← Book details Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 65

Sashe 28

Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Takaicin Hajiya ya cika AT, yasan Hajiya ba kasafai take yarda da mutane ba amma yasha mamakin yanda lokaci guda ta aminta da Ashfaq,... Ashfaq ya katse masa tunanin nasa da fad'in "Ya Dr ni zan wuce, Allah ya bamu alkhairi."

Mik'ewa AT yayi yana zura wayarsa a aljihun gaban riga sannan yace "I'll walk you out.."

Tare suka jera suka fito bayan Ashfaq da Hajiya sunyi sallama.

Har wajen motar Ashfaq suka k'arasa, sosai Ashfaq ya sha jinin jikinsa ganin yanyin AT d'in.

AT ya dafe jikin motar suna facing juna shida Ashfaq idanunsa naga wani b'angaren ya soma fad'in "Emm Ashfaq, you shouldn't have bothered buying presents for Maryam in the first place, amma tunda kayi, pls this should be the first and the last, banaso kai ko ita wani idea ya soma shiga kwanyar ku, kaga Maryama is still young, and kai kuma tamkar k'ani na d'auke ka, so pls banson wani abunda zai kawo mana sab'ani nida kai, pls ka kiyaye."

Cikeda mamaki Ashfaq ke duban AT, d'an k'ak'aro murmushi yayi kafin yace "Insha Allah zan kiyaye Ya Dr, kayi hak'uri, inajin Maryam tamkar k'anwata ta jini ne shiyasa na kawo mata kyautan, amma insha Allah za'a kiyaye."

AT ya gyad'a kansa kafin yace "Good, kana iya tafiya, I'll see you tomorrow...."

Ashfaq ya kuma mik'a masa hannu sukayi masbaha had'i da sallama kafin ya wuce.

K'uri AT yayima Hajiya tana bud'e kyautar tana fad'in "Ah'ah d'iyar tawa fah farin jini ne da ita, daga gama makarantar ta ta soma amsar kyaututtukan samari, wannan yaro da ganin toshi ya kawo..."

Hajiya tana mik'ewa ya shiga tattara kayan rai b'ace....

"A'ah kai menene haka nan, ina zaka da kayan.?" ta tambaya tana k'arasowa.

"Haba Hajiya, kan wani dalili zaki amsa kyautar sa, mayar masa zanyi don bata buk'ata, idanma da wani manufa ya kawo mata ba aure zatayi yanzu ba karatu za......" Fuzge ledar Hajiya tayi tana watsa masa mugun kallo sannan tace "Toh malgofak uban 'yan boko, wai kai lafiyan ka Attahiru, yo idan batayi aure ba zama zatata yi, wllhi ka bud'e kunnuwan ka da kyau kaji yau d'iyata ta sami mijin aure aurarta zanyi, ai da biyu na amshi kyautar, sarai naga yanayinka tun shigowar Ashafak baka so ba, Kai duk wanda ya nuna damuwarsa akan Maryama idan dai na miji ne saika nuna baka so, kaje ka k'araci son bokokon ka akan Sajida amma Maryama kam aure zan mata da zaran ta sami miji ehe, kuma yaron nan yaron arziki ne tunda duk kalan abinda na masa baiyi zuciya ba sannan na lura yanada hankali da ganin dattako..."

AT ya d'an lashi leb'en bakinsa ka kafin yace "Hajiya rana guda fah tak kuka had'u shine har kin aminta dashi..."

Bai kai aya ba ta jeho masa amsa "Eh na aminta dashi, tunda naga amintaceccen ka ne, idan da baka yarda dashi ba bazaka turosa ya kawo mu gida ba, kai Attahiru ka fita a idanu na fah tam..."

Shafe goshinsa yayi kafin yace "Kiyi hak'uri, ni zan wuce..." ya fad'i yana mik'ewa tsaye.

"Toh Allah shi bamu alkhairi, ka gaida min yaran sannan idan Allah ya kai mu gobe kazo min da batu mai dad'i kan maganar da mukayi d'azun."

Saida gabansa ya yanke ya fad'i bai iya amsa mata ba sai sallaman da sukayi ya fice yana mai tunanin maganar Hajiyan.

