← Book details Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 65

Sashe 25

Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har ta zauna ta d'an gabansa baiyi noticing ba, gaba d'aya hankalin sa bai tareda shi.... Muryar Shema'u ya jiyo cikeda kissa tana fad'in "Damuwa bai cancanceka ba sannan bai kamace ka, kayi hak'uri sannan ka sani sam babu laifin Hajiya ko k'ank'ani, wannan duk laifin Momma ce, at times idan Momma tayi wani abin nakanji mamaki sosai, amma idan na tuna girma ya soma sauk'o mata sai na mata uzuri, shakka babu Hajiya ma harda girma a abubuwan da takeyi, AT kayi hak'uri, ka k'ara akan wanda kake Allah yana son masu hak'uri sannan sukeda nasara a rayuwa, watarana komai zai wuce ya zama sai labari... Sannan if you need someone to talk to kar ka mance that I'll be right here kaji..."

D'ago kai yayi yana dubanta sosai, she sounds like Aysha, tabbas kalamanta sun d'anyi calming nasa... Bai iya ce mata komai ba sai gyad'a kai da yayi ya mik'e ya nufi sama. Shema'u ta bisa da kallo tana wata kafiran murmushi... Jim kad'an ya sauk'o da makullan motar sa..
Yasa kai zai fice daga parlorn Shema'u tayi saurin bin bayansa har tura k'ofar ya fice ya jiyo muryar ta tanai masa a dawo lafiya had'i da addu'an Allah Ya tsare....

Juyowa yayi ya dubeta kafin ya d'an murmusa yace "Na gode" a tak'aice.. Daga haka yayi saurin sa kai ya fice...

Bayansa tabi da kallo tana mai cikeda jin dad'i ganin sam baya gwaleta, ita kad'ai ta dinga murmushi tana sak'a abubuwa da dama cikin zuciyar ta....

Iya Kande ta k'araso ta sameta nan tsaye tana washe baki take fad'in "Kai Hajiyan sake hannu, ina mai tabbatar maki keda Datta ba k'aramin dacewa zakuyi ba, dukanku farare sol-sol wanke hannu ka tab'a...."

Shema'u tayi murmushin wanda yafi kama dana rainin hankali kafin ta dubi Iya Kande tace "Kande bari na tuna maki don kar ki mance,."

Iya Kande tayi saurin gyad'a kai alamun toh.

Shema'u ta murmusa tana dafa kafad'an Iya Kande kafin tace "Ba'a cin amanata idan na aminta da mutum don haka ki kiyaye..." Ta k'arashe maganar tana mai bud'e tafin hannun Iya Kande ta dunk'ula mata 'yan dubu-dubu guda uku..

Haba nan fah Iya Kande ta washe baki ta shiga kod'a Shema'u.....

***************

Hisham I'm lost, I'm completely lost... I...i just don't know what to do anymore.. Wllhi bansan yaya zanyi da Hajiya ba bansan me zan fad'a mata ta fahimce ni ba.." Ya k'arashe zancen yana hura iska a bakinsa.

Mik'ewa Hisham yayi daga saman sofan da yake zaune akai ya dawo gefen AT kafin ya dafa kafad'ansa yace "Tahir, you better take things easy, don't stress yourself, kabi komai a sannu, abokina nasanka nasan yanayin ka, wllhi nasha mamaki da naga ka zauna baka k'ara aure ba tun bayan mutuwar matarka tunda nasan kai ba bin matan banza kake ba, don I can still remember sanda muke sch azumi bai wuceka... Baka biye mana.." Ya k'arashe yana murmusawa.

Gajeren tsaki AT yayi kafin yace "Tuzuru banza kak'i aure kak'i canza hali... Wllhi Hisham kaji tsoron kamuwar Allah. Ni bama wannan bane a gabana, I can hold myself, yarana sune min gaba da komai ka gane." Ya k'arashe maganar yana lank'washe 'yan yatsun hannunsa.

