Sashe 43
Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajiya tayi masu k'uri tana kallon ikon Allah yanda Jarka ke warware k'aton buhu wai ita za'a danna kanta ciki, jakar uba!
Bud'e murya tayi zatayi ihu IK ya daka mata tsawa kana yace "Kika kuma yin fit sai na fasa kanki da bakin bindiga...." Dai-dai lokacin Spider ya fito da Maryama daketa faman tarjewa.... Wani mayen kallo Oga IK ya bita dashi...
Haka kurum yaji gabansa ya yanke ya fad'i, ji yayi bai yarda da mutanen da ya gansu layin su Hajiya ba, cikin sauri ya juya kan motar sa ya koma...
Kasancewa sautin injuna sun cika unguwar don babu wutan lantarki yasa baza'a iya sauraren draman dasu Hajiya keyi dasu Spider ba.... Kokawa suke kan faman sha da Hajiya tana kare Maryama da tuni Jarka ya fincike hijabin jikinta. Hajiya fad'i take, "Idan kud'i kuka zo nema sai mu baku 'yankunnayen mu da sark'ok'in mu amma ahir d'inku kuyi tunanin tab'a lafiyar d'iyata."
Oga IK ya fashe da wata kafiran dariya, domin kuwa k'arfin halin tsohuwar ya basa mamaki. Tsawa ya kuma daka masu daga ita har Maryamar dake b'oye a bayanta tana kuka yace "Ke kinada kud'in da har zamu shigo sata ne, umarni muka zo cikawa don haka karki damu an riga an biya mu...." Ya k'arashe yana k'ok'arin finciko Maryam Hajiya na janyeta, Spider na k'ok'arin janyo wuyar Hajiya ta d'ago k'afarta ta hagu ta sai kai masa harbi take still tak'i sakin Maryama.
Mamaki ya cika Ashfaq ganin Ilu a d'aure da sunkuceciyar igiya a k'ofar d'akinsa ga bakinsa rufe da wata tsummar... Cikin tashin hankali ya shiga kwance d'aurin da akama Ilu, ai yana gama kwancesa Ilu ya soma fad'in "Meke faruwa..?" Ilu sai haki yake yana nuna masa cikin gida ya kasa furta komai, duk yayi fitsari a jikinsa sabida tsabagen tsoro... Ai a tamanin Ashfaq ya nufi cikin gidan..
Nan ya tarar Spider sai kokawan tura kan Hajiya cikin buhu yake, ga Maryama k'artan maza har biyu suna kokawan rabata da suturan dake jikinta...
Ai take yayi wata tsalle ya cakumo IK ya soma kai masa naushi, shiko Jarka bai fasa k'udirinsa akan Maryama ba, Spider tuni ya tura kan Hajiya cikin buhu sai shure-shure take tana fad'in "Keenafas ci uwar su...." dama taga shigowar Ashfaq a birkice...
Hannu tasa ta lalumo dutsen da take daka goro a bayan k'yaure aiko nan ta zage k'arfinta ta sauk'e ma Spider kan k'afarsa.... Ya saki wata k'aran azaba, a tamanin ya saki kan Hajiya yana rik'e da k'afarsa da aka dandantsa...
Hajiya tayi k'ok'arin ciro kanta cikin buhun... Ashfaq ya sami daman k'watar bindigar IK nan ya soma pointing nasu dashi, suka soma jada baya....
Ai tuni Spider ya soma k'ok'arin rarrafe da niyar barin parlorn, saidai Hajiya a ankare take dashi, gyara d'aurin zaninta tayi tana fad'in "Ai baka isa gudu ba sai ka fad'i uban da ya turo ka... Ta shiga janyo k'afarsa yana k'ok'arin k'wacewa, dama veranda d'inta akwai buhuhunan shinkafa na Zakkan gona Spider ya shiga kama buhun dake can k'asa yana son tsira, aiko nan buhanen suka shiga runtumo masa d'aya bayan d'aya, Hajiya tayi baya a tamanin.... Hakan yabawa su IK daman tserewa babu shiri... Ashfaq ya bisu a guje saidai inaa, tuni sun tsere...
