Sashe 18
Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin haka yasa Shema'u saurin tasowa ta k'araso yanda suke, tsugunawa tayi itama gaban Ni'ima kafin ta shafi kanta tace "Baby Daddy fah allura zaije, kuma idan kika bisa anjima zamu tafi shan ice-cream babu ke.... Right guys? " ta k'arashe tana duban su Sajida.
Murna suka soma yi nan Ni'ima ta janye hannunta daga na AT ta tafi wajen Shema'u ganin yanda sauran 'yan uwan nata ke murna.
Sai satan kallon AT da ya bisu da kallo take, mik'ewa yayi ya soma tafiya yana zura wayar sa a aljihu. Nan Shema'u ta hangi car keys d'insa saman center table, kafin yaran su kula tayi saurin k'arasawa ta d'au keys d'in.
Har ya kai k'ofa ya jiyo Shema'u ta ambato sunansa
"Dr."
Juyowa ya d'anyi ya dubeta.
Cikin salo da kissa ta tako har yanda yake kafin ta d'ago masa keys d'in tana murmushi tace "You forgot this."
D'an murmushi yayi kafin yace "Thank you." Yasa hannu zai karb'a ta saki keys d'in a k'asa cikin salo. "Ohh sorry,." ta fad'i sanda tabi keys d'in k'asa.... Daidai lokacin da yakai hannunsa kan keys d'in Shema'u ma ta sako nata, nan hannayen su suka mannu da juna, d'ago idanu sukayi suna duban juna, cikin sauri ya janye hannun sa yana bata hak'uri. Cike da kissa itama ta soma basa hak'uri irin a daburcen nan, sai ka rantse har ranta ne.
Cikin sauri ya mik'e ya fice, k'irjinsa na bugawa cikin sauri, rabonsa da jikinsa ya shafi jikin wata macen daba tasa ba tun Ayshar sa na raye... D'an shafe goshinsa yayi had'i da k'ok'arin yakishe hakan a zuciyar sa cikin sauri.
Shema'u dad'i kaman ya kar ta, cike da farin ciki ta shige cikin yaran suna masu ci gaba having fun, sai jefa throw pillows suke a tsakanin su.
*****************
Kallon wayar data sayo d'azun da yamma ta zauna tana yi, kai anya yanzu ne ya kamata ta bama Sajida wayan nan.? What if AT finds out.... Kai ya kamata tayi abu da tunani tunda dai yanzu confirm tanada Buzu a k'asa, umarni kawai yake jira ta basa ya soma gudanar da aikinsa.. Wani tunani ne ya fad'o mata ta Saki murmushi had'i da kwanciya saman gado zuciyarta fal nishad'i......
Wasa-wasa SHAK'UWA CE sosai ta shiga tsakanin yaran AT da Shema'u. A b'angaren AT kuwa sosai yake duk iya k'ok'arinsa ganin yayi avoiding duk wani abinda zai had'asa da Shema'u amma abu yaci tura, ko ya keb'e kansa yaransa zasu had'asu, bazai iya k'aurace ma yaransa ba da yayi hakan. Shi kansa baisan me yake ji ba, amma tabbas zaman mace haka a cikin gidansa yana matuk'ar jefasa cikin wani irin yanayi da tunani kala daban-daban tunda shidai ba waliyi bane.
Tabbas shed'an yayi jagora ma Shema'u don kuwa AT ya sami kansa da matsananciyar Sha'awar ta duk iya k'ok'arinsa na ganin ya yakice hakan a zuciyar sa abu yaci tura, musamman idan ya tuna 'yar uwar matar shi ne, kai ko zaiyi aure don kare kansa daga fad'a ma tarkon shed'an bazai auri 'yar uwar matar shi ba, gani yake kaman yaci amanar Aysha ce. Ganin tunanin hakan bazai ficce sa ba ya sanya sa dagewa da azumin litinin da alhamis.
Shema'u kuwa dama ta samu, ado da kwalliya babu kama k'afan yaro.
***************
Rai b'ace ta turo k'ofan d'akin ta shigo kaman zatayi kuka. Cike da makirci Shema'u ta mik'e ta rik'ota tana fad'in "Baby lafiya, meke faruwa.?"