"Okay fine naji, your children are your top priority, amma Tahir kayi auren mana kaman yanda Hajiya ta buk'ata, yin auren sai kaga ya kawo maka kwanciyar hankali da iyalanka, all this tashin hankula-hankula da kuke shiga sai kaga Allah Ya sauwak'e maka albarkacin auren."

AT yayi shiru yana sauraren sa yana nazarin maganganun nasa, fuzar da iska ya kumayi ya shafi goshinsa kafin ya had'e tafukan hannayen sa waje guda yana mai duban Hisham yake fad'in "Toh Hisham wa zan aura for goodness sake, you're fully aware of banida macen da nake so a halin yanzu, and you know what the worse part is... Waifa Hajiya cewa take zata samomin matar, kaifa kaji saikace k'aramin yaro a shekarunan nan, yo banda abun Hajiya ko Rano taje ta samesu da batun zata min aure ai dariya zasu mata, kaman wani matashin saurayi..." Ya k'arashe yana girgiza kai.

Hisham ya jinjina kai kafin yace "Eh toh nasan kanada masoya masu sonka amma kai baka sonsu, idan zaka daure ka zab'i d'aya daga cikin su fine, idan kuma ba haka ba toooh fah saidai ka karb'i zab'in Hajiya wanda I'm pretty sure gida zataje ta samo maka...." Ya d'anja fasali kafin yaci gaba da fad'in "Tahir auren magidanci kaman kai yana buk'atan lokaci sosai to think of wa zaka auro ka kawo kan iyalanka, it should someone da ka yarda da hankalinta, wacce bazata raba maka kan yaranka ba koda ace Allah Ya azurtaku da rabo kaida ita, sannan wacce zata so yaranka with all her heart, ita ya kamata ka auro ka kawo gidan ka..."

Zuru AT yayi masa kafin ya shiga jinjina kai yace "Haka ne, you are right... Shiyasa banaso Hajiya ta kwaso min ko wace iri."

Hisham ya murmusa kafin yace "Aaff, ina yarinyar can ta gaban Hajiya kodai ita ce ta ajiye maka...."

Zaro idanu waje AT yayi yana dubansa kafin yace "wai Maryama kake nufi, amma bakada hankali Hisham, if not you are a therapist wllhi da na nemo maka therapist ya duba ka, Maryam, Maryam fah... K'aramar yarinya k'awar Sajida..." yayi murmushi kafin yace "You're insane Hisham this is ridiculous."

Tak'aitaccen dariya Hisham yayi kafin yace "Tahir ka daina denying you care so much about her ko ba haka bane.?"

"Yes I care so much about her, sabida tareda Sajida na rainesu, kai kasan da hakan... All I can say SHAK'UWA CE sosai tsakanina da ita ..... Waima ta yaya zakayi wannan maganar, ta ina ni AT zan soma batun aure tsakanina da Maryam, me na zamo... I wonder what's going on on that Skull of yours..." Ya k'arashe yana mik'ewa tsaye.

Hisham ya murmusa don yaji abinda yake sonji kafin ya mik'e shima had'i da zura hannaye a aljihu sannan ya dubi AT yace "Doc ga shawari na k'arshe da zan baka."

AT ya kallesa without saying a word.

Hisham yaci gaba da fad'in "Shema'u is the perfect and right person for you...."

*Sameena Aleeyou Mrs*
[2:00PM, 3/12/2018] ‪+234 803 533 3121‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘

*SHAK'UWA CE*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*20*

*©Sameena Aleeyou...✍🏼*

_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_

"Adda Sajida fah kinsan Daddy yace munyi k'anan muke dawowa gida mu kad'ai, meyasa zakice mu tafi mu kad'ai. " Yayi maganar fuska a b'ace.

