soyayya ta cikin zukatan ku, one by one sai kun so ni da duka zukatan ku."

Hisham ya murmusa kafin yace "Kar ki damu kinada ni, a hankali ya sauk'o da fuskar sa saitin nata yanai mata wani irin shu'umin kallo, hannu yasa ya janye masu labulan window kafin ya soma kissing d'inta....

*Sameena Aleeyou Mrs*
[2:50PM, 3/4/2018] 鈥�+234 703 300 1537鈥�: 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊

_*SHAK'UWA CE*_

馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊

03

*漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�*

_馃寛KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_

Ganin yanda Hisham ke pulling d'inta ga dukkan alamu ma ya mance a yanda suke. Turesa tayi daga jikinta tana wani irin yamutsa fuska kafin tace "Not here hungry Dr." tayi maganar tana wani murmushi had'i da kad'a masa d'an yatsan ta manuniya saman fuskar sa.

Murmushi Hisham yayi yana mata wani irin mayaudarin kallo, su duka biyun kowa da kalan abinda yake sak'awa cikin ransa.

Hisham ne ya katse shirun da fad'in "A gaskiya my whole life ban tan's ganin maras imani irinki ba, ki kashe 'yar uwanki babu ko d'an tunanin soyayyar dake tsakanin ku.... "

Da sauri ta kaste sa da fad'in "No Dr you're quite mistaken, abinda ke tsakanina da Aysha ba soyayya bace SHAK'UWW CE kurum, difference na shekaru dake tsakanin mu babu yawa, shekara d'aya ne da 'yan watanni, so kaga mun taso tare like twins, tunda muka taso komai tare ake mana, ko ina tare muke zuwa, ga wad'anda basu sani ba sukanyi tunanin mu 'yan biyu ne, harta class d'inmu a makaranta d'aya ne, abu guda da Aysha ta fini dashi shine ci gaba, she was always ahead of me bayan kuma ni ce gaba da ita, I should be the one ahead of her... Aysha was always stealing from me, tundaga wannan lokacin na tsane ta na tsani 'yar uwata. Kaji abinda yasa nace maka ba soyayya bace a tsakanin mu SHAK'UWA CE kawai.." Ta d'an ja fasali kafin taci gaba "Sannan Tahir.." ta murmusa kafin taci gaba "Tahir ni na soma sanin shi, ni na soma had'uwa dashi wani rana sunzo gidanmu da mahaifin sa nayi serving nasu drinks... Koda nazo na sanar da Aysha naga man of my dream sosai ta tayani murna, washi gari da Abban AT ya kuma dawowa Aysha tayi serving nasa, ita bata had'u da AT ba so bata sanshi ba a wancan lokacin. Mahaifin AT ya yaba da hankalin yaran Abbah na musamman Aysha da shike ta k'ware wajen makirci da saye zukatan mutane. Kai tsaye ya nema ma d'ansa Ahmad Tahir auren d'aya daga cikin mu , Abban mu yayi farin ciki da hakan sabida lokacin AT bai jima da dawowa daga India ba ya kammala karatunsa na likitanci. Abba da yazo kai tsaye ma Aysha yayi maganar bayan ni ce gaba da ita , a cewar sa itace bata tara samari kaman ni, sannan tafi nutsuwa da hankali , baison abinda za'azo ana jin kunya tunda yasan halina na rashin jin magana. Ni kuwa a lokacin inaji da k'uruciya ta da tashen kyau tunda nafi Aysha kyau babu had'i.... Aysha ta amince wa buk'atan Abbah ita a dole ga d'iya mai biyayya.... Ka fad'a min Hisham, ta yaya bazan yi burin d'aukan fansa ba... ka fad'a min Hisham.... "

Hisham dai kallon ta kawai yake cike da mamaki. Shema'u taci gaba da fad'in "Tun wancan lokacin na k'udiri niyyan d'aukan fansa akan 'yar uwata." Ta murmusa kafin taci gaba da fad'in "Ina son AT soyayyan da ban tab'a yiwa wani d'an Adam irinsa ba, akan AT ni na kashe Mahaifin mu don ya min sauk'in mallakan abinda nake so, tun daga wancan lokacin zuciyata ta k'ek'ashe ta bushe, sannan banyi aure ba duk a saboda shi, sannan na k'udiri niyyan rabashi da Aysha da 'ya'yan data haifa masa, ban sami chance d'in ba sai yanzu... Sannan nayi alk'awari sai na mallake sa ni kad'ai ba tareda kowa ba, even his children wllhi sai na raba sa dasu, ni kad'ai ya kamata na mallaki AT, dagani sai 'ya'yan da zan haifa masa nan bada jimawa ba.... Sannan nayi rantsuwa who ever crossed my way I'll kill him.... " Ta k'arashe tana wani irin hura hanci tana muzurai da dara daran idanun ta...

