← Book details Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 65

Sashe 19

Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sajida tana hangosu ta tafi da sauri tana welcoming nasu had'i da basu wajen zama. Su Jamal tuni sun d'ale kan seats sun zazzauna. Shema'u ta wani juya idanu had'i da mik'ewa kafin ta shiga gyara ma Sajida zaman hular nata, with that fake smile on her face, fad'i take "Sweetheart I'm proud of you, kinyi kyau."

Sajida ta murmusa kafin tace "Aunty naji dad'i kinzo,.... Amma ina kuka baro Daddy.?"

Saida Shema'u ta d'an saci kallon su Jamal da hankulansu yafi karkata wajen d'alibai masu Cultural Dance sunyi shiga k'abila daban-daban kana tace "Baby you know your Dad when it comes that social climber,.... Uhm sorry nasan dai k'awarki ce kin d'auketa 'yar uwa, I just couldn't stand her ne, haba Daddyn ku fah har mun iso nan dashi kawai Hajiya ta masa waya ta ringa salle shi da masifa wai Maryama bata taho ba, babu yanda Daddyn ku baiyi ba ta hawo ko adaidaita ne ko taxi ta taho shi zai biya kud'in amma fir tak'i wai saidai shi yaje ya kawota, hmm Sweetheart I'm afraid she's stealing your Dad away from you... Amma kar ki damu kinada ni, bazan tab'a barinta tayi succeeding ba."

Tuni idanu Sajida ya soma kawo ruwa domin kuwa ana iya kiranta karb'an kyauta a koda yaushe, gashi tasha burin mahaifinta ya gani ya rakata su karb'a tare. Ganin haka yasa Shema'u saurin rungumota kafin tace "Oh no My Sajee, kinsan bana son ganin ki cikin damuwa, this is your Day, don't let anything ruin it for you, besides mu munzo ai, gani ga Siblings d'inki, we're all here for you sweetheart."

Gyad'a kai Sajida tayi kafin tace "Aunty what if aka kirani karb'an kyauta babu Daddy, Aunty babu Mummy na sannan shima baya nan, wa zai raka ni amsar kyautan.?"

Hannayen ta Shema'u ta rik'e cike da kissa kafin tace "My Sajee ni zan raka ki karb'a kar ki damu, I'm here, I'm here for you sweetheart, karma ki b'ata ranki kinji, oya koma seat d'inki, nida su Jamal zamu raka ki gaba d'aya da zaran an kiraki." Haka Shema'u ta ringa calming Sajida da makirci har ta yarda ta koma wajen zamanta, amma zuciyarta fam yake da haushin Mahaifin ta da Maryama.

*****************

Kasa ci gaba da abinda take tayi, gaba d'aya sai ta tsinci kanta da jin nauyin sa. A hankali ta juyo idanunta naga k'asa take fad'in "Sannu da zuwa Uncle."

Har lokacin murmushi bai gushe saman kyakkyawan fuskar sa ba, d'an takowa yayi yana mai karantar yanayin ta kafin ya amsa mata gaisuwar ta Ya k'arada "Congratulations, Allah Ya sanya Albarka."

D'an murmushi ta kuma yi kafin tace "Ameen, na gode Uncle." Kasa cewa komai sukayi daga ita har shi kowa da abinda yake sak'awa a zuciyar sa.

Ita dai Maryama nauyinsa take ji, yayinda AT ya rasa meke faruwa dashi a Al'amarin Maryama.... Hajiya ce ta k'araso cikin cancatewar ta leshi mai jida kyau da tsada, abinka da farar fata sai tayi kyau sosai, yanyin jikinta AT ya d'auko sam jikinsu bai nuna tsufa. Takowa take tana fad'in "A'a Attahiru har ka iso d'in ne, ai sai muyi mu tafi kar mu kuma lattti ko." ta k'arashe tana gyara d'aurin kwalinta jikin madubin window.... Ba Maryama kawai ba harta AT saida Hajiya ta basa dariya yanda take karkata d'aurin kwali.

D'an durk'usawa yayi kafin ya gaidata, Hajiya kam hankalinta fa sam naga cancad'a d'auri take amsa ma AT gaisuwar sa.