Shiko Spider tamkar maras numfashi haka ya koma, wayar AT Ashfaq ya shiga kira yana mai duba Spider ko yana numfashi abinka da likita...
Maryama kam can k'uryar parlron ta tak'ure tana kuka har lokacin tsoro bai bar jikinta ba...
*************
Sam AT bai razana da ganin kiran Ashfaq da dare ba tunda yasan k'ila a hospital ne ake neman wani abin.. Jin wani zance na daban daga bakin Ashfaq yasa sa mik'ewa zumbur babu shiri yana karanto innalillahi wa inna ilaihirraji'un..
Shema'u ta mik'e a birkice tana tambayar sa lafiya..? Fuskarta fal damuwa cikin zuciyarta kuwa fal murna ne, don a zaton ta su Spider sun cika mata aikin da ta saka su ne....
K'arasa closet AT yayi bai ko sami zarafin amsata ba, still waya manne a kunnensa yake fad'in "Okay Ashfaq I'll be right there, ka kula min da Hajiya da Maryama, make sure they are safe..." Daga haka katse wayar yayi ya zari jallabiyar sa ya kwab'e inner white d'in dake jikinsa ya zura jallabiyar...
Gaban Shema'u fah ya yanke ya fad'i, saurin mik'ewa tayi tasha gabansa tana tambayarsa me ya sami Hajiyan..?
Kafad'unta ya d'an rik'e kana yace "zan maki bayani idan na dawo, inaga b'arayi ne suka shiga gidan Hajiya, amma Allah ya taimaka Ashfaq yana can basu masu komai ba, and guda d'aya is unconscious yana can gidan Hajiya d'in sauran sun gudu... Ki kula da kanki da yara..." Daga haka ya fice cikin sauri.
Ai gaba d'aya Shema'u bata fahimci me yake fad'i ba, kenan shirinta ya rushe, kenan Hajiya da Maryama suna nan lafiya, jar uba...! Kai ina da sakel, bama wannan ba an kama guda d'aya kenan, asirinta na shirin bankad'uwa kenan.. Ita kad'ai ta shiga girgiza kai ta soma sambatu tana fad'in "Wllhi k'arya kenan, ni Shema'u nafi k'arfin asirina ya tonu, ban fito ba saida na shirya, wllhi babu wanda ya isa yaja dani..." ta shiga muzurai tana zagaye d'akin tana k'aran takaici, barbaza gashin kanta tayi tana huci. Abubuwa suna neman kwance mata, meyasa duk sanda ta shirya wani abu sai ya ruguje, meyasa yanzu take rasa sa'a kaman da..? Zuciyarta ta shiga shaida mata sabida kin bar mutane da yawa suna rab'arsu, "Ashfaq" ta furta a hankali, ta tuna shine mutumin da ya kub'uto da Sajida daga hannun Buzu gashi yanzu ya kub'utar dasu Hajiya da Maryama, tabbas babu haufi shine tunda ranar da ya kawo aika ma AT tana jinsa da Sajida sai zolayarta yake ita kuma tana basarwa sannan Hisham ya bata labarin yanda Ashfaq yake ruguza masa duk wani shirinsa na cutar da AT a asibiti, a da taji dad'in taimakon AT da yake don guje ma sharrin Hisham amma a yanzu battle d'inta dashi zai soma, muddin Ashfaq na jikin AT she won't succeed, she really need to get rid of him before he causes hell for her... Fuzar da iska tayi idanunta suka kad'a sukayi jazir, fuskar Ashfaq kawai take hangowa...
*******
Sanda ya isa tuni Ashfaq ya kira 'yansanda sun wuce da Spider asibiti, Hajiya na gefe tana lallashin Maryama AT yayi sallama ya shigo Ilu na biye dashi na basa ba'asi saika rantse wani abin kirki ya tab'uka.
A rud'e ya k'araso ya durk'usa gaban Maryama yana tambayar ta "Did they hurt you? Sun maki wani abu,...?" gaba d'aya Hajiya wangale baki tayi tana kallon yanda Attahiru ya susuce akan Maryama..
