Sashe 41
Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Saida ya razana da yaga Shema'u, har wani rama tayi ga fuskarta ta koma multi color nan ja can bak'i can coffee...
A razane yake tambayarta lafiya..?
Huci kawai Shema'u keyi kafin ta soma fad'in "Hisham su Jarka bazasu iya aikin nan ba sun min k'anana, High Killers nake so ka samo min, wllhi sai na shayar da Hajiyar AT mamaki, sai tasan ba'a shiga gonata..." ta k'arashe tana girgiza.
Murmushi Hisham yayi kafin ya k'araso yayi hugging nata ya zaunar saman sofa ya fara fad'in "Wannan daliline yasa duk kika fita hayyacin ki kika d'aid'aice..."
Tana huci taci gaba da fad'in "Hisham AT ya kasa kusanta ta har yau, could you imagine... Duk dare da zaran nayi niyyan kusantsa zai soma ciwo, Hisham bazan iya ba wllhi ji nake mutuwa zanyi idan ban samu biyan buk'ata ta ba, kasan irin gwagwarmayar da nasha kafin na mallake sa, a zahiri na mallake sa amma a bad'ini ban mallake sa ba.... Hisham wllhi zan iya kashe ko waye akan shi...." ta k'arashe tana rarraba idanu tamkar mahaukaciya
Saurin rungumeta Hisham yayi yana lallashinta, kaman jira take nan ta soma responding suka d'aura daga yanda suka tsaya....
Hisham ya dubeta bayan ya gama ja mata zip d'in rigarta kafin ya soma fad'in "My allied ba laifin Hajiya bane, idan baki sani ba ki sani AT is allergic to you, ni tun rananar farko na gane, sannan abinda kike buk'ata kike nema zaiyi wuya... "
Baikai aya ba ta mik'e tana girgiza kai had'i da wani irin murmushi take fad'in "Wllhi k'arya ne, this is ridiculous, wllhi asiri aka masa, babu lafiyayyan namijin da zai kasa biyan buk'atar sa yace allergy ne, wllhi wannan ko a wasan kwaikwayo ban tab'a gani ba, ko a labarai ban tab'a ji ba, wannan aikin Hajiyar AT ne ba ita ta iya asiri ba.... Toh wllhi sai mun tafi har gaban bokan nata naci uwarsu gaba d'aya, da kansa zai nad'e buzun sa ya bar bokanci domin kuwa ko shed'anu masu nuna masa sharri a bayana suke, ita kuma her days are numbered..." daga haka fincikan mayafinta tayi ta fice bata kuma bi takan Hisham ba.
Tunanin wayar da sukayi tareda Buzu take kan yi, amsoshin tambayoyin data masa suka shiga yawo a kwanyar ta, idan kuwa haka soyayya ne toh tabbas Daddynta son Maryama yake ba SHAK'UWA CE ba kenan soyayya ce... Girgiza kai ta soma ita kad'ai tana wani irin huci kafin ta zari mayafinta ta fice ta nufi gidan Hajiya ba tareda ta sanar da Maama Juu ba....
Zaune suke k'asar bishiyar shak'atawan Hajiya Maryama na ma Hajiya tsifa sai ganin Sajida aukayi tsgege saman kansu tana wani irin huci
Baki Hajiya ta bud'e tana kallon ikon Allah yanda ko darajar sallama basuci ba balle gaisuwa.... Jiyo muryar Maryama Hajiya tayi tanai ma Sajida sannu da zuwa.
Bata amsata ba sai fincikota da tayi tana ci gaba da huci take fad'in "Wllhi tallhi sai kin bar gidan nan, wllhi baki isa kiyi soyayya da Daddy ina raye ba..." bata kai aya ba Hajiya ta mik'e tana d'aura kwalinta take fad'in "Ke lafiya kike kuwa, tarbiyar da tambad'edd'iyar can ta soma baki kenan koh.. toh kuwa kinsan bana d'aukan rashin d'a'a sam.... Cikata kafin naci maki mutunci yanzun nan, sokuwa maras wayo da hankali..."
