← Book details Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 65

Sashe 63

Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gadon bayansa ta samu wanda yake jazir sai shek'e yake kafin ta sauk'e masa Vase d'in nan lokaci guda ya tale had'i da sake k'aran azaba....

*Saminah Aliyu Mrs💖*
[8:58PM, 4/5/2018] ‪+234 806 652 0501‬: 💘💘💘💘💘💘💘

*SHAK'UWA CE*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*50*

*©Sameena Aleeyou...✍🏼*

_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_

*_FINALE_*

Jikin Sajida har na rawa ta mik'e tana goge hawaye tayi bayan Hajiya data shak'o Buzu da iya k'arfinta tana k'ok'arin ka dashi, bil hakk'i da gaskiya kokawa Hajiya ke shirin yi dashi saida securities suka k'araso suka k'waci Buzu domin kuwa da k'yar idan k'ashin bayansa bai karye ba...

Sai Huci take tana gyara d'aurin kwalinta da zaninta take nuna sa tana fad'in "Kaji jiki munafuki algungumi mai fuska biyu.... Allah Ya tsaremu da mugaye irinka watsetstse kawai.... Ke kuma wuce ki daina mun kuka ai kinga irin abinda nake fad'a maki kink'i yin hankali wauwata da sokanci sun taru sun maki yawa wuce nace...!!!" ta k'arashe tana daka tsawa ma Sajida dake cazgan kuka....

Bata iya tafiya ba sai rungume Hajiya da tayi cikin muryar kuka take fad'in "Hajiya ki yafe min, wllhi na yarda nayi dolanci amma ki yafe min dan Allah duk abinda nayi bada son raina bane kuma na yarda mutum bai wuce k'addaransa, ki yafe min pls Hajiya tah...." Hajiya jikinta yayi sanyi d'an rungumar Sajida itama tayi tausayinta fal zuciyarta kafin tace "Na yafe ki takwarata Allah Ya k'ara tsare min ku....."

Ta dubi Buzu dake nishi da k'yar hannun securities kafin tace "Yan sanda zaku kira min wannan barin su a gari masifah ne...."

D'aya security d'in ya gyad'a kai kafin yace "K'warai Hajiya already ma suna nan tafe amma wannan kin illatasa sai an kaisa asibiti....."

Hajiya ta tab'e baki kana tace "Sakamakon irinsu kenan nidai bana barin nan sai naga 'yansanda sun kame sa....." Bata kai aya ba wayarta ya shiga ruri tana dubawa taga bak'uwar lamba abinda aka fad'a mata a wayar shi yayi mugun d'aga mata hankali.... Cikin sauri ta shiga janyo hannun Sajida suka fice hawaye na gangaro mata take fad'in "Sajida Mahaifin ki, mahaifinki ne muje.... Muje kar mu rasa shi..."

Sajida na kuka take girgiza kai tana fad'in "Hajiya Aunty Shema'u fuska biyu gareta ki fad'a min me tayi wa Mahaifina... Ina Daddy na...?"

Hajiya sam bata sami zarafin amsata ba sai janyota data ci gaba da yi suka fito suka sami mai adaidaitan su nan ta umarce sa ya wuce dasu Sajmal Hospital....

********

Kuka Haidar keyi shar-shar da hawaye sanda aka zura hannayen Daddyn sa cikin handcuffs da muk'arraban sa su Alh Aminu...

