Sashe 27
Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
AT ya gyad'a kansa kafin yace "Me ya sameki a idonki, yana ciwo ne...?" yayi tambayar idanunsa naga plate yana juya spoon..
"Emm a'a babu komai..."
"Are you sure.. " ya fad'i yana mai tsareta da idanu.
Gyad'a masa kai ta kumayi alamun tabattarwa..... Sallaman da Ilu keyi ne ya katse su.. AT ya amsa murya a dake don sam baya wasa da Ilu.
"Datta dama bak'on da ya kawo su Hajiya d'azun da rana ke sallama yace shi abokin aikin ka ne..." Ilu ya fad'i cikeda ladab.
Kallon Maryama AT yayi kafin yace "Tashi ki shiga." ya dubi Ilu yace "Ce masa ya shigo."
Ilu ya amsa da "An gama rankashidad'e.."
Da sallama Ashfaq ya shigo hannunsa d'auke da shopping bag. AT ya amsa masa babu yabo babu fallasa kafin yace "Ah Dr bismillah, k'araso mana."
Ashfaq ya fad'ad'a murmuahin sa ya k'araso yana fad'in "Ah Ya Doctor (haka yake kiran AT wani sa'in) ashe kana nan kenan.." ya k'arashe yana mik'a ma AT hannu sukayi masabaha had'i da gaidashi.
AT ya amsa yana masa nuni da gefensa yace "Bismillah zauna mana bari a kawo maka plate..."
Ashfaq ya d'an murmusa had'i sosa k'eyarsa kana yace "A'a na gode Ya Dr a k'oshe nake."
AT ya jinjina kai sannan "Da fatan dai lafiya ko...?" ya k'arashe yana kai spoon bakinsa..... Ashfaq baikai ga basa amsa ba domin kuwa shi kansa baisan me zaice ma AT ba, Hajiya ta fito don taji kaman muryar AT da wani ne. Burki tayi tana kallonsa da kyau kafin tace "A'ah Keenafas (Kidnappers) ka kuma dawowa ne.." cewar Hajiya da ta masu tsaye aka..
"Keenafas" abinda AT ya nanata cikin zuciyar sa kenan. Ashfaq kuwa murmushi yayi kafin ya soma gaida Hajiya... Da fari'anta ta amsa masa don ta lura yaron sam bashida fushi tabbas zamansu zai zo dai-dai da Hajiya.
Ajiye spoon d'in hannunsa yayi ya d'an dubi Hajiya kana yace "Hajiya sunansa fah Ashfaq naji kin kirasa da wani suna daban." cewar AT
"Yo baka ga yanyinsa bane kaman keenafas masu garkuwa da mutane, ai d'azun k'in yarda dashi nayi, amma kaga gwara yanzu yayi fasali harda d'an gayu yayi ba kaman d'azun da rana ba.."
Sosai abin ya bawa AT dariya, wai Keenafas, d'an girgiza kai yayi kafin yace "Hajiya sunan sa Ashfaq kuma abokin aiki na ne, shi ba kidnapper bane."
"Yo na sani ai, keenafas maza taso ka shigo daga ciki a kawo maka naka abincin ciki." ta k'arashe tana komawa cikin parlorn.
A ladabce Ashfaq ya amsa kafin yabi bayan Hajiya... AT ya bisa da kallo yana tunanin toh me ya kawo Ashfaq kuma....
Yana jiyo yanda Ashfaq da Hajiya suka sake sai hira suke kaman sun jima da sabawa da juna... Maryama ma ta fito daga uwar d'aki suka gaisa da Ashfaq tana mai shan mamakin yanda Hajiya ta sake dashi kaman ba ita bace d'azun ta sursurfa masa fad'a ba. Hajiya ta umarceta da ta kawo masa abinci, babu musu tayi yanda Hajiya tace..