Girgiza masa kai kurum Maryama keyi alamun babu abinda ya sameta. AT kuwa ji yake kaman ya rungumeta ko zaiji sanyi cikin zuciyarsa sosai kukan nata yake tab'a masa zuciya.... D'aki Hajiya ta kaita kafin ta dawo parlorn suna tattauna lamarin da AT.
Hankalinsa ya kuma tashi jin abinda ya kawo b'arayin bama sata bane, shi kad'ai yake tsuma yana jin dukda basu cimma burinsu akan Maryama ba, runtse idanunsa yayi yana tuna dole sun tab'a mata jiki da k'azantattun hannayen su... Fuzar da iska yayi ya mik'e ya dubi Hajiya yace "Hajiya barinje asibitin nan, sai ya fad'i waye ya turosa...." Daga haka ficewa yayi zuciyarsa naci gaba da tafarfasa. Hajiya kuwa tai masa addu'an kariya da samun nasara. Sosai take mamakin ganin yanda hankalin AT yayi mugun tashi..
*Sameena Aleeyou Mrs*
[9:21PM, 3/21/2018] +234 703 300 1537: 💘💘💘💘💘💘💘💘
*SHAK'UWA CE*
💘💘💘💘💘💘💘💘
*35*
*©Sameena Aleeyou...✍🏼*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*HBD My Little Miss AKA Firdausi Abdullahi, Ubangiji ya Albarkaci rayuwarki 😘❤*
Tunda ya karyo kwanar unguwar su yasha mamakin ganin motar AT na fitowa daga layin, daga can k'ofar gate d'in Hajiya kuwa Ilu ne sai faman lek'e-lek'e take.
Ai Buzu na k'arasowa a guje Ilu ya koma cikin gida ya turo k'ofa yana k'ok'arin gark'ama sakata yake karanto addu'an shiga band'aki.... Jin haka yasa Hajiya fitowa cikin sauri domin gaba d'aya Ilu muryar sa ya bud'e yana karanto addu'ar ida alola da ta shiga band'aki....
Hajiya tana tambayarsa lafiya..? Inaa fad'in yake "Sun kuma Hajiya, aradu sun kuma dawowa..
Sosai abun ya bawa Buzu dariya yana mai ci gaba da bugun gate d'in yana fad'in "Ni ne Ilu, Haris Buzu ne..."
Hajiya ta watsa wa Ilu harara kana tace "Kauce min dalla naga alama kaikam dai maza ka rako...."
Hajiya ta bud'e k'aramar k'ofar Haris ya shigo yana gimste dariyar sa.
"Harisu ina ka fito talatainin daren nan...?"
Hajiya ta tambaya tana d'aura hannaye k'asan k'irjinta..
"Hajiya hayaniya naji shiyasani fitowa.." Cewar Buzu dake danno kai cikin gidan.
"Kai ashema kaine, ai wllhi na zaci b'arayin nan ne suka dawo da na shayar dasu mamaki, aradun Allah sandar shad'ita ta gado zan d'au....." Bai kai aya ba Hajiya da ta sake baki tana kallonsa tace "Rufe min baki, saikace gaskiya, aikin da ka iya kenan cika baki uwa d'an marok'i, inji yanzu ka canza kayan fitsarin naka, kai wannan inaga gidan gona ya kamaceka sam bakada saiti..."
Ilu ya wage hak'wara uwa gonar auduga yana dariya yake fad'in s"Hajjaju namu wanda sukaje Madina suka gaida Manzo ai idan babu mu bakwa iya zaman unguwar ba, muna nan dai mutu ka raba, Dapta yayi iya yinsa ya hak'ura...."
"Kai tafi can da Alla..." Hajiya ta katse sa.
Buzu ya gaida Hajiya kafin ya soma jajanta lamarin, Hajiya ta kwashe labari tsaf ta basa. Gabansa ya yanke ya fad'i, ba kowa ya fad'o ransa ba illa Shema'u, that witch zatayi abinda yafi haka. D'an kintsa kansa yayi kafin yace "Hajiya Maryama fah, da fatan tana lafiya..?"