Tsaki Sajida tayi kafin taja kunnensa tace "Kai wllhi bansan yaushe zaka girma ba, shekarar goma, goma fah Jamal amma bazaka iya kulada Ni'ima a hanya ba, nace maka Hadda zan tsaya badawa, wllhi saura naji wani zancen daban sai kaga abinda zan maka, oya rik'e hannunta ku tafi..." Ta k'arashe tana had'e hannayen su waje guda.

Baki a ture Jamal yaja hannun Ni'ima suka soma tafiya, sauk'in abin isalmiyar a layin bayansu yake.

Daga can yanda yayi parking ya toshe idanunsa da bak'in shades ya sauk'e tint glass d'in motarsa had'i da danna horn (pim pim) yana mai sakar mata murmushi.

Murmushi itama tayi suna wuce ta k'arasa wajensa tana faman waige-waige.

Front seat ya bud'e mata ta shiga kafin ya rufe, sai ka rantse babu kowa cikin motar, sai AC dake tashi da k'amshin turarruka.

Sosai yayi kyau cikin red polo shirt da blue jeans, farin fatar sa har kashe idanu yake, yayi kyau har ya gaji.

***********

Karkatowa AT yayi da kyau yana duban Hisham yanda yayi maganar da iyakacin gaskiyar sa. Tak'aitaccen murmushi yayi kafin yace "Wai kai meke damunka ne, Shema'u, Shema'u fah , yar Aysha fah.....Kai a ina ka tab'a ganin haka ta faru Ya ta auri mijin k'anwa, if to say ita ce k'anwar da sauk'i amma ta ina hakan zata fara kasancewa..." d'an jan fasali yayi kaman ya tuna wani abin kafin yaci gaba da fad'in "Waima tsaya! Ba kaine kwanaki kace min kana son ka nemi aurenta ba ka tuna.?" Ya k'arashe fuskar sa cikeda alamun tambaya.

Murmushi Hisham yayi kafin ya dafa AT yace "Of course anyi haka, but Bro you need her morethan I do, kana buk'atan ta fiye dani Tahir. Shema'u 'yar uwar matar ka ce, she loves your Kids and na tabbata bazata tab'a hurting d'insu ba, think about it... Da kaje ka auro wacce bakasan yaya take ba ka kawo kan yaranka gwara wacce ka sani, kuma a iya zaman da tayi a gidanka na tabbata kana iya gane wacece ita.... Sannan ni bama sonta nake ba kadaisanni ne kawai da iya k'yalla idanu akan farar mace, bamuyi magana ba balle wani soyayya ya soma shiga tsakanin mu, AT koda ace nida ita are in a relationship me anfani na idan banyi sacrificing soyayyar ma kai ba, ka tuna ka min halacci da dama a rayuwa, ka wuce aboki a wajena kai d'an uwa ne and this is exactly what brothers are for.... Pls AT kar ka bari wannan DAMAR ya wuceka, do this for your children, wllhi idan na kalli Ni'ima babu Uwa ina tsananin tausayinta, AT ka auri 'yar uwan mahaifiyar su ko don inganta rayuwar su tunda dama sabida su d'in kake da buk'atan auren." Ya k'arashe fuskar sa fal damuwa sai ka rantse har cikin ransa iyakacin gaskiyar sa kenan.

Shiru yayi yana nazarin kalaman Hisham kaman bazaice komai ba sai kuma ya d'ago yana dubansa kana yace "Na fahimce ka Hisham, but what if it turns out tana da wanda take so... Quite alright nasan Shema'u zata amince ta aureni koda bata sona sabida soyayyar da take ma yarana.... Amma Hisham gaskiya I don't want to be a burden to her sabida she already sacrifices alot, maganar da nake fad'a maka ina tunanin har ajiye aikinta tayi just to be with my children, kaga kuma nazo mata da batun aure alhali tanada plans d'inta maybe da wanda take so kaga ai abu baiyi ba gaskiya sam banason na zame mata nauyi ko na tak'urata.."
Chapter 25 · 0% Book details