"Aunty wai Daddy bazaije graduation d'ina ba... Aunty ina so na ganku duka a wajen, all my family..."
Murmushi Shema'u ta sakar mata tana shafa fuskar ta kafin tace "Sweetheart kinsan Daddyn ku da kafiya, gashi yanzu sam ba sosai yake son shiga sabganmu ba, bansan ko zamana ne a gidan sa baya so ba, amma dai kar ki damu anything for you my dear, zan yi iya k'ok'arina na nuna masa mahimmacin zuwan nasa, ai nasan da zaije, amma sani nima zanje inaga shiyasa ya fasa, Baby bansan me nayi ma Daddynku yake avoiding d'ina haka ba, ko dai ina wani abin maras kyau ne.?" ta k'arashe tamkar zatayi kuka.
Jikin Sajida yayi sanyi, tak'i jinin taga Shema'u cikin damuwa. Da sauri ta soma girgiza kai kafin tace "Aunty don Allah kar kiyi kuka."
Cike da kissa Shema'u tace "Ba dole nayi kuka ba sweetheart, kinsan dai yanda nake sonku nake ji daku, yanzu idan Daddyn ku yace na bar masa gidan sa ai bazan iya rayuwa babu ku ba, ina sonku sannan na shak'u daku, bazan iya barin ku ba, never. " ta k'arashe tana mai rungumar Sajida idon ta harda kawo ruwan makirci kafin tace "Amma dai kije ki bisa a hankali ki nuna masa mahimmancin zuwan nasa, nasan he'll listen to you." Nan ta kitsa mata me zata ce.
Cikin sauri Sajida ta mik'e ta fice daga d'akin ta nufi parlon mahaifinta..
Shema'u ta bita da kallo, kafin ta daka tsalle tana fad'in "Yesssss." kwanciya tayi bisa gado had'i da lumshe idanu.
Bata samesa a parlor ba hakan yasa ta nufi bedroom d'insa, k'wank'wasa k'ofar tayi had'i da sallama kafin ya mata izinin shigowa, yana zaune yana research a computer, kunsan likitoci ba'a rabasu da bincike. Cire medicated glasses d'in idanunsa yayi kafin ya karkato yana dubanta yace "K'araso mana Mama ta."
Baki a ture kaman zatayi kuka ta tako ta zauna gefensa kafin tace "Daddy sanda na gama primary, you were there, harda Mummy da Jamal. Daddy meyasa yanzu bazaka je ba, sabida babu Mummy, wllhi zanyi kuka idan ban ganku gaba d'aya a wajen ba. Nasan kana valuing aikin ka but pls Daddy do this for me... Don Allah kaji Daddy
Tura laptop d'in gabansa yayi kafin yace "Sajida sam ba haka bane, ranar tayi dai-dai ne da ranar ziyarta ta asibitin Bauchi kinsan ni visiting Dr ne a can. Amma I'll see what I can do, kinji...." ya k'arashe yana sakar mata murmushi.
Murmushi itama tayi kafin tace "Daddy na gode. You the best. " Ta mik'e ta fice cike da farin ciki. Ya bita da kallo yana murmushi kafin ya girgiza kai kawai yaci gaba da abinda yake.
Da gudu ta shigo d'akin had'i da d'alewa jikin Shema'u tana mai sanar da ita ya yarda zaije shi. Murna Shema'u ma ta shiga yi tana fad'in "Kinga abinda nake fad'a maki idan kin bisa a tsanake tsaf zai yarda."
Sajida na murmushi take fad'in "Allah barmin ke Aunty." Shema'u ta kuma hugging nata.
****************
Yau ce ranar su ta k'arshe a Makarantar, ranar bukin yayen su. Sunyi kayu cikin graduation gowns d'insu. Kana iya hango tsan-tsan farin ciki a fuskar gaba d'aya d'aliban da ake yaye su.
Fadila ce ta kuma tab'o Sajida tace "Wai har yanzu Maryama bata iso ba, kinga fah the program is about to start, yaya zamuyi kar a soma kiran sunan ta don nasan confirm zata karb'i kyaututtuka."