"Hajiya kema zaki bukin yayen ne." Ya tambaya sanda ya mik'e tsaye.

Karkatowa tayi ta dubesa da kyau kafin tace " Attahiru wuce mu tafi babu lokaci, bana son dogon zance, yo kaima kaje balle ni."

Maryama kam tuni ta shige ta d'auko graduation gown d'inta da d'an hulan.

AT da Hajiya suka k'arasa yanda ya paka motar sa. Daga can yake hangota yanda tayi kyau sosai, ta d'an nad'e wuyar ta da farin Vail, sosai rigar bukin yayen nasu ya mata kyau. Tana shiga AT ya tada mota suka wuce.

***************

Shema'u dai sam hankalinta baya jikinta, burinta kawai taga b'ullowan AT da wannan tsinanniyar yarinyar.

Nan aka soma kiran d'alibai ana basu kyaututtuka da kuma testimonial d'insu na kammala sakandare. Anata kiran d'alibai d'aya bayan d'aya har aka iso kan Sajida.

Shema'u ta rik'o hannun su Jamal da Ni'ima suka nufi Stage gaba d'aya harda Sajidar daketa faman kallon k'ofar hall d'in ko Daddyn ta zai shigo shiru. Haka ta karb'i takardan shaidan k'arasa karatun ta na sakandare da kuma kyaututtukan ta babu Daddyn ta, k'walla da takaici tab suka taru mata, Shema'u sai karantar ta take tana jin dad'i.

Sanda su AT suka shigo Hall d'in dai-dai lokacin aka soma kiran Maryama ta karb'i nata ktaututtukan a matsayin ta na d'alibar da tafi ko wani d'alibi k'wazo....

Ana kiranta daga can baya ta d'aga hannu ta amsa, gaba d'aya Hall aka juyo ana duban su daga can yanda suke tsaye a bakin k'ofa.

Babu abinda yafi k'ona ran Shema'u kaman yanda taga hulan Maryama a hannun AT, wato ma shi ya rik'e mata. Sajida kuwa babu abinda yafi k'ona ranta kaman yanda taga Daddynta da Hajiya sun d'unguma sun raka Maryama karb'an kyaututtukan ta, sai hotuna ake masu don babu shakka ta amshi kyaututtuka masu yawa, Jamal ma ya rik'o hannun Ni'ima suka kutsa anayin hotunan dasu, AT ya kasa rufe baki, nan ya d'auki Ni'ima ya rik'e a kafad'an sa yayinda Maryama ta kamo hannun Jamal aka masu hoton, Hajiya na gefe ta cakare... Lol.

Su Fadila kuwa sai fad'i suke sunyi kyau, banda hararansu babu abinda Sajida take, Shema'u kuwa sai karantar ta take, a hankali ta sid'ad'e ta fice ta wani k'ofar dake gefe da ita kad'an.

Wayar ta ta ciro ta latsa bugu biyu ya d'aga.

"Hello kana jina, yanzu zata fito, kayi duk yanda zakayi ku bangaji juna, ka gane ai, I don't have to remind you." daga haka katse wayar tayi kafin ta dawo cikin hall d'in ta k'arasa yanda Sajida ke zaune can baya tana hawaye. Ta zauna had'i da dafata kafin ta kai dubanta ga AT dake faman gaisawa da manyan mutane irinsu Deputy Governor su Speaker State House of Assembly.

Sajida ta d'ago tana dubanta kafin tace "Aunty ki gani fah ko nemata basuyi ba, wllhi na tsane su."

Shema'u ta dafi kafad'unta cike kissa kafin tace "Kar ki tsane su, wancan makiran zaki tsana, ita ta rabaki da kakar ki sannan tana k'ok'arin rabaki da Baban ki, amma ta Allah ba tata ba, Allah yaga zuciyarki baki rik'eta da komai ba sai alkhairi ita kuma ta maki halin 'yan adam butulu. Yanzu abinda nake so dake, kar ki nuna ma Daddyn ki komai, ki tashi kije waje kiyi refreshing don karma su gane kuka kikayi, they might be thinking you're jealous of Maryama tunda ta fiki yawan kyauta , especially Hajiya. Sannan da yamma I've a surprise for you." ta k'arashe tana wani murmushi.