*Sameena Aleeyou Mrs*
[2:00PM, 3/12/2018] ‪+234 803 533 3121‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘

*SHAK'UWA CE*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*22*

*©Sameena Aleeyou...✍🏼*

_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_

*Fatan Alkhairi Asma'u Galadima (Ummu Fatima) 💘*

Mamaki ne ya isheshi jin babu mostin yaran ko kad'an sanda ya shigo parlorn k'asa, kai tsaye upstairs ya nufa parlorn sa na sama, hannu ya kai ya danna switch d'in wuta haske ya gauraye parlorn.... Sosai yasha mamakin ganin 'yan decorations a parlorn, harda cake a saman center table... A hankali ya taka ya isa har gaban table d'in yana murmushi...

Suna nan lab'e bayan cottons a dinning area, Shema'u ta dubesu kafin tace "Now"

Gaba d'aya mik'ewa sukayi suna fad'in "Surpriseeeee..." AT sai murmushi yake mai bayyana hak'wara... Suka k'araso suna fad'in "Happy Birthday Daddy."

Pecking d'insu ya ringayi a kumatu yana fad'in ya gode, Shema'u ma sai k'wark'wasa take tana fad'in "Happy Birthday Doctor, murmushi ya sakar mata had'i da mata godiya. Ya dubesu gaba d'aya kafin yace "I thought kun manta yau birthday na graduation d'in Sajida ya mantar daku." Sajida ta murmusa kafin tace "Daddy Aunty Shema'u ce ta tuna mana..."

AT ya d'an saci kallon Shema'u cikeda mamaki ya akayi tasan birthday d'insa, murmushin yak'e kawai yayi kafin yace "And who's responsible for the cake..?"

Sajida ta kuma kamo hannunsa kafin tace "Aunty Shemah ce Daddy, kaga cake d'in yayi kyau.."

Nan ma murmushin yak'e yayi had'i da duban Shema'u daketa faman juya idanu.... Kan ya sami zarafin magana su Jamal suka soma jansa suna fad'in a yanka cake d'in zasu ci...

Duk yanda AT yaso yayi dodging yaran sun hanasa, haka yayita biyesu ba don yaso ba.... Shema'u harda masu pictures, Sajida ta jawo hannunta itama ta shiga suka d'au selfie, shiko AT gaba d'aya jinsa yake ba'a sake ba, quite alright yasan babu d'igon soyayyar Shema'u cikin zuciyarsa amma Allah Ya jarabce sa da tsananin sha'awarta... Haka dai k'arshe ya zame ya nufi d'akinsa ya barsu sai hayaniyar su suke, can jimawa ya jiyo muryar Shema'u tana fad'in su shiga suyi ma Daddy goodnight is getting late...

Abun ya burgesa jin har tsarin kwanciya tana masu kaman yanda Aysha ke masu, dama sam baison rashin kwanciyar yara da wuri koda babu school...

Shema'u ta shiga tattara wajen gaba d'aya Sajida na taya ta, saida sukayi tas-tas da parlorn, Sajida ta d'au sauran cake d'in ta nufi kitchen dashi....

Ledan wayoyin su Sajida da Maryama ya hanga yanda ya ajiye, nan ya suri ledan ya fito parlorn da niyyan bama Sajida nata nan suka kusan karo da Shema'u da shigowarta kenan.

D'an ja da baya tayi tana wani mad'e da rausaya ta shiga basa hak'uri tana fad'in bata san na zuwa bane.

K'ak'aro murmushi shima yayi sannan yace "No babu komai, ya juya ya shiga kalle-kallen cikin parlorn nasa kafin yace "Kin manta wani abu ne.?"

Murmushi Shema'u tayi cikeda kissa kafin ta d'ago paper bag d'in hannunta ta mik'a masa kana tace "Na manta ne ban baka wannan ba."

AT yabi d'an jakan da kallo kafin ya murmusa yana mai girgiza kai yace "What's that...?"

Ta kuma murmusawa cikeda rausaya kafin tace "Ka duba da kanka."

D'an tab'e baki yayi had'i da d'age giransa sama kafin ya ajiye ledar dake hannunsa saman sofa ya amshi paper bag d'in hannun Shema'u, hannu yasa ya ciro abinda ke ciki.. Wata arniyan *Armani Shirt* ne gray color wanda ak'alla zaikai dubu goma an rubuta Armani a gaban rigar da rubutu ruwan madara.