AT sai binta da kallo yake sanda ta fito ta nufi kitchen, shifa sam bai aminta da zuwan Ashfaq ba, toh wata gulmar ta kawo sa bayan yayi abinda ya saka shi, b'angare na zuciyarsa ta shiga kokonton anya Ashfaq ba sawun Maryam ya biyo ba, take yaji gabansa ya yanke ya fad'i, gaba d'aya ji yayi ya kasa ci gaba da cin abincin, mik'ewa yayi ya d'auki wayoyin sa da agogon sa ya nufi cikin parlorn, don kuwa gwara ko menene yake tafe da Ashfaq ya fad'esa a gaban idanunsa....
*************
A hankali ta tura k'ofar d'akin tana mai d'an k'wank'wasawa da yatsun hannunta biyu kana tace "May I? "
Sajida dake tsaye gaban wardrobe tana neman kayan sakawa saurin k'arasawa tayi ta rungume Shema'u kana tace "Aunty luv, I thought baki gida don d'azu nayi knocking a k'ofarki banjiki ba."
Shema'u ta murmusa kafin tace "Ina nan sweetheart kawai dai fushi nake dake.." ta k'arashe fuskarta babu walwala.
Idanun Sajida yayi rau-rau. "Aunty me ya faru, pls don't be mad at me." kaman zatayi kuka tayi maganar.
Shema'u ta tsareta da udanu kafin tace "Ina kika tsaya bayan an tashi a islamiya, kindai san nace maki tsakaninmu babu secrets you're my daughter and my best friend, oya fad'a where 've you been..? "
Sajida ta d'an muskuta kafin tace "Aunty wllhi dama I was about to tell you, kin tuna maganar Haris da mukayi."
Shema'u ta gyad'a kai tana mai ci gaba da dubanta..
Sajida taci gaba da fad'in "Toooh dama shine muka had'u yau a school d'inmu shima yaje ma wata cousin d'insa, in short we're friends now.." ta k'arashe tana murmushi.
Murmushin jin dad'i Shema'u tayi kafin tace "Sweetheart naji dad'i da kika zama opened dani, amma dai kinsan your Dad won't welcome the idea Haris ya zama friend d'inki, amma kar ki damu, kinsan nace maki you can always count on me, for now tunda kin sanar dani no need Daddy Ya sani, don idan ya sani zai iya rabashi dake, tunda shi bazai kawo ba wani abu maras kyau kukeyi ba, you know how Daddies are when it comes to their daughters, they're over protective gani suke kaman lalata masu yara za'ayi while idan ba'a bar yara sun d'ansha iska ba at this age of yours shine suke lalacewan, but ni nayi trusting d'inki sweetheart nasan bazakiyi wani abu maras kyau ba.."
Sajida ta murmusa had'i da rik'o hannun Shema'u kana tace "Aunty Shemah na gode da yanda kike fahimta ta, sannan sunan uwa kawai na rasa, amma tabbas ke d'in kin maye min gurbinta, na gode k'warai.." Hugging d'inta Shema'u tayi fuska fal murmushi.. Nan Sajida ta fayyace ma Shema'u gaba d'aya yanda sukayi da Buzu, Shema'u kuwa sai biyeta take tana nuna mata zatayi guiding nata in everything.
Magana Shema'u ta rad'a mata a kunne tana murmushi... Waro idanu waje Sajida tayi kafin tace "Aunty kinsan na mance gaba d'aya, toh cake fah ya zamuyi..."
Shema'u ta murmusa kafin tace "Na riga na shirya komai sweetheart, tashi muje wajen su Jamal suna downstairs mu ci gaba da preparations, tsalle Sajida tayi suka rungume hannun juna itada Shema'u suka fice a tare.
*************
Wayarsa yake kan faman shafawa amma hankalin sa naga Ashfaq da Hajiya dake faman zuba zance, shi kansa baisan Ashfaq ya iya surutu haka ba, sosai Ashfaq yaci tuwon kuwa, yana ci suna labari da Hajiya yana fad'a mata shi d'in d'an Katsina ne, iyayen sa da 'yan uwansa gaba d'aya suna can Katsinan, shine dai aiki ya kawosa garin Kano.
