← Book details Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 65

Sashe 36

Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Meye haka, ko ajiya kayi ne a ciki, inyi.." ta fad'i tana watsa masa kallo.

Komawa yayi ya zauna baice komai ba, uwa maraya.

Ta mik'e tana ci gaba da sababi tana fad'in "Banda bak'in gulma da munafunci ka baro amaryar taka kazo kana neman abin kari a nan,
ai sai kaje amaryar ta dafa maka ruwan shayin wannan kam k'walelen ka ehe.."

Tagumi ya rapka uwa wanda akai ma mutuwa.

*************

Da lalaume ta soma sai faman shafa gado take tana son rungomo angon nata, saidai fah wayam taji babu ango babu dalilin sa, ta mik'e a zabure ta nufi bathroom nan ma baya nan, parlor ta nufo nan ma sammakal, bak'in ciki ya taru ya turnuk'e mata mak'oshi, harga Allah da matsanancin buk'atar AT ta kwana gashi bata sami yanda take so ba, babban abinda yafi d'aga mata hankali shine kardai ace Office ya fice ranar amarcin su, Shema'u fah ta cika tayi fam... For the first time data soma neman abu bata samu yanda take so ba, itafah so na hak'ik'a take so AT ya nuna mata, a ajiye maganar wad'annan shegun yaran nasa don ita ba domin su ta auresa ba ma kanta tayi tanadin sa, sai faman girgiza take ita kad'ai tana huci, wayarta ta rarumo ta shiga neman layin Hisham don shine kawai zai gaya mata ina AT ya tafi da uwar safiyan nan, tasan bazai wuce yana office ba.

Yana ganin wayarta saida yayi wata kafiran dariya kafin ya d'aga..

"Amarya kinsha mai..." ya fad'i yana murmusawa.

Tsaki Shema'u ta buga sabida takaici kafin tace "Ina Ahmad.?"

"A'ah yaya zaki min wannan tambayar keda kuka kwana tare.."

Tsaki ta kuma yi kafin tace "Hisham ka fad'a min idan AT office ya taho.."

Hisham yayi dariya kafin yace "Shege AT salihi mai ra'ayi kikeji, wllhi bai taho office ba, amma nasan idan dai bashi a gida toh gidan Hajiya ya tafi..." bai kai aya ba ta katse wayar tana tururri,

Kai ina da sakel, bazai yuwu tayi sharing AT da kowa ba, AT nata ne, ya kamata tayi taking next step akan gina soyayyar ta a zuciyar AT da kuma raba Hajiya da AT, tana nan tsaye tana huci ta jiyo kukan Ni'ima a parlor tana neman Daddyn ta.. Wani uban tsaki ta buga kafin ta nufo parlorn a fusace, kafiran tsawa ta daka mata wanda ya sata had'iye kukan babu shiri ta shiga matsawa da baya cikeda tsoro.

Tuni Sajida ta nufo parlorn sabida ta jiyo kukan Ni'ima, Shema'u tayi saurin k'arasawa ta d'auki Ni'ima dake faman shan zuciya tana jijjigata take fad'in "Sorry Baby Daddy gidan Hajiya ya tafi, bari yanzu zan kaiki ki gansa ko, yi shiru Baby na, zaki je Daddy..?" Ni'ima tayi saurin gyad'a kai alamun Eh..

Sajida sai murmushi take ta k'araso tana gaida Auntyn nata tana fad'in "Iyye Ni'ima 'yar gatan Daddy da Aunty.."

Shema'u ta kuma rungume Ni'ima dake k'ok'arin k'watan kanta, ta saci kallon Sajida ta zare ma Ni'ima idanu tuni yarinyar ta lafe a jikin Shema'u,

"K'warai kuwa 'yar gatan mu ne 'yar auta ba yanzu ma kuwa zan kaita Daddy..." Sajida dai dariya tayi cikeda jin dad'i...

**********

Tausayin sa ya cikata domin kuwa sai lek'en sa take ta labule, wannan shiri nasa tasan k'ila office zai wuce tunda ya fito da sassafe, gaskiya bazata iya barinsa ya tafi aiki haka da yunwa ba, daurewa tayi ta mik'e ta zura hijabinta kafin ta fito parlorn..