AT yabi rigar da kallo sannan ya kalli Shema'u. "It's your birthday gift." ta fad'i ganin irin kallon da ya mata, taci gaba da fad'in "Na tabbata da Aysha tana nan zata baka gift, toh wannan ma ita nayi, kasa a ranka wannan kyautar Aysha ne."

D'an jim AT yayi kafin yace "look Shema'u, you shouldn't have bothered, duk wad'anan d'awainiyar da bakiyisu, it's not necessary.."

D'an b'ata fuska tayi idanunta naga ledan da ya ajiye saman sofa kafin tace "Banyi da wani manufa ba sai don faranta maka kaida yaranka, especially the kids, nasan zasuji dad'i shiyasa nayi, and the gift, it should be rude idan kak'i karb'a... Amma babu komai, kayi hak'uri idan bakaji dad'i ba inaso wannan family ta kasance cikin jin dad'i ne da farin ciki shiyasa.." ta k'arashe tana k'ok'arin juyawa.

Duk sai yaji babu dad'i, bud'e murya ya d'anyi ya kirawo sunanta, nan ta tsaya cak had'i da jiyowa.

AT ya d'an shafi goshin sa kafin yace "Kiyi hak'uri, and thanks for the gift..." ya k'arashe with a smile on his face.

Murmushi itama tayi kafin ta d'auki ledan da ya ajiye saman sofa tana juyawa take fad'in "Saidai kuma kak'i karb'an kyauta ta sabida wannan, da alama someone special ne ta kawo maka kasan kai d'in yanzu bazauri ne.." ta k'arashe teasingly.

Tak'aitaccen dariya yayi wanda yafi kaman da murmushi donko dariyar nashi baida sauti kana yace "Kema kika ce bazauri, wa zata damu ta kawo ma bazauri gift, wannan kyautar Sajida da Maryama ne na kammala karatun sakandare d'insu."

Wani dad'i ya lullub'e Shema'u, tana murmushi take jujjuya kwalin da shike anyi wrapping nasu, d'an girgizawa tayi tana son sanin menen a ciki.

Murmushi AT yayi kafin yace "Someone's curious..."

Ta murmusa had'i da ajiyewa kafin tace "Kawai dai so nake nasan menen kyautar d'iyata."

"Tohm kiyi guessing.." ya fad'i yana k'arasawa jikin TV ya kunna socket had'i da d'aukan remote kafin ya zauna a 3seater.

Zama tayi bisa armchair tana fad'in "I guess jewelries ne."

AT ya murmusa idanunsa naga TV yana canza tasha yace "Baki canka dai-dai ba, idan kin bada gari a fad'a maki,..

Wani smile d'in jin dad'i tayi kafin tace "Gaskiya na bada gari."

Ya kuma murmusawa kafin yace " Toh tunda kin bada gari cellphone ne."

Take annurin fuskar Shema'u ya d'auke, sam bataso ya bawa Sajida freedom ai plans d'inta zasu tarwatse.... D'an gyara zama tayi kafin tace "Cellphone Dr, gaskiya a ganina is too early Sajee da Maryama su mallaki waya, a ganina instead da Laptop ka saya masu da zaman banza da zasuyi na jiran results sai su shiga computer school, kasan wannan zamani namu wllhi waya itace ummul haba'isin lalata tarbiyan yara, 90% wayace ta lalata su, ni dai gaskiya ban aminta d'iyata ta rik'e waya babba kaman wannan at her age ba, makarantar kawai ta gama da wuri amma har yanzu yarinya ce mallakan waya irin wannan ka iya haifar mata da wani tunani, pls Dr ka duba lamarin."

Shiru AT yayi yana nazarin kalaman Shema'u, tabbas da computers ya saya masu da sai yafi masu amfani, kuma tunda yaga Ashfaq ya soma kawo hari ma Maryama mallakan waya zaisa maza su ci gaba da kawo mata hari... Toh waima meyasa baiso wani yayi tarraya da ita, yayi ma kansa wannan tambayar, zuciyarsa ta shiga raya masa ai har yanzu ita d'in yarinya ce...
Chapter 28 · 0% Book details