Tab'e baki Sajida tayi ba tareda tace komai ba, tsaki Fadila ma tayi tace "Kar Allah sa ki tanka, kuma kyauta ne dai sai ta karb'a.... Su Fauziya sauran k'awayen su sai dariya suke masu. Don dama sun saba 'yar haka da Fadila, wacce suka fi shiri dama Maryama ne.
AT yayi kyau cikin faran yadi mai laushin gaske, ya saka hula dark ash zanna bukar, dark covers ne a k'afafun sa yayinda ya d'aura agogon Aldo zallan silver, k'anshin rantsatstsun turarruka ne kurum ke tashi a jikinsa.
Shema'u dake tsaye dasu Jamal a parking lot baki ta sake kawai tana hangosa. Tun daga nesa ya bud'e masu security lock amma Shema'u bata san ya bud'e ba, tayi nisa cikin duniyar kallon sa.
Saida ya k'araso ya bud'e masu Jamal k'ofar motar kafin hankalin ta Ya dawo jikinta, cike da kissa ta bud'e front seat ta shige tana binsa da mayen kallo, shi kuwa AT sam baison yama kalle ta. Sai biye ta yaransa yake.
Suna tafe suna hira da yaransa Shema'u tana tsomo baki, a dai-dai kwanan shiga makarantar wayarsa ta soma ringing, Hajiya ce mai kira.
Da fad'a ta soma masa don ko zsrafin gaisheta bai samu ba, nan ta sanar dashi Maryama tana gida bata je ba, yauma su Sajidan basu biyo mata ba.
"Subhanallah Ya akayi haka?!" ya furta sanda yake karyan kwanar, Shema'u kuwa k'uri ta masa tana son jin menene ya d'aga masa hankali haka..... Muryarsa ta kuma jiyowa yana fad'in.
"Okay, gani nan zuwa yanzun nan, barin ajiye su Jamal."
Koda ya gama wayan kallo Shema'u ta kuma binsa dashi tana son tambayar sa wa ya kirasa amma babu fuska, iyaka abinda ta fahimta kiran nada mahimmaci a gurinsa.
Sanda ya gama parking a farfajiyan makarantar, ya dubi su Jamal yace "You guys should behave okay, zan dawo bada jimawa ba, just stay with your Aunt okay." Jamal yace "Daddy ina zakaje, Adda Sajida bazataji dad'i ba idan taganmu babu kai.
D'an turo kansa yayi ta k'ofar motar kafin ya shafi kan Jamal yace "Champ, zanje d'auko Addan ku Maryam ce, she supposed to be here by now, tunda harda ita akema yayen. Ku zauna da Aunty ku, yanzu zan dawo..
Kad'an ya rage Shema'u bata saki fitsari a wandonta ba jin yanda AT zaije sabida tsananin tashin hankali...... Tayi nisa duniyar tunani ta tsinkayo muryar AT yana fad'in Ta kula dasu da Allah.
Murmushin yak'e tayi kafin tace "You don't have worry Dr, mu jenku ko babys d'ina, ta rik'o hannayen su suka shige. K'irjinta sai tafarfasa yake.
Cikin sauri AT ya tada motar sa ya bar wajen.
Tana tsaye jikin glass d'in window dashike irin mai kaman madubin nan ne tana gyara d'aurin kwalinta ya hangi bayanta. Kasa ci gaba da tafiya yayi sai mutuwar tsaye da yayi a wajen. Da sauri da sauri zuciyar sa ke bugawa.
Ta cikin mirrorn ta hangesa yayi tsaye yana kallon ta wanda hakan ya sauk'ar mata da fad'uwan gaba.
*Sameena Aleeyou Mrs*
[2:56PM, 3/4/2018] 鈥�+234 703 300 1537鈥�: 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊
*SHAK'UWA CE*
馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊
*16*
*漏Sameena Aleeyou....鉁嶐煆�*
_馃寛KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 馃_
*Fatan Alkhairi k'awayen k'warai Sweetheart Rally Garba 馃槝 and Shawty 馃挄 Darling.... Love you guys from the bottom of my heart 馃槏*