Idanunsa naga wayar salulan sa amma jikinsa ya basa ta fito parlorn, d'ago kai yayi suna duban juna....

*Sameena Aleeyou Mrs*

[6:53AM, 3/13/2018] ‪+234 803 315 3757‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘

*SHAK'UWA CE*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*29*

*©Sameena Aleeyou...✍🏼*

_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝_

*ZAUREN BIEBEE ISA (ZBI) ina yinku ina k'aunarku da zuciya guda, and this spectacular chapter is yours guys 💘 aradu kuyi yanda kuke so dashi amma banda tsinema Amaryar Attahirun Hajiya hilis 😹❤*

Sauk'e idanunta tayi don harga Allah Ya bata tausayi yanda taga fatarsa tayi rod'i-rod'in ja, kenan bashida lafiya...

"Ammm me za'a kawo maka uncle.?" ta tambaya tana wasa da 'yan yatsun hannunta. Shikam AT sosai ta burgesa dukda yaji Hajiya tana fad'in batada lafiya hakan bai hanata fitowa nema masa abinda zaici ba, lallai SHAK'UWAR SU da Maryama daga Allah ne.

Murmushi ya sakar mata kafin yace "Ba naji Hajiya na cewa bakida lafiya ba, kar ki damu jeki kwanta abinki kinji..."

Gabanta ya yanke ya fad'i shikenan yaji maganganun Hajiya, wayyo Allahn ta, wani sabon kunyarsa ya sauk'o mata. AT na hankalce da ita yanda ta tsaya uwa dogariya ta kasa gaba ta kasa baya, ya gane kunyar sa taji. D'an gyaran murya yayi kafin ya kuma cewa "just go and rest kinji..."

Tayi k'ok'arin saita kanta kana tace "Ai na warke ma bari na kawo maka shayin." Bata jira amsar ba ta soma tafiya...

Bud'e murya ya d'anyi ya ambato sunanta. Cak ta tsaya had'i da komowa ta rusunar da kanta...

AT yaci gaba da fad'in "Kin gane just black tea with honey zaki kawo min.." Gyad'a masa kai tayi kafin ta shige....

Hajiya da mai masu d'an aikace-aikace na gida ta samu a kitchen d'in sai hira suke wanda akasarin hiran maganar auren AT ya shafa. Maryama bata bi ta kansu ba ta shiga k'ok'arin had'a shayin Uncle...

Hajiya na hankalce da ita, karkatowa tayi tana dubanta yanda taci magani sabida tsaro tasan ba k'aramin aikin Hajiya bane ta hanata had'a masa shayin...

Aiko bata gama tunanin hakan ba Hajiya ta katse ta da fad'in "Uwar me ya fito dake kike wani k'ok'arin had'a masa shayi keda bakida lafiya inyi...?"

Maryama dai bata amsa ta ba baki a ture take gudanar da aikin nata... Fizge mug d'in Hajiya tayi ta soma sababi tana fad'in "Bazaki had'a masa ba, banda shegen gulma da iyayi ya wani kwaso k'afa jiki duk a daddauje wayasan uwar me su Kulu suka shafe shi dashi fatar sa ta koma haka, uwar me ya hana matar tasa had'a masa inyi..."

Tana soma magana muryarta ya soma rawa sai kuka.. " Ni dai wllhi Hajiya sai na had'a masa, haba haba bakijin tausayin sa ne, bashida lafiya fah, fisabilillahi Hajiya idan baizo gidanki ba gidan wa zaije shi, wllhi gaba d'aya kin daina tausayin Uncle...."

Daga Hajiya har Baaba pause sukayi suna kallon Maryama data dage harda kukan ta, shi kansa AT d'in lab'e yake yana lek'en su, dad'i ne yaji ya mamaye illahirin zuciyar sa ganin yanda Maryama take kare shi a wajen Hajiya, saidai a wani b'angare na zuciyar nasa yana jin zafin zuban hawayen nata...