Gyad'a mata kai tayi kafin ta mik'e ta fice.

Hajiya tana zaune tareda su Jamal sai raba masu snacks da drinks ake.

Maryama kuwa sai tambayan su Fadila take ina suka gano Sajida. Fadila ta tab'e baki tace "Ask me again, ni ina ruwana nasan yanda taje, k'ila tana wajen wannan Antin nata mai k'irar aljanai." sauran k'awayen sai dariya suke, Maryama kuwa b'ata fuska tayi. Fadila ta tab'e baki tace "Na you Sabi, ta dubi camera man tace "Ci gaba da d'aukar mu. Maryama ta sauk'e mata dundun wasa tace "Zaki sani ne."

"Eh d'in na sanin, kunfi kusa keda ita, nikam ba k'yaleta zanyi ba kin sani." Cewar Fadila.

Fitowar ta kenan tana faman share hawayen ta taji ta bangaji mutum, saurin d'agowa tayi da niyan masifa don dama a wuya take. Fuskar da tayi tozali dashine ya hanata furta koda kalma, Cak ta tsaya tana bunsa da kallo.

Durk'usawa yayi ya d'ago mata hanki d'inta da ya fad'i k'asa ya karkad'e kafin ya mik'a mata yana murmushi mai kashe 'yan mata da manyan mata yace "Sorry pls, kiyi hak'uri it wasn't intentional..."

Bata san sanda murmushi ya kufce mata ba, cikin sauri ta shiga girgiza kai tana fad'in "Kar ka damu babu komai."

Buzu ya murmusa kafin yace "Are you sure.?"

Bata sami zarafin amsa masa ba sabida tsaban k'warjinin sa da ya cika idanunta sai gyad'a masa kai tayi alamun eh.

"Kaman na gane fuskar ki." ya fad'i yana k'ura mata idanu.

D'an murmushi tayi kafin tace "A gidan Hajiya koh."

"Exactly." ya fad'i yana mai fad'ad'a murmushin sa had'i da shafa kwantaceccen bak'in sumar sa.

"Congratulations, ashe kema harda ke cikin d'aliban da ake yayewan."

D'an murmushi tayi wanda yafi kama da yak'e kafin tace "Na gode, ka k'arasa ciki, Maryama na ciki, inace wajenta ka zo."

D'an jim yayi kafin yace "No ai banma san tana candy yau ba, don ba ita ta gayyace ni ba, wata cousin d'ita ce nazo mata, kuma mun had'u har munyi pics.... Amma ya na ganki haka, yau ranar farin cikin ki ne kina looking sad, lafiya dai koh..? "

Kasa ce masa komai tayi, sai kallon sa a fuzge da tayi.

D'an gyara tsayuwar sa yayi ya shafi sajen sa kafin yace "Kiyi hak'uri idan na maki tambayan da baki so bane, or maybe na shiga hurumin da ba nawa ba, I'm only concerned about you ne, a beautiful girl like you fushi bai kamace ta ba.." Cikin siga mai cike da jan hankali yayi maganar.

D'ago kai Sajida tayi tana mai tambayan kanta _Did I hear him right, ya kirani Beautiful._..... Ganin tayi sakare tana kallonsa yasa shi sakin wata murmushi kafin yace "Miss Beauriful idan bazaki damu ba mu k'arasa k'asan bishiyar can, inada muhimmiyar magana da nakeso muyi. "

Daga yanda take zaune ta hangesu d'aga masa babban yatsa tayi alamun jinjina, ganin Sajida tabi bayansa kaman rak'umi da akala.

Saurin mik'ewa Shema'u tayi ta lab'e a wani k'ofa don tasan idan su AT basu ganta ba zasuyi tunanin tana tareda Sajida don Karma su nemeta, dad'in da taji AT manyan mutanen nan sun hanasa barin wajen su, Hajiya kuwa tana tareda jikokin ta, Maryama kuwa su Fadila bazasu barta ta fita neman Sajida ba tunda sunsan da gangan ta taho ta bar Maryaman.
Chapter 19 · 0% Book details