Maryama dake d'aki tana jiyo hiran nasu nan gabanta ya yanke ya fad'i jin Ashfaq d'an Kastina ne, garin da Ummi ta fad'a mata asalinsu da tushen su kenan, garin da take mafarkin zuwa amma har yau Ummi sam bata son ko labarin garin ayi, Allah sarki ko don ta rasa kowa nata a zaizayan k'asan ne k'ila shiyasa sam bata so a d'ago mata zancen garin.. Maryama ta sauk'e ajiyan zuciya tana mai ci gaba da rayawa a ranta watarana insha Allahu zataje, wata k'ila ta sami sauran danginta tunda tasan tabbas baza'a rasa wasu ba koda wasu sun mace.
Gaba d'aya AT ya gundura da hiran Ashfaq d'in, shi sam baida hayaniya, shafa wayarsa yake kan faman yi, nan yaga wata lamba ta whatsapp ana turo masa pictures..
Bud'ewa ya shiga yi yana murmushi, hotunan yaransa ne ga dukkan alamun cikin jin dad'i suke, shi kad'ai sai faman murmushi yake yana bud'e pics d'in, nan ya bud'e wani wanda suka d'auka harda Shema'u, wasu da funny faces abin sai ya basa dariya, sosai suka burgesa like a real family, k'asan pictures d'in ya bud'e wani message
_Daddy pls come home soon, we've a surprise for you.... Sajee*_
Murmushi kawai ya kuma yi kafin ya koma yana sake kallon pics d'in.
Kiraye-kirayen sallan isha aka soma, AT da Ashfaq suka mik'e suka nufi masallaci..
Nan Hajiya tasa Maryama ta tattara kwanukan da suka ci abincin, sosai Maryama tasha mamakin ganin AT bai wani ci abincin kirki ba, ita kanta ta gundura da Ashfaq ta lura akwai shi da zak'ewa, bacin haka miye nashi na dawowa bayan ya riga ya kawo su kaman yanda Uncle ya umarcesa..
Sanda suka shigo tana gaban socket tana had'a ma Hajiya chajin wayar ta. AT sai bin Ashfaq da kallo yake yanda yake faman satan kallon Maryama, shifa abun na Ashfaq ya soma damunsa, idan gaisuwa ne ya kawosa ya tafi mana tunda yayi.... Kaman Ashfaq yaji zancen zucin da AT keyi, nan ya mik'e ya jawo ledar da ya shigo dashi kafin ya rusuna ya mik'a ma Hajiya yace "Hajiya ga wannan na Maryama ne kyautar ta ta k'arashe makaranta..."
Daga AT har Maryaman dake k'uryan d'aki saida k'irajensu suka buga, shi sai yanzu yama tuna wayoyin da ya sai masu itada Sajida a matsayin kyautar su.
"A'ah keenafas harda wahala haka, ayya toh Maryama ta gode, kayya da baka tak'ura kanka ba." ta k'arashe tana bud'e jakar turarruka ne masu kyau da tsada had'i da bangles da sark'a ruwan silver, da gani sunada d'an kud'i..
Wannan kyauta da Ashfaq yayi ma Maryama har wuya ya kawo AT, banda iyayi ina ruwansa da ita da har zai mata kyautan kammala makaranta. Shi haushin Hajiya ma yaji data amshi kyautar.
Hajiya kuwa ko a jikinta ta mik'e tana fad'in "Ayya keenafas, kayi hak'uri fah sunan naka ne ke bani wuyan fad'i, amma dai kar ka damu zan koya, bara na kira maka Maryam d'in tai maka godiya ko.."
Maryama tana jin haka tayi saurin rufe idanunta kaman tana bacci, Hajiya ta fito tana fad'in "Oh Maryama sam bacci baya mata wahala, da zaran ta kishingid'a toh shikenan tayi bacci, idanba kallon shirin nan na Dad'in kowa wanda ake nunawa a Arewa tonti po zamuyi ba."
AT har ransa yaji dad'in barcin da tayi.
Ashfaq ya d'an murmusa had'i da shafa kai kana yace "Ai babu komai Hajiya, idan ta tashi ace mata na wuce, sai wani lokacin kuma."
"A'ah keenafas kazo abinka ko yaushe ai nan gida ne, karkaji komai kaji koh..."