Hab'a ta kame tana dubanta kafin tace "Tooh.!!! Eh ina ganin salo ni Fad'ima, idan baka mutu ba kasha kallo, toh yayi, daina b'ata hawayen ki idan dai tausayin Attahiru kikeji kin d'auko aiki ma kanki tunda shi ba tausayin kansa yake ba, da ace yana tausayin kansa da bai soma yunk'urin auren d'iyar Kulu ba, maza had'a masa ai kunfi kusa.." Baaba dai sai dariyar su take, idan kana gidan Hajiya bakayi hawan jini ba.

Ganin ta kusan k'arasa had'awa yasa sa saurin dawowa parlor yayi zaman sa...

Da sallama ta shigo ta ajiye masa k'aramar parantin a gaban sa. Sannu yayi mata had'i da godiya, zata shige d'aki ya kuma kiran sunanta, komowa tayi ta zauna daga can gefe still idanunta a k'asa.

"Yaya jikin naki..?" ya tambaya yana juya teaspoon cikin mug.

A hankali cikeda kunya ta furta "Naji sauk'i.."

D'agowa yayi ya dubeta ba tareda ya furta komai ba kafin ya soma kurb'an shayin.. Har ta cire rai bazai kuma cewa komai ba ta kuma jiyo muryar sa yana fad'in "Dama haka ne yake maki every month.?"

Wayyo Allahnta haba Uncle shi meyasa ya faye tambaya ne, ko duka likiticin haka suke... Ta fad'i cikin zuciyarta... Shigowar Hajiya ne ya cece ta bata amsa tambayar ba...

Tahir saida ya kusan k'warewa jin Hajiya ta shigo, ta dubesa tayi k'wafa. Shiko sai sansan da kai yake uwa munafuki, tashan NTA yake kallo program d'in da ake da sanyin safiya wato _good morning Nigeria_ . Hajiya ta d'auki remote saman hannun kujera ta shiga canza tasha kawai don ta bak'anta ma AT, har ransa yake son Hajiyar sa, gaba gad'i take lamranta.... Maryama ta k'unshe dariyar ta ta silale d'aki tana satan kallon AT dake faman sipping shayinsa, yanayi yana satan kallon Hajiya yanda take dangwala remote control d'in da k'arfi tana manna sa jikin decoder d'in uwa zata shige ciki, magana ne bai kuma isa yayi ba...

**********

Saman chaise lounge ta ajiye Ni'ima dake faman shan zuciya alamun taci kuka, bushesshun hawaye kwance saman fuskar yarinyar abin tausayi. Ta gama fente-fenten da zatayi a fuskar nata uwa zabo bakin nan yasha jan janbaki sosai tayi kama da tsoffin kilaki, tana shafa powder ta juyo ta watsa ma Ni'ima wani kafirin kallo ganin yanda taketa shan zuciya... Tuni yarinyar ta had'iyi d'an sauran kukan da take..

Wayarta ne ya soma ringing ta k'arasa ta d'aga, ganin Hisham ne ya sata shigewa bathroom bayan ta bud'e murya tace ma Ni'ima "Idan kika fita sai na yanka ki da Knife, ai kinsan Knife koh..?" Ni'ima ta gyad'a kai cikeda tsoro. Shema'u tayi murmushi mai firgitarwa kafin ta gyad'a kai tace "Good, you stay right there kinji koh..." ta kuma nodding kan nata a tsorace.

"Hello ya iso office d'in ne.?" ta tambaya tana muzurai.

Fashewa da dariya Hisham yayi kafin yace "Iska na wahal da mai kayan kara, ke wai ya akayi haka ne, tell me what really happened last night." ya k'arashe yana wata ja'iran murmushi.

Tsaki Shema'u tayi kafin tace "You stay out of this Hisham, sirrina da mijina zan fad'a maka ko me kake nufi iyi.."

Dariya Hisham yayi ya wani shafi hab'arsa kaman tana ganin sa kafin yace "Ai nafi mijin naki sanin sirrinki, don't forget we are allied..."

Gajeren murmushi tayi kafin tace "Kana b'ata min lokaci, gidan uwar sa na nufa zan dawo dashi don yau ranata ce bazan sharing da kowa ba.."
Chapter 36 · 0% Book details