Kuka Sajida ta soma tana cigaba da fad'in "Hajiya wllhi dake da Daddy duk kunfi sonta, Hajiya me Daddy yake nufi da ita, soyayya suke a b'oye su duka biyun." ta juyo tana duban Maryama dake zuban hawaye taci gaba da fad'in "munafukar banza munafukar wofi kinji kunya Maryama, kuma wllhi daga ke har Daddy babban kuskuren da zaku tapka kenan don wllhi ina numfashi bai isa......." bata kai aya ba taji an d'auketa da wani wawan mari.... Gaba d'aya suka d'ago suna dubansa ba kowa bane illa Tahir.....
*Sameena Aleeyou Mrs*
💘💘💘💘💘💘💘💘
*SHAK'UWA CE*
💘💘💘💘💘💘💘💘
*33*
*©Sameena Aleeyou...✍🏼*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
_Assalam makaranta SHAK'UWA CE, ina mai baku hak'uri bisa kuskuren da aka samu a shafin da yazo kafin wannan, kamata yayi nayi numbering d'inshi *32* sai na kuma rubuta *31*. Amma dai labarin bai canza ba saidai wannan shafi zai kasance 33 sabida abin ya tafi da tsari. So Sorry for the inconvenience pls.._
*HASIYAT IMAM sak'onki ya iso min, na gode k'warai da addu'o'inki da kuma k'aunarki a gareni. Rabbi ya bar k'auna, Sameena tana sonki tsakani da Allah ❤*
Huci kawai AT keyi yana kallon Sajida disbelievingly, yaushe ta zama haka, har ita ke irin wad'annan maganganun akansa saikace sa'an wasan ta...
Tsawa ya kuma daka mata "Shige mu tafi stupid..!!!"
Rik'e da k'uncinta ta soma tafiya kaman zata fashe har lokacin hawaye bai daina zuba mata ba.
Hajiya ta bisu da kallo baki a tab'e kafin tace "Yo bakaga komai ba idan dai wancan gogeggiyar ka d'auko masu matsayin uwa.." ta dubi Maryama dake nan tsaye itama tana hawaye kana tace "Ki k'yaleni da ita idan dai tace halin wancan kod'edd'iyar ta d'auka toh kuwa ta d'auki Dala ba gamo.." ta k'arashe tana rik'e da hannun Maryama suka nufi cikin gida..
D'aki Maryama ta shige tana hawaye, toh kodai har mutane sun fahimceta son Uncle take, wannan wani irin jarabawa Allah Ya jarabceta dashi, tabbas tana son Uncle tana jin soyayyar sa har cikin jini da tsokar ta, toh wai dama hakan takan faru da mutane ko ita d'in ne dai kawai Allah Ya jarabceta da son Uncle, mutumin da yafi k'arfin ajinta nesa ba kusa ba, mutumin da ya raine ta tun tana k'arama, mutumin da ya kasance gata a gareta, sannan uwa uba mahaifi ga babban aminiyar ta, tabbas zuciyarta batayi mata adalci ba sannan batayi ma Sajida adalci ba, inama zuciya tana shawartanka kafin ta soma son abu, inama ziciyarta soyayyan wani ta kamuda ba Uncle ba.... Hawaye suka ci gaba da kwaranya mata, wannan abu ne da bazai tab'a yuwuwa ba koda a duniyar tunani ne...
***************
Hannunta ya rik'e yana fincikarta da iya k'arfinsa zuciyar sa na tafarfasa, har yanzu ya kasa yarda da kalaman da yaji Sajida 'yar cikinsa nayi a gamedashi...
Doka kira ya ringa yi ma Shema'u, ta fito babu shiri domin kuwa itama bata jima da dawowa gidan ba, yanayin da taga AT da Sajida yasa gabanta fad'uwa, ta k'araso tana tbayar lafiya..
Fuska a dake Ya dubi Shema'u yace "Daga yau ko k'ofa ban yarda ki kuma barinta ta fita ba..." daga haka saman sa ya wuce zuciyar sa naci gaba da tafarfasa..