Tsoro abin ya bawa Hisham, nan yaga ashe shi k'aramin k'waro ne. Duk wani iskancin sa a bayan Shema'u yake. Ta kashe mahaifin ta da 'yar uwanta na jini duk a sabida namiji.... Nan ya soma tsoron anya Shema'u batada mental case.... Bai gama tunanin ba yaji tana kad'a masa yatsu a fuskar sa...

A firgice ya d'ago yana dubanta. Amma da shike shima wani shak'iyin ne nan ya gwada kaman baiji tsoron abinda tayi ba, saima dariyan da ya fashe dashi ya d'aga mata babban yatsa alamun jinjinawa kafin yace "Bravo, gaskiya na yarda kina son Tahir, anya kuwa zaki bari na d'auki fansa na da na jima ina nema akan sa...?

Mik'ewa tayi sosai tana duban sa kafin tace "Don't even start, don't mess with my man, wllhi idan wani abu ya samu AT zan halak'a ka.."

Hannu yasa ya jawota cikin jikin sa yana wata irin murmushi yake fad'in "Don't be such an idiot, nida ke are team, tare muka soma, and you must help me take back what's rightfully mine from AT..."

Kallon sa Shemah keyi tana k'ok'arin k'wacan kanta daga irin rik'on da ya mata amma ta kasa.. Cike da masifa take fad'in "Me yayi maka da tsanani...?"

Hisham ya murmusa kafin ya soma fad'in "That idiot is always ahead of me, tare mukayi karatu but Ya fini samun nasarori da ci gaba a rayuwa. Nida shi mun zama kaman 'yan uwa, sabida babu wanda bai sanshi a gidanmu ba haka nima babu wanda bai sanni a gidan su ba... Nida Tahir burin mu shine mu gina asibitin kanmu, mu mallaki asibitin kawunan mu. Mahaifi na yanada wani babban fili wanda Tahir yasan cewa banida burin da ya wuce na gina nawa asibitin a wannan filin, shida kansa yana fad'in tabbas wajen zaiyi kyau da asibiti..." Ya d'an ja fasali sanda idanunsa suka kad'a sukayi jazir kafin yaci gaba da fad'in "Mahaifi na ya rasu ban mallaki filin ba, tunda ya rasu fili ta zama na magada.... A lokacin banida kud'in sayan wannan filin, su kuma 'yan uwana sun dage saidai a sayar da fili.... Ganin rikici na neman b'arkewa a family yasa Tahir ya saya filin sabida hankalin kowa ya kwanta... I thought da ya saya zai barmin filin koda aro ne daga baya na biyasa, tunda yasan burina na mallakan filin domin na gina asibiti na.... Kafin na dawo daga Germany yin wani course domin a zahiri ya fini karatu, kwatsam na tarar Tahir sai ginin asibitin sa yake a very same filin. I was quite devastated then, I was like, how could my very own best friend betrayed me kaman haka. He knew yasan yanda nake burin gina asibiti a wann filin, meyasa zai min haka...... Babban abinda yafi bak'anta min rai shine na rasa aiki k'arshe dole nayi joining nasa a nasa asibitin muna aiki tare..... Ever since then, my plan is to ruin him, and you'll be my ally in doing that.... Da ke zanyi amfani wajen cimma buri na, and you've no option than ki bi umarni na, if not... " Ya wani murmusa kafin yace "I'll ruin you too, and I won't back down until I see him on the ground.... I'll take back Sajmal Clinic, I'll take back this very hospital sabida nawa ne, DREAM d'ina ne.... " Ya k'arashe yana mai matse mata fuska yana hura hanci.

Sauk'e ajiyan zuciya tayi cike da tsoro kafin ta ware hannaye tana muzurai take fad'in "Okay okay fine, naji but you've to promise me bazaka tab'a lafiyan sa ba, coz ni ba abin hannun sa nake so ba, shid'in kawai nake so. Zan taimake ka ka mallaki Sajmal, ni kuma zaka taimake ni na mallake sa ni kad'ai...."

Murmushi Hisham ya sakar mata had'i da wani shu'umin kallo. Daidai nan suka jiyo ana tab'a k'ofa.... Cikin sauri ya mik'e yana tab'a drip ita kuwa Shema'u lumshe idanun ta tayi tamkar maras lafiya..

Wata nurse ce ta shigo da wani drip a hannun ta... Ganin Dr Hisham yasata d'an sadda kai kafin ta gaishe sa. Ya wani sha mur kafin yace "Don't you know how to knock.?"
Chapter 3 · 0% Book details