Sashe 30
Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nan ya hangi kayan Momma jikin trunk d'in motar SShema'u na gefe ta rik'e Sajida dake zuban hawaye yayinda Hajiya da Momma aka rasa mai bama wani hak'uri, ko wacce gaya ma 'yaruwarta magana take...
"Wllhi Kulu duk tsiddabarun da kuka zuba wa d'ana sai Allah Ya maidashi kanku, bacin haka har yaushe Attahiru zai soma maganar auren wannan mai suffar agwagwan..." ta k'arashe tana nuni da Shema'u...
Daga Shema'u har Momma a sama suka tari zancen, kenan AT yana son auren Shema'u, dad'i ya lullub'e Shema'u ta kuma rik'o hannun Sajida tace "Muje ciki sweetheart kinji.... " Ai kan tayi wani yunk'uri Hajiya ta fizgo wuyar ta baya tana fad'in "Ki shiga ina, ai yanda kikaga uwarki ta fito toh kuwa binta zakiyi, annoba kawai, tunda kuka zo gidan nan hankula basu kwanta ba, munafuka ni tunda naga kina nan-nan da yaran nan nasan da biyu kikeyi, kin lik'e ma mijin k'anwa banda asara, gadon jaraba gadon Kulu..."
Har wuya AT yazo ganin a gaban Sajida Hajiya take wad'an nan maganganun, cikin sauri ya juya ya koma cikin gidan... Shema'u ta bisa da kallo kaman ta zuba ruwa a k'asa ta sha, cikeda makirci take bawa Hajiya hak'uri tana rok'onta tayi shiru ko don Sajida.... Gaba d'aya Hajiya ta had'e su gaba d'aya taci gaba da sille su...
Momma kuwa tunda Shema'u ta kwab'eta ta had'iye bak'incikinta don kuwa tabbas ta yarda da shawarin Shema'u ta ringa hak'uri da Hajiya har su sami biyar buk'atar su...
Shema'u ta gyara zaman hijabin kanta don dama kayan barci ne a jikinta, cikin zuciyarta ji take tamkar ta damk'o Hajiya ta mak'ureta a wajen kowa ya huta, har tana hasashen irin kisan gillan da zatama Hajiya, daurewa tayi kafin ta lank'wasa murya tana kuma bawa Hajiya hak'uri, Sajida kam tsanar kakan nata ne tab ya cika zuciyar ta, jiyo kukan Ni'ima da sukayi daga cikin gida yasa Shema'u saurin shigewa a rud'e tamkar gaskiya Sajida ta take mata baya da sauri...
Momma ta murmusa ta dubi Hajiya kafin tace "Fad'ime kin koma tamkar zararriya, barikiji na fad'a maki nafi k'arfin nayi asiri ma uban jikoki na, saidai idan ina numfashi baki isa ki auro ma Tahir wata ta zauna kan jikokina ba tunda Allah yasa mahaifiyar su tanada 'yaruwa... Ta murmusa kafin taci gaba da fad'in "Ayyiriri, Alhamdulillah Masha Allah tunda shi da kansa ya gane abinda yafi masa kyau yafi dacewa dashi, nikam saidai nace Allah sanya alkhairi na bisu da fatan khairan, kuma tafiya ne dole na d'ageta sai nasan matsayin da d'iyata take a gidan nan..." Daga haka ta shiga janye akwatinta ta nufi cikin gida.
Zuciyar Hajiya kaman ya fito waje ya tawarwatse, yau ita za'a ma wannan cin kashi a gidan Attahiru. Gyad'a kanta tayi kafin ta juya ta soma tafiya bata ko ganin gabanta, idan anyi duniya don manzo ta gama shiga hidiman gidan Attahiru, yaje yayi duk yanda yake so da rayuwarsa tunda shi ba k'aramin yaro bane...
Kusan karo suka kusanyi da AT suka jima suna kallon juna, tuni Sajida ta shige ta d'ago Ni'ima... Cikin sauri Shema'u ta saita kanta ta shiga murmushin yak'e tana basa hak'uri, bata jira cewar sa ba tayi saurin k'arasawa yanda Ni'ima da Sajida suke ta amshi Ni'ima tana rarrashinta don da alama firgita tayi ta tashi a baccin.