Ya tako har gaban VP fuskar sa tayi jazir kafin yace "Tun ba yau ba, Daddy tun ba yau ba nasan bak'in zaluncin da ka aikata shekarun baya, ka kashe min tilon k'anwata sabida neman duniya, duniyar da bazata tabbata maka ba, ka kashe ta ka kashe Mama Juwaira sabida ka sami cimma burin ka.... Meyasa su meyasa Nabila meyasa ni baka kashe ni ba ka k'yale Nabila tayi rayuwarta...." Bai kai aya ba VP dake huci yana nuna sa da d'an yatsa ya kaste sa da fad'in "Because you're not my son, kai ba d'ana bane Aliyu, you don't have my single blood running in your veins....... Sannan Nabila ni nasan ban kashe su ba uwarka wacce ta bada kyautar ka wa Maryam wacce take rainon Nabila babu dare babu rana ta gudu da Nabila.... Skulls d'in daka gani d'auke da sunayen su ba Skulls d'insu bane ba k'ok'on kayukan su bane, Boka ya tabbatar min idan na tsafe tilon gudan jini na zan dawwama ina mulki, b'acewar da sukayi shiyasa na boka ya manna sunayen su jikin wad'ancan k'ok'on kayukan da ka gani.... I don't owe you any explanation boy.... Iyakaci Haidar saidai nace ka cika butulu sabida na maka gata ka kasance ungrateful daga k'arshe.... Abu guda da nake son sanar da kai shine kwabo na ban yarda kaci ba while I'm in jail......"

Haidar da sama ke neman juya masa k'asa baisan sanda ya durk'ushe a wajen ba yana raba idanu ya kasa fahimtar komai.... Shin wanene shi..? Tambayar da ya ringa yima kansa kenan .... Baisan sanda aka fice dasu Daddy ba bai kuma sanin yanda kansa yake ba...

*****

Maryama na rik'e da hannunsa gefe guda yayinda su Sajida ke d'aya gefen, gaba d'aya kuka suke Hajiya ita kad'aice mai k'arfin halin k'arfafa masu gwiwa hak'ik'a yau sun had'u da iftila'i wanda ba'a saka masa rana....

A hankali AT ya bud'e idanunsa ya sauk'e su kan iyalansa, hannunsa d'aure cikin bandage.... Hawaye na gangaro masa.... Lumshe idanunsa ya kuma yi yana fad'in "She killed them... Ta kashe su, Shema'u ta kashe su gaba d'aya..." wani sabon kuka ya kuma kufce masu gaba d'aya domin i zuwa lokacin magana ta gama fitowa fili.....

Hajiya ta dafe goshinsa tana karanto masa addu'o'i Al'ajabi ya rufeta gaba d'aya... Su Sajida da Maryama kuwa ko wacce mahaifiyarta ta tuna, lallai Shema'u abin tsoro ne ba 'yaradam bace....

Hannun Hajiya ya rik'e still idanunsa a lumshe yake fad'in "Hajiya ki yafe ni, ki yafe min, hak'ik'a bijire ma umarnin ki yana d'aya daga cikin abinda ya jefani cikin halin da na tsinci kaina a yau, ki yafe ni Hajiya...."

Hajiya tasa bakin mayafi ta goge hawayen da suka zubo mata kafin ta kuma dafa sa tace "Attahiru na yafe ka, idan da laifin ka nima da nawa laifin, hak'ik'a na kasance mai kausasa harshe a gareka, bana la'akari da cewa ni mahaifiyar ka ce.... Ka yafe ni Attahiru ka yafe ni kaji.... Allah shi kad'ai zai mana sakayyan abinda roba-roba tayi mana....." ta k'arashe tana kuka....

A hankali ya mik'e ya zauna yana dubansu gaba d'aya yanda suka tak'ure waje guda suna kuka daga Maryama har su Sajida...

Takowa yayi yana dafe da hannunsa ya k'araso har gabansu.... Cikin sauri yaran suka k'arasa suka rungume sa suna kuka sosai..

Lallashin su yake kuka shima ya carke masa murya... Sajida ta d'ago tana dubansa take fad'in "Daddy I'm sorry, it's all my fault... Da ace ban aminta da ita ba duk da batakai ga aurenka ba, I Was stupid and naive, she was only using me..... If only I knew..... Da ace nasan ita ta kashe mahaifiyata da ban barta ta kusance mu ba... Daddy don Allah ka yafe min wauta na shi ya haifar mana da tashin hankalin da muka tsinci kanmu ciki.... Forgive me pls for all the pains I caused you.... Wllhi duk ita ke sakani yin abubuwan da nayi....." Hugging d'inta AT ya kuma ya shiga share mata hawaye yana fad'in "It's okay sweetheart, we all are victims here, non of this is your fault... She manipulated us all, she played innocent with all of us..... Amma Allah bazai barta ba zata girbe abinda ta shuka koma nace ta soma girba.... Zata tafi yanda suka tafi itama..... Oya kuzo nan...." ya had'esu gaba d'aya yayi hugging..