Shema'u ta bisa da kallo cikeda mamaki kafin tayi saurin k'arasowa tayi hugging Sajida tana tambayarta me ya faru..
Sajida ta goge hawayen ta kafin ta soma fad'in "Wllhi bazai tab'a yuwu ba, wllhi na tsani Maryama kuma sai ta bar gidan Hajiya...." daga haka ta wuce ta nufi d'akinta.
Shema'u ta lek'e gabas ta lek'a yamma kafin ta nufi d'akin AT, Zaune ta samesa ya k'ura ma goran ruwa idanu, har lokacin mamakin abin yake.
Zama tayi gefensa ta kalallame kafin ta soma fad'in "My AT dukda bansan me ya faru ba kayi hak'uri kasan yara, sannan nima ban jima da dawowa ba kasan na sanar da kai zanje gidan Karima k'awata, toh na barsu a gida tareda Maama Juu bansan me ya faru ba....." Katseta yayi ta hanyar d'aga mata hannu kafin yace "Ya isa daga yau kar ki kuma barinta ta fita ko k'ofa ne, zan sami Maama Juu ma na mata magana..." ya k'arashe yana kwanciya cikin kujera had'i da lumshe idanunsa... Abunda zuciyarsa ke fad'a masa tabbas k'arya ne, babu yanda za'ayi soyayya ya shiga tsakanin sa da Maryam, SHAK'UWA CE kawai...
Shema'u ta bisa da kallo tana karantar sa.
************
A d'aki ta sami Sajida tana zaune ta had'e kanta da gwiwoyinta tana hawaye, yau kam ko takan Buzu batabi ba thought d'in Daddyn ta is in love with Maryama ya hanata sukuni.
Zama Shema'u tayi gefenta ta dafata.. Suna had'a idanu Sajida ta kuma fashewa da wani sabon kuka. Rungumeta Shema'u tayi itama tana k'ok'arin rau-rau da idanunta.
"Let it out my Sajee, yi kukanki ki sami sa'ida dukda bansan musababbin abinda ya had'aki da Daddyn ki ba, sannan Sajida bai kamata ki fita ba tareda sanin mu ba, wani abin ka iya samun ki, Daddyn ki yana sonki ne baison wani abu ya sameki... " ta k'arashe tana k'ura ma Sajida kallo babu ko k'yafta idanu.
"Aunty wllhi barin gidan nan zanyi muddin hasashe na ya tabbata, Aunty wllhi bazan iya zama inaji ina gani Maryama my childhood friend ta zama matan Daddy ba, wllhi gwamma na shiga duniya..." ta k'arashe tana kauda fuskarta gefe wasu hawayen na zubo mata.
Murmushin yak'e Shema'u tayi kafin tace "Sam kar kiga laifin mahaifinki wannan yarinya tun ba yau ba na gane k'udirinta akan mahaifin ku, amma sam banso na shiga tsakanin ku tunda naga yanda kuka d'aukesu daga ita har mahaifiyar ta, tun kafin ya tabbata soyayya suke yafi nuna kulawansa akanta fiye daku yaransa, toh mai zai faru ranar da ya auro ta matsayin mata. Wannan yarinya sam bata bar kanta yanda Allah Ya ajiyeta ba bacin haka ina ita ina soyayya da mahaifin ku, wannan yafi k'arfin cin amana ma ya zama zalunci.. Sajida ina sonku ki sani insha Allahu Daddyn ku bazai tab'a falling mata ba duk da k'warewa a salo na yaudaran ta... Oya zo nan." ta k'arashe tana mai hugging nata.
************
"Mummy pls ki daina kukan nan, kiyi hak'uri don Allah naji zan dawo, zan dawo sabida ke, Mummy don Allah kar kisa ma kanki wani ciwon pls kinji Mummy na.." Ya k'arashe muryar sa har rawa..."
"Haidar yaya bazanyi kuka ba sannan yaya bazanyi ciwo ba bayan kaima na rasa ka kaman yanda na rasa Nabila."