Cikin sauri AT ya nufo downstairs ya nufi motarsa yayi mata key ya fice daga gidan, yabi bayan Hajiya.
Yana gani ta patattake malam Habu dake rok'onta ta tsaya ya kaita.. Hankalin AT idan yayi dubu ya tashi.. Cikin sauri ya fice daga motan ya nufeta da sassarfa...
*Sameena Aleeyou Mrs*
[2:00PM, 3/12/2018] +234 803 533 3121: 💘💘💘💘💘💘💘💘
*SHAK'UWA CE*
💘💘💘💘💘💘💘💘
*24*
*©Sameena Aleeyou...✍🏼*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
Kaman ya durk'usa saman gwiwoyinsa haka yabi Hajiya yana bata baki yana rok'onta tayi hak'uri ya kaita...
Tasi na tsayawa tayi shigewarta sai faman huci take, AT yayi saurin kama gaban tasi d'in zai shiga ta watsa masa mugun kallo kafin tace "Wllhi ka shiga motar nan kai ba d'ana bane..."
Gaban AT ya yanke ya fad'i, jiki a mace ya saki marfin motar, Hajiya ta dubi d'an tasi tace "Muje Malam." Nan mai tasi ya ja motar suka wuce.
Jigum yayi a wajen yabi bayan motar da kallo, tunowa yayi fah Hajiya nada mota amma tsaban masifa da fad'a irin nata direbobi basu iya zama da ita, da an kawo su sati d'aya sati biyu yayi yawa sun k'ara ma kansu gudu sabida Hajiya..... A hankali ya ambaci sunan Allah kafin ya nufi motar sa ya tada ya nufi gidan nata.
***********
Maryama na zaune a parlor tana kallon wani series film mai suna *Jenifer's Diary* a sabon laptop d'inta don dama Buzu ya jima da bata plate d'in kyauta sabida yaji yanda take labarin a makaranta su Fadila na gani suke bata labari hakan yasa ya sai mata CD d'in, sai faman shan dariya take don film d'in akwai abin dariya lokaci guda tana goge inners d'inta dangin pants.... Ganin Hajiya ta shigo fuska babu walwala yasata dakatawa da abinda take..
"Hajiyata lafiya, Allah sa ba wajen Momma kika je ba..." Maryama ta fad'i tana mai saka pause ma kallon nata.
Hajiya bata furta komai ba sai k'wafa da tayi had'i da cire hijabinta ta d'aura saman hannun kujera.... Tabbas idan kaga Hajiya bata amsa ka ba toh kuwa ranta ya kai k'ololuwa wajen tashi.
Kasa furta komai Maryama tayi sai sanyi da jikinta yayi, tana son Hajiya duk fad'a irin nata bata son ganin ranta a b'ace.... Kaman daga sama sai ganin AT sukayi ya d'aga labule ya shigo sallama saman bakin sa... Ai tun kan ya gama shigowa Hajiya ta mik'e ta fad'a uwar d'aki had'i da tura k'ofan.
Maryama ta bisa da kallo ganin yanda ya shigo a birkice, gaba d'aya kaman ba Uncle ba, blue long sleeve ne a jikinsa da alama suite zai d'aura a saman bai sami zarafin yin hakan ba...
Shi d'inma kallonta yake lokaci guda idanunsa suka sauk'a kan kayan da take faman gogewa..
Ganin yanda idanunsa ke kallo yasata jin kunya sosai..... Cikin sauri ta tattari kayan tana turawa bayanta, shi kuwa AT sam hankalinsa ba'a wajen yake ba, gaba d'aya rasa meke masa dad'i yayi... Jiyo muryarta yayi tana gaida shi, ya d'an saita kansa kana ya amsa mata gaisuwar nata had'i da zama bisa sofa.
Maryama sai kallonsa take yanda ya dafe goshinsa, tausayin sa ya cikata tama rasa me zata soma fad'a masa, tambayar sa zatayi ne ko hak'uri zata basa, toh ma tace me?. Gabanta ya kuma yankewa ya fad'i, ita harga Allah Uncle na matuk'ar bata tausayi don tunda Aunty Aisha ta rasu bai huta ba....