Ido suka had'a da Maryama tayi saurin saka bayan hannunta ta share hawayen ta... A hankali ya k'araso gabanta.... Ta kasa d'ago idanu ta dubesa, hannayenta AT ya kamo murya can k'asa ya furta "Thank you, thank you Maryam ...... Banida bakin maku godiya keda Ashfaq Allah Ya saka maku da aljannah, sannan.... Sannan kiyi hak'uri kashe mahaifiyarki da Shema'u tayi, ku yafe min daga ke harsu Sajida I couldn't protect.....Na.... Na kasa tsare iyayenku..." Maryama ta d'an girgiza kai tana goge hawayenta kafin tace "Uncle ka daina min godiya sannan kuma babu laifinka ko d'aya a mutuwan Aunty da Ummi nah, tuntuni hakan ya jima a rubuce.... Nasan chan d'in yafi masu nan saidai mu bisu da addu'a...... Bata kai aya ba AT ya rungumeta hawaye na gangaro masa.... A haka Sajida ta jawo hannun k'annenta suka rungumesu gaba d'aya.

Hajiya dake gefe share hawayen da suka zubo mata tayi lokaci guda fuskar ta Ya cika da murmushi...... Ihun Shema'u dake kwance wani d'aki suka jiyo don ba'a jima da kawota asibitin ba...

*********

Tashin hankali wanda ba'a saka masa rana, haka Mummy ta biyo jirgi ta nufo garin Kano, idan kaga Mummy sai ka tausaya mata.... Kuka ta ringa yi shar shar da hawaye tamkar k'aramar yarinya don labarin kwatsam kawai ya risketa cewa anyi arresting mijinta....

*******

Idan ba muryar Shema'u kaji ba bazaka shaidata ba gaba d'aya ta canza ta koma wata halitta ta daban.... Taci gaba da kuka daga saman gadon da take kwance take fad'in "AT ka yafeni wllhi sonka nake yi, ka yarda dani duk abinda nayi nayisu ne out of love, dan Allah kar ka juya min baya kaji my love..."

Jijiyoyin jikinsa gaba d'aya sun mimmik'e idanunsa sunyi jazir... k'arasowa yayi yana toshe hanci sabida wari da Shema'u keyi....

Da k'yar ya soma furta "Kin cuce ni kin zalunce ni kin ha'ince ni kin ci amanata in the most horrible way.... Yaya kike tunanin zan tab'a yafe maki bayan duk abubuwan da kikayi..... Meyasa Shema'u Why..... Ki sani wannan shine dalilin da ubangijina ya hanani kusantarki, sabida shi ba azzalumi bane sannan ya sanya zalunci ta zamo haramun a tsakanin bayi..... Ban tab'a ganin mugun d'an adam irinki ba.... Allah bazai barki ba Shema'u koda na yafe maki...." Aysha was pregnant.... Muryarsa ya sark'e ya kasa ci gaba da magana sai kuka yana dafe da wajen ciwonsa daidai lokacin dasu Maryama Hajiya da kuma Sajida suka shigo..

Maryama tayi saurin k'arasawa ga mijinta yayinda Sajida ta k'arasa gaban Shema'u.... Idanunta jazur hawaye na zubo mata..

Shema'u ta soma d'ago hannunta da ya k'one da ruwan acid tana fad'in "Sajee my Sajee ki yarda dani nasan bazaki tab'a juya min baya ba sweetheart pls believe me....."
Chapter 63 · 0% Book details