Su biyu d'in jigum sukayi aka rasa mai magana ma wani cikinsu.... Jin shiru yasa Hajiya fitowa don a tunin ta ya tafi ne...
Aiko tana ganinsa tasa kai zata juya Tahir yayi saurin mik'ewa yabi bayanta...
Zama tayi bakin gado ta cika tayi fam, sautin huci da turirinta kawai kake jiyowa...
Kaman wani munafuki haka ya k'araso da sand'a, zuba gwiwoyinsa a k'asa yayi saman rug dake gaban gadon yana fuskantar ta jdanunsa a k'asa, Hajiya kuwa idanunta naga gefe ko kallon kirki bai samu ba, sai faman girgiza hannunta take wanda d'abi'arta idan ranta ya b'aci...
"Hajiyata kiyimin afuwa pls, Hajiya ki fahimce ni ki fahimci halin da nake ciki, bazan iya kawo wata macen da zata tarwatsa min kan gida ta rabani da yarana ba, na d'auka idan nace zan auri Shema'u zan sami goyon bayanki, Hajiyata ki duba lamarin Sajida itace babba cikinsu wacce ita kanta tana buk'atar uwa ballantana Jamal da Ni'ima wanda na tabbata ganin su haka babu uwa yana karya maki zuciya.... Hajiya a halin yanzu ba auren soyayya zanyi ba na wuce wannan babin tuntuni, aure zanyi sabida yarana sannan nasan kema sabida su kike so nayi auren, yau idan nace zan kawo wata mace cikin gidan na tabbata fitintunu ne zasuta tashi especially with Sajida, sannan.......suna son Shema'u suna so ta zauna dasu for good, hakan bazai tab'a yuwuwa ba idan ba aurenta nayi b........" D'aga masa hannu tayi alamun dakatarwa kafin ta jinjina kai tace "Yayi Attahiru tashi kaje, Allah Ya sanya Alkhairi ya bada zaman lafiya...." Daga haka mik'ewa tayi ta nufi bathroom, ta barsa nan durk'ushe uwa maraya...
Cikin sauri ta fice daga parlorn tana k'unshe kukanta, shikenan da gaske uncle auren Aunty Shema'u zaiyi, shikenan Aunty Shema'u zata zama matar Uncle..... Wani sabon kuka ya kufce mata sanda take shiga d'an madaidaicin parlorn Maama Juu...
Mik'ewa Maama Juu tayi tana tambayarta lafiya....
Cikin kuka ta soma fad'in "Ummi wllhi da gaske Uncle yake aurenta zaiyi, Ummi meyasa zai aureta wllhi ni na sani akwai bak'in k'ulli a cikin zuciyarta ba soyayyan gaskiya take nunawa su Sajida ba, Ummi ni dai wllhi banaso Uncle ya auri Aunty Shema'u...." ta k'arashe tana mai zama dirshan a saman tiles...
Mamaki ne ya cika Maama Juu, toh banda abin Maryama Tahir shi ya zab'i hakan ma kansa kuma yanada tabbacin hakan shine masa dai-dai.. Hannun Maryama ta rik'e tana duban idanunta da tsan-tsan gaskiyar kukan da take kana ta soma fad'in "Maryam, Ahmad shi ya zab'i hakan ma kansa sannan nima idan da zai nemi shawari na zan amince masa da auren Shema'u domin kuwa a iya zamana da ita kyautatawa ne kawai ke shiga tsakanin mu, itada marigayiya Aysha sam basuda halin mahaifiyar su ke shaida ce, ki duba ranar yanda sam bata goyi bayan Hajiya Kulu ba sanda ta k'ala maki sharri, sannan har ita saida Hajiya Kulu ta caje a gabanki, ni na zauna dasu a gidan naga yanda take kula da yaran sosai, koma babu wannan 'yaruwar mahaifiyar su ce ita yafi cancanta rik'onsu ya koma hannunta domin kuwa jini ya wuce wasa, dole ta kula da yaran tamkar ita ta haifesu, sannan Tahir bai kamata ya auro k'aramar budurwa ya had'a da yaransa ba don kuwa sabon raino zai k'ara ma kansa amma kinga babba kamar Shema'u sai tafi kula masa da yaran...."